Showing 102001 words to 105000 words out of 232912 words
Chapter 35 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
'kal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa. Shigar kanannun kaya ne a jikin sa masu kyau da tsada. Bakin wando ne da orange kalar riga, sai bakin takalmi cover mai masifar tsada. Sai sheki yake haka nan hannun sa makale da bakin agogo mai kyau da tsada. Yana da doguwar fuska wacce take zagaye da saje mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya kwanta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido.
Bayan sa jingine da kujera hannun sa daya akan sitiyarin motar dayan kuma counter ne a hannun sa yake ambaton Allah. Fararen idanun sa ya lumshe bayan ya iso bakin gate din gidan su tare da dannan horn din motar wanda daya daga cikin security yai sauri ya bude gate din.
A hankali ya bude idon sa ya sauke akan sa yace
"Welcome Doctor!"
Hannu ya daga masa yace
"Thanks!"
Sannan a hankali ya karasa tura hancin motar cikin katon compound din nasu wanda duk da dare ne wajen tamkar rana saboda hasken wajen ko allura ce ta fadi zaka gani a wajen. Idon sa ya juya ya kalli bangaren Ummi. Murmushi ya saki ganin bangaren Ummin da haske ba kamar kwanakin baya ba da bata nan. A hankali yai parking a wajen da ya saba parking sai da ya dauki minti wajen goma sannan ya bude kofar motar ya zuro kafafun sa kasa. A hankali ya fito ya zura wayoyin sa cikin aljihun wandon sa. A hankali yake taku cikin nutsuwa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar bakin sa dake zage da siraran lips yana motsi a hankali a hankali hannun sa na pressing counter din sa. A haka ya karasa bakin kofar Ummi, knocking yayi, Abbah ya bashi izinin shiga. Ya shigo a hankali, A hankali ya shigo cikin tafiyar sa a nutse, karasowa falon yayi a kasa ya zauna kan sa a kasa yace
"Barka da dare Abbah!"
"Yauwah Doctor Ya kake?"
"Alhamdulillah. Abbah kun dawo lafiya ya hanya da mai jiki?"
"Alhamdulillah!"
Ya dan kalli dakin yace
"Ina Ummi na?"
"Tana sama ita da Inna!"
Mikewa yayi ya nufi stair yana fadin
"Me Inna tazo yi da daren nan!"
"Tazo ganin marar lafiya."
"Tab tazo dai damun ta!"
Ya fada a hankali ya karasa hawa. Yana hawa ya fara jiyo muryar Inna na fadin
"Na shiga uku har yanzu aman yaki tsayawa!"
Dakin da yajiyo muryar ta ya karasa yai sallama a hankali ya bude dakin ya shiga. Inna ya gani tsaye a kofar bandakin tana ta magana. Karasawa yayi a hankali ya ra'ba ta gefen ta ya shiga ciki.
Ummi ya gani rike da Maryam. Amsar Maryam yayi a hannun Ummi ya cire mata hijab ya dafa bayan ta hade da tallabo ta. Ido ta lumshe ta daura kan ta a kirjin sa tana sauke ajiyar zuciya.
Famfo ya kunna ya janyo ta ya dauraye mata baki sannan ta koma jikin sa ta kwanta tana ta numfarfashi.
"Sannu!"
Ummi ta fada. Hannun ta ya kamo suka fito kan gado ya ajiye ta yana kallon dakin.
"Menene wannan kuma?"
Ya fada idon sa aka plate din da Maryam ta gama shan faten
"Fate ne!"
Inna ta fada
"Menene fate? Zaki bata wannan abincin haba ai dole ya sata amai tsaki ne ma fa! Menene value nasa a jiki?"
Kallon sa Inna ta tsaya yi sama da kasa sai da ya gama tace
"Kai kasan menene value din? Kuma naga uwar ka shi taci da tana da cikin ka ma. Kullum shi take sawa nake mata dan shi take jin dadin sa abakin ta har kazo duniya shin me ya faru da ita zaka zo ka ishe ni da wani kaza da kaza!"
Ummi ya kalla da ta fito ta gama gyara bandakin kamar zai kuka ya kalli Maryam da ta kife akan gado yace
"Ummi dan Allah ki daina bata abinda zai na saka ta amai."
