Showing 117001 words to 120000 words out of 232912 words

Chapter 40 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1255

daina turo kan nasa da yake hankalin Aliyu ya tashi nan da nan yasa hannu kan a shiga da ita ya nufi dakin da take.

Kwance ya same ta idon ta a lunshe ya karasa ya kamo hannun ta da sauri ta bude ido tana ganin sa ta bude baki a hankali tace
"Yaa Haidar...."
"Na'am Habibty sannu Habibty!"

Ya daura hannun sa akan ta. Ido ta lumshe tace
"Yaa Haidar ba zan haihu ba, Yaa Haidar ba zan cika maka burin ba, Yaa Haidar naso na zama sirrin ka ta har abada, na so na cika maka buri na haifa maka ya'ya masu yawa amman Yaa Haidar ba zan iya ba."
"Zaki iya Habibty zaki iya kice zaki iya kinji!"

Kai ta girgiza tana fadin
"Yaa Haidar Ciki na!"
Da sauki ya mike yana tofa mata addu'a a cikin, ido ta lumshe ta kamo hannun sa tana fadin
"Nasan tafiya zanyi Yaa Haidar ba zan iya ba. Kan na tafi zan gode maka abisa yadda ka kyautata min da yan uwan mu, ina son ka Yaa Haidar amman ba yadda zan haka zan tafi na barka. Dan Allah Yaa Haidar kar ka taba mantawa dani kana sani a addu'a kaga ban bar baya ba kai kadai gareni sai iyaye na. Kaji Yaa Haidar!"

"Dan Allah ki bar yi min wannan kalaman naki masu kama da wasiya na fada miki zaki haihu mu cigaba da rayuwar mu i know my Baby jaruma ce ko?"
Wani murmushi tayi, tace
"Ka yafe min Yaa Haidar! Ka yafen!"

"Baki min komai ba Habibty i forgive you!"
"Thank you my soul mate, thank you my love, i love you, i will miss you, Allah sadamu a aljanna."

Kiss ya kaiwa goshin ta yace
"Za a shiga dake aiki Baby a ciro mana nasan Matata jaruma ce. *Matar Haidar* jaruma ce ko?"
Murmushi kawai tayi yace
"Say yes!"

"Yaa Haidar jarumi nah!"
Ta fada tana lumshe ido sai kuma ta bude a hankali tana kallon sa ba ko kitawa, nurses ne suka shigo da likitoci za a tafi da ita ya mike ta kamo hannun sa sai kuma ta dafe cikin ta da dayan hannun yadda yaji rikon da tai masa yasa ya gane azabar ciwo ne, likito ne suka yo kan ta nan sukaga yadda dan ke son fitowa, amman ba karfi a jikin uwar da babyn fara taimaka mata sukai sai ta fara salati hannun ta rike da na Aliyu jin tana salati yasa ya durkuso kan ta yana mai yi tana amsa a hankali yaji tai shiru sannan ta saki hannun sa da sauri ya dago yana fadin
"Habibtyyy...."

Wannan yasa hankalin sauran likitocin dawowa kan su, zata sukai numfashin ta ne ya dauke dan haka suka fara dubawa wasu na son mata connecting oxygen. Dayan doctor dake duba tane yace
"Ta mutu fa!"
Da sauri Aliyu ya karaso yana fadin
"A'ah Doctor Abbas bata mutu ba duba dai!"

Ya karaso yana kama hannun ta dan dubawa, Doctor Khaleel ya karaso yana fadin
"Bari na duba doctor!"
Doctor Fateema dake gefe ta karaso tana saka hannu a bayan kunnen Maryam Doctor Khaleel kuma rike da hannun ta. Ajiye hannun yai Dr Fateema ta girgiza kai. Dr Abbas yace
"Am sorry Dr Aliyu but she...."

Bai karasa ji ba ya zube a wajen da sauri suka dauke shi suka fice a dakin da shi wanda yan uwa hankali ya tashi sunga an fita da Aliyu kamar gawa. Da kyar ya farfado yana farfadowa ya mike yana fadin
"Ina Matata?"
Ya dire kafa. Dr Abbas yace
"Ka tsaya Aliyu!"

