Showing 189001 words to 192000 words out of 232912 words

Chapter 64 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1248

su tsakanin ta da aliyu ta wuce tunanin mai tunani.

Mikewa yayi ya zura hannu a aljihu ya bi hanyar da tayi da kallo ya girgiza kai kawai ya juya zai fita yaga Aliyu tsaye fuska ba yabo ba fallasa hannu ya mika masa sukai musabaha ya fice. Ran Aliyu in yayi dubu ya baci, hanyar da ta shiga yabi duk da bai san dakin waye ba amman tabbas sai yaje.

Akan gado ya same ta kwance tana kuka ya shigo ya karasa ya dago ta a fuskace ta kusan yin baya zata fadi ta dafe bango ido ta zaro tana kallon sa fuskar nan a hade ransa a bace yace
"Kina kuka akan aure na ko? Saboda an aura miki wanda bakya so ga wani yazo da zaki iya soyayya da shi ko? To ki sani da aure akan ki, kome zaki ki bari na fara sauwake miki, na fada miki in har bakya so na, bakya son zama dani zan miki abinda kike so amman a yanzu ba zan iya ba sai dai ke ki fadawa iyayen mu cewa bakya so na ni kuma nai miki alkawarin zan tsaya miki har sai kin auri wanda kike so, amman ba haka ne zai sa kina kula wasu da aure na akan ki ba. Ina da kishi akan abun da yake nawa dan haka kada ki kara, kwanaki kinyi dan banyi magana ba shiyasa kika karayi ko to bana so bana so na fada miki. Ina da kishi mai zafi wanda ban taba sanin kaina dashi ba sai a kanki."

Kai ta dafe dan wani irin sara mata yake, ta dago da niyyar magana ya juya a fusace ya bar dakin. Kan gado ta fad'a tana sakin wani irin kuka.

Tun bayan rasuwar Aliyu ta cire rai da sake samun soyayyar wani d'a namiji sai dai kaddarar ta na farko da ya mantar da ita komai wanda ta so Muhammad a yanzu kuma zuciyar ta ta fara rinjayar ta ga Yaa Haidar amman kuma meyasa yake haka? Ta sani ko giyar wake ta sha ba zata ta'ba tinkarar iyayen su da cewar bata son sa ba ko da bata son sa zata zauna dashi a haka balle zuciyar ta, taje ta fada tarkon sonsa, wanda da tana da iko da ta hane ta. Meyasa yaki ya tsaya yaji me yake faruwa zai zo ya fara fad'a.

"Kishin ki yake."
Zuciyar ta, ta fada mata, kai ta hau girgizawa fana fadin
"Ana kishin abinda ake so ne."

"Kika sani ko son ki yake."
Wata zuciyar ta bata amsa. Kai ta hau girgizawa tace
"Never i know matar sa kawai yake so nice Allah ya dauran son sa wanda nasan wahala kawai zan sha wanda nasan wannan wata sabuwar jarabawar ce rayuwa da wanda baya son ka."
Da wadan nan tunanin bacci barawo ya dauke ta bayan ta sha kukan ta ta gama.


Aliyu ma daki ya koma ya fada saman gadon sa yana dafe kan sa da yaji yana masa ciwo saboda fadan da yaje yayi, ya rasa meyasa yake jin kishin ta meyasa bai son kowa ya tunkare ta.
"Saboda igiyar dake kan ta."
Kai ya girgiza yana fadin
"A da da ba igiyar tawa fa?"

Ido ya lumshe take fuskar ta ta bayyana a cikin idon sa, wanda yana kallon fuskar ta wacce yanzu ya baro ta take cike da rudani, tsaki ya saki yana fadin
"Allah kai ka dauran son wannan yarinyar Allah ka dauran dangana da hakuri akan lamuran ta, Allah kada kasa ta wahal dani, Allah kada kasa ta amshi shawara ta wajen zuwa ga iyayen mu tace bata so na da yaya zanyi da alkawarin da nai mata."

