Showing 6001 words to 9000 words out of 232912 words
Chapter 3 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
na shigo da ita, na manta amman in na dawo zan baki sai ki bata."
"To Angode Allah kara budi Allah maka albarka."
"Amin! Son ya karya?"
"A'ah."
"Taso muje kaci abinci na ajiye ka a makaranta."
Suka sauka kasa tare sukai karya sannan suka fita. Inna sukaje suka gaisar ta amsa tana fadin
"Yanzu kuwa Maryam ta tafi."
Mikewa yayi yace
"Sai na dawo."
Ya fita shi ya kai Haidar makaranta sannan shima ya wuce wajen aiki.
A bakin department driver yai parking ta fito, a hankali tace
"To Baba Anas sai yamma zan fito zan kira ka in na gama."
"Allah bada sa'a."
"Amin nagide."
Ta wuce, waya ta kai kunnen ta tana dan dube duben tace
"Banganki ba."
Ta baya taji an rufe mata fuska ta saki murmushi tace
"Uhmm to sakar ni kar na fadi."
Ta bude tana fadin
"Ya akai kika so ki makara?"
Murmushi tayi tace
"Hajiya Inna da kyar na fito."
"Wallahi kinji dadin ki Maryam ina ma nice nake tare da Kaka ta wallahi da na more shiyasa nake son nazo gidan ku muyi ta shan hira da Inna."
"Hmmm muje kema uwar surutu."
"Ni din?"
"Eh mana."
Suka shiga lecture hall.
*
Sai karfe uku suka fito Maryam ta kalli Jawahir tace
"Yanzu me zamu fara?"
"Abinci sai muyi sallah."
"Amman yaushe mukaci cake."
Ido Jawahir ta zaro tace
"Tab wallahi ni yunwa nake ji."
"Acici."
"Naji jikin ai yana nunawa ke kuwa kowa ya ganki yasan bakya cin abinci."
"Ai ba anan yake ba."
"Ki ci kiga in baki kiba ba."
Suka karasa cafteria wani waje suka shiga wajen mai kyau suka shiga VIP suka zauna, ba kowa a wajen suka zauna nan da masu aiki suka kawo musu ruwa da lemo, Jawahir ta amshi menu ta zabi abinda take so ta mikawa Maryam amsa tayi tai selecting shawarma kadai. Lokacin da aka kawo Jawahir tace
"Shi kawai zakici sai fa 6 zamu tafi."
"Ta ishe ni."
Baki ta cije tace "Zaki sani wallahi Ummi zan fadawa."
Dariya tayi tace "Ai dai ina ci."
Haka suka ci sai wajen hudu suka fito sallah sukai sannan suka shiga dakin daukar karatu. Sai shida suka fito lokacin drivern su duk suna waje suna jiran su.
Sallama sukai kowa ya shiga mota. Tana shiga gida ana kiran sallah ta fito a gajiye ta nufi sashen su, Mama ta gani ta fito zata fita, ganin sun kusa haduwa yasa Maryam tace
"Ina yini?"
Ko kallon ta batai ba, Maryam tai murmushi ta juya sai ta ga Aliyu rike da hannun Haidar. Haidar ya karaso yace
"Adda welcome!"
"Thanks!"
Ya daga mata hannu suka fice ita kuma tai ciki Ummi na daki tana sallah dan haka Maryam tana lekawa ta koma dakin ta wanka tayi ta fito ta saka kaya marar nauyi tai sallah. Tana zaune tana tsabihi har akai isha'i sannan ta mike tayi sallah ta idar tai addu'a.
Littafi ta dauko tana aiki a ciki har karfe tara sannan ta mike ta bude firij ta dauki nono ta sha ta koma ta zauna tana matsa kafafun ta. Kofar dakin aka bude Ummi ce, ta shigo Maryam ta dago ta shagwabe fuska. Ummi ta karaso tace
"Ya akayi daughter?"
"Ummi na gaji bayana ciwo yake da kafata."
Jakar system ta ajiye tana fadin
"Sannu."
Ta isa gaban mirrow ta dauko man zabi ta karaso ta lakata ta shafa mata a kafa tana fadin
"Sannu me kikai?"
"Zama kawai."
"Sannu."
Ta fada tana matsa kafar ta. Zamewa tai ta kwanta tace
"Me kika ci?"
"Nasha Nono."
"Shi kadai daughter nayi pepper chicken nasa a kawo miki?"
Kai ta gyada ta mike tace
"To ga kyauta nan daga Yayan ki sai kije ki masa kyauta."
