Showing 126001 words to 129000 words out of 232912 words

Chapter 43 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1238

ta tana kuka wannan ya kara sa ta jin tausayi da karaya akan Maryam.

Ya kalle ta yace
"Haba *Matar Haidar* ki tashi muje ki dan motsa jikin ki, ki zabarwa Namesake kaya masu kyau ko bakya so."
Tin da ya kira ta da *matar haidar* ta dago tana kallon sa. Ya gyada mata kai ta fara kokarin mikewa tai sama. Wanka ta shiga tayi ta fito ta saka wata armless rigarta budaddiya ta dauki hijab wanda iyakar sa gwiwa ta saka ta shafa turare mai saukin kamshi ta saka flat shoe ta sauko kasa.

Ummi ta sama zaune da mayafi a jikin ta tana ganin ta ta mike tana fadin
"Yauwa kin sauko?"
Kai ta gyada. Umm ta kama hannun ta suka fita. Aliyu suka hanga cikin mota yana ganin su ya karaso da motar. Ummi ta bude gidan baya ta shiga Maryam ta bude gidan gaba ta shiga.

Can wani hadadden super market suka shiga, wajen kayan babies suka karasa tana zuwa ta hango wasu kayan na baby skyblue da ratsin milk wajen ta karasa ta dauka kayan sanyi ne mai laushi sosai. Aliyu ne ya karaso yace
"Sun miki kenan?"

Kai ta gyada yace
"Kuma fa zaiwa namesake kyau!"
Hannu tasa ta rufe fuska ya amsa ya saka a kwandon da yake turawa. Wasu takalma ta hango na yara ta karasa ta dauka tana jujjuyawa Aliyu ya karaso ya tura mata kwandon yace
"Saka mana!"

Ta saka suka cigaba da zagayawa duk abinda taga yai mata sai ta dauka shi kuma yace ta saka da taga ta diba da yawa sai ta daina dauka tace sun isa amman Aliyu ya cigaba da jidar duk abinda yake so. Ummi na can tana dibarwa Maryam nata kayan. Daga nan suka wuce wajen kayan ciye ciye. Duk ya san abinda take so da haka da kan sa ya zazzabar mata sai da suka kusan awa a shagon sannan sukaje akai total kudi masu uban yawa haka suka biya suka fito suka saka a mota sannan suka wuce gida suna shiga ana magariba da haka a falo Aliyu ya ajiye ya shiga yai alwala ya tafi massalaci.

Sai da akai isha'i ya dawo Ummi kadai ya sama a falo tana kallo ya zauna yace
"Ina take?"
"Tana daki wajen kayan baby!"

Mikewa yayi ya hau sama dakin ya nufa ya same ta zaune a tsakiyar kaya tana kuka zama yayi daga gefe yace
"Meyasa kike kuka?"
Hannu ta saka ta goge hawayen dan bata ji shigowar sa ba. Yace
"Tashi muje!"

Kallon sa tayi sai tai saurin yin kasa da kai dan wani kwarjini take mata, ta mike a hankali ya fita tabi bayan sa. A kasa suka samu Ummi yace
"Zamu zaga Ummi!"
"To a dawo lafiya kar a gajiyar min da ita dai!"

Suka fita. Farouk suka sama zai yi hanyar Inna yana ganin su yaso ya juya sai dai kan ya juya sun hada ido da Aliyu dan haka ya karaso yana fadin
"Barka da dare Yaya Dr."
"Barka ka dai ya aiki?"

"Alhamdulillah"
Ya fada yana yin gaba Maryam na bin bayan sa. A haka suka fita suka fara zagaye unguwar sannu a hankali sukai dan tafiya sannan suka juyo suka dawo gida. Tara saura suka shigo gida ba kowa a falo dan haka kowa yai dakin sa. Tana shiga ruwa ta watsa ta saka kayan bacci sannan ta saka hijab ta sauko dan cin abinci.

