Showing 15001 words to 18000 words out of 232912 words
Chapter 6 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
su a haka a cikin mota ta same su ta zaune suka dauki hanya, suna zuwa suka shiga bata da abinda zasu dauka turare da mai ta dauka kawai sai chocolate da wasu ribom da ta gani, lokacin da a kaje biyan kudi Aliyu ya dinga mamaki dan abinda zata dauka baki ya tabe dan ya fara gajiya ace in ba shi ya dibar mata abu ba ita daga turare shikenan, gaba tayi dan ta riga su gaba tana tsaye jikin mota tana danne danne a wayar ta kamar ance ta ta dago taga wani tsaye jikin motarsa ya rungume hannu yana kallon saitinta ta cikin black glasses dake idonsa, mamaki ta fara shin ita yake kallo ko kuwa, baki ta tabe ta cigaba da abinda take dagowar da zatai taga ita yake kalla sosai, tunani ta tafiyi can ta dago sai taga ya cire glass din idonsa yana cigaba da kallonta da kyau, murmushi ta saki tunawa da a inda ta sanshi, dai dai kuma karasowar Aliyu ya bude booth aka saka kaya sannan ya juyo ganin bata shiga ba, wanda a lokacin ta daga kai tana kallon mutumin Aliyu yabi wajen da take bi da kallo wani abu yaji ya tokare shi ya karasa wajen ta yace
"Kinsan shine?"
Kai ta girgza da sauri ta bude mota ta shiga, ta dago tana kara kallon mutumin da bai fasa kallonta ba, Aliyu ya lura dan har yai reservse mutumin take kalla dan haka a guje yaja motar suka fice daga wajen.
Washe gari lahadi tin da tatashi taji yanayin jikin ta ya sauya, calendar ta duba ta zaro ido tana fadin
"Watakila gobe."
Gaban mudubi ta koma ta janyo tana dubawa ledar pad dinta, ta dauko taga saura daya komawa tai ta zauna sai kuma ta mike ta sauka kasa wajen Ummi zama tayi a kusa da ita tace
"Ummi ina son zan je supermarket in siya pad"
Ummi ta kalleta tace
"Naga jiya kuka je."
"Ummi na manta ban dauka ba."
Wanda fada kawai tayi dan in har da Aliyu zasu shopping kunyar dauka take a gaban sa wani lokacin ne ma shi da kan sa in zai karayo mata siyayya yake hadowa da ita to gashi tana tsammanin gobe yazo dole taje ta nemo ta kan yazo mata.
"Toh driver ya fita wa zai kaiki tinda ke kin ki, ki koyi mota ma."
"Ummi zani da kai na, kuma Yaa Farouk yace da munyi hutu zai koyan."
"Ya dai kamata Baba Anas ma ya huta da fitar safe ai."
Maryam ta mike tace
"Bana so magariba tayi min bari naje na shirya."
Ta haye sama, siket ne da t-shirt a jikin ta dan haka ta dauki katon hijab ta zura wanda ya saukar mata har kasa, sannan ta dauki purse da wayar ta ta fita, Ummi ta sama a falo tace
"Ummi na fito."
Waya ta dauka tai danne danne wanda wayar Maryam yai kara tace
"To sai kin dawo."
Maryam ta duba taga 5k Ummi ta tura mata ta rumgume ta tace
"Nagode Ummi."
Tunda Maryam ta fito Yaa Farouk dake jikin motar sa fita zai yi ko dawowa yayi oho dai yake hangen ta murmushi yake ta saki, ta nufo gate bama ta lura dashi ba lokacin Mama ta fito zata sashen Inna, Maryam ta durkusa tace
"Ina yini?"
Ko kallon ta batai ba ta wuce mikewa tai tana murmushi ta karaso gate Yaa Farouk dake tsaye yace
"Ina zaki?"
Ba yadda zatayi tai murnushi tace
"Super market."
"Ke kadai kuma?"
"Kai Yaya zan iya ai."
"A'ah ni ban yadda ba ina Baba Anas?"
"Baya nan Ummi ta aike shi."
"A'ah ai kuwa ba zaki fita ke kadai ba bana son."
"Kai Yaya sai kace wata yarinya."
"Ita ce mana."
"Ni din?"
Yai murmushi zai magana kenan yaji Mama tana kiran sa
"Farouk."
Da sauri ya juya, ya karasa tace
"Me kake anan?"
