Showing 27001 words to 30000 words out of 232912 words
Chapter 10 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
ya juya ya bar wajen dagowa tayi taga ya bar wajen ta sauke ajiyar zuciya ta fara tafiya.
A bakin babba parking space na bakin gate ta ganshi zaune cikin mota tana karasawa ya bude sit din gefen sa tare da mata nuni da gefen sa ta kalli wajen kamar zatai kuka tace
"Yaya yanzu ka dawo kaje ka huta driver zai kaini."
"No shige muje."
Ya fada ba alamar wasa a tare dashi. Kamar zatai kuka ta shiga motar wayarta ta dauka ta fara rubuta masa text kamar haka
"Am sorry kaga Yaya zai dropping dina nace ya barshi yaki kayi hakuri."
Ta tura masa mota suka tayar suka fita a gate din.
Muhammad yana mota yaji shigowar text din ta ya bude yana karantawa ya tada mota kan motar su ta fito ya bar layin, sai da yai nisa sannan yai mata reply
"Ohk no problem, anjima da yamma zanje can gidan insha Allah"
Sakon na shigowa ta bude tana ganin abun da ya rubuta ta sauke ajiyar zuciya ta kara typng wani da cewa
"Kayi hakuri don Allah"
Sakon na zuwa wani ya kara shigowa
"Noo ba komai dear, ai Yaya ne, kar mu yi laifi ko"
Ido ta lumshe sannan ta bude ta mai da masa da amsa da
"Toh nagode"
Duk abinda take Aliyu na kallon ta ta gefen idon sa tana gama typing Fuska daure Aliyu yace
"Inga wayar?"
Da sauri ta dago ya gyada mata kai yana mika mata hannu. Jiki a sanyaye ta mika masa wayar ya amsa ya zura a aljihu sannan ya cigaba da driving din sa. A haka suka iso gidan Sitti ba wanda yace da dan uwan sa kala, yai parking tai sauri ta bude motar ta fita shima kashe motar yai ya fito, ya bude boot ya dauko akwatin ta yai ciki da ita dan har ta shige.
Sitti zaune parlor sai Maryam dake jikin ta kamar zatai kuka Aliyu ya shigo da sallama Sitti ta amsa ya zauna yana gaishe ta, Sitti ta amsa da fara'a tace
"Ashe kai ka kawo ta?"
Kai ya gyada kawai ya jingina da kujera yace
"Daga aiki nake yunwa nake ji."
"Ai ga abinci nan a dining je ka zuba ka ci.".
A hankali ya mike ya karasa dining din, Maryam ya kalla yace.
"Zo ki zuban."
Da kyar ta mike ta karaso kamar ba zata karaso ba dan yadda take tafiyar ta zuba masa ta shige dakin Najwa kwance ta same ta tana waya ta daka mata duka ta dago da sauri tana ganin Maryam ta saki ihun murna tace
"Oyoyo."
Ta zauna Najwa tace
"Ke da wa?"
"Baki ta tabe tace
"Yaya mana."
"Sarkin yan fada."
"Uhmmm."
Kawai tace, Najwa tace
"Meyake damun ki ne?"
Kan gadon ta haye tace
"Ba komai."
Yana gama cin abinci ya mike yace
"Sitti bari naje na dawo."
"To sai ka dawo."
Ya fita, Maryam da Najwa ne suka fito, Maryam ta kalli dining taga ba Aliyu da sauri ta karaso tace
"Sitti Yaya fa?"
"Yanzu ya fita."
Da sauri ta fita dai dai lokacin da zai fita da mota tace
"Yaya."
Ya tsaya ta karasa tace
"Yaya don Allah ka ban wayata"
Wani kallo da ya tsoratata yai mata, ta koma baya a hankali, yaja motar ya bar gidan.
Ciki ta dawo ta zauna a kusa da Sitti, Sitti tace
"Kin same shi ne?"
Kai kawai ta girgiza. Sitti tace
"Ai zai dawo nan baya ya tafi."
Gaban Maryam ne ya fadi, da sauri tace
"Zai dawo kuma?"
"Eh."
Najwa ta kalla tace
"Kina da number Muhammad ne?"
"Wanne Muhammad?"
"Abokin Abdul."
"A'ah."
"To kira Abdul din nai masa magana please."
Wayar Najwa ta bata ta fara dailing number sa amman bata shiga sam, ajiye wayar tayi tana tsaki, Sitti tace
"Lafiya?"