A dining ta same shi zaune yana cin abinci shima ya canja shiga daga gani wanka yayi karasawa tayi ta zauna ya dago yana fadin
"Me zaki ci?"
Abinda yake ci ta nuna ya mike yai serving nata sannan ya tura mata gaba ya zuba mata lemo ya ajiye ya koma ya karasa cin nasa sannan ya mike ya koma dakin sa. Tana gamawa ta dauke kwanukan ta kai kitchen ta dawo ta wuce sama. A falo ta samu Ummi da Abba ta karasa ta zauna a kasa.

Abba yace
"Ya jikin?"
Tai masa alamu da hannu da sauki. Yace
"Allah kara sauki."

Ummi ta amsa da amin. Mikewa tayi tai musu sai da safe ta shiga daki. Dakin ta ta shiga ta wanka ta dauro alwala tazo ta kwanta tare da tofa addu'ar bacci ta lumshe ido. Juyi ta fara dan sam baccin yaki yazo tana ji Ummi ta shigo ta duba ta. Har karfe daya da kusan rabi ta kasa baccin mikewa tayi da kyar tana dafe bayan ta dan yadda taji ya rike mata da kyar ta shiga bandaki tai dauro alwala tazo ta tada sallah tana zaune a wajen tana lazimi har aka fara kiraye kirayen sallah jin ana kiran sallah yasa ta fara kokarin mikewa amman sai ta kasa tana cikin wannan halin Ummi ta shigo, ganin ta a durkushe yasata karasa wajen ta da sauri tana fadin
"Lafiya me yake miki ciwo."

Kai ta girgiza. Takarda ta mika mata, ta amsa tai rubuta mata
"Ummi ba fa komai jimawar da nayi a zaune ne."

Dagata Ummi tayi tace
"Sannu to meyasa?"
Ta kamata suka shiga bandaki tai wanka tare da alwala tazo ta kara zama. To fa ciwon baya kuma ya kamata dan da kyar ta idar da sallah anan kasa ta kwanta wani bacci mai dadi ya dauke batai rabin awa ba wani ciwon mara ya tashe ta mikewa tai zaune da kyar ta jingina bayan ta da gado tana cije baki tana ambaton Allah cikin ranta can kuma sai ya saki komawa tayi ta kwanta tana mai maida nunfashin wahala.

Sai wajen takwas bayan Ummi ta gama break ta leko dakin ta same ta kuma tana bacci fita tayi taje tai wanka sannan ta sauka ta debo mata abinda zata bukata. Tana kan matattakalar bene Aliyu ya fito daga dakin sa. Ta juyo tace
"Ka zauna kaci ina zuwa."

Tayi sama dakin ta koma ta same ta ta daina ta hade kai da gwiwa. Dafa ta tayi ta dago ta kalli Ummi cike da karaya da tsoro. Ummi tace
"Lafiya?"
Kai ta girgiza ganin har hankalin ta ya tashi. Ummi tace
"Ki fadan in da wani abu."

Kai nan ma ta girgiza. Ummi tace
"To ga abinci nan ko akwai abinda kike so?"
Kai ta girgaza ta ja faratin dan yunwa take ji. Sai da Ummi taga taci sosai tasha magani sannan ta dauko kwanukan ta sauko kasa.

Aliyu ta sama zaune a dining yana jagwalgwala abinci ta zauna tace
"To kai ma me ya faru?"
Murnmushin da bai kai zuci ba ya zaki tace
"Allah ya shirya min kai da zurfin ciki."

Sama ya kalla yace
"Ya jikin nata?"
"Da sauki."

"Tana shan maganin kuwa?"
Ya tambaya cike da damuwa.
"Tana sha."

"To Allah raba lafiya. Na fara fitar da rai da maganar ta gaskiya Ummi."
"Saboda me?"

"Naga na daura ta akan magani tana sha kuma shiru more than five month."
"Haba Dr kai fa likita ne kai zaka bawa wasu kwarin gwiwa ba karya gwiwa ba, ai sauki sai a hankali insha Allahu wata rana zatai magana da izinin Alah."

"Allah ya yadda abinda ke damuna kenan yanzu dan in tana maganar zata samu ragin wata damuwar ba tai ta rubutu ba."
"Haka ne Allah bata lafiya ya sauke ta lafiya."

"Amin ya Hayyu ya qayyum."
Ya mike yana fadin
"Zanje asibiti inda wata matsala a sanar dani."

