Showing 42001 words to 45000 words out of 232912 words
Chapter 15 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
bata zabi ta zabi duk kasar da take so dan karasa karatun ta, domin hakika irin wandan nan yaran ba karamin cigaba suke kawowa ba."
Dai dai lokacin da Maryam ta karasa ta tsaya inda aka dauko award da gift da akai raping nasa mai girma shugaban kasa da kansa ya mika mata wannan kyautar sannan aka miko mata kyauta daga bangaren isilamiyya wanda aka ce Malam, Sheikh Muhammad Jabeer shi zai bata a matsayin sa na malami kuma uba ga Maryam wanda wajen ya dau kabbara wasu suna fadin
"Ah ai dole ashe yar Malam ce za tayi abinda yafi haka ma."
Wata tace
"Ai fa ko maganin karatu ya bata."
Dayar dake gefen su wacce take mahaifya ga aminiyar Maryam tai murmushi tace
"Hmmm daga Allah ne dan Malam bai taba basu abu dan suyi kokari ba dai dai tin suna yara na basu tsari da kuna duk abinda ya dace wanda tin a can suka samu gogewa a kwakwalwar kuma ma banda abin ku, ya'ya nawa ne a ya'yan nasa basu da kokari su kuma ace me?"
"Ai fa kuma haka ne. Amman dai yarinyar ta burgeni kuma karama da ita."
"Shekarar ta sha bakwai watan azumi zata shiga sha takwas"
"Allah sarki Masha Allah."
Ta fada ta mai da ido kan Maryam wacce hawaye ke zubo mata a idon ta. Lordspeaker aka bata dan tayi bayanin karshe a makarantar, wanda ta amsa tayi kasa da kan ta. Hawaye na zubo mata.
Aliyu dake zaune ne ya fara kokarin mikewa da sauri na kusa dashi ya rike shi juyowa yayi yace
"Menene haka Alkasim?"
"Ina zaka je?"
"Bakaga kuka take ba!"
Ya fada kamar shima zai kukan.
"Haba Aliyu wai meyasa kake haka yanzu can wajen ta zakaje ko......"
Ai bai barshi ya karasa ba ya kwace hannun sa ya mike da sauri ya nufi stage din wanda security ke tsaye a wajen yana zuwa suka bashi hanya ya wuce. Handkerchief ya zaro a aljihun sa ya karasa ya amshi lordspeaker ya mika mata, dagowa tayi ta kalle shi ya sakar mata murmushi cikin muryar sa mai dadin sauraro yace
"Goge mata hawayen ki *Matar Haydar* "
Amsa tayi ta goge hawayen nata wamda kamshin turaren Aliyu ke jikinsa, abin da ya kara kwantar mata da hankali kenan, sai da ta share hawayen sannan ta dago, murmushi yake sakar mata, dan haka itama murmushin ta sakar masa.
"Ma'ul ayn!"
Ya kira sunan da yake kiran ta dashi dagowa tayi yace
"Nasan kukan farin ciki ne but please kiyi komai kamar yadda aka tsara ina tare dake (am with you) kinji!"
Kan ta tayi kasa dashi, tace
"Stay by my side please (Ka tsaya a gefe na dan Allah) My Hayyat!"
Kai ya gyada mata sannan ya mika mata lordspeaker ya koma bayan ta ya tsaya kamar bodyguard din ta.
Rukayya da Aisha dake wajen zaman su wanda suke kawaye ga Maryam ne suka sakarwa juna murmushi. Rukayya tace
"Oh Yaa Haiydar da Maryam ko?"
Dariya Aisha tayi tace
"Allah har so nake ayi bikin nan naje naga irin soyayyar da za a sha kina gani dai ko kwana biyu bayayi bai zo ya ganta ba."
"Kinsan ni ba wannan ke dauren kai a soyayyar su ba sai ko ciwo daya yayi sai daya yayi."
"Shakuwar tasu ce tayi yawa. Allah dai ya kaimu wani satin mu mika masa matar sa mu huta."
"Sai su cinye kan su, mu huta ba. Ma huta da kullum yace *Matar Haiydar, ko Ma'ul Ayn"
Sukai dariya. Aisha tace
"Kin manta da *My din My* kenan"
"Sunan nasu ne ba adadi but wanda suka fada din kenan *Matar Haiydar* sunan yana min dadi."