"Aliyu ko taci ko bata ci ba amai takeyi ai gwara ace ma taci ta dawo dashi da ace bata ci ba tana amai!"
"Kyale shi dai ba abinda ya sani sai haka ai. Kai ka samar mata abinda zataci kada tai amai wai shi likita..."
Inna ta fada ta karasa wajen Maryam ta dafa ta tace
"Sannu 'yar nan!"
Shiru taji ta leka fuskar ta taga ta fara bacci tace
"Aha kunga ba har ta samu bacci ai ko yaya ne ya zauna dai da ace bata cin ba."
Ta mike ta kalli Ummi tace
"Ni zan tafi sai da safe in kika biye ta wannan yaron kuwa zai kashe 'yar mutane dan kyale ta zai yi bataci komai ba haka ake fisabilillah ai ko dura a mata da ta zauna bata ci komai ba."
Ummi tabi bayan ta tace
"To Inna an gode!"
Suka sauka ta zauna wajen Abbah tana fadin
"Ka rabani da yaron nan na wajen Sule haka ake rayuwa ina ruwan sa dani ni shiga harkar sa ne shiyasa fa na daina shiga ma harkar sa yanzu duk abinda nayi bai gani ba yana can yana fada dan taci faten da nai mata sai kace wacce na saka guba."
"Kiyi hakuri Inna kinsan likitocin nan ba komai suke so ana ci ba."
Ummi ta fada.
"Likitan banza likitan wofi mu a da ba haka muke rayuwa ba, ba wasu likitoci muke kula da kanmu da cimar mu kuma bamufiku lafiya ba? Haba dan Allah sai kuma ace bamu iya ba dan zamani dai."
Ummi tace
"Kiyi hakuri bari na koma sai da safe!"
Ta juya ta koma sama. Inna ta bita da kallo ta kalli Abba tace
"Sam Aisha bata son nayiwa yaron nan fada na rasa saboda me kamar ta zane ni take ji in nai masa fada."
"Ah haba dai Inna itama ai tana masa, yanzu dai kiyi hakuri bata ci ba!"
"Wallahi shehu taci da yawa baka gani ba, sai da ta gama sai ga amai nan haka tai tayin sa kamar zata amayar da kayan cikin ta da kyar ya tsaya shine fa dan tayi aman ya hau ni da fada dan me na kawo mata abinci wai bai da mene da menene kaji yaro."
"To Inna kiyi hakur!"
"Bazan hakura ba kai masa magana ya daina shiga harkata to."
Ta mike Abbah ma ya mike yace
"Zan masa tafiya zakiyi?"
"In ban tafi ba ai sai yaron nan ya koreni ina jin baka ga fa yadda ya dinga min ba kamar zai doke ni dan ba uwar sa bace in uwar sa ce ai ba zai mata haka ba."
Tare suka fita tana ta mita har ya rakata bangaren ta sannan yai mata sai da safe ta rufe kofa ya juyo yana murmushin. Falo ya koma ya zauna yana aiki a system.
Aliyu kuwa bayan su Inna su fita gadon ya dinga kallo a haka Ummi ta dawo yai sauri ya dauke kansa yai kasa dashi. Yace
"Ummi gaskiya ki daina bata komai tana ci yana da kyau ta samu abu mai kyau taci dan ya gina jikin ta da na Babyn amman kalle ta fa yanzu duk jikin ta ba kwari saboda bata cin abun gina jiki."
"To shikenan amman wannan ma fa is nutritive ta saka protein as gyada, ta saka alayahu as vitamin and some vitamin, she put fat and oil, ga carbohydrate it's balance."
"Ummi she should eat first class protein not second class."
"Shikenan ni bamu gaisa ba."
Kai ya shafa yana murmushi ya karasa wajen ta ya rumgume ta yana fadin
"Ummi na Barka da dare da fatan kin dawo lafiya ya hanya?"
"Alhamdulillah! Ya kake ya aikin?"
"Ji yadda duk na rame Ummi wallahi I miss you!"
Kansa ta shafa tace
'Na dawo ai kaci abinci?"