"Shikenan Allah tsare ya bada sa'a."
"Amin Ummi na."

Ya juya ya fita. Wajen Inna ya wuce ya gaishe ta tare da ajiye mata ihsanin da ya saba bata, sannan ya shiga wajen su Mami suka gaisa.




*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani amin.*



*Antty*[11/23, 12:32] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 51

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


ο»ΏSam bata sauko ba dan a hankali dai nakuda take ita kuma sam bata sani ba za dai taji marar ta ko bayan ta sun rike sai kuma taji ya saki wanda yana sakin ta take bingirewa da bacci da ya tashi kuma zai tsayar da ita daga baccin da take. Ummi na hawa wani ta ganta na bacci wani idon ta biyu haka dai kuma duk tambayar da zatai mata sai ta girgiza kai kawai. Aliyu ma ya kira yafi sau nawa yana tambaya ya jikin ta dan ya kasa samun sukuni har yamma da ya dawo ma a kitchen ya samu Ummi yace
"Ya jikin nata?"
"Da sauki fa ka kwantar da hankalin ka."

"Ummi bata ce komai na damun ta ba."
"Bata fada ba meyasa ka tada hankalin ka ne?"

"Yau ne EDD ta shiyasa nake tunanin ko zata sauka a yau."
"To ai kasan zata iya karawa ko ragewa ko daga yanzu dai zuwa ko da yaushe zamuna tsammani ne."

Saman ya kalla sai ya juya ya nufi sama da dan saurin sa. Knocking yai wanda in taji knocking tasan shi ne dan haka ta dauki hijab ta zura tare da mikewa a hankali ta bude masa kofar taja baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna, tin da ya shigo yake kallon ta har ta karasa ta zauna. A jikin bango ya jingina yana binta da kallo. Dagowa tayi jin shirun ita yake kalla idon ta, tana gaishe shi da hannu amsawa yayi yana fadin
"Me yake damun ki?"

Kai ta girgiza ya karaso ya durkusa a gaban ta yana kallon fuskar ta, kan ta ta rasa kasa dashi dan idon Yaa Haidar ba karamin kwarjini yake mata ba, dan murmushi ya saki yace
"Kin tabbata?"
Kai ta gyada yace
"Good ki sauko muje ki motsa jikin ki."

Dagowa tayi da sauri idon ta cike da kwalla yace
"Menene?"
Kai ta girgiza yace
"Ki fada min abinda yake damun ki."

Ka ta girgiza yace
"To tashi mu tafi."
A hankal da kyar ta mike ya bude mata kofa ta fita yabi bayan ta. Kitchen suka karasa wajen Ummi tana ganin su tace
"Ah ta sauko?"

"Gata nan zamuje ta dan tattaka."
"To a dawo lafiya."

Suka fita yana fadin
"Kinyi azhkar dai ko?"
Kai ta gyada yace
"Good girl."

Dan murmushi ta saki suka fita a gida suna tafe in ta gaji ta tsaya ta huta su cigaba sun yi tafiya mai tsayi ta tsaya ta marairaice idon ta dan yadda taji kafar ta da bayan ta sun rike kallon ta yai yace
"Ya dai?"

Hannu ta yafe ta nuna masa bayan ta, yace
"Ko haihuwar ce?"
Ya tambaye ta dan ya manta Maryam bata san wata haihuwa. Kai ta girgiza ta masa alamar ba zata iya tafiya ba. Napep ya tsayar ta shiga ya shiga suka koma gida kan suje gida har kafar ta saki da kan ta ta shige gida ya biya mai napep yai alwala ya wuce masallaci.

Tana shiga ta wuce sama da Ummi ma bata kasa alwala ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta tada sallah a zaune tayi tana idarwa wani bacci ya dauke ta. Cikin baccin taji wani a zababen ciwo ta farka tana ciccije baki tare da addu'a a cikin zuciyar ta. A hankali taji ciwon na sauka zuwa can koma taji komai ya lafa.

Ummi ce ta shigo tace
"Maryam sauko kici abinci."
Kai ta girgiza, Ummi ta durkusa tace
"Dan Allah meyake damun ki? Ki fada min ki dauken a matsayin uwa na fada miki."

