Showing 81001 words to 84000 words out of 232912 words
Chapter 28 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
nasan Fadima mai iya rike kice ba tare da sanin Abbi na ku ba kuma nasan zata iya kare zata kula dake bazaki dade ba zaki bar gidan nata kije kinji. Ko bari nazo na kaiki da kai na."
Kai ta girgiza tai mata nuni da A'ah Abbi bai sani ba ta zauna kawai.
Mikewa Ammi tayi ta dauko kudi ta mika mata tace
"Kudin mota kinji!"
Kai ta gyada sannan ta mike Ammi na biye da ita suka je bakin gate fadawa jikin Ammi tayi ta rumgume ta tana kuka. Ammi ma kukan take tana fadin
"Allah miki albarka ya tsare ki Allah ya shiga lamuran ki! Sai nazo naji komai game da cikin!"
Kai ta gyada tana mai jin kunya da nauyin Ammi, har ta fita a gidan Ammi na kallon ta. Itama tana fita tabi gidan da kallo......
*Allah ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe Amin*
*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 30
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Tana fita taji kirjin ta ya hau dukan uku uku ga kan ta da ya wani sara wanda hakan yasa ta durkusa tana dafe kan ta. Ta jima a haka sannan ta mike ta fara kalle kallen wajen sai kuma ta mike ta nufi babban titi tana tafiya tana haki a haka ta karasa kallon ababen hawa ta tsaye yi napep sai zuwa suke suna tsayawa a gaban ta amman ta kasa tsayar da daya a cikin, sam bata san me ko wanne hali take ciki ba a hankali ta fara taku wanda bata san kan titin ta hau ba wata mota ce taho a guje wanda tana ganin Maryam yasa ya danna wani uban horn tare da taka burki. Da sauri ta dago dan jin horn din shi ya dawo da Maryam daga tunanin da tatafi ta dago da sauri ganin yadda ya taho da gudu yasa ta rude sai kawai ta fadi a sume. Motar yai parking ya fito yayo wajen ta tare da mutanen dake bakin titin ganin bata numfashi yasa ta dauko ruwa aka yayyafa mata amman bata farfado ba da sauri yasa ta a mota ya bar wajen da sauri wani private asibiti ya gani nan ya shiga da ita nurses suka amshe ta. Cikin hukuncin Allah nan da nan ta farfado. Suka duba sukaga ba wata matsala bayani sukai masa sannan sukace zasu iya tafiya.
Dakin da take ya shiga ya same ta zaune ta hade kai da gwiwa tana kuka. Karasawa yayi yace
"Akwai inda yake miki ciwo ne?"
Kai ta girgiza ba tare da ta dago ba. Yace
"Kukan me kike to?"
Kai ta kuma girgizawa. Kallon ta ya tsaya sai kuma yace
"Tashi mu tafi"
Da sauri ta dago sai ta zuro kafafun ta, ta mike tabi bayan sa. A haka suka fita compound din asibitin wajen motar sa. Mota ya bude mata sai ta tsaya kallon sa yace
"Shiga mana!"
Kallon sa ta tsaya sai ta girgiza kai. Murmushi yayi yace
"Na miki kama da barawon mutane ne? Shiga na kai ki inda zakije."
Addu'a tayi ta shiga sannan ya tada motar kallon ta yayi yace
"Ina zakije?"
Shiru tayi dan ita sam bata san ina zata je ba. Shiru tayi can sai ta dauko papper da pen a jakar ta ta rubuta masa. Amsa yayi ya karanta yace
"Tafiya zakiyi?"
Kai ta gyada yace
"Wanne garin?"
Kai ta dauke dan kuma me zai dame ta da tambayoyi tinda dai ta fada masa inda zata ba shikenan ba.
"Fada min mana."
A paper ta sake rubuta masa. amsa yayi yace
"Yan uwan ki ne acan ko kece can!"
Kai kawai ta gyada. Tasha ya nufa da ita sannan yai parking suka fito tana ta kallon tashar daman haka tasha take tamkar kasuwa, a tsorace ta dinga bin bayan sa har sukaje wajen motocin ya saka ta a mota ya biya sannan ya juya ya kalle ta yace
"Allah tsare hanya kina kula in zaki tsallaka titi in ba zaki iya ba ki nemi taimakon wani kinji!"
Kai ta gyada sannan tai masa godiya da hannu. Tana zaune a motar har ta cika aka tashi mota suka fara tafiya. Tafiya sukai mai nisa dan bata san hanyar ba kwata kwata bata taba yo nan wajejen ba a rayuwar ta to dan me zataje inda bata sani ba amman ta rasa amsar da zata bayar a hankali tana nesa da gida a hankali take manta komai dake tare da ita. Abu daya kawai take ji da jin zata kara nesa dashi shine Yaa Haidar shikenan garin da kabarin sa yake ma ta barshi, hawaye ne ya zubo mata ta daura hannu akan cikin ta da taji yana dan motsi a zuciya take fadin
"Yaa Haidar yasan da cikin jiki na kenan kome? In bai sani ba tayaya yake min zancen dan sa na kula dashi nace yana son sa, saboda me yake ce min insa yana masa addu'a kuma na fada masa Dadyn sa na son sa, kenan Yaa Haidar yasan da cikin!"