Cikin sa ya shafa sai ya kalli gado yace
"Rabo na da abincin kirki tin tafiyar Ummi na."
"Ai na dawo muje kaci abinci!"
"Ummi yanzu ya zamuyi da yarinyar nan ita me zata ci?"
"Taki cin komai faten Inna ta dan sha da kunu to suma tai amai amman tinda muka hadu abinda taci da yawa kenan!"
"Allah sarki!"
Ummi ta kwashe kwanukan ta bar basket da flask din tea sannan ta wuce Aliyu yabi bayan ta yana tafe yana waiwayon dakin har suka sauka. Ba kowa a falo, zama sukai a dining Ummi ta bude flask ta zuba masa abinci ya janyo ya wanke hannun sa a bowl sannan ya faraci yana ci yana lumshe ido hadi da gyada kai ko magana ya kasa malmala daya yaci yai hamdala yasha lemo da ruwa sannan ya kalli Ummi yace
"Ummi ta dawo ciki na ma yasan Ummi ta dawo dan yau ya koshi."
"Allah shirya ka duk yunwar ai na zata zakaci more than two ball!"
"Ummi more two inkai ina ai in samu ince dai kar ya zama ban cin ba. Kinsan jiya Inna wani gashin tukunya tayiwa kaza kinji kamshi dukka gidan nan amman cinya daya ta sammin ta tadan kwadayi fa."
Ummi tace
"Sai kaje ka siya ai!"
"Kinsan ko na siya bazai dadin nata ba fa. Kuma Ummi da gayya tayi min haka!"
"Ai sai ka lallabata!"
"Ummi sai da ta gama tsokanata na gamai mata sannan ta fara aikin da gayya tayi haka ai Ummi!"
"Ni dai ba ruwa na tsakanin ku da Inna kun fi kusa."
"Da Innan Allah kiyaye ni kam ai sai su Abbi da Abba su kadai zasu iya da ita."
"Kuma zaku iya da itan duk hakuri zamuyi tayi Allah rabamu dasu lafiya."
"Allah dai ya rabaku da ita, mu kuma ya rabamu daku lafiya."
Agogo ta kalla tace
"Dare yayi gashi na gaji dan bana iya bacci a asibiti let me go and rest!"
"Ok muje na duba jikin nata naga magungunan ta zuwa gobe sai muje clinic na duba jikin nata sosai ko?"
"Allah yayi albarka my son!"
"Amin Ummi nah!"
Ta shafa kansa. Ta mike yabi bayan ta. Tana yadda suka barta. Magungunan ta bashi da file din ta sannan ya fita yana mata sai da safe.
Dakin sa na bangaren Ummi ya nufa dake kasa. Ya bude ya shiga a kan bedside ya ajiye file din da magungunan da wayoyin sa sannan ya rage kayan jikin sa.
Bathroom ya wuce wanka yayi tare da alwala a cikin bathroom nashi mai kyau da tsafta sai ka rantse daki ne dan yadda yake da kyau. Komai na bathroom ɗin glass ne mai ruwan garai-garai, bathroom ɗin katone, mai ɗauko da babban drower glass wanda yake cike da ƙananun kayan sirrin jikinshi kamarsu vets boxes and pants kana towels da rigunan wanka da jalabiyoyinshi masu masifar kyau da tsada da taushi da yawa, sai kuma threequater da kuma turaruka dasu brush da su makilin da dai sauran kayan buƙata na aske private part. Ko ina na kusurwan ban ɗakin da madubai. Sai kamshi yake komai fes dashi gwanin sha'awa.
Sai da ya gama wanka sannan ya karasa yai rolling sure ya koma ya dauki boxes ya saka sannan ya cire towel din jikin. Sannan ya wuce ya dauki wasu cotton kayan bacci milk kala a wanke a goge ya saka ya shafa turare mai dadin kamshi.
Bayan ya fitone, ya nufi bakin gadon shi ya zauna, idonshi ya zubawa woyoyinshi dake kan bedside drower. Wacce take haske ya sa hannun sa ya dauka. A hankali ya saka a kunnen sa. Sallama yayi sannan yai shiru. Bayan sakkanni yace
"Haba matar ni dai na nayi kewar ki. In Uncle Salis ba zai dawo dake ba tabbas na kusa komowa kasar. Sai muyi zaman mu tare ko?"