Jakar ta kalla Ummi tace
"Eh!"
Murmushi ta saki, taja jakar tace
"Kai Alhamdulillah nagode sosai kuwa Yaya kamar yasan ina so. Allah saka da alheri."
"Amin."
Ummi ta fada. Har ta bude kofa Maryam tace "Ummi!"
Juyowa tai tace
"Dazu an min aikin 1500 ya amsa."
"To Daughter ba da kudi a account ba, komai kikai sai kin fada min kudin kine fa in ya kare ki min magana zan dada miki ke dai kiyi duk abinda kikaga ya dace."
"Nagode Ummi."
Ta juya ta fita. Tana kwance akai knocking ta mike ta karasa mai aikin suce rike da plate da lemo amsa tayi tai mata godiya sannan ta koma shi taci ta sha lemon sannan ta mike ta wanke hannu. Haijab ta saka fuskar ta dauke da murmushin farin ciki ta fita rike da plate din ba kowa a falon kasa dan haka ta wuce kitchen ajiyewa tayi sannan ta fito ta nufi dakin Aliyu.
Da sallama ta shiga falon yana zaune akan three sitter Haidar yana kwance a gefen sa yai bacci sai system dake gaban sa yana aiki akan stool. Amsawa yai ba tare da ya dago ba. Ta shiga ta zauna a kasa tace
"Yaya!"
A yadda ta kira sunan sa sai da gaban sa ya fadi ya dago yana kallon ta, da lumsasun idanun su, ba tare da ya amsa ba, tace
"Yaya bani da bakin godiya a wajen ka, domin godiya tai kadan akan abubuwan da kake min, "
Hawaye ne ya zubo daga idon ta amman murmushi take, tace
"Abu da zan kasance ina maka shine addu'a baki na ba zai tabai daina maka addu'a ba, zan kasance kullum cikin maka addu'a Allah jikan Anty Maryam, Allah ya baka madadin ta, Allah ya saka maka da gidan aljanna, yasa ka gama da duniya lafiya, Allah ya maka tukwici da gidan Ajanna. Nagode sosai Yaya Allah ya biyaka."
"Amin Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum menene na kukan to?"
Ya fada cikin muryar mai sanyi dasa nutsuwa, tare da jingina kan sa da kujera. Kai ta girgiza yace
"To tashi kije sai da safe."
Ta mike ya kalli Haidar da ke bacci yace
"Zaki iya daukar Haidar?"
Kai ta gyada, yace "Zo ki dauke shi."
Ta karasa ta dauke shi ta fita, ya bisu da kallo tare da lumshe idon sa wani murmushi ya saki wanda kumatun sa suka lostsa, lips din sa dan taune yana mai shafa sumar kansa.
***
Sam Maryam bata da matsala a fanin komai, gida sai abinda take so Ummi ke mata, haka ma Inna sosai take ji da ita dan har snacks take mata in taje gaishe ta da safe ta bata, a fanin karatu ma basu da matsala dan suna ganewa sosai.
Yawanci karfe biyu zuwa uku suke gama lecture sallah kawai suke su nemi abinci daga haka zasu shige library ita da Jawahir suyi ta duba abinda akai in da inda basu gane ba suje wajen na sama dasu su ganar dasu dan haka basu da matsala yawanci sai shida suke dawowa gida. Drivern ta kawai take kira nan da nan zaka ganshi sai dai in na Jawahir ya riga zuwa kan nata wani lokacin suke dire ta gida, shima da ta koma wanka kawai takeyi tai sallah zata Kara daukar littafai ko kasa bata fiya sauka ba dan bata cin abu mai nauyi da dare duk abinda take so light akwai a firij in ma babu kan ta shigo zata siya Wanda in wata yai Kuma ko weekend Yaa Aliyu sukan fita da Haidar suyo shopping to itama ba a barin ta a baya za a siyo mata abubuwan da take so, takanyi sati daya bata saka Yaa Aliyu a idon ta ba wani lokacin sai weekend Shima in ta leka wajen Inna to anan tafi ganin sa amman a sashen su kan ta ganshi sai ta sauko kasa wanda a yanzu bata fiya ba, bama da taga wani lokacin kamar in ya ganta yake barin wajen. Dan sau da dama da taje waje zataga ya mike tin bata damuwa har ta fara damuwa, gaisuwa ma a share take gani yana amsa ba, wanda hakan kesa ta shiga damuwa amman kuma ita ta rasa me tai masa da ya canja mata tasan da ba haka yake mata ba.