Zancen da take da zuciyar ta kenan.
" *Ummu Haidar* "
Zuciyar ta, ta ambata. Ido ta runtse tana fadin
"Na tashi daga *Matar Haidar* na koma *Ummu Haidar* "
Da sauri ta runtse idon ta tana fadin
"Ba zan taba tashi daga *Matar Haidar* ba zan kasance matar ka har a aljanna da izinin ubangiji na yadda na amince ni *Matar Haidar* ce kuma *Ummu Haidar* "
Sai ta saki murmushi wanda take yi hawaye na zubo mata a idon ta.
Hannun ta, ta daura akan cikin ta, tana fadin zance a zuciyar ta
"Tamu kalar kaddarar kenan mun rasa Abban ka. Allah ya jikan Abban ka."
A haka suka cigaba da tafiya zazzabi na damun ta, ga ciwon ciki ga ciwon jiki ga gajiya. sai karfe biyu suka tsaya sukai sallah masu siyan abinci na siya sannan suka shiga mota suka cigaba da tafiya. Da akai la'asar ma haka.
*Bauchi*
Karfe shida suka sauka a tashar garin Bauchi. Kallon tashar ta dinga yi dan zatace tin da take bata taba zuwa tasha ba sai yau dazu da kuma yanzu gani tayi tamkar kasuwa duk da magariba ta doso kai amman sai hada hada ake yi.
Kalle kalle ta tsaya yi wanda ta rasa ina zata dosa. Ga zazzabin da yake damun ta duk magariba zuwa asuba ya fara tasowa gefen wani shago ta zauna take kuma taji cikin ta ya hau kogin yunwa duk da a gida ba abinci take ci ba amman ko zata dawo dashi ana bata data zauna da yunwa ga karin ruwa da ake mata ko da yaushe. Rabon ta da abinci tin shekaran jiya dan jiya ba ma abinda taci gashi yau tea ne kadai shima cokali uku tasha taje ta harar dashi.
"To me zanci?"
Ta fada tana shafa cikin nata mikewa tayi tana zagaye kasuwar tana rurufe fuskar ta dan ganin mutane da yawa ga maza masu hankali da marasa shi nutsatsu da wanda ba nutsatsu ba ko a gida bata zuwa kasuwa iyakacin store shima bata fiya zuwa ba gwara ta rubuta abinda take so Biba ta siyo mata da taje in ta fita da Yaa Haidar ne shima tana tafiya tana buya a bayan sa. Mai gasa nama ta gano shi ya bata sha'awa dan haka ta karasa ta bude jakar ta dauki dubu daya a cikin kudin da Ammi ta bata, mika masa tayi tai masa nuni da ya saka mata gurasa guda daya sai nama na dari biyar."
Zuba mata yayi ya bata taga mai saida lemon kwalba ta siyi guda daya da ruwa biyu komawa inda ta baro tayi ta zauna ta wanke hannun ta sannan ta juya wa mutane baya ta dauki gurasa daya ta kai bakin ta, da kyar ta cinye ta cire hannun ta, ta bude lemon nama daya ta dauka tana kaiwa bakin ta sai amai haka ta dinga kakarin aman da ba abinda yake fitowa sai gurasar da taci kawai. Rufe naman tayi ta dauraye bakin ta. Lemon fanta ta dan kurba ta hadiye ta rufe dan tasan yanzu zata dawo da ita itama. Amman cikin hukuncin Allah sai bata dawo da ita ba. So take ta dada amman tasan da ta dada zata dawo da shi, ido ta rufe tana kuka tana kiran Yaa Haidar a cikin zuciyar ta.