"Gaskiya ne amman kan lokacin zan so kazo ka duba cikin yan uwan ka na nan ko akwai wacce zatai maka ta maye maka gurbin Maryam!"
"Grandma please kiyi hakuri banki ta taki ba amman a duniya ba wacce zata iya maye min gurbin Matata. Nasan kinsan wacece Maryam Sitti!"
"Ba a cire rai da rahmar Allah Abin so, duk da yadda kake ganin Maryam daban sai kaga Allah ya kawo maka wacce tafi Maryam cikin rayuwar ka. Da kasan zaka samu Maryam din ne a matsayin mata ai baka sani ba amman Allah ya baka dan haka yanzu ma kada ka cire rai da rahmar Allah. Allah yana sane da kai da izinin Allah zai baka wata Maryam din insha Allahu. Yanzu dai bana son kace zaka saka damuwa akan maganar nan amman Abin so ka girma ya kamata by now ace ka kara samu kayi aure ka samu mai taimakon ka da baka shawara a rayuwa."
"In nazo zamuyi maganar Sitti na. Amman masu taimako da ban shawara kun ishe ni Grandma! Ina son ki da kaunar ki!"
"Nima ina son ka da kaunar ka ya gidan dasu Ummi dinka?"
"Grandma Ummi yau ta dawo bamu jima da rabuwa ba. Tazo mana da bakuwa......"
Nan ya bata labarin zuwan Maryam da komai.
Murmushi matar tayi tace
"To Allah bata lafiya ya raba lafiya!"
"Amin! Yaushe zaki dawo Nigeria?"
"Sai lokacin da Salisu ya barni ya nace wai ban gama ganin likita ba ni kuma ina da kai wane likita zan ta tsayawa gani!"
"Gaskiya ne dan bana nan ya dauke ki ne amman da ba zai dauken mata ba."
Haka suka gama wayar su sannan sukai sallama bayan tai masa addu'a. Dayar wayar ce tayi haske ya dauka yace
"Mami yanzu nake shirin zuwa fa."
Yai murmushi yace
"Ummi na ai ta dawo sai a hankali kafin ki ganni!"
Yai murmushi sannan yace
"Sai da safe!"
*Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*
"Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 41
By
*MARYAM S INDABAWA*
Hakuri da Juriyya Online Writer's ✍
HAJOW
File din da ya ajiye ya dauka ya fara dubawa a nutse sai da ya dauki kusan 1 hour yana duba file din da nazarin abinda ke ciki sannan ya dauki bag din medicine duba su yayi ya ajiye. Kan gado ya hau ya bude hannun yai addu'a ya tofa ya shafe dukka jikin sa. Ya kwanta yana mai ambaton Allah a zuciyar sa da saman leben sa.
Karfe 3:30am ya mike bandaki ya shiga ya watsa ruwa ya fito daure da towel, ya fito yai rolling din sure ya dauki wata brown kalar jallabiya wacce take a goge ya saka ta sannan ya dauki hula, tashi ka fiya naci ya saka ya shafa turare mai dadin kamshi.
Kan sallaya ya hau yin sallah sannan ya zauna yana tasbihi ga Allah. A haka aka kira sallah ya tafi massalaci yana zuwa yai rala'atanil firij sannan aka tada sallah asuba. A masallaci ya zauna yai karatun Alkur'ani da azkar. Karfe bakwai ya fito daga masallacin dake jikin gidan su wanda masallacin ma a cikin gidan su aka cire shi.
*
Ummi kuwa daki ta koma tai wanka ta shirya cikin kayan bacci dakin Abbah ta nufa ta same shi yana aiki a system zama tayi tace
"Ranka ya dade bakai bacci ba?"
"Banyi ba wallahi aikin nan nake son na karasa!"
Kai ta karya tace
"Daman nazo nai maka sai da safe ne!"
Dagowa yayi yace
"Ina zaki?"
"Alfarma nake nema zani wajen yarinyar can kaga halin da take ciki in da mutum a kusa da ita zata fi jin dadi!"