Bangaren Farouk kuwa in yai kwana biyu bai ganta ba zai kira su sha waya ko in ya ganta a online su dan taba hira wani lokacin kuma suna haduwa a wajen Inna.
Haidar kuwa daman in ya dawo karfe biyu isilamiyya yake zuwa wanda karfe biyar yake dawowa, a falo zaku ganshi yana damun Ummi da surutu wani lokacin shida ko shida saura Yaa Aliyu ke dawowa da gudu Haidar yake nufar sa ya rumgume shi, Shima haka zai dauke shi yana tambayar sa ya makaranta yaron yai ta masa dariya daki sukeyi ya dire shi akan gado ya cika masa gaba da kayan ciye ciye da na wasa shi kuma yakan shiga yai wanka kan ya fito an kira magarib tare suke tafiya masallaci har sai anyi isha'i suke dawowa suci abinci tare, wani lokutan tare suke kwana da Haidar bama week wanda sauran ranakun kuma yana tare da Ummi ko Maryam bama in Abba baya gari.
*** *** *** ***
Bayan wata biyu
*** *** *** ***
A haka rayuwa take tafiya har su Maryam suka zana jarabawar first semester, lokacin da suke jarabawar ko bacci batayi abinci ma ba sosai take samun damar ci ba, sati biyu sukai suka gama jarabawa sannan aka basu hutun sati uku.
A gajiye ta shigo gidan dan ranar suka gama jarabawa kana ganin ta zakaga yadda ta fada, har bakin kofa driver ya ajiye ta, ta fito tana fadin
"Baba nagode kai ma ka huta na kwanaki."
"Allah dai ya bada sa'a Hajiya."
Tsayawa tai tace
"Haba Baba ni dai kace min yarka ko jikar ka yafi."
"To 'yata. Allah bada sa'a aje a huta gajiya."
"Nagode Baba kaima Allah huce gajiya."
Ta fada tanayin hanyar kofar, budewa tayi ta shiga da sallama. Akan kujera ta fada tana sauke numfashi.
Ummi ce ta sauko rike da waya, tana fadin
"Daughter ta, ta dawo."
Ido Maryam ta bude tana kallon Ummi da murmushi akan fuskar ta tace
"Eh Ummi."
Karasowa Ummi tayi ta zauna a gefen ta, tare da janta zuwa jikin ta, tana fadin
"Allah bada sa'a yanzu kije kiyi wanka ki samu ki dan kwanta kan la'asar, zamu fitar da rana muje mu rakaki shakatawa na gama jarabawa."
"Ina godiya Ummi na. Amman kan nan kunyi waya da sitti?"
"Munyi menene?"
"Naga missed call nata na kira bata shiga."
"Ta miki albishir ne?"
Kai ta girgiza tace
"A'ah."
"To in kunyi waya ta fada miki."
Fuska ta shagwabe tace
"Ni dai Ummi ki fada min?"
Hancin ta Ummi taja tace
"In Haidar yaga kina haka ya miki dariya."
"Ina ruwa na ba Ummi na nakewa haka ba, shima yaiwa Abbin sa."
"Ai yana abinda yafi naki."
"To nima zan nayiwa Ummi na da Abba."
"Tashi dai kije ki watsa ruwa yau na shirya miki special dishes."
Rumgume Ummi tayi, ta sumbace ta a kumatun tace
"Shiyasa nake son ki Ummi na."
Ta mike tana daukar Jakarta da mayafin ta, tayi sama. Tana shiga ta kwanta saman gado tana salati Ido ta lumshe tana hamma tare da rufe bakin ta, tana salati, ido ta lumshe tana addu'a a cikin zuciyar ta, take bacci ya dauke ta.
***
Kiran sallah la'asar shi ya tashe ta, ta mike tare da yin mika hadi da hamma, ta rufe bakin ta tana salati ta mike ta cire kayan ta, sannan ta daura towel bandaki ta shiga.
Tana fitowa ta tsaya ta shafa mai, tai kwaliyya mai kyau ba mai yawa, sosai tayi kyau ta manta rabon da tayi kwalliya, dorowa ta bude ta dauki wata daguwar riga da Yaa Aliyu ya siya mata lokacin da sukaje shopping taki daukar komai. Rigar mai kyau da tsada pink-peach duk jikin ta stone ta saka under wears ta daura ta sosai tai kyau mayafin ta dauka ta yafa ta fesa turare wani half cover ta saka kalar rigar ta saka silver agogo tai kyau. Sallah tayi sannan tai addu'a da azkar ta fita.