A haka tana zaune aka fara kiran sallah magariba alwala tayi da ruwan da ya rage mata sannan ta ciro dakwalin ta, ta shimfida ta tada sallah. Tana zaune tana rawan sanyi a wajen har aka kira sallah isha'i sallah tayi, ta zaune ta hade kan ta da gwiwa tana mai cigaba da rawar sanyi ga ciwon kai ga yunwa. A hankali ta dinga jin hayaniyar tashar yana raguwa wanda tasan dare ne yayi ko ba a fada ba goma zata iya yi. Tunanin ta daya to ina zataje ina zata kwana. A haka ta rakube jikin wannan shagon wanda bacci barawo ya dauke ta ga zazzabi ga ciwon kai sai firgita take a haka har asuba da baccin ya dan dauke ta ciwo ke tada ta. Ganin an kira sallah yasa ta mike dan neman ruwa tai alwala. Cikin tashar ta dinga bi har ta hango masalaci ta isa ta debi ruwa tai alwala sannan tai sallah a kofar masallacin har karfe shida tana zaune can gefe taga wata mata mai kosai ta fito ta fara soyawa. Zata ce ita bata cin kosai ko a gida amman sai taji yau duk duniya shi kadai take son taci. Mikewa tayi ta karasa ta bata dari biyu tai mata nuni da ta bata kosan. Amsa tayi ta bata tashi da uban yawa komawa tayi gefe ta shiga hijab dan taci amman daya taci kawai taji ya tsaya mata a kirji. Wannan yasa ta bawa almajiran dake wajen sadakar sa. Haka ta koma inda ta zauna jiya lemon ta na jiya ta kara kurba shine kadai ya zauna a cikin ta.
Har karfe goma tana wajen wanda a lokaci rana ta zo dan haka ta mike ta canja waje haka ta dinga garari a kasuwar gashi ta gaji tana son ta samu ta kwanta ta huta ga yunwa ga ciwo, a haka har magariba ta kara gabatowa. Wajen jiya anan ta kara zama anan ta kwana washe gari a masallacin cikin tasha taje tai alwala tai sallah gaba daya jikin ta damun ta yake ga ciwo ga rashin wanka.
Lemo kawai ta sha bata ce zata siyi wani abu ba dan tasan in ta siya ma asara zatayi, tana zaune ta hade kai da gwiwa kuka kawai take yadda rayuwa ta juya mata. Duk da ba wani abu take tinawa a baya ba amman tasan bata saba da wannan rayuwar ba, abu daya take iya tinawa shine Ammin ta da Yaa Haidar.
To Ina Ammi? Shine tambayar ta? Tana wane gari? Sai kuma Yaa Haidar da tasan baya tare da ita ya mata nisan da bazata taba ganin sa ba. Hawaye take dan ga ciwo ga rashin mataimaki. A haka ta yini sallah kadai ke tayar da ita sai lemo take dan kurba wanda in ta sha da yawa shima amai take wanda aman ba komai a cikin ta sai wahala da take sha kawai.
Kwana ta biyu a tasha wajen da ta sauka anan yau ma ta kara zuwa ta zauna da akai sallah isha'i tana kwance wajen karfe goma sha dayan dare taji wasu samari suna fadin
"Ata ina ma yarinyar take?"
Daya a ciki wanda muryar sa take a buge yace
"Wajen shagon Bala!"
"To muje muga Allah yasa tana nan dan tin shekaran jiya yarinyar ta dauki hankali na."
Maryam dake kwance ta jiyo su suna magana dan suna bayan layin shagon da take ta mike duk yadda jikinta ke ciwo ga zazzabi da ciwon kai a hankali ta bi ta layin gaban ta, ta bar wajen tana ganin ta musu nesa ta diba a guje ta fita daga cikin tashar.
Titi ta gani babba wanda yake da hasken fitilu tafiya ta fara wanda bata san iya yadda tayi tafiyar ba. Sai da ta ji kafar ta na neman kasa daukar ta, ta zauna ana gefen titin ga yunwa ga zazzabi tana zama ta kwanta anan kasa take bacci ya dauke ta.
Karfe biyar na asuba ta farka dan ta fara jin kiran sallah mikewa tayi tana tafiya dan ta samu inda zataga masallaci sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta samu wani gida Mai wanda gefen sa yar kasuwa ce ga masallaci a ciki. Ciki ta shiga bangaren mata wanda ta samu bandakin nasu a wanke wanka tayi duk da ba sabulu sannan ta fito tai alwala ta shiga masallacin tai sallah tana idarwa ta kwanta dan akwai wuta ga fanka. Bacci ne ya dauke ta wanda bata tashi farkawa ba sai wajen daya da wani abu shima kuma ciwon ciki ne ya tashe ta da motsin da taji cikin ta na mata. Dafe cikin tayi sannan ta mike ta fita yar kasuwar nan ta shiga ta siyi fura da nono da ta gani sannan ta siyi fanta. Masallacin ta dawo ta sha furar wanda tana gama sha ta fita ta amayar da ita. Alwala tayi ta dawo tai sallah sannan ta kurbi fantan ta kwanta. Da ta gaji da kwnaciyar ta isa inda taga Alkur'anai ta dauko Alkur'ani ta fara karantawa shi ranar ta yini tana karantawa. Har yamma da dare anan ta kwana washe gari ma anan tai wanka dan har sabulu ta siya sannan ta kara siyan abincin nata wato fanta wandan sai ta kwana biyu taba shanye daya ba, gashi shi kadai take iya sha a cikin ta.
