Showing 39001 words to 42000 words out of 232912 words

Chapter 14 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1226

ai tafi karfin sa, Ummi in ta tawa ce a hanata kula sa in har zai na saka mata damuwa bana so sam"

"To menene na daukar zafi ne haka, ai laifin mune da bamuyi masa bayani ba zanwa Abban ku magana sai ai masa magana ya sanar dashi in yaga yana so to in baya so ni nasan wani zai zo mata insha Allahu."
"Is better dai."

"To kaje ka huta."
"Sai da safe."
Ya fada ya kashe wayar sa dan ransa ba karamin baci yai ba, kwanciyya yai akan gadon yana dafe kansa da yaji ya dau zafi, kila fa yanzu tana can tana kuka akan wani can yazo ya tada mata da hankali yasa mata damuwa. Mikewa yai ya dauki wayar sa, layin Maryam ya fara nema amman sai aka ce masa a kashe take kira ya kara yi same a kashe take wayar yai cilli da ita, ya mike ya shige ban daki. Yana shiga ya sakarwa kan sa ruwan ya jima a karkashin shower ruwa na zubo masa amman bai bar wajen ba, sai daga baya ya fito daure da towel, jallabiyya ya dauka ya saka, ya hau kan sallaya dan yayi sallah yana idarwa yaji ana knocking budewa yayi yaga Yasmeen yar yar Ummi ya saki murmushi yace
"Baby Yasmeen."

"Big bro Momy ce tace wai kazo kaci abinci."
Hannun ta ya kamo yace
"Am not hungry dear."

"But Big bro u having eat any thing since u came."
"Yess Baby i take something there."

Kai ta gyada ta juya ta fita, komawa yai ya kwanta, bai jima da kwanciyya ba yaji ana knocking kofa kamar ba zai tashi ba amman jin muryar Antyn sa, yasa ya mike yana budewa ya koma ya zauna a gefen gado, Momy ta shiga tana kallon sa, ta jima a tsaye har sai da ya dago yana kallon ta sannan ya dan saki fuska yace
"Momy nayi laifi ne?"

Zama tayi akan resting chair dake dakin tace
"Me yake damun ka? Tin zuwan ka na gane kana cikin damuwa."

"Momy zuwan ne bana so kwata kwata."
"Oh wajen namu ne baka son zuwa."

"A'ah Momy in wajen ku ne nasan zanyi two to three week na juya amman yanzu shekara fa, ina da abubuwa da nake son yi a can da yawa."
"But Aliyu naga kai ka nemi tahowa ko?"

"A lokacin da na nema basu ban dama ba sai a yanzu da bana so."
"To ka daina damuwa kaji kayi addu'a Allah yasa zuwan naka a wannan lokacin shine mafi alheri, ka sani ni ba zan yadda da rashin cin abinci ba, balle ka koma rame ayi zaton bana kula dakai ko da dura sai kaci kaji ko?"

"Momy naci abu a jirgi fa yanzu hutawa kawai nake son yi."
Mikewa tayi tace
"Ni dai na fada maka za a kawo maka ko tea ne ka sha."

Ta juya ta fita, kansa ya dafe yana mai lumshe ido, Basma Yayar Yasmeen ce ta shigo da tray a hannun ta, dagowa yai ta ajiye akan stool ta matso masa dashi gaban gado, dagowa yai ta zauna tace
"Big bro ina ta zuba ido ka fito amman shiru?"

Murmushi ya saki yana fadin
"Na gaji ne."
"Yasu Sitti?"

"Suna lafiya suna gaishe ku."
"Big bro dan kai ta tafi kaima kuma ka dawo."

"Ni ba jimawa zan ba zan koma"
Tai murmushi tace
"Bikin Anty Najwa?"

"Kila."
Ganin bai son surutu yasa ta mike tace
"To sai anjima."