Tin kan ta sauka ta fara jiyo magana sama sama a kasa, murmushi tayi ta sauka tace
"Yau baki mukayi?"
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/23, 14:06] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 3
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Tana sauka taga wasu mata dayar babbace amman wacce zatai shekara hamsin saura sai ta gefen ta wacce ba zata wuce shekara talatin ba zaune suna hira, daga gani kasan jini daya ne dan kamar su daya dukka sai dai Ummi da Dayar da suke manyanta, da fara'a ta karasa tana fadin
"Mami."
Wacce aka kira Mami ta dauke kai tana fadin
"Ba wani Mami."
Jikin Mami ta kwanta tana fadin
"Kiyi hakuri Mami wallahi makaranta shiyasa bana shigowa."
Wacce take zaune ta kalla tace
"Kinji ko? Wai makaranta Muna gida daya sai nai wata ko satituka ban ganta ba in ba fita zanyi ba ko na shigo nan."
Jikin Mami ta shige tana fadin
"Mami na kiyi hakuri Ummi ki sa baki "
Ummi na murmushi tace
"In zata yadda amman Wallahi Yaya tin kan exam Maryam bata dawo sai magariba, ko Inna kullum sai ta shigo ta min mita."
Baki ta gefen Ummi ta tabe tace
"Bare ni dake nesa ko ziyara ta batayi a shekara bai fi tazo sau daya ko biyu ba."
"Haba Anty Asiya ai da cewa nai gidan ki zan zo hutu ko Ummi."
Kai ta dauke. Ummi tace
"Haka tace."
Mami tace
"To ya jarabawar Daughter?"
"Mami Alhamdulillah."
"Allah kawo sakamako mai kyau "
"Amin!"
Duk suka amsa.
Mami ta taba jikin ta tace
"Ya naga duk ta rame?"
"Jarabawa Mami."
"Gata nan ko abinci bata ci kwana take karatu."
Ummi ta fada. Mami tace
"Ah Daughter kina cin abinci da bacci kinji zakici jarabawa ai kina karatu."
"Allah yasa."
"Amin."
Sallama suka jiyo ta Aliyu da Haidar duk suka amsa, Haidar ya shigo a guje yai wajen Ummi, Ummi ta dauke shi ta rungume Mami tace
"Au mu ba asan damu ba ko mai gida?"
Saukowa yayi ya tafi wajen Mami a guje yana fadin
"Oyoyo."
Ta dauke shi tace
"Ya makaranta Mai gidan?"
"Fine."
Ta shafa kan sa. Kallon Anty Asiya yayi ya mike a guje yai wajen ta tace
"Yaro na ya girma."
Ta sumbaci goshin sa yace
"Ina yini Anty?"
"Lafiya lou Son ya school?"
"Lafiya lou. Ina su Abid"
"Suna can gidan Garnny din su."
Ya tashi ya nufi Maryam yana fadin
"Addah ya exam?"
"Alhamdulillah!"
"Allah bada sa'a."
Ya fada da kalar bakin sa da magana bata fita sosai.
Kallon sa tayi tana murmushi. Aliyu ya karaso sanye yake da milk kalaf wando sai riga longsleeve coffe kala, sai tashin kamshi yake, Ummi a kalla yace
"Ummi barka da gida."
"Yauwah ya aiki?"
"Alhamdulillah!"
Anty Asiya ta dago tace
"Sannu da zuwa Yaya."
"Yauwah ya gidan da yara?"
"Lafiya lou."
Ya kalli Mami yace
"Mami Ina yini?"
"Lafiya lou ya gida?"
"Lafiya lou "
"Sannu da zuwa Yaya."
Maryam ta fada tana wasa da Haidar."
"Yauwah ya exam din?"
"Alhamdulillah."
"Allah bada sa'a."
"Amin nagode."
Yayi dakin sa Haidar ya bishi a guje. Mami ta bisu da kallo tana fadin
" 'Da da Uba kenan."
Sukai murmushi Ummi ta kalli Maryam tace
"Bafa kici komai ba."
Ciki ta shafa tace
"Zanci anjima"
"Kin gani ko Yaya."
"A'ah daughter kina cin abinci kinji ko?"
Kai ta gyada.
Farouk ne ya shigo da sallama, suka amsa Mami tace
"Aisha duk kin dauke yara dai bangaren mu kullum shiru mu ke kuwa kalli fa."
Ummi tai dariya tace
"Shi wannan yanzu zai fita Haidar din ne dai."
Ummi ya gaishe tare da Mami sannan ya zauna, Anty Asiya ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ya yaran. Sai kuma tace
"Wai na gaishe shi Ummi ba na girme shi bama."
