Showing 186001 words to 189000 words out of 232912 words
Chapter 63 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
ke meyasa bazaki neman ba."
Ido ta dan zaro tace
"Mata ita ke zuwa wajen namiji?"
"Menene a ciki, naga yanzu kin zama matata."
Kai tayi kasa dashi yace
"Ko dan ni ba a so na, ai da Muhammad ne da zaki nemesa ko a waya ne, amman ni fada min tin da kuka zo Kano kin neman in bani na neme ki ba."
Baki ta dan turo tace
"Uhmm kai ma ai Haidar kake nema."
"Ohk naji na nemi Haidar amman ai ta wajen ki ko? Kuma sai mun gaisa in naso zan kira Aunty Nusy ta kira min shi ko Alkasim."
"Uhmm uhmm to kayi hakuri ni bansan me zan kira nace ba."
"Oh har gaisawa."
"Uhm uhmm to naji kayi hakuri."
Kamo hannun ta yayi ya juyo da ita yace
"To na hakura, yanzu gani kalle ni shikenan gani."
Ta dago ta dan kalle sa sai ta dauke kan ta, yace
"Oh har kin gama kallon nawa."
Mikewa tayi tace
"Uhmm ni wajen Sitti zani sai da safe."
Ta juya zata tafi ya kamo hannun ta ya juyo da ita suna fuskantar juna kamshin turaren su na tashi, dagowa yai yana kallon ta, itama shi take kalla, Yaa Farouk ne ya shigo kamar ance ya juyo ya gansu baki ya saki yana kallon love wayar sa ya zaro ya fara snapping nasu picture hasken flash din shi yasa suka juyo a tare da sauri Aliyu ya sake ta yana hade rai ya kalli Farouk yace
"Menene haka?"
"Alhaji Yaa Hamma tuba nake soyayya na gani kuma abun yai kyau shiyasa na tsaya koya."
Ya fada yana murmushi Haidar ya karasa yana kama kunnen sa yace
"Gidan ku."
Da sauri Maryam ta bar wajen, Farouk ya hau ihu yana fadin
"Tuba nake Yaya, Dr Hamma."
Ya rankwashe shi ya amshi wayar yana kallon screem din picture din yayi kyau sosai, sun shagala kallon junan su ba karamin kyau sukai da dacewa da juna ba. Ya mika masa wayar yace
"Tafi ka ban waje."
"Allah kara girma da lafiya Yaya na."
Farouk ya fada yana dariya dan murmushi Haidar yai ya juyo wajen Maryam sai dai me? Ba kowa a wajen dube dube ya fara sai ya saki murmushi kenan ta gudu, fita yayi ya tafi kawai.
Tana shiga ta zauna a gefen Sitti tana fadin
"Bakuyi bacci ba?"
"Bamuyi ba daga ina kke?"
Yaa Farouk da ya shigo yace
"Daga soyayya take Sitti."
Maryam ta dago tana marairacewa tace
"Kai Yaa Farouk soyayya kuma dawa?"
"Da mijin ki Dr Hamma na."
Ido ta zaro tace
"A ina ka gamu tare."
Wayar sa ya nunowa Sitti Maryam ta mike da sauri ta warce wayar tana fadin
"Sharri zai mana Sitti."
Sitti na murmushi tace
"Ai Faruku bashi da dama."
"Sitti menene kuma Faruku ko dadi babu Farouk ake cewa fa."
"Dan nace Faruku da bance Umaru ba."
Daman ke da Inna haka kuke kuyi ta batawa mutane suna."
Inna dake gyangyadi ta bude ido tace
"Me nayi ake kira na."
Juyawa yayi yace
"Ni sai da safe."
Maryam ta mike tace
'Nima bari na tafi Yaya Faruku tsayani."
Juyowa yayi ya harare ta ta sunne kai tana fadin
"Sorry Yaya na."
Tare suka fita ta shiga sashen su shi kuma ya shiga bangaren Yaa Abdullah dan tare suke.