"Alright."
Ta mike ta fita, kurawa kayan abincin ido yayi daga karshe saboda yasan halin Momy in bai ci ba da kanta zata zo ta tsaya har sai yaci wannan yasa ya dauki dan fulas din dake kan tray din ya tsiyaya tea din a cup, bai saka komai ba sai dan sugar ya dauka ya fara sha, yana gamawa ya mike ya shiga toilet ya jima a ciki ya fito yana kara tsane jikin sa da alama wanka ya karayi, kan gado yazo ya kwanta amman me sam bacci yaki ya dauke shi sai juyi ya dinga yi, abubuwa na damun sa ganin ba baccin zai ba yasa ya mike ya shiga ya dauro alwala akan sallaya ya kwana yana addu'a.


*
Washe gari Ummi ta samu Abba tai masa bayani kai ya dafe yana fadin
"Wallahi Aisha na sha'afa sam saboda mantawa nake da Maryam ba 'yata bace amman insha Allahu zan kira yaro sai nai masa bayani in yaga yana son ta a haka shikenan Allah yasa mu dace."

"Amin nima na damu bana son damuwar ta gaba daya."
"Insha Allahu komai zai tafi normal."
Kan Abba ya fita ya kira Muhammad yace yazo da dare in ya dawo daga aiki.


Haidar ne ya tashi Maryam da safe yana fadin
"Adda cornflask zan sha kinji Adda."
Ido ta bude tana kallon sa tace
"Ina Ummi?"

"Ta fita aiki?"
"Bakai breakfast bane?"

"Nasha tea ni cornflask zan dada."
"Ai Iyya na kitchen dan Allah jeka ta hada maka."

Ta fada tana dafe kan ta dan har lokacin ciwo yake, baki ya turo kamar zai kuka yace
"Adda nata ba dadi na Abbi na yafi, Adda ki kira min Abbi ya hada min."

Kai ta dafe tana fadin
"Ni muje na hada maka."
Ta mike ta fita har ya kai kofa yaji wayar ta na kara komawa yai ya dauka ya fita a guje yana cewa
"Adda ana kira."

Bata falo har ta sauka dan haka ya bita kitchen tana hada masa madara ya karasa ya mika mata yace
"Adda ana ta kira."
Amsa tayi tana kallon screem din ganin sunan Yaa Aliyu yasa ta zubawa screen din ido tabbas itama tana son taji ya ya sauka tinda bata samu ta tambayi Ummi ba. Wayar ce ta kara yin kara ta duba da sauri ta dauka ta kai kunnen ta, sai dai ta kasa furta komai, sallama yai mata cikin muryar sa mai dadi da sanyi wacce take kwantar da hankalin mai sauraron ta ido ta lumshe tana amsawa a kasan makoshi tare da yin shiru.

Aliyu dake kwance yace
"Tinda baki iya gaisuwa ba bani yaro na."
Duburburcewa tayi tace
"A'ah Yaya ina kwana? Ya ka sauka? Da fatan ka sauka lafiya?"

"Alhamdulillah ina Haidar!"
Haidar dake zaune a dining ta kalla tace
"Gashi nan."

"Ok bashi wayar."
Mika masa tayi tana fadin
"Ga Abbin naka."

Ya amsa ya kai kunne yace
"Abbi ina kwana?"
"Lafiya lou My son ya kake?"

Ya fada yana jingina da kujera.
"Alhamdulillah Abbi."
"Masha Allah me kake yi?"

"Abbi, Cornflask Ummi ta hada min nake sha."
"Iyyee dan gatan Adda, na kira Ummi mu gaisa tace ta fita."

"Yes Abbi."
Maryam fita tayi daga kitchen din, Aliyu yace
"Ina Addar taka?"

"Ta fita Abbi."
"Ok zan fita yanzu in na dawo zan kiraka kaji."

"To Abbi yaushe zaka dawo."
Dan murmushi yayi yace
"Haidar kenan jiya fa na tafi zan dan jima ban dawo ba, ina son ka maida hankali a school sosai da sosai kaji?"

Kai ya gyada yace
"Insha Allah Abbi."
"That is my good boy Allah maka albarka."

"Amin Abbi."
Yace
"Ok bye ka gaida Inna da Mami."