Bai saurare shi ba ya fita yabi bayan sa a lokacin har an fito da Maryam za a tafi da ita gida. Abbah ne ya kamo hannun sa suka fita. Aliyu yace
"Abba bata fa mutu ba."
"Na sani Aliyu muje gida kawai."

Kamar mara laka haka ya bisu a baya suka fita a wajen. Da sukaje Abbi ne ya rarashe shi da nuni akan ta mutu fa a lokacin aka suturtata aka kira Aliyu da mahaifin ta. Dakin suka shiga mahaifin na rike da hannun Aliyu. A gaban gawar ya zauna ya kura mata ido ga cikin ta nan kato a jikin ta. Karasawa yai a hankali ya yaye mata fuska. Fuskar nan shar da ita kamar zakai magana ta amsa da sauri ya rufe fuskar yana fadin
"Inna lillahi wainna illahir raiun. Allah ya jikin ki ya amshi shahadar ki na yafe miki Maryam Allah yasaki a aljanna firdausi nayi rashin mata mai so na."

Da kyar aka lallashe shi lokacin da yaga an daga ta za a fita da ita kuwa a lokacin Hankalin Aliyu ya tashi sosai dan gani yake a lokacin kamar mafarki yake so yake ya farka kawai. Abbi ya kamo sa suka fita a mota suka je makabarta inda har an haka kabari, aka ajiye Maryam a bakin kabarin Abbi yace
"Aliyu kamo kan!"

Kallon Abbi yai. Abbi ya gyada masa kai karasawa yai a hankali ya dago kan da bismillah mahaifin ta ya kamo kafafu suka saka ta wanda aka fara rufe ta ganin da gaske ya rabu da matar sa yasa ya fada jikin Abbi daga nan kuma bai sake sanin me ya faru ba.```


*
*
*
*
*
Kiran sallah magariba shi ya katse masa tunanin da yake a hankali Aliyu ya bude idon sa da yai jajir dashi. Ummi ce ta sauko suka hada ido da sauri ta karaso tana fadin
"Lafiya Son?"
Mikewa yayi murya a shake bata fita sosai yace
"Ba komai Ummi!"

Ya nufi daki yai alwala ya fito ya tafi masallaci. Acan akai sallah bai tashi ba sai addu'a da yakewa Maryam bai fito ba har kai ishai yana masjid din sai wajen tara ya fito yana tafiya a hankali ya shigo gida. Ba kowa a falo dan haka yai dakin sa. Kwanciyya yai akan kujera yana pressing counter dinsa.

Ummi jin shiru har goma ba Aliyu yasa ta fito lekawa tai ta window taga ga motar sa dakin sa ta nufa a kan kujera ta same shi kwance karasawa tai ta dafa shi sai a lokacin ya san da mutum a dakin. Mikewa zaune yayi ta kalle shi tace
"Me yake damun ka?"
"Ummi am missing my wife, i can't stop recalling Maryam. Maryam is such a good and kind lady she loves me, she give me all i want, she always want to see my smile my happiness how should i forget her Ummi.... Nasani zakice naki daukar takwalli Ummi in dai zan tina Maryam to zuciya ta na raunana ina ma ni na mutu ita ke raye."








*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe, Allah ya jikanmu. Amin*



*Antty*
[
[11/21, 10:19] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 48

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Kano
A haka suka cigaba da neman Maryam ba dare ba rana, Alkasim kuwa saboda Maryam ya dinga tafiye tafiyen gari gari duk inda yaje yake bada cigiya ko zai samu wanda zai ga Maryam. Wani aiki da ya kai shi Bauchi ranar da ya gama zai dawo kamar da wasa duk inda ya tsaya sai ga nuna picture din Maryam ko akwai wanda Allah zai sa ya ganta, a lokacin ya tsaya a wajen wani mai siyar da lemo a hanya bayan sun gaisa ya nuna masa picture din Maryam, kallon hoton mutumin yai, sai ya shiga shago da sauri ya dauko wata jaka ya mika masa, a zabure Alkasim ya amsa dan ba zai manta ba tare suka siyo jakar, sunje shopping zata makaranta taga jakar tace lallai sai ya siya mata, dan haka yana amsa ya hau budewa yana fadin
"Ina Maryam din a ina take?"

