Showing 195001 words to 198000 words out of 232912 words
Chapter 66 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
mutum dashi. Sai da ta gama abinda zatai sannan ta nufi dakin da Maryam take, kwance ta same ta ta zauna tana fadin
"Bacci kike ne?"
Mikewa tayi tana kallon ta, Aisha tai murmushi tace
'Menene kike kallo nane?"
Mikewa tayi ta shige bandaki dan bata so Aisha ta sata a gaba, wanka tayo sannan ta fito Aisha ta bita da kallo, kai ta dauke ta fara shafa mai ta saka kaya ta kalle ta tace
"Kiran sallah dai ake kin zauna kin sani gaba kamar TV."
"Amarya Matar yaa Haidar."
Dan hararar ta tayi ta hau kan sallaya dan yin sallah, Aisha kuma ta shige bandaki dan dauro alwala.
*
Da dare, Aisha ta tafi sashen ta ita da Yaa Alkasim, Haidar ma ranar yana wajen Ummi, Ammi ta tafi sashen Abbi, ita kadai ce a dakin ta kwance ta kasa bacci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki, wani irin feeling take ji, dan in ta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaa Haidar tsigar jikin ta tashi take yi, tana cikin wannan halin, wayarta ta fara kara, dan tsaki ta saki dan bata san waye zai dame ta ba, har ta katse bata dauka ba wani kiran ya sake shigo, jin kiran ya isheta sai ta mika hannu ta dauko wayar ta saka a kunnen ta ba tare da ta duba me kiran ba.
"Bacci kike?"
Ya fada cikin muryar sa mai dadi da sanyi.
A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu, saboda wani sanyi da taji, kan tai magana yace
"Na kasa baccin ni amman ke kina ta baccin ki ko?"
Da kyar ta iya cewa
"Eh"
"Anya kuwa? Fada min gaskiya ba boye boye tsakanin mu uhmmm."
Ido ta lumshe tai shiru kawai, yace
"Ni gani tunanin ki ya hanani bacci ke kuma kina ta bacci ko? To hira na kira muyi."
“Hira Yaya nifa bacci zan yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka?"
Wani murmushi ya saki mai sauti yace
"Wannan lokacin yafi dadi ga ma'aurata Maryam."
Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce,
"Uhmm ki min hira wacce miji da mata suke yi ko na samu sassauci."
Shiru ta karayi, ya lumshe ido yace
“Maryam haka zamu yi da ke ko?”
Shirun ta karayi ya mike zaune yace
“Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Ammi ba za ta ki hanani ba."
Shiru tayi dan ta rasa me zata ce, wayar ya kashe tabi wayar da kallo, baki ta tabe ta mike ta cire kayan jikin ta da ta kasa cirewa tin dazu take juyi akan gado, doguwar riga ta saka iya gwiwa ta saka hula akan ta sannan ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito, dagowar da zata taga mutum tsaye a jikin kofa gaban ta ne ya yanke ya fadi, ta sunkuyar da kanta kasa. A hankali ya karaso sanye yake da kayan bacci wando da riga farare tas, wanda suke cotton masu laushi, karasawa yayi inda take tsaye yana binta da wani kallo, hannun sa na dama ya mika mata yace
“Zo mu yi hirar!”
Jikinta na makyarkyata ta ce,
“Ni bacci nake ji”
“Tunda na kasa kema ba za ki yi ba”
“Yaya don Allah ka zo ka tafi, kada Ammi ta fito, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka. Cewa zatai ni nake kai kaina wajen maza.”
Dan murmushi yayi yace
"Ai da aure in ma kinbi."
Kafada ta make abin sai ya bashi dariya ma, Maryam kuwa gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto.
A tausashe ya ce,
“Zan tafi, but on one condition....”
Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata.
“I only want to kiss you again! matata don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!”
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606
*Allah yai mana rahna, Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*
.