Kai ta kuma girgizawa. Ummi ta kalle ta tace
"To sauko kici abinci."
Nan ma kai ta girgiza. Ummi tace
"Yau fa baki ci komai ba ki fada min ko akwai abinda kike so sai nai miki."

Dagowa tai tana kallon Ummi idon ta cike da kwalla. Gyara zama Ummi tayi tace
"Bana son kukan ki sam Maryam ki fadan me kike so?"

Hannu Ummi ta kama ta matse a cikin nata tare da lumshe ido, Unmi ta bita da kallo daga baya ta saki hannun nata ta sakar mata murmushi abun da take rubutu ta dauko tace
"Ummi bana bukatar komai ki daina damuwa."

"To shikenan me zaki ci?"
"Bana jin yunwa Ummi."

"Yau fa tin karin safe baki ci komai ba ko dan cikin ki ai kya ci wani abu ko? Bari Dr ya dawo nai masa magana ya samo miki wani abu."
Ta mike ta sauka. Bayan Isha'i Aliyu ya shigo ya zauna a falo yana kallon kafar bene Ummi ta sauko tace
"Yauwa daman kai nake jira."

"Haihuwar tazo ne Ummi?"
Ya tambaya da sauri. Murnushi Ummi tayi tace
"Oh oh oh likita ba ita bace."

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"To menene Ummi?"
"Taki cin komai tin safe rabon ta da abinci fa."

"To me take so?"
"Sai da a tambayo ta wai ita bata jin yunwa."
Mikewa yayi ya hau benen kofar dakin ya isa ya buga kofa fitowar ta daga bandaki kenan ta saka hijab ta nufi kofar ta bude, sannan ta juya yace
"A'ah dawo ai fita zamuyi."

Dagowa tai ta kalle shi cikin fuskar tausayi yai murmushi yace
"Ban daukar wani excuse zo muje kema kya samu nishadi a waje."
Ba dan ta so ba ta biyo bayan sa suka sauko.

Ya kalli Ummi yace
"Zamu fita Ummi sai mun dawo."
"A dawo lafiya."

Ummi ta fada tana kallon Maryam da katon ciki sai kace na yan biyu. A hankali tabi bayan sa suka fita. Shi da kan sa ya bude mata kofa ta shiga sannan ya rufe ya zaga ya shiga dayan side din ya nufi gate yaba saka kai Motar Mama na shigowa kallon juna sukai yace
"Barka da zuwa Hajiya Mama"

Tsaki ta saki ta dauke kai ya saki murmushi yaja motar ya bar wajen ta bisu da kallo tana fadin
"Na tabbata akwai wani abu tsakanin yaon nan da yarinyar nan sai rainawa mutane hankali ake bari dai yau naje na samu Alhaji."

Ta shiga da mota tai parking ta fito ta nufi sashen su. Dakin ta ta shiga ta ajiye jakar ta da mayafi sannan ta fito ta nufi bangaren Abba. A falo ta same shi yana kallon BBC ta shiga tana fadin
"Ashe ka dawo?"
"Daga ina kike da daren nan."

"Haba Alhaji naga na fada maka zani bikin yar Hajiya Karima ko?"
"Amman karfe nawa yanzu bayan isha'i ake dawowa daga unguwa na fada miki bana son ana fita ana kaiwa dare amman ke sarar ki kenan."

"Kayi hakuri."
"Kada ki sake na fada miki."

"Naji."
Ta fada ya dauke kai daga kallon ta gyara zama tayi tace
"Wai Alhaji kayi bincike kuwa game da yarinyar da Aisha ta kawo gidan nan?"

Juyowa yai yana kallon ta yace
"Me ya faru?"
"Eh to nifa ban yadda da wai tsintar yarinyar nan sukai ba ina ganin ko dan ta ne ya dirkawa yarinya ciki iyayen ta suka koro ta shine suka kawo ta nan ta haife su mai da ta gidan su."

"Wane d'an kenan?"
"Zai wuce Aliyu tinda ita bata ganin laifin sa sam, komai yai dai dai ne ita ke daure masa gindi shiyasa ya raina mutane yake abinda yaga dama yanzu ma fa na ganshi tare da yarinyar sun fita me yake hadasu in ba wani abu tsakanin su."