Kai mutumin ya girgiza yace
"Yau kusan wata biyu kenan, da na tsinci jakar nan, anan saboda akwai wata rana wata yarinya tazo tsallaka titi wanda anan wasu suka zo suka kusan kade ta, to bamu sani ba dai tana da rai ko bata da rai suka tafi suka bar ta, sai bayan sun bar wajen naga jakar shine na dauka na ajiye, to kaji a inda na samu jakar."

Wata rumguma Alkasim yayiwa jakar hawaye na zubo fuskar sa yace
"Ina suka yi?"
Hanya ya nuna masa yace
"Amman kila asibiti suka kai ta."

Daga nan ya shiga bin asibitoci wanda a ranar bai koma gida ba sai da ya dada sati akan neman Maryam amman ba Maryam sama ko kasa. Hankalin sa ya tashi domin kuwa yaga samu yaga rashi, a haka ya koma gida cike da damuwa.


****
Zaune yake cike da damuwa a dakin sa, wayar sa ce tayi kara kamar ba zai duba ba, dan rabon sa da waya tin mutuwar Haidar, tin lokacin komai ya fita a ransa sannan ga rashin kanwar sa, mostly ma wayar a kashe take, in bai kashe ba kuwa tana flight mood, janyo wayar yayi yana kallon da sauri ya mike yana kai wayar kunnen sa, wani kuka yaji yana son ya taso masa yace
"Ahmad."

"Ba wani Ahmad ku me yake damun ku ne, daga aure duk kun kashe waya, kai sai kace kai ne kayi aure, na shiga damuwa na rashin samun ku a waya amman nasan wancan dadin aure yasa ya manta dani ya kashe waya....."
Sheshekar kukan da yaji ne yasa yai sauri dauke wayar a kunnen sa ganin wayar nayi yai sauri ya mayar kunnen sa yana fadin
"Alkasim meyake faruwa?"

"Ahmad mun rasa Haidar, Haidar ya tafi ya barmu."
Cike da razani Ahmad ya dago yana fadin
"What? Me kake nufi? Ina ya tafi ya barmu?"

Kai ya hau girgiza yana fadin
"Haidar has died for more than three month."

Wani duhu-duhu Ahmad ya fara gani da kyar ya iya cewa
"kai karya ne Wallahi. Haidar din? Haidar aminina fa, a'ah dan Allah kada kai min wannan wasan Alkasim."

Alkasim yasan za'a rina. Ahmad da Haidar abokai ne tin yarinta sannan suka kara karatu tare matsala daya ba a gari daya suke ba sai kuma da ya samu aiki ya bar kasar amman Ahmad shine aminin sa a ta dalilin haka ya zama abokin Alkasim, dan a da ma haka kawai zai zo yai kwanaki a Kano, a garin su Ahmad Aliyu yai service dan a gidan su ma ya zauna. Cikin nutsuwa ya labartawa Ahmad abinda ya faru.

Tamkar karamin yaro haka Ahmad ya rinka kuka. Har wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara murya yace
"Innalillahi wainn illahir rajiun!"
Abinda ya fada kenan wayar hannun sa ta subuce ta fadi, komawa yayi ya zauna hawaye na bin fuskar sa, Alkasim ma na gefe yana kuka, dan kiran Ahmad ya dawo masa da komai baya. Shi kadai yai jinyar rashin abokin nasa, yana gamawa ya tashi ya fara shirye shiryen barin kasar dan ji yayi ba zai iya kara zama a garin ba.

Ranar da zai sauka ya sanar da Alkasim shi yaje ya dauko shi, a airport da suka hadu suka rumgume juna suna kukan rashin Haidar wanda sai ka zata a lokacin akai rasuwar, daga nan gida suka wuce, wajen Mami suka fara nan suka zauna a gaban ta suna ta kuka, da kyar Mami ta lallashe su, daga nan dakin Haidar suka je nan ma kuka suka ci sannan suka tafi gidan su Alkasim.