"Ni kuma sai ki barni."
'In ka barni in kace a'ah kuma ba zani ba. Amman nasan ka da taimako."
Hannun ta ya kama yace
"Bazan hanaki ba amman tayaya zakina kula dani?"
"Baka da matsalar wannan insha Allah!"
"Shikenan tashi kije ki kula da ita."
"Nagode sai da safe!"
Ta mike ta fita. Maryam tana ta bacci kan gadon ta hau ta kashe wuta ta kwanta. Can dare Maryam ta tashi da yunwa da ishi mikewa tayi ta kunna fitila sannan ta diro kafar ta kasa. Basket din dazu ta gani ta nufa ta bude ta dauki spoon ta fara shan faten, tana cikin sha Ummi ta mike ta tsaya kallon ta tasha da yawa ta shiga bandaki ta dinga kakarin amai amman batai ba. Can ta fito ta zauna a bakin gado tana rawar sanyi.
Ummi tace
"Zazzabi kuma kike ji?"
Kai ta gyada ta miko mata bargo ta lulluba baccin da basu koma ba kenan dan yadda jikin Maryam yai zafi.
Sai asuba bacci ya dauke ta Ummi tai sallah ta tashe ta tayi sallah ta koma bacci mai nauyi ya dauke ta
A hankali yake taku cikin kamala da nutsuwa a haka ya karaso cikin gate din nasu da yake gaisawa da securies din gidan nasu sannan ya nufi sashen Ummi kai tsaye. Ummi daga nan dakin Abbah taje suka gaisa sannan ta sauka ta fara aikin gidan duk da ba datti yai ba ta saka turare mai dadin kamshi sannan ta shiga kitchen
Ba kowa a babban falon dan haka dakin sa ya wuce kai tsaye yana shiga ya cire tattausan jallabiyar dake jikin sa ya shiga bathroom daga shi sai gajeren wando da singlet.
Wanka yayi cikin tamfatsen bathroom ɗin nashi. Yana fitowa, ya wuce gaban dresing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikin shi ya karato.
Gaban wardrobe ya karasa ya shirya cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wando kayan sun kasance farare ƙal-ƙal ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue black color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma baƙiƙƙirin mai sulɓi da sheƙi, hular itama farace sai ratsin blue black, hakama takalman sawunshi da suka kasance half cover, Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin ɗigon blue mai garai-garai. Yai wanka da turare wanda nan da nan kamshi ya kara cika dakin.
Wayoyin sa ya dauka ya zura a aljihu sannan ya dauki jakar system ɗinshi ya ɗauka da hannunsa na hagu kana hannunshi na dama rike da counter yana dannawa a hankali tare da motsa lips din sa dake ta sheki kamar wanda ya shafa man lebe.
A haka ya fito daga cikin ɗakin nashi. Ya karaso cikin tamfatsen falon Ummi. Ido ya lumshe lokacin da ya shaki kamshin turaren da Ummi ta turara mai dadin kamshi. Ji yayi an dafa shi.
A hankali yake juyo yana ganin Ummi ce ya rumgume ta yana fadin
"Good morning My Ummi!"
"Morning too my son how are you, how was your night?"
"Alhamdulillah! Ya gajiyar ku ya mai jiki?"
"Alhamdulillah!"
Ta kamo hannun sa suka karasa dinning area, kujera ya ja ma Ummi ta girgiza kai tace
"Zauna"
Zama yayi bisa kujerar, kana, ya kalli Ummi yace
"Abbah fa?"
"He has alot to do har ya fita!"
Ta janyo flask ta tsiyaya masa ruwan tea, zata zuba madara ya rike hannun ta yana fadin
"Ummi kina kara sangartani fa shiyasa in bakya nan nake wahala kawai!"
"In ban maka ba wa zanyi wa?"
"No one Ummi but by now you have to rest ni na cigaba dayi miki ko?"
"Ah haba ni kuma in ka tafi ka barni fa."
"Ina zan tafi na barki Ummi?"
"In kai aure mana."
"Ko nai aure i will always be with you Ummi!"
"Tayaya My Son!"
"Dauke