"Ko *My din My* "
Sukai murmushi.
Maryam kuwa jin sa a bayan ta sai ya kara mata kwarin gwiwa tayi gyaran muryar sannan ta bude baki cikin muryar ta mai zaki da dadi tace
"Assalamu alaikum!"
Wanda sautin muryar ta mai dadi da zaki ya karade duk wajen ya janyo hankalin kowa ya dawo kanta, akai shirubkanarbruwa ya cinye su, sai ido da suka zuba mata,
"Sunana Maryam Muhammad Jabeer wacce nake matsayin Head student ta wannan makarantar gaba daya.
Ina Mai farin ciki da Allah Ya hadamu a wannann rana Mai Albarka wacce take cike da abubuwa da dama, ranar da ta kasance ranar farin ciki, Ina miqa godiya ta ga Allah (S.W.T) da ya hada mu a wannan rana, Ina miqa gaisuwata ga manyan ba'ki na musamman da malaman mu da sukayi tsayin daka dan ganin cewa burin mu ya cika, suka bada gudunmuwa dari bisa dari, Ina kuma mi'ka gaisuwata ga Iyaye na Yan uwa na, Yaye na, da suka tsaya min har na kawo wannan matakin da aljihun su da jikin su da addu'ar su, sannan ina mika gaisuwa da fatan alheri ga duk member ta makarantar nan class mate dina da duk suka ban goyan baya wajen ganin komai ya tafiyu dai dai dan ba wayo na bane ko da bara ta bace."
Ta dan tsagaita taja numfashi sannan ta cigaba da magana wanda in tana maganar kamar baturiyya dan yadda take fitar da komai dai dai a tsare cikin nutsuwa da iyawa
"Wannan makarantar tana daya daga cikin makarantun da wuya a same su amman cikin hukuncin Allah yasa na zamo daliba a ciki wanda wasu na neman gurbin da kudin su ma basu samu ba. Gaskiya fadin irin karuwar da muka samu a wannan makarantar ba karama bace, domin kuwa ko ba komai mun ilmantu kuma mun fa'idantu sosai, ko a yau na mutu na cika buri na, na zama hafiza na haddace Alku'ani wanda shine babban buri na a duniya, wanda ya tsaya maka wajen samuwar cikar burin ka kuwa babban masoyi ne a gareka wanda suka hada da malamai na, iyaye na, My Hayyat duk ina godiya dan ban da abinda zan biya ku sai addu'a Allah ya saka muku da gidan aljanna ya bani ikon amfani da abinda na sama"
Hawaye ne ya zubo mata ta sa handkerchief ta dan share sannan tace
"Nayi matukar farin ciki da har bansan da wane kalma zan mika godiya ta ba, da nuna farin ciki na ba zan bawa yan uwa na shawara akan mu dage mu samu mu cika burin mu da na iyayen mu dan duk wanda iyayen suka kawo shi wannan makarantar da kudin ya kusa 1M ya kamata ya tsaya ya basu farin ciki ya bawa kan sa da malaman sa farin ciki a karshe ina muku fatan alheri."
Juyawa tayi ta fuskanci Malam Muhammad Jabeer ta dan duka tace
"Fatan Alheri a gareka, "
Sannan ta kalli Iyaye mata tayi musu haka ta juya ga Director da malamai tayi musu haka sannan tace
"Nagode kwarai da karamcin da muka samu Ina fatan yadda muka hadu lafiya Allah ya maida kowa gida lafiya. Maryam Muhammad Jabeer Bisalam!"
Tafi aka dauka raf raf. Har ta bada lordspeaker zata juya Malamin yace
"Maryam kan ki zauna ina son ki jan hankali akan ilimi da mahimmancin sa ga mata."
Juyowa tayi ta amsa lordspeaker sannan ta kara sallama wanda yasa aka karayin tsit sannan tace
"Alhamdulillah duk wanda yake nan nasan yasan mahimmancin ilimi amman nasan maganar da nake ba iya nan zata tsaya ba kila a wata kasa can ma wasu su gani ko anan kasar to ni fata na gareku ko da an gani ayi amfani da abinda zan fada.