Wajen Ammi suka je ya gaishe ta yai musu ta'aziyya, bayan sun koma daki ya kalli Alkasim yace
"Ni kuwa ina Maryam? Wane hali take ciki? Na tabbata rashin Haidar ba karamin barazana yai ga rayuwar ta bane."

Hawayen dake idon Alkasim ne ya zubo yace
"Tabbas domin a rashin Haidar muka kusa rasa ta itama, a halin da ake yanzu Maryam bata magana saboda shock din da ta shiga na rashin Haidar."

"Ni na sani, tana ina?"
Kuka Alkasim ya fashe dashi yace
"Maryam bata gidan nan."

"Tana ina?"
"Bayan rasuwar Haidar, Maryam tayi jinya na kusan wata wanda duk muke zaton alhini ne sai dai ashe abu biyu ne bayan alhini sai muka gane Maryam na da ciki har na wata uku."

Da sauri Ahmad ya dago yana fadin
"Da gaske?"
Cike da murna yai tambayar kallon sa Alkasim ya tsaya yace
"Kasan me nace kuwa?"

"Naji kace Maryam tana da ciki, kai Alhamdulillah burin Haidar kenan, amman naji masa dadi ya bar baya mai kyau, Allah ya jikan sa ya raya abinda zata haifa Allah ya bamu ikon kula dashi, dan Allah ka tashi ka kaini naga Maryam na kwantar mata da hankali."
"Ka gane me nake nufi kuwa?"

"Na gane mana Maryam na da cikin Haidar."
"To meyasa kake murna bayan kasan ba a daura aure ba ta samu cikin."

"Wa ya fada maka?"
"Ahmad a ranar daurin auren fa Haidar ya rasu, tayaya kuma zaka ce haka."

Ido Ahmad ya lumshe sannan ya bude yana fadin
"Yanzu wata shida da auren Maryam da Haidar."
"Wanne Haidar din?"

"Kaga kaini naga Maryam tukkuna."
Fuskar Alkasim ce ta sauya yace
"Ahmad a lokacin da Abbi yasan da cikin Maryam yaki amsar cikin ne."

"What Ammi da Mami fa?"
"Ammi ya zatayi she sent her to our sisters house, Mami bata gari but kasan me?"

"No."
"Tin ranar bamu sake ganin Maryam ba yau sama da wata biyu kenan."

Da sauri Ahmad ya mike yana fadin
"Ba a ga Maryam ba to ina ta shiga Innalillahi wainna illahir rajiun."
"Abinda bamu sani ba. Amma Malam ya fada mana tana nan kamar an samu wani mugun ya kawar mata da hankali daga gida, tunani hannun wadan da zata fada domin Maryam bata da lafiya, ga ciki, ga rashin magana."

"Ba zama zamuyi ba ai Alkasim."
"Kasan watan mu nawa muna neman ta? Kasan gari garin da akeje neman ta? Allah ya boye ta a wani wajen muna fatan nan gaba Allah ya bayyana mana ita."

"Innalillahi wainna illahir rajiun shi Abbi bai tambaye ta game da cikin ba?"
"A lokacin ran Abbi ya baci bai tsaya jin komai ba, yace Haidar ba zai taba aikata zina ba."

"Maryam ma haka. Nasan waye Haidar tabbas ba zai taba aikata zina ba dan lokacin da ya samen da matsalar sa cewa nai ya nemi yan mata ya rage zafi amman sam yaki aminta yace gwara ya mutu da haka in ya mutu mai zai cewa Allah, hakika koni Haidar ke min fada akan kula yan mata Haidar yana da tarbiyya da halaiya masu kyau tabbas ba zai aikata zina ba kamar yadda ita Maryam din take ko da abin ya faru da kyar ta yadda ta aminta."