Haka ya dinga juyi da tunanin mafita da kyar bacci ya dauke shi cike da tunanin Matar sa.


*
Kwana ta biyu rabon da ta ganshi shi wanda har komawa sashen su Inna tayi amman ina ba Aliyu ta shiga damuwa gashi in ta tafi kamar ta kira sa sai ta fasa, ganin bata da mafita yasa ta hana Haidar fita kwana d'aya tal ba inda yaje wanda abun ya damu Aliyu dan daman tare suke yini da Haidar shine dauke shi su fita yau da bai zo ba kadai duk ya damu haka ya shigo gidan da rabon sa dashi tinda ya shiga ya mata fada sai yau, bangaren su Inna yaje babu shi ba alamar sa ya jima har ya tambaya suka ce bai shigo ba haka yaje bangaren Ammi ita kadai a falo suka zauna suna dan ta'ba hira a siyasance yake tambayar Ammi Haidar danya fara tunanin ko bai da lafiya amman batace komai ba dan ita bata san yau bai fitan ba. Maryam kuwa ta rike shi a daki ta cika masa gaba da kayan wasa dana ciye-ciye.

Har dare ba Haidar hankalin Aliyu ya tashi, yana son ya kira Maryam kuma baya so duk da ya damu da rashin ganin ta koyaya ne. Fara neman layin ta yayi tana shiga ba a jima ba aka dauka yanajin tana sallama yai shiru kawai, ganin ko baya jin tane, ta kashe, kara kira yayi ya kara shiru bayan ta kashe yai murmushi ya fara rubuta mata sako.

Gaban ta ne ya fadi lokacin da taga sakon
_Idan Haidar baiyi bacci ba ki hadani da shi, ba muryar ki na kira na ji ba ai kin sani amman kin tsaya sai Hello kike._

Wani dan murmushi ne ya subuce mata, sai ta dan saki tsaki tana cije lebe, baya minti uku sai ga kiran nasa nan, Haidar ta bawa tace
"Ga Abbi nan."

Ta shiga bandaki tai wanka har ta fito waya suke, shirin kwanciyya tayi ta zo ta amshi wayar duk da basu gama ba ta saka a kunnen ta dan murya sa kawai take so taji ko ta samu nutsuwa.
"Hello, Hello, Haidar."

Ya fada cikin sanyin muryar sa mai dadin sauraro, ido a lumshe tana sauke wata ajiyar zuciya da tasa ya gane wayar na wajen ko wanene, ido ya lumshe ya bude a hankali. murmushi yayi kamar tana kallonsa kawai ya kashe wayar.

Shi kadai yace
"Me hakan yake nufi?"
Zuciyar sa tace
"Itama tana son ka."

Kai ya girgiza yace
"Anya kuwa kar na yaudari kai na. Amman zan gwada na gani."
Shi kadai yake maganar murmushi dauke akan fuskar sa.


*
Ahmad zata yayi Maryam ta'ki tsayawa ne dan ya kawo mata maganar soyayya wanda shi shaidane in aka ce Maryam zata amshi wani bayan Aliyu zai ce karya ne amman ba komai zai cigaba shi ko bata so shi ba ta yadda suyi aure wanda a sannu zai koya mata sonsa. Ya sani Maryam zata iya cewa ba zata kara aure ba wanda shi aure wani babban jigo ne a rayuwa, auren shine mutuncin ta shi ba cewa yayi ta daina son Aliyu ko ta cire shi a rai ba in yai mata haka ma bai mata adalci ba sam, ya sani a yanzu ba zata gane me yake nufi ba amman zai bata lokaci tai tunani zai je ya samu iyayen sa da suke so yai aure cewar su fara shiri domin matar sa ta dawo.

Da wannan ya tafi yana mai kara son Maryam na riko da alkawari da har bayan ran Aliyu ta kasa bawa wani soyayyar ta.