*Antty*
[12/8, 12:31] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 79
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ba ta motsa daga inda take ba, sai shi din ne ya taso ya tako a hankali ya tadda ita har inda take. Ya dauke ta suka koma kan gado, jikin sa ya jata yai mata wani irin rikon tare da cafkar bakin, yadda ya rike ta da irin yadda ya fara kissing nata ya tabbatar mata he will go far beyond abinda ya roka din, za ta gayawa aya zakinta idan ta sake ta bashi dama.
Bata taba sanin haka romancing yake ba sai yau, domin kuwa taji jiki, basuyi aune ba sai ji sukai an fara kiran sallah, bai nemi ya tara da ita ba amman fa bakin ta da kirjin ta sun sha matsa har zugi suke mata.
Jin ana kiran sallah ne yasa ya barta ba dan yaso ba sai dan lokacin sallah yayi, wannan yasa ya tafi ya bar ta cikin bargo. Jikinta babu sauran kuzari ko kadan ya gama gigitata na fitar hankali, da kyar bayan taji Abbi ya tada sallah ta sauko daga kan gadon da kyar take tafiya ta shiga bandaki, bakin ta ta hau dubawa dan ji take kamar ya cinye mata bakin, ba abinda yayi sai dai gaba daya yayi ja haka fuskar ta ma, rigar ta ta cire inda dukiyar fulanin ta ta bayyana, kan niples din nan yayi jajir, bakin yana tsatsaye saboda azabar da ya sha, ruwan dumi ta hada ta gasa jikin ta sannan tai wanka ta dauro alwala ta ta fito ta tada sallah, bayan ta idar ta mike ta fada saman gado dan rama baccin da bata samu ba.
Sai karfe goma ta farka, tayi mika tana runtsa ido ta mike ta shiga bandaki, wanka ta kara ta fito ta shafa mai ta shirya cikin wata doguwar rigar material maroon kala ta zura hijab ta nufi kitchen dan yunwa take ji, tana shiga ta hada tea kan ta nemi komai sai da ta fara sha sannan ta bude flask ta zuba dankali, da plantain da kwai, sai da ta ci ta koshi sannan ta mike ta shiga dakin Ammi, a zaune ta same ta ta karasa ta zauna a kusa da ita tace
"Ina kwana Ammi?"
"Lafiya lou yau baccin me kike tayi Ummi?"
"Wallahi Ammi, kinsan kwana biyu bama bacci da su Rukky sai yau na samu na dan rama."
"Yanzu Fadima ta kira ai, tace yanzu zata karaso."
"Yaya Zainab fa?"
"Itama nasan zata zo, Ummulkairi dai tace in zaki tafi zatai rakiya har Abujan."
"Ammi ke bazaki zo ba?"
"Me zanzo nayi Ummi?"
"Au ba zaki kaini dakin ba."
"Daman Uwa ce ke kai 'ya dakin miji."
"Ammi dan Allah kizo kema kinji?"
"Zan zo Ummi amman sai daga baya kinji?"
"Shikenan nasan Mami na tare zamu tafi."
"Oh Ummi, ga Ummin ki nan ai ke fa baki da matsala kina da uwa tana son ki tana kula dake, ki godewa Allah, yana hada ki da sirikan kwarai."
Kwanciyya tayi a jikin Ammi, a haka Yaya Fadima da Yaa Abdullah suka shigo Yaa Abdullah yace
"Me nake gani haka?"
Tai murmushi tace
"Ammi na ce ai ba taka ba."
"Yarinya ke da zaki tafi."
Baki ta turo, tace
"Ammi ni nama fasa anan zamuyi zaman mu."
Yaya Fadima tace
"Kinga ni tashi muje."
"Ina?"
"Daki."
Ta kalli Ammi, ta gyada mata kai mikewa tayi ta fita Yaya Fadima tabi bayan ta.
Daki suka shiga Yaya Fadima na nuna mata wasu abubuwa bayan nan ta dinga bata sirrikan kula da miji da na rayuwa, wanda Aisha ma ta shiga suka cigaba da wayar mata sa kai, ita dai jin su kawai take, suna zaunen nan taga kiran sa yafi sau biyar amman bata dauka ba har sai sa Yaya Fadima ta lura tace
"Ba kiranki ake ba?"