Kwanan su uku suka wuce Adamawa, Shigar yamma sukai nan aka hau tarbar su dan sun san da zuwan nasu Malam kuwa da yaga Maryam bakin sa yaki rufuwa, haka da yaga Haidar ya kamashi yana fadin
"Masha Allah, kamar su daya kuwa da mahaifin nasa, Allah masa rahma."
Masauki aka basu, dan kowa yaje ya huta aka cika su da kayan ci da sha kala kala, Maryam kuwa daman sakin shan fura ai ita tai ta dirka Haidar ma ita ya sha sai gashin nama da suka ci amman sunki cin abinci shi da Maryam sam.
*
Washe gari da safe, Malam ya kira meeting, domin kowa yana gidan Abbi da Yaa Usman ne kadai ba a garin ba to shima bayan su Abbi sunzo ya iso da iyalan sa. Bayan kowa ya hallara ne, Malam yayi godiya da Allah da ya dawo da Maryam lafiya tare da godiya ga su Ummi akan rikon da sukai wa Maryam.
A take ya umarci Maryam da ta basu labarin abunda ya faru da ita, da asalin cikin waye, Malam ya kalli Maryam dan ta fara, tai kasa da kai murya a sanyaye ta fadi komai da ta sani bayan ta gama ta mika masa wata jakar ta inda a ciki ne sadakin ta yake na sarkar gold din da Aliyu ya bayar da marriage certificate tare da wayar da akai vedion komai.
Malam ya dauka ya bawa Yaa Alkasim ya duba komai ya kunna wayar tare da nuna musu vedion wanda Malam yasa akai connecting nasa da TV dake dakin, wanda kowa yaga abinda akai kamar a lokacin a kai, wanda duk jikin mutanen dakin yai sanyi, Mami da Maryam kuwa kuka suke dan ganin Aliyu a vedion sai ya dawo musu da rasuwar sa sabuwa ganin sa yana motsi da murmushi da magana.
Bayan an gama Malam ya dago ya kalli yan dakin yace
"Alhamdulillah duk da Muhammad yai min bayanin komai akan auren sirrin dasu Maryam sukai nasa ta bayyana komai saboda ku sani kuma ku tabbatar Maryam ba zina tayi ba da aure ta haifi yaron ta wanda ga shaida nan, Ahmad abokin Haidar ya kai Muhammad har wajen malamin kan Maryam tazo da wadan nan shaidu, dan haka ba abinda zamuce sai godiya ga Allah da ya tsare mana zuria daga aikata zina, sai dai akwai jan hankalin da zanyi ga kowa na nan wajen, wannan kaddara ce ga Maryam ya tashi jarabtar ta duk da tayi aure da Aliyu amman kasancewar bata bawa iyayen nata damar aurar da ita ba shiyasa bata samu abinda take so ba, kuma Allah ya nuna isharar sa, dan da Aliyu bai son ta bayan ya same ta zai iya watsi da ita amman da yake ba abin Allah wadai sukai ba sai soyayya ce ta dadu, to kunga yadda karshen su ya kasance duk da ba su sa'bawa Allah ba amman sa'bawa iyaye da rashin sanin su shine silar barin ta gida da shiga wata rayuwa wanda 'kaddarar auren Aliyu ita ce zan ce ta sa ta bar gida, jan hankalin da zanyi shine mu kasance masu bawa iyayen mu mahimmanci a komai, yau da Maryam da Aliyu sun sanar da iyaye akai musu aure da kan rasuwar Aliyu sun jima da zama a inuwa daya wacce ba zasu na jin shakar komai ba, haka nan da Muhammad ba zai fushi ya kori Maryam ba, amman da yake Allah ya k'addarta haka sai mu gode masa, amman ku sani ba kowa ne karshen sa zai zo irin nata ba naka zai iya fin nata in har kace zakai koyi da nata, kamar lokacin da ta bar gida zata iya cin karo da mutanen banza ko a 'ki taimaka mata shaidan yasa ta fada mummunar hanya amman Allah sai ya takaita wanda kila dan basu bi son zuciya wajen sa'ba masa ba ya hada ta da wadan nan bayin Allah to mu kiyaye shi Aliyu Allah masa rahma yasa ya huta.