Ilimi shine haske da yake haskaka maka hanyar da kake zagaya duniya baki daya. Hakika daga lokacin da baka da ilimi ka zama makaho, kurma, bebe ku fadan tayaya mutum zai ji dadin rayuwa a haka to ilimi zai kore maka duk wannan abun.
Masana na cewa in ka ilimantar da namiji ka ilimantar da mutun daya amman in mace ka ilimantar tamkar ka ilimantar da duniya ne.
Ina masu cewa ilimin mace haram ne hakika ba haka bane sabida a duk lokacin da matar ka take da ilimi ko a mu'amala zamantakewar aure zaka ga canji da abubuwa dan Allah maza ku gwada in kana da mata guda mara ilimi auro mai ilimi wallahi hatta matar ka ta gida zata koyi abu a wajen ta shin ta samu ta kawar mata da wannan jahilcin ko kuwa haka nan ko ta tarbiyyar ya'ya in ka hada mai ilimi da marar shi zaka ga banbanci ta tarbiyya kai har kula da kai kan ka.
Ba wai kin bawa mace ilimin zamani kawai ba har na addini ba wai in ka bata aka ce tai aiki ba babban aikin ta zaka ganshi a gida dan wallahi daga ranar da ka dauke ta ka kai ta, ta samu ilimi kai da kanka zaka gane banbanci.
Babban misalin da zan baku shine akwai wata mata wacce tana zaune da mijin ta da yaran ta cikin rufin asiri mijin ta yafi karfin komai ya dauke mata komai na rayuwa wanda ya bata ilimi amman yace aiki sam ba za tayi ba haka ta zauna dashi lokaci daya Allah ya dauki rayuwar sa, bayan ya rasu ta koma gidan yar ta suka cigaba da rike ta da ya'yan ta bata da damuwar kowa, wanda kowa ke taimaka mata yaran in sallah tazo sai su samu kaya sama da kala goma, shekara daya a tsakani da mutuwar mijin ta mijin yar ta ya rasu, daga lokacin suna samun rufin asiri itama yayar bayan shekara ta rasu rayuwa ta fara basu kashi wanda a lokacin matar nan ta dauki takardun ta, ta koma ta nemi aiki ta samu dashi ta ke rike yaran ta da ya'yan yayar tata. Shin yanzu kunga amfanin ilimin nata ko? Da bata da ilimin wane hali kuke zata zata fada zata iya shiga ko wanne hali ko karuwanci, ko bara ko aikin wahala da karfi shin da wannan ba gwara aikin da zaka ci halak ba.
Bance kowa zai fada wannan rayuwar ba amman kana hango kan ka a cikin ta. Bance dole sai aiki ba kina gida zaki na dan yiwa yara lesson da ilimin nan zaki operating business ta online da abubuwa da dama. Hakika amfanin ilimin mata yana da adadi bashi da iyaka dan haka iyaye maza mu daure muna samawa yaran mu ilimi domin in da ilimi barna zata ragu sosai wani yana fadawa barna ko halaka na rashin ilimi dan haka mu daure mu ilimantar da ya'ya mata. Nagode."
Raf raf raf raf haka wajen ya dauki sowar tafi kowa da abinda yake fada akan Maryam domin yarinya karama mai hankali da nustuwa da kalamai kamar na manya. Lordspeaker ta bayar ta juyo ta kalli Aliyu da ya sakar mata murmushi yana bin ta da wani kallo mai ma'anoni wanda duk ya sakar mata da jiki. Dan hararar sa tayi ta gefen ido tace
"My Hayyat please ka bari!"
Ta fada tana yin gaba bin bayan ta yayi yace
"Na bar me?"
Juyowa tayi ta tsare shi da idanun ta da sauri ya runtse idon sa murmushi ta saki shi kuwa lips din sa ya dan datse da hakori yace
"Zan kamaki ne ai nace ki dainai min irin wannan kallon kina zauta ni."
"Ni kai min!"
Kwafa yayi ya juya ya tafi. Murmushi tayi ta juya itama ta koma wajen zaman ta haka aka cigaba da bada kyauta ana basu damar yin bayanai da godiya. Takeaway aka fara rabawa iyayen yara da daliban wanda hudu saura aka tashi taro duk iyayen maza aka tafi sallah. Matan ma masallaci akaje akai sallah. 4:15pm hall din ya kacame an saka Kida yan matan sai rawa suke.