"Keee ya isa haka Barira na rantse da Allah ki kiyaye ni da kwason ko wanne irin shirgi kina fada min. Yanzu a gaban ido na kike tuhumar d'ana da fasikanci, kada ki manta Aliyu fa d'anane na ciki na amman ko kunya bakya ji, waye zai boye miki gaskiya. Wallahi Barira ki fita a ido na da irin wadan nan halin naki, shikenan ba zasuyi taimako saboda Allah ba da izinin Allah ban haifi fasiki ba bare wanda zai kawon dan shege ba dan haka ki kiyayen tashi ki bani waje."
Mikewa tai tana magana kasa kasa
"Uhmm kada ka yadda ai nasan ko banza na saka maka wasi-wasi kuma nasan zaka bincika Allah yasa cikin sane in an bincika a lokacin naga da wane ido da baki zakai min bayani."

Ta fice a daki komawa Abba yai ya jingina da kujera yana tunanin maganar, Mami ce ta shigo da sallama yana daga inda yake ya amsa ba tare da ya bude idon sa ba. Juice din da ta shigo dashi ta ajiye akan center table sannan ta karaso ta zauna a kusa dashi tare da dafa shi tace
"Lafiya Alhaji?"

Ta saka dayan hannun ya kamo hannun ta tana wasa da hannun nasa sun jima a haka wajen minti uku sannan taji ya sauke ajiyar zuciya. Sakin sa tayi ta mike ta zubo masa juice din a kofi ta kawo masa a baki ta saka ya kurba tare da lumshe ido yana mai kara sauke wata ajiyar zuciyar. Sai da ya sha rabi ta janye ya kalle ta yace
"Matar Aljanna Allah miki albarka."

Wani dadi Mami taji a cikin ranta tace
"Amin Mijina kana hakuri da halin da ka tsinci kan ka kada kace zaka dauki wani mataki a duk abinda za ai maka mai hakuri shike da riba kuma ko wanne tsanani yana tare da sauki, kuma Allah yana tare da mai hakuri kayi hakuri Mijina."
"Madallah ga matar Aljanna ina alfahari da kasancewa tare dake a ko da yaushe kin ban soyayya kin bani yara masu albarka ba abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da mafificin Alheri."

"Amin godiya nake miji na taso muje kaci abinci."
Ta mike tana son kamo hannun sa. Kamo hannun ta yayi yace
"Zauna muyi wata magana tukkuna."

Komawa tayi ta bashi hankalin ta ya kalle ta yace
"Me kika sani akan yarinyar da su Aisha suka kawo gidan nan?"
"Oh Maryam ina ce Inna tai maka bayanin komai."

"Ina so na kara ji daga bakin ki dan nasan ba zaki boye min komai ba baki tabai min karya ba kuma nasan ba zaki fara ta a yau ba."
"Me ya faru ne Alhaji?"

"Ba komai fada min."
"To kasan tafiyar da sukai Bauchi a can suka dawo da ita a hanyar su ta dawowa suka kade ita yarinyar da aka kai ta asibiti bata farfado ba har washe gari to kaga ba zasu tafi su barta ba to data farfado suka so su gana da dagin ta amman bata san komai akan rayuwar ta ba kamar tayi losing memory kuma bata magana wani abun al'ajabin ma ciki da ita amman tace tana da miji da mahaifiyar ta abinda take iya tinawa kenan. Kasan Aisha da tausayi wannan yasa ta kasa barin ta acan, dan bata san wane hali zata fada ba kaji dalilin tahowar ta da ita gida."

Tinda Mami ta fara magana yake kallon ta har ta gama yace
"Kin tabbata?"
"Eh Alhaji."

"To tashi muje."
Hannun ta sa ta kamo tace
"Meyasa kai min wannan tambayar?"

"Ba komai."
Ya fada yana mikewa tabi bayan sa dining ta zuba masa abinci yaci sannan ya shiga dan yai wanka bayan ya fito ya shirya cikin kayan bacci ta window ya leko yana kallon harabar gidan ko ina tsit dan dare ya fara lokacin kusan goma da wani abu. Mami ce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login