"Kyale shi damuna zai."
Ido ta zaro tace
"Oh damunki zaiyi ko kin dauka ko sai na batar miki."
Dauka tayi ta kai kunne yace
"Matar Haidar."
"Uhmm ina kwana?"
"Alhamdulillah ya na baro ki?"
"Uhmm..."
"Fada min, in dawo?"
Kamar zatai kuka tace
"A'ah kai zaman ka"
"Uhmm uhmm ni wallahi i need my wife."
Ya fada cike da shagwaba baki ta saki kawai jin wai wannan Yaa Haidar ne anya kuwa.
"Kinji."
Ya fada kamar zai kuka."
"Yayahh."
Ta kira sunan sa cikin wani irin salo.
"Matar Yaya."
Ya fada, tace
"Kayi hakuri."
Kafada ya make yace
"Naki."
"Uhmm ni yaya kake so nayi to?"
Ta fada kamar zatai kuka.
"No nifa bance ki min kuka ba, amman kinsan me inzo mu dan fita?"
"Uhmm a'ah ni kunya nake ji."
"Kunyar wa?"
"Uhmm Ammi, Ummi."
"Matatace fa."
"Dan Allah Yaya kai hakuri."
"Na hakura matar Haidar amman say u love me."
"I love u."
Tana fada ta kashe wayar
*
Da dare ta fito daga bangaren su Ummi, bacci takeji tana shiga barander bangaren su taji an janyo hannun ta, a tsorace ta juyo sai dai ganin Yaa Haidar yasa ta hau sauke ajiyar zuciya, sanye yake da blue black boyel yai masa kyau ya fito da hasken fatar sa sai hula dake kan nasa wacce ta kara masa kyau sai tashin kamshin turare yake bata san lokacin da ta lumshe idon ta ba, yace
"Me yasa ake gudu nane?"
Shiru tayi ya sa dayan hannun ya dago fuskar ta da sauri ta lumshe idon ta ya saki murmushi yace
"Wai kunyata kike ko? Ko da yake kina so na kara abin jiya ko?"
Da sauri ta bude idon ta tana girgiza kai yace
"Ki min magana in ba haka ba...."
Yai kwafa, baki ta turo yace
"Inyi kenan?"
Dagowa tayi ta dan harare shi da gefen ido, yace
"Uhmm ni kike harara ko?"
Kai ta girgiza ya kalle ta kasa kasa yace
"I want to hug you"
Ta bata fuska a shagwabe, tace
"Wai Yaya kai baka jin kunya."
"Kunyar wa zanji ni da matata."
Agogo ya kalla yace
"Goma ta wuce me ya fito dake ko ni kike fito nema?"
Ya fada yana kanne mata ido daya tare da kokarin danne dariyar sa, dan yaga yadda ta saki baki tana kallon sa,
"Ko baki taba fito neman nawa bane?"
Hijab din jikin ta taja ta rufe fuskar ta, tana murmushi kasa kasa ashe yasan ta fito neman sa ranan.
Kunya yake bata ji take kamar kasa ta bude ta shige, fargaba kada wani ya fito ya gansu. Dan matsawa tayi ya matso yana magana a hankali
"Gobe zaki tare ne?"
Juya masa baya tayi tana girgiza kai, tace
"Yaya ni dai sai da safe, kada Abbi ya fito ya ganmu fa."
"Matsoraciya Matata, kada kisa na dauke ki yanzu mu tafi can wani waje mu kwana."
Yai maganar yana zuro kansa ta wuyan ta, hannun sa ya sa ya zagaye kugun ta, sai kuma ya sake ta ya juyo da ita suna fuskantar junan su, kanta ya dago yana kallon lips din ta, ido ta lumshe wanda tana rufewa taji ya hada bakinsa da nata.
Ido ta zaro tana dukan sa da hannun sa, amman sai da ya dauki minti biyu yana kissing bakin ta sannan ya dago kansa yana karewa fuskarta kallo, ji yake kamar ya dauke ta suje su kwana abinsu, kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rumgumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna, sakin ta yayi, yai kissing goshinta sannan yace
"In ban tafi ba zanyi iya wani abun, sai da safe."
