Showing 135001 words to 138000 words out of 232912 words
Chapter 46 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
Maryam ta shige kitchen bata jima ba ta fito da dan bowl tana fadin
"Dan ke nayi fa jiya kuma baki zo ba, shine nace zan zo biko sai na taho miki dashi."
"Kai Hajiya Inna shiyasa nake sonki."
Ta bude bowl din kaza ce akai mata pepper chicken ajiye bowl din tayi tace
"Bari na wanko hannu na."
*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*
*Antty*[11/25, 11:27] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώ
ππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 55
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ta shiga kitchen ta wanke ta fito dauke da lemo mai sanyi ta zauna tana ci Inna na bata labari tana ji tana dariya hade da lumshe ido dan dadi nama bata farga ba taji sallamar mutum dankwallin ta dake ajiye akan kujera tai saurin dauka ta yafa a jikin ta, tin kan ya shigo kamshin sa ya danno kai.
Dakin ya shigo, sanye yake da dogon bakin wando da farar riga, mai dogon hannu, ba a inda idon sa y fada sai akan Maryam, kai ya dauke ya karaso gaban Inna ya ajiye mata ledar da ya shigo ya juya ya nufi kofa Maryam tace
"Sannu da zuwa."
"Yauwah."
Kawai ya fada ya sa kai za fita, Inna tace
"An gode Allah maka Albarka."
"Amin!"
Ya amsa tare da ficewa. Inna ta tabe baki tana fadin
"Duk jikoki na nafi son yaran nan amman shi matsala wani lokacin miskilanci da nukufarci ji dai yadda ya ke magana kamar bai so. Dubi dai yanzu fura ya kawon da nono kusan kwarya guda dan yasan ina so."
Ta fada tana leka ledar da ya ajiye mata. Murmushi Maryam tayi, Inna tace
"Wallahi shima yana so na, da sam ba haka yake ba yaro mai fara'a da son mutane amman daga mutuwar matar sa duk ya koma haka, nayi nayi suyi masa aure sunki, da sun masa da kila ya koma yadda yake Allah dai ya bashi mai tausaya masa da son sa kamar matar sa. Ina fada miki yar yayar Babar sa ce acan turai suke inda Najwa take karatu in kinga yadda suke soyayya a da sai sun burge ki, wallahi ban taba ganin Aliyu da ita sunyi fada ba tana da sanyi hali da hakuri yarinyar kirki mai tarbiyya da son mutane ga kyauta to Allah ya fimu son ta shekarar su biyu bata haihu ba sai da ta samu ciki kuma ya hau bata wahala, haka aka sha fama ke dauke matar sa yai ya kai can uwa duniya sai da cikin ya isa haihuwa da kyar ya kawo ta gida ashe rabuwar ta kusa lokacin basu kwana ashirin ba ta tashi da nakuda ina fada miki, ta sha wuya baki ga yadda ya tashi hankalin sa ba ke kace shi ke nakudar haka sukace ba zata iya haihu da kanta ba shine fa za a shiga aiki, ba ai aikin ba Allah ya amshi a barsa kan ai wata wata yaron yabi uwar zo kiga Aliyu wallahi kamar ba zai rai ba ya daina ci ya daina sha ga tunani ai fa nan ciwo yai raf dashi, ciwon nan da yanzu ba tsoho ba babba ya kama shi wai hawan jini, mu dai Allah raba mu dashi ace yaro sai kaji shi da hawan jini ai duniya ta zama abinda ta zama, ina fada miki ga ulcer yaro sai ya hau tsamurewa da kyar da addu'a da rokan Allah, Aliyu yake rayuwa amman da tini shima mun rasa, to fa shikenan tin lokacin ya canja ko magana bai fiya so ba yafi son ya kadai ta abinci kuwa kina ganin sa zandamemen nan sai Aisha ta saka shi a gaba da lallashi, da komai kamar jariri, ai ita dai Aisha yar albarka ce, ta iya riko, kinga yadda ta riki Aliyu kuwa ko uwar sa bata rike shi kamar yadda ta raine shi ba, ita dai tana son yara amman Allah bai bata zaunanne ba, kinga fa haka ta samo mana wani yaro Abubakar wanda na fada miki yana auren yar autata suna can Canada da ya'ya su har hudu, ai Aisha Allah ne kadai zai biya ta, ta kula da Aliyu da matar sa, ke yau suna gidan ta gobe suna gidan su basu da wajen zama tsayayye ita ke dawainiyya da su, ai kuwa itama taji mutuwar haka da rokan Allah fa aka fara samk kan sa, to kinji fa tin rasuwar matar sa ni ban 'kara ganin sa cikin nishadi ba sai haihuwar ki da yadda yake wa yaron ki, dan Allah da iyayen zasu dau tawa ai da an masa aure ko shima zai ga gudan jinin nasa ko? Ace yaro ya girna amman ba aure ga farouk nan ma yana koyi da dan uwan nashi."