"To Abbi, bari naje na fada musu."
Ya cire wayar a kunne ya karasa falo inda Maryam ke kwance ya mika mata waya, yana bata yace
"Zanje wajen Inna da Mami Abbi ya aike."

"To agaishe su."
Ya fita da gudu, Maryam ta maida ido ta kwanta.


Yini tayi tana bin waje tana kwanciyya, har Ummi ta dawo yace
"Maryam jikin ne?"

Kai ta girgiza tace
"Bana jin dadin jiki nane."
"Munyi waya da Aliyu likita zai zo ya dubaki yanzu."

"Ummi ni naji sauki fa."
"Daman tinda bakya son magani ba, kuma Allah yazo ya duba sai kinsha magani."

Baki ta turo ta koma ta kwanta kawai, Ummi ta mike ta wuce sama tana fadin
"Ki gama turo bakin ki, dan Aliyu baya nan ba zan zauna dake ina ganin ki, kina ciwo ba."




Flash Back
July 2017
Kano State







*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




*Antty*

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 13

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



~Flash Back~
```July 2017
Kano State```

```*MANS GIRLS COLLAGE* shine sunan dake rubuce a saman wani katon gini wanda aka kwata shi rubutun kan sa abun kalla ne, banda ginin da yake katon gaske wanda ginin mai kyau ne, da tsari dan ba dan an rubuta makaranta ba da ba zakace makaranta bane dan kyau da tsarin ginin, wanda yake da bene har wajen hawa uku. Wanda makarantar tai fice a cikin garin Kano da kewaye duk wani d'an wane wato masu kudi, yan siyasa, da masu mulki, da wanda ke ji da kansa nan ba wai dan tsadar makarantar ba a'ah sai dan yadda makaranta take da manyan kuma kwararrun malamai. Dan malaman duk kan su kwararrun ne kuma suma dan suna samun salary mai kyau shiyasa suke kara zama a wajen duk da wasu suna aikin gwamnati kuma suke kara zuwa suna aiki a wajen.

Da ka shiga babban gate din babban harabar (compound) wanda yake dauke da wajen adana motoci (parking space) an saka masa rumfa an kwawata harabar wajen (compound) da shuke shuke, wanda har wani round about akai a tsakiyar makarantar an rubuta sunan makarantar da manyan baki kuma an kwatashi. Duk ka makarantar an malaleta da kwalta wajen yayi kyau, kato ne sosai dan in anzo ziyara (visiting) din dalibai duk anan ake ajiye motoci (parking) duk yawan mutane wato iyayen yaran da zasu zo wannan harabar (compound) din na dauke su kamar yadda yau yake ma cike da manyan motaci masu kyau, tsada duk ka dai saboda yau dalibai makaranta ake yaye su (graduation) wanda duk iyaye suka zo daukar yaran su.

Ba motar da ta karewa kowa in zai fita duk da wajen ba kowa sai d'ai d'ai kun drivers sauran ma kuwa duk suna cikin mota iyayen kuma suna can cikin makarantar. Wanda bayan wannan harabar (compound) din akwai wani a ciki wanda anan bangaren malamai yake da ajujiwa (classes) din daliban makarantar shima wannan compound din an kwata shi sosai dan har filin (wasanni) sport, Assembly hall, meeting hall, da Special hall wanda anan ake duk manyan taro na yaye dalibai ko speech and price giving day da holidays da sauran abubuwan duk anan suke, wanda iya nan wajen da dalibai suke iya fitowa daga nan sai can cikin makaranta wanda a can ne hotel yake da sauran abubuwan entertainment na makaranta.