Kai kawai ta girgiza ta mike tai cikin dakin Najwa kan gado ta kwanta tana tunanin mafita dan hankalin ta a tashe yake kar Muhammad yazo Yaa Aliyu kuma yana nan tasan kashin ta ya riga ya bushe, bama haka ba kada ya kira wayar ta tana wajen Yaya Aliyu duk sai ta kasa nutsuwa
Har la'asar tana dakin Najwa na falo ita da Sitti dan ta shigo tana ta jan Maryam da hira amman da yake bata cikin nutsuwar ta sai ta kasa biye mata wannan yasa Najwa ta fita itama Maryam sai taji hakan ya fiye mata, can wajen biyar sai ga Najwa ta shigo tana makeup Maryam na kallon ta tace
"Ina zaki?"
"Abdul ne yazo."
"Oh haba ki gaishe shi."
"Ba zaki fito ku gaisa ba."
"Ke kyale ni yau bana jin dadi."
Dagowa tai ta kalle ta tace
"Shikenan."
Ta fita Maryam ta koma ta kwanta can bayan mintina ashirin sai ga Najwa ta dawo wayar ta ta mika mata tace
"Ana kiran ki."
Amsa tayi ta kara a kunne muryar sa taji cikin sanyi yace
"Ina wayar ki ne?"
"Tana motar Yaya."
"Motar Yaya kuma?"
"Eh na manta ne dazu."
"Alright tare muka zo da Abdul duk da ni ina compound wajen ki nazo ina jiran ki."
"To ina zuwa."
Ta fada zuciyar ta na bugawa, kar ta fita Yaya ya dawo yanzu.
Mayafin ta ta yafa ta fita falo gefen Sitti ta zauna murya cike da damuwa tace
"Sitti wai Muhammad ne yazo yana waje."
Kallon ta Sitti tayi tace
"Wanne Muhammad?"
"Abokin Abdul."
"Me yazo yi?"
"Uhm daman uhm yazo mu gaisa ne."
Murmushi Sitti ta saki tace
"Ah ko dai saurayin ki ne? Ai yaron yana da hankali."
"Kai Sitti"
Ta mike ta nufi kofa Sitti tace
"To ke ba zaki shafa ko yar hoda ba."
Fuska ta shagwabe tace
"Sitti nifa ba saurayi na bane."
"Naji amman zo nan."
Ta koma tace
"Shiga ki dan shafa hoda ko kadan ne."
Maryam ta juya ta shiga ta shafa hoda har da man lebe tana fitowa falo Aliyu na shigowa, wata faduwar gaba taji tayi wanda sai da ta dafe kirjin ta, ciki ta koma da sauri tana jin sa ya shigo ya zauna. Komawa daki tayi a gefen gado ta zauna can ta mike tana son ta kira number sa amman wayar akwai security cillar da wayar tai dan ita tata wayar ba wani security kwanciyya tayi kawai.
Muryar Sitti taji tana kwada mata kira ta mike da sauri amman bata amsa ba Sitti jin shiru ta mike ta shigo dakin dafata tayi ta dago da sauri alamar ta shiga wata duniyar tunanin, Sitti tace
"Kin bar yaro waje fa."
"Ai suna tare dasu Najwa."
"Duk da haka dai kije ko gaisawa ne kuyi."
Mikewa tayi tace
"To Yaya fa?"
"Ina ruwan sa dake tashi kiji maza kinji."
Mikewa tai Sitti ta fita, Najwa ta leko tana leken Aliyu da kyar tai ta maza ta fito bata kalle sa ba ta fice Sitti ya kalla yace
"ina zata?"
"Zasu gaisa da Abdul ne."
Shiru kawai yayi, a cikin mota ta ganshi ta juyo tana kallon kofar falon tace
"Ni dai sauko mu shiga daki wajen su Najwa."
"Saboda me?"
"Yaya zai fada."
Yai murmushi yace
"To shikenan."
Ya sauko ya rufe motar suka shiga dakin dasu Najwa suke gaisawa sukai da Abdul sannan suka zauna a dining space din dakin, kallon ta yake ita kuwa ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun ta yace
"Long time ba haduwa."
"Eh ya aiki?"
"Alhandulilah."
"Ina Jawahir?"
"Tana gida."
"Ka gaishe ta."
Kai ya girgiza tace
"Saboda me?"
"Just."
Yai murmushi tace
"Uhmm."
"Kinyi kyau sosai."
Dagowa tai tana kallon sa sai kuma ta sauke idon ta da sauri yace
"Da gaske ke me kyau ce."
Boye fuskarta tayi tana murmushi, ya dinga kallonta, tace
"Ina aiki da Sitti fa."