To kunga barin ta gida ta samu kalubale da yawa wanda har auren ta aka fasa wanda ba abinda yafi wannan tashin hankali amman sai gashi wadan nan bayin Allah suka hada auren 'dansu da ita ba abinda zamuce sai godiya, Allah ya saka muku da gidan Allah, Maryam ke kuma Allah ya miki Albarka ya kiyaye gaba rayuwar Maryam ta zama izina garemu, Haidar ya rasu wani ya dawo ya maye gurbin sa a matsayin mijin ta Allah ya basu zaman lafiya ya raya Haidar karami yai muku albarka."
Duk dakin jikin su yai sanyi dan haka gaba daya suka hada baki wajen fadin
"Amin!"
Haka Malam ya kara musu nasiha mai ratsa jiki akan tsoron Allah da illar sa'bawa iyaye wanda su Maryam rashin sanar da iyaye ne kawai sukayi amman Allah ya nuna musu wanna isharar to wannan izna ce ga yan baya in tata tai kyau to ta wani ba dole ne tai kyan da tata tayi ba.
Bayan komai ya lafa ne aka yi liyafa anan babban falon Malam inda akaci aka sha anyi yanka raguna kaji da abubuwa sosai, suna tsaka da liyafa, Ahmad ya shigo tare da jagorancin d'aya daga cikin almajiran Malam, Yaa Alkasim ne ya mike suka karaso ya zauna, bayan an gama yace
"Ina Maryam din ne?"
Ciki Yaa Alkasim ya shiga bai jima ba sai gashi ya dawo dauke da Haidar, Ahmad na ganin Haidar sai da gaban sa ya fadi ya amshi yaron ya rumgume hawaye na zubowa a idon sa yace
"Masha Allah, burin Aliyu ya cika ya sunan ka boy?"
"Haidar!"
Haidar ya bashi amsa ya kara rumgume shi yace
"Masha Allah."
Hijab ne sanye a jikin ta, ta fito daidai lokacin da Ahmad ya d'ago kansa. Suna hada ido, idonta ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai.
Ya kura mata ido yana kallonta Maryam ta dad'a kyau ta zama cikakkiyar mace ba kamar shekarun baya ba. Ta karaso yace
"Maryam kece haka?"
Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. Ya dada zama cikakken mutum, a gefen Yaa Alkasim ta tsaya ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye, bayan sun gaisa tace
"Yaa Ahmad ai bazan ganeka ba"
Ya dan saki murmushi dan wani dadi yake ji, ji yake kamar ya rumgume ta dan farin ciki da dadi yau Maryam ta dawo gida cikin iyalan ta ga yaron su burin sa kenan ya kusa ya cika.
Haidar dake hannun sa ya hango Aliyu yace
"Adda kinga Abbi na."
Gaba daya suka waiga suka ga Aliyu tsaye yana kallon su, suna hada ido da Maryam ya hade rai ya juya ya bar wajen, Haidar ya hau kwada masa kira yana fadin
"Abbi Abbi."
Juyowa yayi Ahmad ya sauke shi ya tafi a guje yaje yace
"Abbi ina zaka?"
"Yanzu zan dawo jeka maza."
Ya juya ya koma wajen su Maryam yace
"Abbi unguwa zai je Adda?"
Ahmad yace
"Boy kasanni?"
Kai ya girgiza ya rumgume yaron ya kara yana jin wani son sa da kaunar sa na dada shigar sa burin sa kawai ya auri Maryam su kula da dansu. Ahmad yace
"Nima Abbin ka ne."
Dagowa Haidar yayi ya kalli Maryam yace
"Adda ni Abbi na uku ne?"
Ahmad yace
"Kana da Abbi da yawa."
Ya zaro wayar sa yace
"Kasan wannan?"
Ya nuna masa picture din Aliyu, amsa yayi yana murmushi yace
"Adda ta nuna min tace shine Abbi na na farko, kuma Abbi muna kama ko?"
Ya jefa tambayar ga Ahmad.
Ahmad ya gyada kai yace
"Sosai ma to kaga Abbin naka da yawa ga Uncle Alkasim ga Uncle Muhammad da yawa fa."