"Daman zan anjiye ta ne."
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/23, 14:06] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 5
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
This page is for you *Momy* Hajiya Nafisa Allah ya kara lafiya da nisan kwana, Allah ya raya zuri'a yasa kiyi kyakyawan karshe Allah kara budi da wadata, Allah kara rufa miki asiri duniya da lahira amin
Yai murmushi zai magana kenan yaji Mama tana kiran sa
"Farouk."
Da sauri ya juya, ya karasa tace
"Me kake anan?"
"Daman zan anjiye ta ne."
"Ban yadda ba."
Ta fada ta wuce su, ya karaso yana ya'ke yace
"Sis Mama tace zan kai ta unguwa, kuma ba hanya daya bane da na ajiye ki mun wuce."
"Ah haba ba komai Yaya nagode."
Ta nufi bakin gate yace
"To ai kya bari na samo Malam Bala driver ya kai ki ko?"
"Dan Allah Yaya kada ka damu yau so nake na fita ni kadai, yanzu Ummi ma take magana akan koyar driving nace kace zaka koyan gwara ka koyan kaga da sai dai na dauki mota kawai na fice."
"Haka ne bari na baki kudin mota."
Kai ta girgiza tace
"A'ah Ummi ta bani."
Ya zaro kudi ya mika mata yace
"Na Ummi da ban na Yaya daban."
Amsa tayi tace
"To Yaya nagoge."
Ta juya sai ga Baba Anas nan Yaa Farouk yace
"Yauwah."
Ta juyo tace
"Ni dai na tafi."
Baba Anas ya fito yace
"Ba dai fita zakiyi ba Hajiya?"
"Baba 'yarka dai."
"To 'ya ina zuwa?"
"Unguwa."
"Bari na kawai Hajiya sai nazo na kai ki."
"A'ah da ka barshi."
Farouk ne ya kalle ta yace
"Wai kin taba fita ke daya ma tukkuna."
"Kaji ka Yaa Farouk da wata magana."
"To ai naga kullum driver ke fita dake."
"Shiyasa nake so in fara yau, kan na fara driving ko?"
"No tinda ya dawo ki hakura kawai."
"Ya zanyi da Yaa Farouk ka zama kamar me?"
Yai murmushi Baba Anas ya dawo ta shiga suka bar wajen. wani karamin super market ta gani tace
"Baba mu tsaya anan ma."
Ya karasa yai parking ta fito tana kallon wajen, kamar ance ya waigo ya hange ta ta fito a mota wannan yasa ya karaso shima yai parking motar sa, ciki ta shiga ya fito yabi bayan ta, tana shiga tayi wajen turarurruka, wani turare da ta dade tana nema ta gani ta dauka tana mai jin dadi dan taji dadin sa lokacin da Yaa Aliyu ya siyo mata duk lokacin da sukaje shopping sai ta duba sai dai bata sake ganin sa ba sai yau, tama dauka ta tafi bangaren su pad, ta durkusa ta dauki Virony da Moppid mai talatin da uku uku, tana cikin duba jikin su dagowar da zatayi suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa don rass ta ganesa, da sauri ta juya tare da ajiye pads din hannunta, kin juyowa tayi har ya iso kusa da ita kallonta yake daga cikin bakin spec dake idonsa, duk da ta juya masa baya tana jin kallon da yake mata, tafiya ta farayi kawai sai taji wannan muryar tasa mai dadi yai mata sallama
"Assalamu alaikum"
Wani iri taji ta amsa a hankali ido ta runtse jin kamshin turaren sa, wanda ya kashe mata jiki, ya zagayo gabanta, yace
"Ya kika?"
Ba tare da ta kallesa ba ta
"Ina yini?"
A kunyace. Yai murmushi yace
"Ya exam?"
Shiru tayi sai ya kara murmushi yace
"Oh baki gane ni ba?"
Dagowa tai ta dan kalle shi yace
"Ko da yake tin jiya nasan kin gane ni ma."
Ji tayi ya gundure ta to me zatai masa daga ya taimaka mata sai yana bibiyar ta ko dai aljanni ne.
"Ni ba aljani bane kawai dai Allah ya hada mu da farko, sai jiya na ganki yanzu ma zan shige na ganki nace bari nazo naji ya exam?"
"Alhamdulillah."
Ta fada ta juya ta fara tafiya, Pad din da ta ajiye ya dauka yabi bayan ta har ya kamo ta ya kama basket din ta da sauri ta sakar masa ya saka pad din ya mika mata, kai tayi kasa dashi yace
"Ko kin gama?"