"Ka warwaren wannan zargen ko na gane me kake nufi?"
Zama yayi yace
"Lokacin baya Haidar yazo ya samen akan yana fama da sha'awa wanda ya shasha magani abun bai raguwa dan kai shaida ne har suma yake yi to da ya fadan nace ya samu wata ya rage zafi yaki, ba sau daya ba ba sau biyu ba ya kawon wannan matsalar ta shi wanda a karshe nace ga Maryam nan zai samu nutsuwa yace ba zai taba tunkarar ta da wannan abun ba Maryam matar sa ce, wannan dalilin ma yasa ya fara janyewa Maryam amman ita kuma sai ta fara shiga damuwa idan har yaje ya ganta a makaranta ranar dawowa yake da ciwon ciki mai tsanani.
Tinda ya dauke mata kafa, abin ya dame ta................

Haka ya zayyanawa Alkasim komai daga shi har Alkasim kuka suke na abinda ya faru.



*
Ba karamin tashin hankali Ahmad ya shiga ba domin kuwa ya tausayawa Maryam, take rasuwa Haidar ta saka masa soyayyar Maryam, domin yanzu burin sa ya nemo Maryam ya aure ta ya bata kulawar da Haidar bai samu ya bata a lokacin baya ba, fatan sa yasa tana hannu na gari sannan ta sauka lafiya hakika babyn ta zai samu so da kulawa tamkar baban sa, baban sa mutumin kirki ne ya dauke shi a matsayin amini masoyi, tabbas yayi kewar aminin sa saboda ba shi da tamkar sa shi bashi da mai basa shawara da daura sa akan hanya Haidar ne kawai, sai a yanzu da suka kulle da Alkasim wanda suka kara bazama neman Maryam sosai suka bincike a Bauchi amman duk da ba wani cigaba da aka samu, duk da haka Ahmad da Alkasim basu hakura ba duk wasu garuruwa in suka samu sukaje sai sun bincika.


Abuja
Washe gari Mama na tsaye a window tana ganin fitar Ummi ta fito ta yo sashen Ummi yau ma a falo ta samu Aliyu sai ta kara tsarguwa ya dauke kai ya gaishe ta, ta amsa tana tambayar me jiki sannan tayi sama. A kwance akan sallaya ta samu Maryam na jan carbi, dan walha ta idar ta dan kwanta. Mama ta karasa ta zauna a gefen gado tace
"Ya jikin?"
"Da sauki!"
Tai mata nuni. Mama tace
"Nazo muki da wani karuwa ne in har kika yadda zan biki 5million nasan zata ishe ki kije kiyi rayuwar ki ba takura da sa ido."

Ita fa Maryam tin zuwan matar nan jiya taji bata kwanta mata ba dan haka sai ta tsaya kallon ta kawai. Mama tace
"Nasan irin ku da yawa wasu karuwanci ya fito dasu suka samu ciki su rasa mai amsar ciki su zo su makalewa wasu. To abu daya nake so ki min da wannan cikin duk da nasan bai da uba yanzu zan masa uba zan je na fadawa mahaifin yaron nan cewa kin fada min cikin nan na Aliyu ne shi ya hada komai har kuka hadu da Ummi ta kawo ki gidan nan ki nuna musu anan ma neman ki yake in har kikai min haka ko?"
Mama ta fada tana murmushi tace
"Ni na miki alkawarin baki wajen zama da 5 million kamar yadda na fada miki ya kike gani zaki iya?"

Mikewa Marym tayi ta dauko memo da take rubutu ta fara rubutu sannan ta mika mata. Amsa Mama tayi ta fara karantawa.
"Ciki na yana da uba ba zan taba sheganta shi ba dan haka ki rabu dani, ni ba abinda ya kawo ni ba fatana na samu na tuno rayuwa ta ta baya na koma wajen iyaye na. Yau ko da ace cikin shege ne ba zan taba lakabawa Aliyu shi ba mutanen da suke kai na dare da rana ke kuwa me Aliyu yai miki kike son saka sa a wannan halin?"

"Ban sani ba aiki na kawo miki in zaki min shikenan in ba zaki min ba shikenan arziki ke neman ki kike son guje masa."
Rubutu Maryam tayi a paper ta mike mata amsa tayi ta fara karantawa
"Dan Allah ki kyale ni naji da abinda yake damu na. Arziki na Allah ne in ina da rabo zanyi shi."
Mikewa Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login