*
Kwance take a daki Haidar kwance akan ta sai damun ta yake dan bata cikin mood din ta, ganin taki ta kula sa yasa ya mike ya farai mata kuka ta mike tace
"Wai menene Habiby?"
"Adda ki taso mu fita."

"Dan Allah ka kyale ni tashi ni kaje ai duk ni na janyo da na hanaka fita."
Kuka ya fara yana dira kafa shi lallai sai tare zasu fita, ganin yana kuka yasa ta mike dan su fito ko wajen Ammi ne daga nan ta samu ya tafi wajen su Sitti, ta mike ya sauka yace
"Adda ki goyani."

Kallon sa tayi tace
"Ai ka wuce goyo Habibty sai dai kai ka goyani."
"Yes Adda zo in goya ki."
Ya juya mata baya, daukar sa tayi tana fadin
"Tayaya zaka goyanin."

Yana dariya yace
"Adda zan iya fa."
Suka shiga falon tana murmushi tace
"Iyye yarona jarumi zai goya Addar sa."

Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su sauka akan sa. Shadda ce ruwan madara a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a lokacin ba, Haidar ya dire a jikin ta ya karasa wajen Yaa Aliyu yana fadin
"Oyoyo Abbi."

Ya rumgume shi yace
"My son ya kake?"
Ammi dake zaune sai murmushi take, Maryam ta zauna a gefen Ammi kan ta a kasa tana satar kallon sa tace
"Ina yini?"

"Lafiya lou ya kuke?"
"Alhamdulillah."

Ta daura kan ta a kafadar Ammi, Ammi ta mike ta bar wajen ya rage daga Aliyu sai ita da Haidar. Gaba daya Aliyu ya bawa Haidar hankalin sa sai hira suke tana zaune tana kallon su, can sai ga Aisha nan tai sallama mikewa tayi tana murmushi hadi da fadin
"Maman biyu."

Ta karaso sai ga Rukayya a bayan ta, a guje suka karasa suka rumgume juna, wanda Aliyu da Yaa Alkasim suka tsaya kallon su, daga murna kuma sai kuka aka rasa mai lallashin kowa dan har Aishan ma kuka take.

Yaa Aliyu ne yai karfin halin fadin
"To menene abun kuka, komai da ya faru ga bawa kaddarar sa ce ku godewa Allah ku bar kukan nan."
Yai maganar cikin sanyin murya wanda gaba dayan su sukai dif, sai hawaye zubowa yace
"Kukan ba abinda zai kara muku bashi da amfani kunji."

Kai duk suka gyada, Yaa Alkasim ya shigo yana fadin
"Ai basu da aiki sai kuka."
Ya zauna suna dada gaisawa da Yaa Aliyu.

Rukayya ta gaishe da Yaa Aliyu, Aisha ma haka sannan suka mike suka shige dakin Maryam. Acan aka bude babin hira wani ai kuka wani jimami wani kuma ai dariya har akai magariba sai kiran sallah sukaji duk suka mike sukai sallah.



Washe gari
Da dare suna daki suna hira Yaa Ahmad ya kira wayar ta bayan ta dauka yace
"Ina waje kizo muyi wata magana."
"Yaa......"

"Ki fito kawai."
Ya fada yana katse ta ba yadda zatai ta mike fuska cike da damuwa kamar zatai kuka. Rukky tace
"Ya dai?"

"Yaa Ahmad ne."
"Abokin Yaa Haidar ko? Daman yana nan?"

"Taso muje."
"Ku barni ni kadai nima bari naje wajen su Ummi."
Aisha ta mike da katon cikin ta, Maryam tace
"Sannu maman biyu."

Sukai dariya, Aisha tace
"Zan rama ne."
Suka fice Aisha ta gaisa da Yaa Ahmad, Maryam da Rukky suka fito, kanta a kasa ta karaso Rukky ta gaishe dashi ya amsa yana fadin
"Rukky kwana yawa ko a bikin Aisha bamu hadu ba duk kun girma wallahi."