Yace
"Ni da nazo muyi hira to."
"Ka bari ko gobe ko?"
"Shikenan."
"Kayi hakuri please."
"No problem since we will meet tommorow."
Ta danyi murmushi ta mike tace
"To nagode sai anjima ko?"
"Ok bye."
Ta mike ta fita shima ya mikewa ya kalli Abdul yace
"Am going fa."
"Tin yanzu?"
"To ni ai ba zance nazo ba ko?"
Yai murmushi yace
"Uhmm haka ne sai mun hadu to."
"Aha bye."
Ya fita ya shiga mota ya bar gidan. A kofa ta tsaya tana jin Sitti na magana
"Gaisawa ne ta dade Aliyu meyasa kake haka ne?....."
Sallamar Maryam ta katsewa Sitti abinda zata ce, ta shiga ta zauna tana sauke ajiyar zuciya jin komai yazo da sauki Muhammad zai tafi Aliyu bai gansu tare ba. Sitti tace
"To gata nan ta dawo, a haka za ai min hutun kuwa."
Murmushi Maryam tayi kawai ta kwanta a jikin Sitti. Bayan Magrib suna dakin Najwa zaune akan sallayar da sukai sallah basu tashi ba, Aliyu kuma yana masallacin bai dawo ba, wayar Najwa ce tai kara ta dauko taga sabuwar number dauka tayi taji ance
"Uhmm Please Najwa, Maryam nake so ki bawa wayar zan mata magana."
"Oh Muhammad ne?"
"Yeah "
Ta mikawa Maryam wayar, mikewa tayi ta fita ta nufi dakin Sitti ba kowa a ciki dan haka ta zauna gefen gado ta kai wayar kunne tace
"Hello."
Yace
"Hello ya na baro ki?"
"Lafiya kai fa?"
"Gani nan dai da na rufe ido sai ina ganin fuskar ki."
Dan murmushi tayi yace
"Oh dariya kike min?"
"A'ah kana da abin dariya ne."
"Uhmm ina wayar ki?"
"Tana fa motar Yaya."
"Dazu naga ya shigo baki amsa ba."
"Eh."
Kawai tace, yace
"Shikenan zan kira ki anjima."
"To sai anjima."
Mikewa tai ta fita ta koma dakin da Najwa take wayar ta mika mata Najwa dake kwance ta mike tace
"Wai ina wayar ki?"
Fuska Maryam ta bata tace "Yaya ya kwace min"
Najwa ta zaro ido tace
"Saboda me?"
"Shi ya sani amman kila dan yaga ina wa Muhammad text dazu ne."
Najwa tace
"Kaji Yayan nan, toh shi ina ruwansa, ai yanzu an daina takurar nan duniya ta canja ace kina level 400 kuma ya hanaki kula samari"
Baki ta tabe tace
"Toh ko tanadi yake?"
"Tanadin me?"
"Auren ki."
"Shi zai min tanadin Ummi ce zatai min bashi ba."
Dariya Najwa kawai tai dan taga Maryam bata gane inda ta dosa ba.
"Nima fa da yai min haka amman bai tsaurin naki ba."
"Uhmm shiyasani."
Tinda ta shiga daki bata fito ba sai wajen karfe goma, tana fita ta tadda Sitti zata shiga daki, Sitti tace
"A ba bacci kike ba daman?"
"Ni ina kwance Najwa waya take."
"To ni kwanciya zanyi."
"Yaya fa?"
"Yanzu ya tafi.
"Bai baki wayar ba?"
"Bai bani komai ba."
Juyawa tayi ta koma daki ta canja kaya kawai ta kwanta, Najwa na waya taji alamun ana kira katse wayar tai taga Muhammad Maryam ta bawa ta dauki karamar wayar ta ta fara kiran Abdul, Falo Maryam ta koma ta kwanta, wayar ce ta kara a kunnen ta yace
"Baki bacci ba?"
"Eh."
"Nima yanzu zan kwanta nace bari nai miki sai da safe."
"Nagode."
"Aha kije ki kwanta ki huta gobe zamuyi magana."
"To nagode sai da safe."
"Allah ya tashe mu lafiya."
Waahe gari karfe biyar sai ga Aliyu tin da yazo bai da shirin tafiya Maryam na daki taki fitowa da Muhammad ya kirata akan zai zo sai hanashi tayi tace zasu fita yaso yazo ya kaisu ma amman tace masa Yaya ne zai kaisu dole ya hakura, kusan kwana uku kullum da ya tashi a aiki gidan Sitti yake zuwa bai tafiya kuma sai wajen tara ko goma dan haka sam Maryam bata hadu da Muhammad ba.