Amsa tayi tai ciki da sauri tana kara dube dube tanayi tana waigowa ganin bata ganshi ba yasa ta saki jikin ta, ta cigaba da shopping dinta bayan ta gama tayo wajen counter dan biyan kudin ta ta ganshi tsaye a gefe, fuska ta hade ta karasa ta mika kayan aka lissafa ana fadar kudin zata mika atm din ta, taga ya mika nasa kan tai magana har ya saka pin, suka zuba mata a leda kan ta juyo har ya fice daga wajen
"Innalillahi wainna illahir rajiun."
Ta fada dan ita bata son wani abu ya hada ta da maza sam tana fitowa ta ganshi a tsaye kai ta dauke ya nufi motar su ya karasa yace
"Kin fito?"
Kai ta gyada kawai yai murmushi yace
"Toh muje in ajiye ki a gida?" Kamar jira take tace
"Nooo da da driver muke."
Daga haka ta nufi motar su, Baba Anas na ganin ta ya karasa ya bude dai dai karasowar Mutumin ya karasa tare da bawa Baba hannu suka gaisa. Baba da ya gane shi yace
"Kai ne?"
"Nine Baba ya aiki?"
"Alhamdulillah! Ga fa mutuniyar a ciki."
Kallon motar yayi yana murmushin sa mai kara masa kyau yace
"Ita na gano nace bari nazo mu gaisa"
"Amman ka kyauta."
Baba ya leka yace
" 'ya ga mutumin nan."
Ya bude mota ta dago ta kalle shi, fuska ba yabo ba fallasa tace
"Ina yini?"
"Lafiya ya makarantar?"
"Lafiya." Ta kalli Baba tace
"Muje ko?"
"To Hajiya."
Ya dago ya kalli Mutumin yace "Sai anjima."
Mutumin yace
"To ku gaida gida."
Baba ya shiga ya tayar da motar suka fara tafiya juyowa tai taga yana tsaye yana kallon su, har sukai nisa yana tsaye kai ta dauke tana mai sauke ajiyar zuciya, godiya tai da Allah da yasa da driver suka fito da ace ita kadai ce da bata san ya zatai ba da gaskiya Yaa Farouk da yace sai tazo da driver ita kanta ba zatana fita babu wani ba tagane tsaro ne a tare da ita. A haka suka karasa gida ta fita a motar tai cikin gida.
Aliyu ta sama a falo tin da ta shigo yake bin ledar hannun ta da kallo, ta gaishe shi bai amsa ba sai kallon ta da yake har ta wuce sama yace
"Daga ina take?"
Ya tambayi Ummi bayan ta haye sama, Ummi tace
"Super market taje."
"Super market tayi ne?"
"Tace ta manta jiya bata siyo wani abu ba."
"Wa ya kai ta?"
"Ita kadai ta tafi."
"Saboda me?"
"Saboda Baba Anas baya nan."
"Amman ai da sai ta fada min, Ummi ki daina barin ta tana fita ita kadai fa."
"To shikenan."
Ya mike yai dakin sa, kwanciyya yayi yana tunani tare da lumshe idon sa.
**
Washe gari bayan Isha'i Maryam ta taho daga bangaren Inna da taje gaishe ta dan kwana biyu basa haduwa saboda makaranta a hanya ta hadu da Yaa Farouk zai je sashen Inna, gaisheshi tayi ya amsa yana kallon ta, tai kasa da kai, ya saki murmushin sa mai kyau yace
"Jiya ban ganki ba da kika dawo daga shopping."
"Ban ga motar ka ba da na dawo."
Kai ya gyada yace
"Yes na fita unguwar, to ina tsaraban shopping dina ne?"
Ta dan fiddo da ido waje tace
"To ai baka ce in siyo maka wani abu ba."
"Oh sai nace ki siyon to ke me kika siyo."
"Turare ne da...."
Sai tayi shiru yana murmushi yace
"Turare da me?"
"Shikenan."
Ta fada tana kau da kai daga inda yake yai murmushi yace
"Nasan ba daya kika siyo ba sai ki ban wani a ciki."
"Na matan?"
Tai tambayar da mamaki, ya gyada kai yace
"Eh na matan menene a ciki sai dai in ba zaki bani ba."
"A'ah zan baka, muje na dauko maka."