Filon dake kusa dashi ya cilla mata yace
"Kin rainani wallahi Asiya."
Ummi tace
"Ba dole ba ta ganta da yara kai kana zaune ba auren ma."
"Kai Ummi."
Ya fada yana bata fuska. Maryam tai dariya ya juyo ya dan harare ta sai kuma yace
"Ya jarabawar?"
Mami tace
"Oh Daughter Yar gata kowa bai manta ba."
Tai murmushi ya mike yace "Ummi Yaya fa?"
"Yana ciki."
Ciki yayi yana shiga ya tadda shi ya fito daga wanka shi da Haidar. Mai ya shafa masa ya saka masa wasu kayan, sannan ya kalli Farouk yace
"Daga ina?"
Haidar ya dauka yace
"Na shigo gaishe da Ummi ne."
"Ok!"
Ya saka kaya ya fito yace
"Lokacin sallah muje."
Suka fice gaba daya, ba kowa a falon Mami ta tafi sai Maryam da Anty Asiya dake dakin ta Ummi na dakin ta Sai da suka idar suka fito tare sukaci abinci da Maryam sannan suka tafi bangaren Inna.
Inna na zaune akan sallaya da carbi a hannu tana ganin Maryam tace
"Ke 'yar nan ciwo kikayi ne?"
Zama Maryam tai tana murmushi tace
"A'ah."
"Kinga yadda kika rame kuwa ko abinci ne Aishan bata baki."
Anty Asiya tayi murmushi tace
"Haba dai Inna sai a hanata abinci."
"To gata nan duk ta kare, ya jarabawar?"
"Inna mun gama"
"Allah bada sa'a."
"Amin."
"Me zan samu yar tsohuwa."
Cewar Anty Asiya.
Inna tace
"Ce nake tin da kika shigo kika gaishe ni kuka fice ke ko yar hirar nan ma bazaki zo mu yi ba."
"Hajiya Inna zuwan ki daban ne zan zo na yinar miki."
"Kan kizo, zamu zo ni da Maryam."
"Allah ya kawo ku daman Inna kin jima baki zo ba ita kuwa wannan sai shekara shekara."
Maryam tace
"Kai Anty nafi zuwa gidan ki fa akan Anty Hanna."
Wayar Anty Asiya ce tai kara tana dubawa taga mijin tane Maryam ta kalla tace
"Tashi muje ki tayani hado kan kayana wajen Mami dan nasan yanzu zaki ganshi."
Ta fada tana kai wayar kunnen ta fita sukai suka nufi Sashen farko na gidan wanda yake duk yafi sauran girma ko ciki suka shiga bangaren Mami suka shiga tana zaune tana kallo a TV ta dago tace
"Juya ki koma."
Karasowa Maryam tayi tace
"Haba Mami ni ana ma zan yi hutun nawa."
"Naga kafar ki ma."
Sukai Dariya. Anty Asiya ta kalli Mami tace
"Mami na dauki jug din?"
"A'ah wai meyasa kike min haka Asiya ace ni kenan ban isa naiwa miji na kayan gari ba sai kina dauken."
"Mami ai ku, kun tsufa"
Maryam ta fada.
"Oh kema haka zakice ko? Zanci gidan ku, kuma ba zan bayar ba to ni kada na tararayi nawa mijin ko?"
"Ah Haba Hajiya Mamin mu dan Allah ki bata."
Hararar Maryam tayi tace
"Kuje daki na fito miki da naki saboda haka yanzu in naga abu nake siyar har bakwai sai kace mai siyar wa."
"Mami bakwai kiyi me dashi?"
"In na siya dole na siyawa yar uwata."
Hada ido Maryam da Anty Asiya sukai suna murmushi, Mami tace
"Gani da yan mata biyu ga ku uku da bakwa barina da abu shiyasa kullum cikin kashe kudi nake."
Karasawa sukai wajen Mami suna fadin
"Allah sarki Mamin mu Allah kara budi muna son ki Mamin mu."
"Allah muku albarka."
Wayar Anty Asiya ce tai kara ta dauka tana fadin
"Ba dai ka karaso ba."
Yace
"Eh ina sashen Inna."
"Ok sai ka shigo."
Ta mike ta shige daki Maryam tabi bayan ta. Da katuwar leda ta fito suka shiga Kitchen Mami tace
"Me kuma za a daukar min anan."
Basu jima ba suka fito suna dariya. Mami tace
"Allah in ma wani abu kuka