Maryam na fitowa daga hostel junior din su suka biyo ta da gift din da aka bata wanda ba wanda ya samu kyauta kamar nata abubuwa masu yawa. Haka a cikin JS1 to 3 and SS 1 to 2 duk kowa akwai abunda zai bata kowa da sunan sa da class din ta dan haka kaya ne masu yawa ta hado su. Yaa Alkasim da Biba mai aikin su ne suka amsa suka kai mota sannan suka dauko mata bag din da zata raba wanda a jikin bag din an saka hoton ta tayi kyau tana murnushi kamar zatai magana a fili. A cikin jakar memo da pen da handkerchief da handpan da lemo da ruwa da snacks aka wasu an saka musu agogo wasu shoe wani hijab duk dai a cikin jakar.
Special hall ta nufa inda tana shiga ta hango Ammin ta da sauri wanda in ka kalla zaka ce bama tafiyar take so ba ta karasa ta fada jikin Ammi tana fadin
"Ammi nah!"
Rumgumme ta Ammi tayi tana shafa bayan ta tace
"Auta ta an girma fa. Allah yasa ki amfani karatun naki"
Yaya Abdullahi wanda shi take bi ne ya karaso yana fadin
"Wannan magen ce ashe."
Ammi ta kalla tace
"Wai Ammi nice mage."
"Kyale shi kishi yake "
"Ammi akan me zan kishi bayan daga next week zata bar gidan mu gaba daya ta barmin ke sai dai tazo da ziyara fa."
Hawaye ne ya hau zubo mata ta matse Ammi a jikin ta tana fadin
"Wai Ammi haka?"
Yaa Fadima da Yaa Aliyu ne da Ummah mahaifiyar sa suka karaso leka fuskar Maryam yayi hankali a tashe yace
"Kuka kuma wa ya taba min ke?"
"Ba Yaa Abdullah bane wai daga next week zan bar Ammi
"Waya fada masa a mu kullum muna tare da Ammi ko an mana auren ko?"
Kai ta gyada masa dai dai karasowar Yaa Alkasim da Biba da mai daukar musu picture. Dagowa tayi a jikin Ammi ta juyo tana ganin Ummah ta fada jikin ta tana fadin
"Ummah nah!"
"Na'am Daughter na congratulations!"
"Thanks Ummah na."
Kan ta ta dafa tace
"Muna alfahari dake "
Murmushi Maryam tace
"Nima ina alfahari daku Ummah na."
Mai picture ya dauke su, nan ya fara daukar su. Can ta fara wage wage Yaa Aliyu dake gefen ta ya matso yace
"Menene?"
"Ina Abbi?"
"Suna nan waje "
"My Hayyat muje ai mana picture nasan Abbi yanzu sai yace tafiya zai yi."
Tayi gaba yabi bayan ta, mai hoto yabi bayan su. A can parking space suka same su shida Gwamna da Shugaban kasa da Sarki. Suna tahowa Security suka tsare su saboda Shugaban kasa. Dagowa yayi ya hango su yace
"Ku kyale su."
Karasawa sukai. Ta durkusa har kasa ta gaisu Amsawa sukai Shugaban kasa ya kamo hannun ta yana fadin
"Allah miki albarka."
"Amin!"
Suka amsa
Abbi ta kalla ta dan karya wuya tare da shagwabe fuska tace
"Abbi tafiya ko?"
"Eh Maryam tafiya zamuyi."
"Ayyah Abbi ba ai mana hoton tarihi ba fa."
"To azo ai mana."
Ya fada yana kiran Yaa Alkasim yasa ya dauko masa kati a jaka a can mota ya juya ya tafi. Nan akai musu sannan aikai musu har da shuganban kasa da gwamna da Sarki. Sannan Yaa Aliyu da ita suka saka Abbi a tsakiya akayi musu. Ana gamawa Yaa Alkasim ya dawo ya mika masa amsa yayi ya mikawa Mr president yace
"Katin daurin auren yar ku sati mai zuwa!"
"Wacce kenan!"
Maryam ya nuna musu wacce tai sauri ta sunne kai sannan ya nuna Aliyu yace
"Ga angon."