Ta fada tana yin gaba suna zuwa kofar part din su ya tsaya yace
'Ina jiran ki."
"Ah Yaya ka shigo mana."
Kai ya girgiza yace
"Je ki kawon sauri nake."
Ta juya ta shiga taje ta dauko masa guda daya a wanda ta siyo ta taho, ta same shi yana tsaye yana waya yana jin ta ya katse wayar yana juyowa tace
"Kai da Anty nane ko?"
"Wacce Antyn taki?"
"Yaya ka dai ki ka hadani da Anty na."
"Kece Antyn kanki ai."
Baki ta turo tace
"Ya dai kamata kuyi mana sabbin Aunties."
Ta mika masa turaren ya amsa ya bude kamshin ya shaka ya lumshe ido yana budewa da sauri yace
"Amman akwai dadi wa ya nuna miki shi?"
"Yaya shi ya fara siyon shi na jima ina neman sa da kyar yau na samu."
"Kuma kika bani."
"Na siyi guda uku ai kaga na baka daya sauran biyu."
"To nagode sosai."
Tai murmushi yace
"Bari naje."
"Sai da safe."
Ta fada ya juya, itama juyawa tai sai taga Aliyu tsaye bakin kofa, kai tayi kasa dashi ta wuce, ta gefen Ido Aliyu ya kalleta daga inda yake amman ba zakace yana kallon nata bama.
Yau Asabar ba makaranta tin safe take fama da ciwon kai sam bata fito ba, wannan yasa Ummi ta nufi dakin nata a kwance ta same ta ta zauna tace "Yau bacci kike sha?"
Dagowa tayi taga yadda idon ta yai jajir wannan yasa tace
"Subhnallah me yake damun ki?"
Kai ta nuna mata, Ummi tace
"Bari ki ci abinci sai kisha ko paracetamol ne."
Ummi ta fada ta fice bata jima ba ta dawo da dankali da tea da kyar Maryam ta sha ta koma ta kwanta sai bacci, Ummi ta fita bayan mintina ta dawo ta same ta tana kwance idon ta biyu, Ummi ta zauna tace
"Kinsha maganin kuwa?"
"A'ah Ummi."
"Saboda me to?"
Kamar zatai kuka tace
"Ummi kinsan tsaya min yake a wuya."
"A'ah tashi ki sha magani kinji."
"Ummi..."
Ta kira sunan ta. Spoon Ummi ta dauko ta dama mata maganin ta mike ta bata, ta shanye sannan ta kora da ruwa."
Fuska ta dinga batawa ta koma ta kwanta a haka wani baccin ya kuma dauke ta, har yamma abinda take fama dashi kenan, ganin bata son ta kara kwanciyya yamma tayi yasa ta mike ta sauka kasa, a kitchen ta jiyo Ummi ta karasa tace
"Ummi bari naje wajen Inna."
"To ya kan?"
Da sauki ta fada tana fita, sashen Inna ta shiga da sallama Inna dake kitchen tana yan soye soyen ta ta fito kwance ta ga Maryam ta karaso tace
"Lafiya?"
"Kaina ke ciwo ne."
"Kinsha magani?"
Kai ta gyada Inna tace
"To bari naje a karasa soyar can na fito."
Ta koma, Maryam ma ido ta rufe daga haka bacci ya dauke ta. Wajen shida saura ya shigo dakin da sallama Ummi ta amsa ya zauna ya gaishe da ita, shiru yai yana nazari yasan yau weekend suna tare da Maryam to tana ina da kamar ba zai magana ba sai kuma ya daure yace
"Tana ina?"
Ya fada yana nufar dakin sa, Ummi tace
"Taje sashen Inna bata jin dadi ma."
Juyowa yai da sauri sai kuma ya wayance yace
"Me yake damun ta?"
"Kasan ai ita ciwon kai dai ciwon kai."
"To Allah sauwake."
Ya shiga dakin sa, jakar sa ya ajiye sai kuma ya juyo ya fito da sauri ya fice da kallo Ummi ta bishi.
Bangaren Inna ya shiga ya bude kofar falon yai sallama ya shigo dakin Innan tsaye yayi yana kallon Maryam dake bacci amman daga fuskar ta zaka sam bata jin dadi, dan tayi ja, karasawa yai wajen kujerar ya durkusa yana son daura hannu yaji zafin jikin ta amma kuma ya kasa, Inna ce ta fito tana goge hannu dan ta gama wanke wanke kenan tace
"Ya kan."