Idon Maryam har yayi ja jin labarin Aliyu maikon kwallar dake kwarmin idon ta, ta saka hannu ta goge tana fadin
"Allah mata rahma. Ina rashin masoyi babban damuwa ce ni gani nan na rasa nawa na rasa iyaye na, na kasa sanin kowa nawa sai ku."
Maryam ta fada tana fashewa da kuka. Inna tace
"Haba yar nan ke kuwa kada kiyi kuka wani yazo ya zata wani abu nai miki dan Allah kiyi hakuri, ke kuwa kike da masu son ki, wallahi zan iya rantse miki da Allah ina jin ki tamkar jika ta dan haka ki bar kuka komai kike so ki fada min ni nai miki alkawarin kula dake da miki duk abinda nake so kinji?"
Kai ta gyada tace
"Ban taba haduwa da mutane masu karamci kamar ku ba kun min komai duk da baku sanni ba Allah ya saka muku da gidan aljanna nagode sosai da sosai."
"Ba komai yiwa kai ne kai kasan halin da naka zai fada a ciki? Ki daina kukan to."
Hawaye ta goge Inna ta cigaba da mata hira tana sata dariya har ta dan sake amman abun na damun ta dan labarin Aliyu ya taba mata zuciya.
Fura Inna ta dama musu har da madara da kwakwa Maryam ta saka afirij dan ta dan yi sanyi sannan ta fito tai alwala dan an tada sallah magariba sallah tayi tana zaune tana addu'a har akai isha'i sukai sallah sannan ta mike tace
"Inna zan tafi sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
Har ta kai kofa Inna tace
"Oh zo ki anshi furar ki."
Ta dauko jug Inna ta zuba mata da yawa sukai sallama. Ta fita, ta kusa zuwa sashen Ummi sai ga Farouk nan kallo daya yai mata ya gane tana da damuwa ba kamar dazu da ya ganta ba dan haka ya tsaya kallon ta can kuma yace
"Lafiya dai ko?"
Dagowa tayi dan ita bata san dashi ba. Kai ta dauke tace
"Ba komai."
"To sai da safe."
Suka bar wajen yai bangaren Inna ita kuma tai bangaren su. Tana shiga ta samu Ummi da Aliyu, Haidar a hannun Aliyu yana jijjiga shi, sama tayi Ummi da Aliyu suka bita da kallo Ummi tace
"Lafiya kuma?"
Hannu ya daga alamar 'Waya sani.' Haidar ya kalla yaga yai bacci ya mikawa Ummi yace
"Ummi a kwantar dashi, daga nan kiji me yake damun ta?"
Amsar sa tayi tai sama. Dakin Maryam ta shiga taga bata ciki, motsi taji a toilet ta kwantar da Haidar tare da dauko masa kayan baccin sa ta saka masa ta lullube shi sannan tai masa addu'a zaman jiran fitowar ta tayi. Bata jima ba ta fito daure da towel da hijab a saman kan ta.
Ummi ta kalla ta dan saki murmushi ta nufi doruwa ta dauki kayan baccin ta, ta koma ta saka sannan ta fito hula ta saka akan ta ta nufi gadon tana fadin
"Ummi, Abba bai dawo bane?"
"Ya dawo menene?"
"Na ganki a zaune anan ne."
"To me zanje nai masa?"
Murmushi Maryam ta saki tace
"A'ah ba komai wai nace yaci abinci ne?"
"Yaci nasan yanzu ma ya kwata zauna muyi magana."
Zama tayi a gefen ta Ummi ta kamo hannun ta tace
"A duniya a halin yanzu baki da sama da Haidar to amman Haidar ba zai iya tambayar ki damuwar ki ba, ni din dai nice makusanciyar ki fiye da kowa a yanzu dan haka ki fada min me yake damun ki?"
"Ummi ba komai. Ni ba abinda yake damuna. Me zai damen ina dake?"
"Kin tabbata?"
Kai ta gyada tace
"To Allah ya dafa bari naje na kwanta kiyi addu'a sannan kiyiwa mai gidan nawa."
"To Ummi."
*Allah ya jikan mu ya sa muyi kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
[11/25, 11:27] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 56
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Bayan wata hudu.