Yai dariya yace
"Yeee ina son ku dukka Abbi."
Ahmad ya rumgume shi yace
"Muma muna son ka Haidar. Allah maka albarka."
Ya amsa da amin. A haka suka rabu Haidar na wajen sa daga ya kalle sa sai ya rumgume sa.
Kwanan sa daya ya tafi gida sanar da labarin ganin Maryam, wanda Maryam tin lokacin ko sun hadu da Aliyu sai dai hade fuska ko gashe shi tayi sai ya gadama yake amsawa duk ta damu.
Aliyu kuwa sosai ya saba da su Inna da Hajja kakkanin Maryam dan zasu zauna su sha hira wani lokacin har dan tsokanar su yake bama in su Sitti na nan yai ta fama wannan yasa suke son sa sosai.
*
Kwance take a kan gadon Inna mahaifiyar Abbin ta wato takwarar ta, sallamar sa ta jiyo ido ta lumshe dan tayi kewar sa na kwana biyun nan ba magana ba dan sakin fuska sam.
"Mai gidan."
Innar Abbi ta fada ya zauna yana fadin
"Yauwah Uwar gida na furar nan nazo na sha kan mu fita zaga gari."
Inna ta mike tana fadin
"Ai gata cikin daki bari na kawo maka."
Ta shiga ta dauko ta kalli Maryam da tai saurin rufe ido, ajiye masa tayi ya fara sha yana santi hadi da mata hira, zaune Maryam ta tashi tana mamakin anya kuwa Yaa Haidar ne a falon Inna, tabbas muryar sa ce amman kuma har yaushe ya saba da Innar da suke hira haka, mutumin da magana wahala take masa, mikewa tayi ta nufi kofa ta tsaya a gefen labule tana leken sa, dago kan da zai ya hango ta kai ya dauke dan har yanzu bai huce ba ganin tan da yayi da Ahmad tana tai masa murmushi. Haka ya gama sha ya mike yace
"Gaskiya za aje dake Uwar gida zan zo na sha ta yamma godiya nake."
Sukai sallama, yana fita ta fito ta zo ta zauna a gefen Inna tace
"Oh daman ba baccin kike ba takwara"
Ido ta mutsaka tace
"Hirar kuce ta tashen."
"Oh mai gidan naki ne ai, yaron yana da hankali da ladabi ya dauke mu tamkar nasa kakanin ke dai kina dace Maryam dan Allah kiyiwa yaron nan biyayya ko dan yadda yake son yaran ki kinji."
Kai kawai ta gyada tana mamakin Aliyu.
*Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe Amin.*
*Antty*
[12/5, 13:30] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 76
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ana gobe zasu tafi Malam ya kirata a parlorn sa, ta shiga kan ta a kasa zama tayi daga gefen, dagowar da zatai taga Aliyu zaune a kusa da ita, kai ya dauke ta gaishe da Malam ya amsa sannan ta gaishe da Aliyu ya amsa ba yabo ba fallasa, ita ta rasa saboda me yake mata haka kwanan nan ko dan yaga ta damu da shariyar da yake mata ne, kai ta dauke kawai. Malam ne ya fara magana wanda duk nasiha ce yake musu mai shiga jiki, daga nan kuma ya fara jan su da hira ita dai shiru tayi amman tana jin yadda suke ta hira da Aliyu sai kace wanda suka jima da sanin juna.
Suna zaune taji sallamar Haidar karami ta dago tana kallon kofa shima yana shigowa ita ya fara arba da ita dan yau kwata kwata bai ganta ba dan daga wannan ya dire wannan zai dauke shi kuma akwai sa da son mutane ganin sa cikin yan uwa yasa ya sake. A guje ya fada jikin ta yana murnar ganin ta, ta rungume shi tana mai jin wani iri, dan Yaa Haidar ne kadai ya fado mata da ace yana raye da komai bai faru ba da ta ina Yaa Aliyu zai na bata mata rai ta ina ma zata san shi bare har ya share ta taji haushi. Yana lura da yanayin ta duk sai yaji ba dadi, kai tayi kasa dashi tace
"Malam bari naje na kwana sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya, Allah muku albarka."