Ganin Aliyu a gaban tace
"Lafiya?"
Ido Maryam ta bude sukai ido hudu da Aliyu da sauri ya mike yace
"Me yake damun ki?"
Kai ta girgiza kamar zatai kuka dan tasan yanzu zai sata shan magani, Inna tace
"Kan tane yake ciwo amman ai tasha magani."
Juyawa yai ya fita Maryam ta mike tace
"Inna yanzu zai lodan magani."
Inna tace
"Kyale shi kar ki sha shi ai haka yake sai ya lodawa mutane magani."
Ta mike ta jingina da kujera Inna tace
"Kinci abinci?"
Kai ta girgiza tace
"Na koshi."
"Ai ita Aisha sam bata iya jinya ba ace haka zata barki ai sai tayi miki ko dan kunu ne kisha bari ina da ragowar na miki sannu kinji."
Ta koma kitchen kiran Sallah akai Maryam ta mike tai alwala tazo ta tada sallah zama tayi tana addu'a bayan ta idar Inna ma ta fito daga daki ta koma wajen kunun ta dama ta zuba mata suga kadan sannan tazo ta ajiye mata tace
"Daure ki sha kinji."
Dauka tayi tana saisaita shi sannan ta fara sha, Yaa Farouk ne ya shigo dakin da sallama. Sanye yake da ash kalar rga da bakin wando, sai silver agogo, sai kamshin turare take, zama yayi ya gaishe da Inna sannan Maryam ta gaishe shi ido ya kure ta da shi can yace
"Me yake damunki?"
"Batajin dadi ne."
"Ayya kinsha magani."
"To mutum zai rasa shan magani bai da lafiya?"
Inna ta fada. Murmushi yayi yace
"Ai ke Inna bakya son magani kuma koyawa duk wanda yake tare da ke kike."
"Gidan ku, nace gidan ku nice bana son magani?"
Yai dariya yace
"To so kike? Naga har kuka kike kan ki sha."
Maryam tai dariya yace
"Kema ai Ummi ta fadan bakya so har kukan kike."
Baki ta turo tace
"Kai Yaya."
"Eh ya kan naki?"
"Da sauki."
"Allah sauwake."
"Amin."
Ya kalli Inna yace
"Inna me zan samu?"
Tace
"Tinda Barira ce ta kawon ai sai na baka."
"A'ah amman ai Abba ne ya kawo miki."
"Baice na baka ba in yace na baka na baka kuma ba Suleiman din ne ya kawon abinda nayi yau ba da zakai min gori shehu ne ya kawon."
*
Aliyu yayi zarya a sama sau nawa yana tambayar Ummi ina Maryam sai tace bata dawo ba sai yayi kamar yaje sashen Inna sai ya fasa wajen karfe tara ya shiga wajen Inna ya samu, Farouk, Inna da Maryam suna ta hira zama yai fuska ba walwala, duk bayan mintuna sai ya duba agogo ganin har tara darabi tayi ya mike yana kallon Farouk yace
"Dare yayi kaje ka kwanta."
Agogo ya kalla yace
"Yaya bacci yanzu."
Inna ya kalla yace
"Ke dai ki kwanta dan ana hira kina gyangyyadi."
"A ina nayi gyangyandin kai Ali kaji tsoron Allah."
Ya mike yace
"Ni dai nace a kwanta."
Farouk ya mike yace
"Inna bari na tafi sai da safe."
Maryam ta mike tace
"Bari na bika."
Ya kalle ta yace
"Ai na zata anan zaki kwana."
"A'ah."
Taiwa Inna sallama ta fita, ba wanda yai magana har suka karasa gate din su Maryam suka shiga sai da ta kusa kofa ya tsaya yace
"Sai da safe."
Ta juyo ta daga masa hannu, yai murmushi yana kallonta yace "Good night"
"Sweet dreams."
Ta bashi amsa ya juya ita kuma ta shige, A bakin gate ya hadu da Aliyu yace
"Sai da safe Yaya."
"Allah tashe mu lafiya."
Ya rufe ya nufi ciki a matattakala ya hange ta yace
"Zo nan."
Juyowa tayi ta nuna kan ta sannam tace
"Ni?"
"A'ah ni."
Ya wuce dakin sa, fuska ta bata ta sauko tabi bayan sa akan kujera ta ganshi zaune ta