"Masha Allah! Allah sanya alheri insha Allahu zan zo da izinin Allah."
"Allah ya yadda!"
Ya bawa Gwamna da Sarki nasu dukka sannan su Maryam suka koma ciki nan taje ta dinga raba bags din ga classmate dinta da junior din ta kowa ta bawa sai an musu pictures haka suka dinga yi suna tare ita da Aisha da Rukayya duk inda zasu je.
Yaa Aliyu kuwa idon sa da hankalin sa duk na kan ta. Duk motsin ta ji yaje kamar ya dauke mata dan kar ta gaji. Haka akai ta taro wanda duk dalibai da malamai dai da ta bawa bags din kuma har ragowa sukai.```
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 14
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Karfe shida duk sun fito suna parking space sun rumgume juna ita da Aisha da Rukayya. Sai kuka suke. Yaa Aliyu ne ya karasa yace
"Ma'ul Ayn menene na kukan?"
Kukan take bayan ta sake su. Ya kalle ta cikin so da kulawa yace
"Amman kinsan bana son kukan ki ko?"
Kai ta gyada yace
"To stop it in bakya so nima na fara!"
Hannu tasa ta fara goge hawayen duk da tana gogewa yana kara zubowa ya sa handkerchief yana goge mata sai da ta daina kukan yace
"To ku menene na kuka naga next week kuna tare fa."
"Haka ne Yaa Haidar, Besty yaushe zamuje rabon?"
"Rabon me?"
Yaa Aliyu ya tambaya.
"Kati man."
"No My Queen ba rabon da zatai zan kawo muku kuje ku raba ku bar min Mata ta huta yadda take kwana bata bacci dis week ramuwar bacci zatayi ko Baby?"
Kai ta gyada. Aisha tace
"Mu kuma kada muyi?"
"No ku da ita da bambanci ita aure zatayi gwara ta huta kan mu tare ko? Ku kuwa kullum zakuyi ta baccin ku, ku yini ku kwana kuna yi."
Yaa Alkasim ne ya karaso yace
"Please Aliyu ka barta suyi sallama kafiya jaraba kai kam."
"What?"
Ya fada yana kamo hannun sa sukai can gefe ya murda hannun sa yace
"Ai Matata ce ina ruwan ka."
"Za dai ta zama matar naka ka bari in ta zama sai ka takura mata, wallahi irin kune ke sa mace ta rame dan jarabar ku."
A can kuwa Rukky ce tace
"Allah Besty kinji dadi kin samu mai son ki."
Murmushi tayi ta kalli gefen su Yaa Haidar sai ta saki murmushi tace
"Alhamdulillah! Kuma zaku samu masu son ku da yaddar Allah."
Aisha tace
"Allah yasa. Amman fa naga Yayan namu zai yi naci Besty!"
Rukayya ce tace
"Itama ai da alama."
"Kuji sharri mu ba ruwan mu."
"Ku din kada ki manta ko ya yazo sai kin canja ki ta wani lumshe idanu kamar....."
Duka ta kai mata tace
"Iyee kace ido kika sa min."
"Hmmm ni ai last dawowar da yayi da ita nan da taje ganin likita nasha mamaki naga love wallahi kamar ya dauke ta haka ya dinga yi. Gaskiya zan zo ina koyar course na soyayya."
"Ji ku,"
Ta fada tana nuna su
"Ku wa yasan ya kuke dan dai ni kullum yana zuwa shiyasa kuka saka mana ido."
"Hmmm Allah Maryam ki godewa Allah Yaa Haidar na son ki kinyi dace sai dai muce Allah tabbatar da alheri. *Matar Haiydar* in the next seven days, Allah nuna mana."
"Amin. Allah ya kaimu next week musha shagali mu mika ki dakin Yaa Haidar sai ku cinye kan ku."
"Ai kam ko kadan bazamu rage kan mu ba."
Maryam ta fada
"Ku ba?"
Rukayya ta fada.
Kanwar Aisha ce ta karaso tace
"Yaya Aisha wai kizo mu tafi"
"Toh!"
Ta fada tana fadin
"Sister bye!"
Har ta juya Maryam tace
"Larabar zaki taho ko?"
"Insha