To yau special hall ne ya dauka dan yau SS 3 student sukai graduation wanda tin 9:30am suka shiga exam suka fito 12:30pm suna fitowa dukkan dalibai cikin makaranta suka koma suka wanka sukai sallah sannan suka shirya cikin kayan su na graduation. Duk kan su yan mata ne wanda suke daga kan shekara 16, 17, 18 and 19 kuma duk wacce zaka kalla zaka gane yar hutu ce domin in kana *MGC (MANS GIRLS COLLEGE)* tamkar kana gida ne yadda ake kula da kai da komai na rayuwa dan kowa yana da system a hannun sa haka suna da wayoyi amman duk inda takwas na dare yayi an amshe wayoyin su haka nan karfe tara duk dalibai dole su tafi su samu entertainment sunyi kallo na awa daya zuwa awa daya da rabi da sun tashi kowa zai wanka da alwala sannan a kwanta kan sha daya dole kowa yai bacci kuma duk bayan awa daya zuwa daya da rabi Nanin dakin zatana mikewa tana duba lafiyar kowa wanda karfe biyar duk suke tashi suyi wanka suyi alwala sannan su shirya suyi sallah. Kan 6:00am sun gama komai har azkar wanda daga nan dining hall suke tafiya a can kowa zai zabi abinda yake bukata wanda kafin 7:00am an kawowa kowa nasa yai break daga nan su tafi assembly hall minti talatin suke yi ake tafiya aji wanda a ragowar minti talatin din zasuyi kintsa kan a fara class activities at 8:00am wanda karfe 10:30am ake fita tara, shima kowa abinda yake so zai zaba ya amsa, 11:00am ake dawowa 1:30pm ake tashi wanda ana tashi ake sallah daga nan abasu minti talatin dan suje suyi wanka suci abinci sannan su fito isilamiyya. 3:45pm kuma ake sallah sannan su koma sai 5:30pm ake tashi wanda anan kowa ake bashi wayar sa inda abinda zai yi yayi har ai magariba da isha'i a amsa. Haka rayuwar su take daga Litinin zuwa Laraba wanda Alhamis da Juma'a basa isilamiyya suna shiga catering class ne a koya musu girki kala kala wanda Asabar da Lahadi kuma tahfiz suke zuwa tin 7am har 5pm. Hatta uniform wanke musu ake kowa da sunan sa a jiki za a ajiyewa kowa nasa. Kuma basa taba saka kayan gida kullum kayan makaranta suke sakawa (personal wear they always put uniform) wanda suke da na normal school, na Isilamiyya, na catering, na tahfiz, sport, entertainment, da kayan bacci (sleeping dress) duk iri daya sai dai kowa da sunan sa ko kuma yan room kaza su zama on one colour like red, blue, yellow, pink etc

Babu zancen wannan yafi wannan aji ace za a saka wani aiki ko makamantan su duk sun dauki junan su yan uwa bama in dakin ku daya ko hostel din ku daya. A ka'ida tin kana JSS 3 suke saukewa wanda suke walima mai kyau shima iyayen ka zasu zo a bada kyaututuka (gifts) da sauran su. Wanda a SS 3 kuma suke haddace Alkur'anin wanda ba a tashi walima da bada kyauta sai a ranar kammala karatun (graduation) gaba daya anan ake yi.

Shiyasa duk iyaye da yan uwa da abokan iyaye dake wannan makaranta suke jiran wannan ranar domin kuwa rana ce ta farin ciki d'an ka ya haddace Alkur'ani mai girma kuma ya gama karatu wanda ilimin ke da inganci saboda samun kwararun malamai da kulawa da suke sosai.

Karfe 1:30pm Special hall da aka kwata shi da decoration ya cika da iyayen yara maza da mata, wanda a hall din akwai sarakuna na mabambanta garuruwa da yawa ga gwamna da mataimakin sa da wasu kusoshin gwamnati ga manyan malamai da yan kasuwa dukka da iyalan su dan a cikin su kowa da akwai nasa da zai gama makarantar. Yara guda dari ne suka yi graduation da haddar Alkur'ani wanda suke aji guda hudu dan duk aji daya ana saka dalibai ashirin da biyar.

Iyaye ne zaune atsakiyar hall din akan kujeru kowa gaban sa an anjiye masa lemo da ruwa da tissue wanda manyan baki kamar shugaban kasa da gwamna da sarkin garin da Babban malamin garin suke gefe suma gaban su lemo da ruwa ne. Dayan gefen kuma malaman makarantar ne a wajen. Wanda saman benen kuma gefe daya na sauran student dake JS 1 to 3, haka nan SS 1 to 2 wanda a gaban hall din kuma wajen zama ne na dalibai guda 100 din da suka gama makarantar.