Ya juya yana daga mata hannu, tana jin rufe kofar sa jiki a mace ta ja kafa ta shiga dakin, Ammi ta gani, da sauri tai kasa da kanta dan gani take tamkar Ammi zata ga abinda tai, dan haka taki yadda ta dago, Ammi dai da ido ta bita har ta shige daki, girgiza kai kawai tayi ta fita ta rufe kofar ta nufi sashen Abbi.
Tana shiga daki bandaki ta fada, wanka tayi ta dauro alwala ta fito. Ko mai bata shafa ba ta saka kayan bacci ta kwanta, juyi ta dingayi akan gadon har kusan daya saura, ba alamar bacci a idon ta sam, tana tsaka da tunanin mijin nata, wayarsa ta shigo.
Zaune yake akan gado ya jingina da pillow. Shima tunda yayi wanka bacci ya kaurace masa. Matarsa yake tunani kawai, tana dauka yace
"Me ya hanaki bacci?"
Muryar nan tasa taji ta har cikin jikin ta, rufe ido tayi taki magana
"Ni ne ko? Am sorry daga gobe zaki ta baccin ki mai dadi a kirjin mijin ki."
Sake runtse ido tayi kamar yana gabanta tana jin kunyar kalamansa, shiru tayi yace
"Ko bakya so?"
Kai ta gyada tace
"Eh!"
Yai murmushi yace
"Kar na fara karyata matata amman dai wannan ta fada ba dai dai ba."
Shiru tayi, yace
"Kinsan me?"
"Aah."
Ta bashi amsa. Yace
"Ina so na zama komai naki, Miji, Yaya, Aboki, da, jigo, yadda komai kika debo ni, dan haka ki saki ranki kina fadan komai zanyi kokarin fahimta ba zan taba jin haushi ko makamancin wani abu ba kinji. Ina so ni da matata mu zama abokai ko fada mukai ba mai jin mu, mu zamu shirya kanmu, mu kasance kullum cikin farin ciki da fahimtar juna, mu samu ya'ya masu albarka kyawawa kamar Haidar ko?"
Tayi dan murmushi tace
"Allah ya tabbatar da alheri"
Ta fada tana gyara kwanciyya tare da yin hamma dan ta fara jin bacci har biyu tayi, yace
"Bacci ko?"
Tana ji amman bata so ta daina jin wannan muryar tasa dan haka sai ta girgiza kai.
Yace
"Gobe muna da tafiya ki samu ki kwanta ki huta kinji. Sai da safe take care."
"Allah tashe mu lafiya."
"Amin."
Ta kashe wayar tana rufe ido wani bacci mai dadi ya dauke ta, wanda sai da ta kusan makara da asuba.
*
Washe gari da safe suka tafi Abuja, da Yaya Fadima, Yaya Zainab, Yaya Ummulkhairi da wasu daga cikin kannen Abbi, sai Rukayya da Aisha, sai kuma su Ummi, da su Yaa Abubakar da Mami. Maryam ta sha kuka kamar kar ta tafi Abbi da Ammi sukai mata nasiha sosai. Tana jikin Ummi a kwance ta rufe fuskar ta da hijab din jikin ta, Yaa Aliyu na gidan gaba gefen driver sai Yaa Farouk dake driving inda, Aisha ke gefen Maryam.
Bayan ta gama kukan nata ta mike ta jingina da kujera, Yaa Haidar ya karkato da mudubin motar yana kallon ta kamar ance ta dago suka hada ido, ido daya ya kanne mata da sauri ta lumshe idon ta, wayar ta ce tai kara alamar shigowar sako, dauka tayi ta duba sai tai sauri ta rufe wayar ta ajiye kawai tana ji wani text din ya kara shigowa amman taki ta duba daga haka ma sai bacci karya da ta hau yi dan ya kyale ta.