Ranar Alhamis da yake ko a gida bai fiya dawowa da wuri ba dan yana bawa mutanen sa appointment wannan yasa ko a gida wani lokaci yakan kai har bayan isha'i bai dawo ba. Sanin haka da sukai waya da Muhammad yace zai zo bata hanashi ba tace sai yazo. Da yamma tana zaune a daki Najwa ta shigo tace
"Gashi Muhammad ya kira"
Maryam ta mike zaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da masa sallama, ya amsa yace
"Na karaso."
Tace
"Toh bari in fada ma Sitti gani nan"
Daga haka ta katse ta fita falo, samye da wani oramge material mai kamar boyel wanda akai masa ado da mint colour dinkin doguwar riga ce, ta yafa mint colour mayafi tai kyau duk da batai kwalliya ba amman tai kyau sai tashin kamshin intensive oud take, ta zauna tai kasa da kai tace
"Sitti Muhammad ne yazo."
Sitti tace
"Toh ya shigo mana, kuje can sitting room din."
Ta mike ta fita sam baya compound gate ta fita ta hange shi tsaye a jikin motarsa, sanye yake wata sky blue din shadda wacce tai masa kyau sosai, sai kamshin yake kansa ya saka hula baka da bakin takalmi, yai kyau sosai, ta karasa kanta a kasa ta tsaya daga nesa dashi, Muhammad kuwa ya kasa dauke idonsa akan ta,
"Yan mata."
Fuska ta bata yace
"To Baby."
Dagowa tayi ta dan harare shi yai murmushi yace
"Kinga ai naga idanun ki."
Juya masa baya tai tace
"Mu shiga ciki ka tsaya anan."
"Menene da nan din?"
"Yayi hanya."
Unguwar ya kalla ba kowa a layin yace
"A hakan?"
Kai ta gyada tai gaba yabi bayan ta, sitting room suka shiga ya zauna akan one sitter ita kuma ta zauna akan three sitter. Dagowa tai suka hada ido wannan yasa tai saurin dauke idon ta tare da dukar da kanta tana mai cigaba da wasa da yatsun hannun ta,
"Meyasa bakya son ina ganin fuskar ki?"
Kai ta girgiza yace
"Gashi nan bakya iya kallo na kullum kan ki a kasa, rabo na daganaga fuskar ki sosai tin farkon haduwar mu."
Fuska ta rufe da hannun ta tuna ranar da rashin yadar da tayi dashi, yai murmushi yace
"Eh a lokacin an zata ni mai sace mutanene ko? Sai gashi ke a ranar kikai min sata."
Da sauri ta dago kamar zatai kuka ta nuna kanta tace
"Ni kuma?"
Kai ya gyada yace
"Kwarai kuwa."
"Gaskiya ba abinda na daukar maka sai dai ko kayar da abun."
"Ba a ganin abun ma bare na yar."
Kallon sa take da rashin gane me yake nufi ya gyada mata kai yace
"Anan abun yake."
Ya nuna kirjin shi tace
"Me kenan?"
"My heart."
Da sauri ta sunkuyar da kai yai murnushi yace
"Yeas you stole my heart Maryam daga ranar kika sacen zuciya ta, ban kara ganin ki ba amman kika tafi da zuciya ta sai Allah yayi zan ganki a super market da gidan mu ashe kece wacce ake yanwan bani labari ban sani ba, sai ga Abdul ya kara hadamu ashe ba a banza kika dauken zuciya ta ba Allah yayi zan ganki har na bayyana miki kila ki zama matata uwar ya'ya na."
Ya fada yana lumshe ido.
"Ban taba son abu kamar yadda nake son ki ba, thur ba anan nai rayuwata wajen da nai rayuwa farar fata ne, dawowata ba dadewa muka hadu, kuma Allah ya jarabce ni da sonki please Maryam kar kice min A'ah wallahi na kamu da son ki ta yadda ba zan iya rayuwa bake ba ko a yau kika ce na fito zan fito."
Saukowa yai ya durkusa agaban Maryam yace
"Please ki amshi soyayya ta."
Dagowa tai tana kallon sa durkushe a gaban ta duk kyan sa, ajin sa amman yake zube a gaban ta yana neman soyayyar ta, kai ta dauke da sauri tace
"To ka koma ka zauna."
"Sai ki amshi soyayya in ba haka ba, ba zan taba tashi daga durkushen nan ba."
"To naji tashi ka zauna."
"Kice kin amshi soyayya ta."
Shiru tayi yace
"Baki amsa ba kenan."