Kwanan ta biyar a cikin masallacin nan masu kula da wajen suka gane da zaman ta wannan yasa suka ce tabar wajen ba wajen kwana bane. Haka ta fito tana bulayin inda zataje ga jiri dake dibar ta dan rabon ta da taci abinci har ta manta duk abinda ta siya zataci loma daya take zata amayar dashi lemo da take dan kurba ya zauna shima ba da yawa take shan sa ba, kuma ko da yawa ne bashi da nutritive value da yake dashi a cikin ta da zai samar ta da duk abinda jikin ta ke bukata. A haka ta dinga tafiya, bata san iyakar lokacin da ta dauka tana tafiya ba, jin baza iya ci gaba da tafiyar ba ta samu karkashin wani bishiya da ta hango duk gefe bawon rake da giginya ta zauna tana sauke numfashi a hankali, iskar wajen yasa ta saka jakar ta tayi pillow dashi, bacci ne ya dauketa lokaci daya a hakan saboda iskan da bishiyar ke ta bayar wa, bata san lokacin da ta dauka tana bacci ba hayaniyar wasu almajirai ya tada ta, da sauri ta mike tana kalle kallen wajen jakarta ta dauka a hankali ta tashi da kyar ta ci gaba da tafiya kamar bata son yi wannan karan ma tafiya me nisa tayi da kafa ganin wani masallaci ta dau buta dake cike da ruwa ta samu gefe ta zauna ta daura alwala sannan ta tafi jikin wani shago tayi sallahn da bata yi ba, mayar da butan tayi ta ci gaba da tafiya, har aka kira magrib tafiya kawai Maryam take, ganin ta a wani kasuwa ta dinga zaga kasuwar, a hankali a hankali kasuwar ta fara watsewa ta shimfida dankwalinta gaban wani shago da aka duk aka rufe tayi magrib da isha ta jingina da table din gaban shagon, wasu hawaye suka dinga bin kuncinta, sanyi sosai ke shigarta ga zazzabi kan kace me kasuwar yayi tsit kowa ya wuce gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga zaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska zai hura ta, ta fadi ga wani ciwon kirji da ta tashi da, banda zugi da azaba babu abinda yake mata. masallaci ta samu a kasuwar tai alwala tai sallah sannan ta mike ta cigaba da tafiya.
*Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan amin.*
*Antty*[11/13, 13:59] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 31
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
HML MY SISTER HASSANA ALLAH YA SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA DA ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN
Har karfe hudu ba Alkasim ba wayar Yaya Fadima, wannan yasa hankalin Ammi ya dan tashi, amman kuma sai tai zaton ko Alkasim ya riga ya bar gidan Yaya Fadiman ya tafi wani wajen, ita kuma tana can tana aiki kila shiyasa bata kira akan zuwan Maryam din ba.
Tunanin mafita take akan Maryam, tin da tayi sallah isha'i ta kasa tashi a wajen, ji tayi zuciyar ta ta karye so take ta tashi ta kira Fadima amman sai taji ta kasa tashi ta rasa me take ji, sallamar Alkasim shi ya katse mata tunanin da take, ta amsa ya shigo ya zauna a gefen gadon nata yana fadin
"Daga dakin Maryam nake naga bata nan ina ta shiga?"
Kallon sa tayi cike da damuwa, ta sauke ajiyar zuciya tace
"Dazu bayan kun kawo ta Abbin ku yace bai yadda ta zauna masa a gida da cikin da bai san uban sa, lallai sai taje ta nemo masa mahaifin yaron sannan ta zo a yanke musu hukunci."
"What? Abbi me yake so yace? Yana so yace Maryam mazinaciya ce?"
Kai ya hau girgizawa yana fadin
"Ko duniya zata taro akan cewa haka ni ba zan yadda ba, me Maryam ta sani?"
"Na shiga rudani da damuwa amman nace zan tura ta can Saudiyya wajen Ummun ku."
Kallon Ammi yayi yace
"To yanzu Abbi da yace ta bar gidan ina take so taje, meyasa idon Abbi ya rufe akan alamarin nan, ai dole abi komai a sannu bai ga halin da take ciki bane?"
Tagumi Ammi ta sauke, ya mike yace
"Ina yanzu ta tafi?"
"Gidan Fadima tin dazu nace ta tafi."
Da sauri ya juyo yace
"Tin yaushe?"
"Baku dade da kowa ta, yazo yai maganar lokacin ko azahar ba ai ba ta tafi."
"Ammi har bayan la'asar ina gidan Fadima fa, kuma Maryam sam bata je ba."
Ido Ammi ta zaro tace
"Bangane bata je ba, daukon waya ta na kira dai naji ko taje daga baya."
Wayar sa ya zaro ya fara neman layin Fadima tana dauka tace
"Tin dazu nake so na