Tana murmushi tace
"Kaji ka Yaa Ahmad kai ma ai ka girman."
Ido ya zaro yana kallom Maryam yace
"Kina jin ta ko? Wai na girma da yaya nake?"

Duk sukai dariya, a dai dai wannan lokacin Yaa Aliyu ya shigo gidan da motar Yaa Alkasim, Haidar na gefen sa, yana shigowa ya hango Maryam da Yaa Ahmad suna dariya ransa in yai dubu ya baci, tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa.

Maryam ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Sai taji ta tsani kanta da har tayi abinda zai bata masa rai, meyasa ba zata gujewa bacin ransa ba, dan me bayan a yanzu bata da wandan zata farantawa bayan shi, dama bata fito ba abinda take ta tunani kenan. Amman kuma dole ta fito ko dan ta sanar da Yaa Ahmad tana da aure ko ya hakura ya kyale ta.

Daga Rukky har Ahmad sun kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Maryam haka ma Rukky dan taga gaba daya hankalin Maryam na wajen.
******



*Allah mana rahma ya jikan mu. Amin*


*Antty*
[12/6, 13:31] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 77

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ido ya lumshe zuciyar sa kamar zata fito dan bacin rai, baya so ya fito yayi abinda ba dai dai ba shiyasa ya fara ambaton Allah a cikin zuciyar sa, a hankali yaji bacin ran ya ragu sannan ya bude kofar ya sanyo kafar sa, farar kafar sa dake cikin brown kalar takalmin ce ta fara bayyana sannan ya fito gaba dayan sa, sanye yake da milk din shadda tai masa kyau kan sa sanye da hula brown kala yai kyau sai tashin kamshi yake yi, zagayawa yai inda Haidar yake ya bude masa ya fito ya dauke shi tare da daukar ledar da yayo masa siyayya.

Tin da ta daura ido akan sa taji bugun zuciyarta ya tsananta, a haka ya fara tinkaro su, yana tunkaro su kamshin turaren sa na kara musu sallama wanda ya kashewa Maryam jiki, so yai ya wuce amman kuma sai ya fasa ya karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Ahmad hannu yayi masa sallama.

Ahmad ya karbi hannun shima cikin fara'a suka gaisa sai kuma suka kalli Maryam. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya.

Da kyar ta saita kanta tace "Yaa Ahmad wannan shine Yaa Aliyu, wanda yake a matsayin miji na a yanzu."
Dif haka gaban Yaa Ahmad ya buga, bata lura ba ta nuna Yaa Ahmad da yatsa tace
"Wannan shine Yaa Ahmad abokin Yaa Aliyu ne sosai."

Duk halin da Ahmad ya shiga bai hana sa kara mikawa Yaa Aliyu hannun ba yana murmushi, tace
"Ummin sa ita ta tsince ni a wajen su nai rayuwa na tsawon shakara bakwai ban san kowa ba sai su, sun rike ni tamkar 'yar cikin su basu taba kyama ta ba wanda suka fifitani a fiye da ya'yan su a karshe suka aura min shi a matsayin miji na, Haidar bai taba sanin wani a matsayin Abbin sa ba sai shi, saboda yadda ya kula dashi sosai fiye da yadda na bashi kulawa Yaa Haidar ya bashi."

Ji yai abinda ke ransa ya fara yayewa haka ma Yaa Aliyu, dan haka Ahmad ya kara rike hannun Aliyu yana fadin
"Masha Allah, muna godiya Allah ya saka da alkhairi ya bada lada. Gaskiya kunyi abinda ba kowa zai ba kun cancani komai a rayuwar Maryam Allah ya saka da mafificin alheri ya biya ku da gidan aljanna."

Murmushi Yaa Aliyu yayi kawai ya saki hannun sa, yace
"Bari na shigar da Haidar yayi bacci."
Yai ciki Maryam tabi bayan sa dan ta amshe shi, amman yana shiga sai ya nufi dakin ta kamar ta juya sai tabi bayan su, tana shiga yana ajiye Aliyu akan gado.