Kai ta girgiza tana rufe fuskar ta da hannu yace
"Ok to kin amsa?"
Kai ta gyada ya mike yace
"Alhamdulillah nagodewa Allah, Allah ka mallaka min Maryam ta zama matata kuma uwar ya'yana."
Ita kunya yake bata daga ganin sarkin fawa sai miya tai zagi, haka ya dinga fada mata yadda yake jin ta da karai mata bayani akan rayuwar sa har kusan magariba suna tare sai daga baya sukai sallama ta fito har bakin gate ta tsaya tana daga masa hannu ta koma cikin gida.
Tana zama taji an bude gate, ta taga ta leka taga motar Aliyu ta shigo mamaki ya kamata na zuwan nashi a yanzu sai kuma ta fara tunanin Allah yasa Muhammad ya tafi basu hadu ba, tana ganin sa ya fito sanye yake da coffe wando da brown kalar riga, yai kyau dashi baki ta tabe ta saki labulen ta koma ta zauna sitti tace
"Waye?"
"Yaya ne."
Sai kuma ta mike kan tabar falon ya shigo amman bata juyi ba ta shige daki da kallo ya bita har ta shige sannan ya karaso ya zauna suka gaisa da sitti, sitti tace "kaje kaco abinci kan magariba"
"Na gaji kira Maryam ta zuba min."
Kiran Maryam Sitti tayi, Maryam ta fito, Sitti tace
"Kawo masa abinci nan."
Ta nufi dining ta kawo masa flask din tace
"Ina yini?"
"Lafiya."
Har ta mike yace
"Zuba min mana."
Ta zuba masa sannan ta mike zata bar wajen yace
"Zo nan."
Komawa tai ta zauna yana cin abinci yana satar kallonta ta kasan ido ita kuwa sai turo baki take, shi dariya ma taso ta bashi to ita kadai sai abu take,
sai da ya gama cin ya jingina da kujera yana lumshe ido kiran sallah aka fara ya bude ido a hankali ya sauke akan fuskar Maryam, mikewa yai ya nufi kofa yace
"Bari nai sallah na dawo."
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/23, 14:18] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 9
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Wannan shafin naki ne, Ubee from Sona Hausa Novel group i really appreciate😍😍
Ya fita, baki ta murguda ta shige daki, alwala tayi tai sallah tana zaune akan sallaya wayar Najwa tai kara Najwa na gani ta mika mata amsa tayi ta dauka ta kai kunnen ta yace
"Kinyi sallah?"
"Eh."
"Ina fatan kin mana addu'a."
"Eh."
"Me kika rokar min?"
"Allah biya maka bukatun ka na alheri."
Wani murmushi mai sauti yayi yace
"Nagode sosai, sai anjima."
"Nagode."
Sukai sallama ta ajiye wayar, bayan isha'i Aliyu ya dawo yana falo suna hira da Sitti har tara, sai da ya mike zai fita yace
"Ina Maryam ne?"
"Tana ciki."
Sitti ta fada, Najwa ce ta fito daga daki, Aliyu na ganin ta yace
"Turo min Maryam."
Ya juya ya fita, cikin mota ya shiga, bai jima ba ta fito sanye da hijab har kasa ta karasa tace
"Gani."
"Waye Muhammad?"
Kai tayi kasa dashi yace
"Ba magana nake miki ba?"
Nan ma tayi shiru yace
"Ok sai da safe."
Kan tai magana tini yaja motar ta dago tana kallon sa har ya kai gate mai gadi ya bude ya fice aguje kai ta dafe tace
"Wai meyasa haka ne?"
Baki ta murguda tace
"Kayi ka gama."
Ta juya tai ciki tai kwanciyyar ta.
Gaba daya Aliyu bai bar Maryam ta sake ba dan kullum yana gidan da yamma kuma bai tafiya sai dare duk yadda Muhammad ke son yazo taki ta bashi dama dan tana tsoron haduwar su da Yaa Aliyu, a daddafe da kyar ta kwana bakwai tace zata tafi Najwa taso ta kara amman taki, Aliyu ne yazo da yamma ya maida ita gida.
A compound din su ta samu Haidar na buga ball yana hango ta ya karaso a guje yace
"I miss you Adda."
Ta daga sa tana fadin
"I miss you too."
Ta sumbaci kumatun sa tana fadin
"Ya makaranta?"
"Alhmadulillah."
Ta shafa sumar kansa tace
"Masha Allah."
Ya rumgume ta. Duk abinda suke Aliyu na tsaye yana kallon su sai murmushi