Suna zaune daliban suka fara shigowa cikin shigar su ta iri daya wanda kowa ya saka graduation gown a ciki kuma wasu kaya ne iri daya riga three quater da wando red colour sai farin hijab wanda ya sauko kan kirjin su. Sai takalmi cover shoe baki da white socks kowa wuyan sa sakale da tag kowa da matsayin sa kamar headgirl, assitant, prayer, da sauran su.

Suna zama aka fara gudanar da taron kamar yadda aka fara. Wanda Babban malamin dake zaune a gefen Sarki uba ga daya daga cikin daliban shi zai bude taron da addu'a wanda aka kira sunan shi Sheihk Muhammad Jabeer Muhammad. Wanda ya mike cikin shigar sa ta babban malami yayi addu'a sannan ya zauna. Sannan akai national anthem da national plag, Daliban JS 1 aka kira dan suzo suyi barka da zuwa ga iyayen su. Nan suka sauko cikin shiga iri daya wanda kusan kan su daya haka kamar su ma iri daya ake gani suka zo sukai musu barka da zuwa da Hausa da Turanci sannan sukai da Larabci suka koma. Nan aka bada tarihin makarantar da irin nasarar da makarantar ta samu, haka aka dinga gudanar da program din har aka bawa kowa allon sa da certificate na cewar sun haddace Alkur'ani.
Wanda a cikin manyan baki su suka dinga represnting suna bawa yaran wanda yan jarida gidan radio kamar Freedom, Express, Rahma, Dala, Gurantee, Vision, da gidan television na Arewa 24, NTA, ARTV, Farin wata, Tauraruwa da sauran su, suka dinga dauka haka nan photo graphers na makarantar sai aikin su suke yi. Wanda bakin iyaye ya kasa rufuwa kowa murna yake da farin ciki nasarar da yaran su suka samu.

Maryam Muhammad Jabeer 'ya ga Sheikh Muhammad Jabeer Muhammad kenan wanda shine babban malami a jigar Kano babu wanda ya kai shi ilimi, shine sunan da aka kira wacce ita ce head of student wato headgirl, kuma tinda ta fara makarantar tin daga JS 1 har SS 3 ba ai daliba kamar ta ba mai kwazo dan ita ce overall duk section tana fin kowa mark kuma duk gasar da zata shiga sai tayi nasara dan haka ba karamin ji makarantar keyi da ita ba.

Wani Balaraben saurayi ne ya mike da sauri, lokacin da ya hango Maryam tana saukowa dan zuwa inda akai kiran ta. Na kusa dashi ne ya kamo hannun sa, juyowa yai ya kalle sa. Kai ya dan langwabar masa sannan yace
"Haba Aliyu ka zauna mana."

Maryam ya kara kalla sannan ya kuma kallon na kusa dashi sai kuma ya kalli gefen mata yaga Ammi na kallo sa murmushi ya sakar mata sannan ya koma ya zauna. Na kusa dashi da yace ya zauna wanda daga kallo zaka san dan uwa ne ga Maryam saboda yadda suke kama da ita. Shima kyakyawa ne dan na rasa wane jinsi ne shi balaraben ne shi ma ko kuwa bafulatani ne. Muje zuwa dai a sannu zamu san su waye su.

"Aliyu kana rage wannan abun fa!"
Juyowa yayi ya kalle shi sai kuma ya mai da kan sa kan Maryam dake karasawa inda aka kira ta cikin tafiyar ta mai daukar hankali wacce a nutse take yin ta kamar baza ta taka kasa ba, ba yanga take ba sam haka yanayin ta yake a ko da yaushe.

"Daliba mu mai kwazo wacce ta kawo mana cigaba da nasara marar adadi a wannan makarantar, jiha da kasa baki daya, wanda ita taci gasar musabaka da akayi last month wanda ta samu kujerar makkah da umrah, shugaban kasa kuma ya bata kudi har 1 million haka nan a yanzu makarantar nan ta dauki nauyin karatun ta na gaba wanda aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login