Ta mike ta fita dauke da Haidar da ya rumgume ta, da kallo ya bisu yana mai jin kamar yabisu ya lallashe ta sai dai kuma wata zuciyar tace ya barta. Tana shiga ta samu kakanin nata gaba daya dasu Inna da Sitti zama sukai Haidar ya lafe a jikin ta dan ya gaji bacci yake ji.
Hankalin su suka dawo dashi kansu, ganin yanayin ta duk yasa sukaji ba dadi, nan su Inna suka hau lallashin ta da mata nasiha da jan kunne, kafin daga bisni suka 'buge da hira, wajen tara da rabi suka shige daki ita da Haidar suka kwanta.
*
Washe gari wajen karfe 10am suka kammala shirinsu gaba dayansu, Malam dasu Inna har bakin mota suka rako su Abbi, Maryam har da hawayen ta dan sati dayan da sukai taji dadin garin taga gata da kulawa Haidar karami ma da Abbin sa sunji dadin garin sosai ba wanda yaso ya bar garin a lokacin, haka Malam ya loda kayan abinci da amfanin gona dasu nono, kaji, zabi, kwai akan a bisu Ummi dashi wanda daga nan kayan aka sa su tafi can Abuja su Ummi saje su tadda shi dan sai sunje Kano kafin su wuce Abujan.
Ranar da suka iso a ranar Yaa Ahmad ya sauka a garin Kano shima, da dare suna zaune a falo ita da Ammi ya aika cewa ace Ahmad ne yazo. Ammi tace "Allah Sarki Ahmad gaskiya ya rike alkawari kinsan baya wata bai zo ba duk da kina ganin ba a garin nan yake ba kullum yana cigiyar ki yau kun dawo ma ya kasa zaune bare tsaye, shi ya fara warware mana komai akan alamari nan. Allah ya saka masa da alheri dai."
Maryam ta amsa da amin tana daukar hijab din ta, ta saka, sallamar Ahmad suka jiyo suka amsa ya shigo cike da ladabi ya gaishe da Ammi ta amsa fuska a sake.
Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma daki, Maryam ta durkusa ta gaishe shi ya amsa yai mata ya hakurin Aliyu, wanda har hawaye ya kawo a cikin idon ta, cikin lallashi yace
"Kiyi hakuri haka rayuwa tayi damu ban tashi sanin rasuwar Aliyu ba sai bayan wata kusan uku, a lokacin naji mutuwar na shiga damuwa da tashin hankali wanda na rasa yaya zanyi dana zo shine Alkasim yake fada min bakya ma gida ga abinda ya faru, ni na fara sanar dasu cewa da aure tsakanin ki da Aliyu na wata uku, ni na dauki Abbi na kai shi wajen malamin da ya daura auren anan aka kara bazama neman ki sai dai Allah bai nufa za a same ki ba sai yanzu, naji dadi da farin ciki da aka ce an ganki."
Kanta a kasa tana wasa da yatsun ta, ta dago tace
"Nagode Yaa Ahmad Allah saka da alheri."
"Ba komai ai an zama daya."
Shiru sukai can yace,
"Kinsan ni da Aliyu abokai ne, wanda dagani har shi bama boyewa juna sirri dan ni na karfafa masa gwiwar yin auren ku, to Maryam bayan rasuwar Aliyu sai na yanke shawarar akan ko yaushe kika dawo ina son ki zan aure ki dan mu rike amanar yaron da kika haifa ni nai alkawarin zan rike shi tamkar d'an ciki na."
A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa. Yayi sassanyar dariya
"Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba wai na maye gurbin Aliyu bane. Ina so ki bani dama a matsayin masoyi na sami kaunarki."
Mikewa tayi tana girgiza kai, dai dai shigowar Yaa Aliyu, wanda bata san dashi ba, daki kawai ta shige ta bar Ahmad wanda ya bita da kallo, yasan haka zata faru dan yasan kan Maryam taso wani abune mai wuya dan soyayyar