A haka suka karasa wanda Mami tai musu tarba mai kyau, a sashen Mami suka sauka gaba daya, suna falo bayan an gama cin abinci Mama ta shigo gidan, da kallo ta bisu sai ta karaso suka gaisa cikin mutunci, sosai Ummi tai mamaki, bama da taga yadda Maman tai la'asar dan har ita ta gaisar tana tambayar ya hanya. Mami ta kalla Mami tai murmushi kawai.
Sai yamma duk sukai daki, Kannen Abbi biyu da Mami suka wuce sashen Ummi, wanda Yaya Ummulkhairi da Zainab da Yaya Fadima suna sashen Mami, Maryam da Rukayya kuwa wajen Inna suka gudu. Aisha tayi tayi su taho sunce zasuje daga baya.
Da yamma Maryam na dakin Inna, Jawahir ta shigo suka tashi suka rumgume juna, Jawahir ta zauna tana fadin
"Dan kin samu su Aisha shine kika yadani ko?"
"Kina raina wallahi abubuwa ne sukai min yawa kawai."
Ta zauna tana mikawa Rukky hannu suka gaisa, tace
"Kun dawo lafiya?"
"Alhamdulillah ya gida yasu Momy?"
"Suna lafiya ai munzo bakwa nan."
"Ayyah."
"Yaa Khalifa ya shiga damuwa sosai, baki ga yadda ya koma ba Sister ya rame yayi baki tinda aka daura auren sa bai kara lafiya ba kullum yana asibiti, daga farko jinin sa ne ya hau, sai ulcer, wanda a haka kullum yake damuwa da rashin bacci ya hana jinin sa ya sauka."
Idon Maryam ne ya ciko da hawaye, a ranta take fadin daman haka yake son ta, Allah yayi ita ba matar sa bace sai dai zatai masa addu'a basa lafiya kuma yayi hakuri ya amshi zabin iyayen sa kila ya zamo masa alheri.
"Kira min shi a wayar ki nai masa sannu."
Nan da nan ta kira mata shi yana kwance yaji kiran ya dauka tace
"Yaya nazo gidan su Maryam ne tace na baka kuyi magana."
Ta mikawa Maryam, amsa tayi tace
"Yaa Muhammad ina yini?"
"Lafiya lou Maryam ya gida yasu Haidar?"
"Suna lafiya ya jikin?"
'Alhamdulillah."
"Allah kara sauki, kayi hakuri Yaya ka amshi kaddarar ka, Allah yayi ni ba matar ka bace, dan haka ka amshi zabin iyayen ka kila ya zamo alheri a rayuwar ka bana jin dadi da akace ka saka damu baka ci baka sha baka bacci in har kana so na to Yaya ina so daga yanzu ka cire ko wacce irin damuwa dan Allah ka cigaba da rayuwar ka dan Allah."
Hawaye ya biyo fuskar sa yace
"Nagode Maryam Allah miki albarka, naji ance kin hadu da iyayen ki insha Allahu, in komai ya warware har Kanon zani na gaishe su, nagode sosai ina miki fatan alheri."
"Nagode Yaya. Sai anjima."
Ta kashe wayar hawaye na zubo mata ko ba komai yana son ta kuma ya damu da ita ya nuna mata kulawa da tsantsar soyayya ta san ba zata taba mantawa da Yaa Muhammad ba.
Shiru kuma sukai, sai bayan magariba Jawahir ta tafi, tana fadin
"Yaushe zaki dawo makaranta an koma wannan satin fa."
Baki ta dan tabe tace
"Next week."
"Ke da zaki tare ai nasan kyayi hutun a kalla two week."
Murmushi kawai tayi sukai sallama.
Da dare Inna na daki tana gyara durowar ta, Maryam na falon tana kallo, Rukayya taje wajen su Yaya Fadima, idon ta na kan TV taji an bude kofa dagowa tayi sai taga Yaa Aliyu da sauri ta mike tana gyara zaman ta daga kashingiden da take hijab take nema ta saka, ya karaso ya dauke hijab din yana binta da wani kallo wanda yasa tsigar jikin ta ta tashi zama yayi a kusa