"Sannu."
Ta fada dan tasan zai iya barin ta ba tare da yace mata komai ba, dagowa yai ya wulla mata wani kallo yace
"Maryam wallahi ina da kishi sosai. Kada ki bari na kara ganinki da wani namiji tsaye da ba muharamin ki ba. Na fada miki in bakya son auren mu kije ki sanar da iyayen mu ni na miki alkawari zan fahimtar da su."

Kai ta sunkuyar tana jin furucinsa kamar yana caka mata wuka a cikin zuciyar ta wai ta fada bata son sa zai shige mata gaba. Jin yayi tana sheshekar kuka abinda yafi tsana kenan kuma ace matar da yake so ita ke kuka shi ya bata mata rai ko har ya juya mata baya sai ya juyo ya karaso hannun sa ya saka ya dago habar ta, ido suka hada da sauri ya saki habar ta ya janyo ta jikin sa ya rumgume yana shafa bayan ta a hankali wanda jin ta a jikin sa yasa ya fara jin wani yanayi, abinda ya gani a cikin idon ta yake so ya gaskata, shin da gaske ne son sa yake gani a cikin idanun Maryam ko kuwa gizo abin yake masa, a hankali ya matsar da bakin sa saitin kunnen ta yana fadin
"To ya isa menene na kuka?"
"Ni ka daina cewa bana son ka Yaya."

"To kina son nawa ne?"
Shiru tayi yace
"Uhmm gashi nan, na sani bakya so na auren dole akai miki, duk da haka kina da chance na sanar da iyayen mu i will do you what u want and i will support you kinji."

Jikin ta ta janye dan da gaske maganar sa bata mata rai take cikin murya kuka take fadin
"Ko da bana son ka ba zan taba fadawa iyaye na ba, ko da bana son ka nayi alkawarin zama dakai na har abada, ko da ba zaka na kallo na a matsayin mata ba zan kasance a matsayin kanwar ka, amman ka daina cewa bana son ka, kun min abinda ba zan ta'ba kin ku ba, kun dauken a lokacin da baku san ko ni wacece ba, baku kyamacen ba har kuka fifitani a cikin yan uwan ku, a karshe aka aure min kai Yaya meyasa zan 'ki ka, wane aibu ne da kai da zan ki ka, bayan ni tin baku san wacece niba kuka soni kuka kaunacen Yaya in nace bana son ka nayi karya a duniya daga iyaye na a yanzu sai Ummi da kai nafi so da kauna."

A hankali ya tako gaban ta yace
"Wannan kaunar ta hallacin da mukai miki ce Maryam ba 'kauna ta auratayya kike min ba."
"Menene bambamcin ta, tinda duk 'kauna ce Yaya?"
Matsowa yayi dab da ita ya dago kanta yace
" 'Kauna da soyayya da sha'awa kuma wacce ita zata bamu damar sanin sirrin juna."

Ido tai saurin runtsewa jin yadda yake yawo dan idonsa a cikin nata, hannun sa dake rike da kanta ya saka yana shafa gefen fuskar ta wanda hakan ya fara haifar mata da wani iri a jikin ta so take ta kwace amman ta kasa, ta janye jiki ta juya zata bar dakin cikin zafin nama ya kamo hannun ta ya janyo ta da karfi ta fado jikin sa, hannun sa ya sa ya zagaye ta dan yasan yanzu zata ce zata gudu, ganin ba zata iya kwacewa ba yasa tayi kasa da kanta yace
"Kunyar kuma fa?"

Kai ta girgiza ya dago kanta wanda hakan yasa tai saurin runtsa idon ta ya saki murmushi yana fadin
"Ni dai dan Allah ki daina tsayawa da ko wanne namiji wallai baki ji yadda nake ji ba."

Kai ta gyada yace
"Ki min magana ba gyada kai ba."
"To Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login