Tsaye take a kitchen tana karasa miyar da ta daura, Ummi na gaban sink tana wanke kwanuka, gas din ta rage ta rufe miyar sannan ta tafi wajen Ummi tana fadin
"Ummi nace ki bari na karasa dan Allah!"
Ta dauki kwanon tana dauraye wa. Ummi tace
"Ai na kusa bari kawai na karasa."
Haka suka cigaba dayi Ummi na wankewa Maryam na daurayewa. A haka har suka gaba Maryam ta kwashe ta kai ma'ajiyar, Ummi kuma ta dauraye wajen.
Sallamar Aliyu suka jiyo suka amsa Ummi na fadin
"Mai gida ya dawo."
Ta fita Maryam ta karasa wajen miya ta kashe gas din ta zuba a flask sannan ta dauraye hannun ta. Fita tayi zuwa falo.
Haidar ta gano yana daddafa kujera yana tafiya tare da gwaranci. Aliyu na zaune ya jingina da kujera Ummi na kallon Haidar tana fadin
"Wato Haidar dai ya dage kan ya shekara sai ya taka."
Yana ganin Maryam ya fara daga mata hannu yana fadin
"Ammmmiii Mommmi Annnttti."
Karasowa tai ta dauke shi tana fadin
"Oyoyo yaron Ummi."
Ta dauke shi tare da kallo Aliyu da tin da ta haihu ya daina sakar mata duk wannan kulawar ya daina sai dai Haidar ita daga gaisuwa shikenan. A hankali tace
"Sannu da zuwa Yaa Aliyu!"
"Yauwah!"
Kawai ya fada ba tare da ya kalli inda take ba ya cigaba da danna wayar sa. Ummi dai bata tanka ba itama sai ta cigaba da kallon Haidar dake tai mata gwale gwale shi alallai labari yake bata ita kuma tana ta biye masa can Aliyu ya mike yai daki dukkan su da kallo suka bishi.
Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Zo nan Maryam!"
Mikewa tayi rike da Haidar suka karasa, Ummi tace
"Kada ki damu da halin yayan ki, haka yake wani irin miskili ne ba kasafai aka fi gane abinda yake so ba, amman zan fada miki Aliyu bai son rawar kai sam duk da nasan ke ba ruwan ki, yana son nutsatsen mutum kamar yadda kike bai son hayaniya dan haka please kar ki sa damuwa kinji?"
Murmushi Maryam ta kwakwalo dan sam bata son wannan canjin daga gareshi da safe da rana da dare sai ya dubata da lallashin ta me take so da matsa mata akan abu ko zuwa motsa jiki in tana damuwa yafi kowa damuwa amman yanzu ya canja bai damu da ita ba ko zasuyi kwana nawa bai ganta ba bai damu ba, sam bata son haka amman ya zatayi tinda haka yake zata daure ta daina damuwa insha Allahu. Dagowa tayi ta kalli Ummi tace
"Ba komai Ummi na jima da gane hakan."
"Yauwah Maryama."
Ta mike sukai sama ita da Haidar tana fadin
"Bari nai masa wanka kan ai magariba."
*
8:15pm
Dakin sa ta Shiga da sallama, ya amsa ta Shiga, yana zaune akan carpet gaban sa system Haidar na kan gado gaban sa biskit, alawa da chocolate.
"Ummi!"
Haidar ya fada yana mika mata wata alawa.
"A'ah Haidar kayan zakin nan ai sai ku."
Ta zauna tana fadin
"Shiyasa kake gudowa nan, dan sai abinda kake so kake yi ko?"
Aliyu ya kalli Haidar dake shan alawa, murmushi yayi ya juyo yace
"To Ummi ai gwara abarshi yai abinda yake so ko?"
"Hmmm wajen ka nazo Doctor."
Dagowa yayi yace
"To Ummi lafiya dai ko?"
"Yadda kakewa Maryam kasan bata da kowa sama damu a yanzu dan haka dole mu jata a jiki Dr dole mu sakar mata."
"Ummi ni kuma ke dai amman ni me zan mata kuma? Duk abinda take so ta fadan zan mata insha Allahu."
"Duk da haka nasan kai daman halin ka wani lokacin kana da wuyar sha'ani."
Haidar ne ya sauko ya gangaro yana son ya dauke shi, daukar sa yayi ya amshi chocolate din hannun sa ya bude masa sannan ya mika masa amsa yayi ya saka a bakin sa sai kuma ya fito da ita ya saka a bakin Aliyu ya gutsura ya mikawa Haidar yace
"Sha abinka."
Ummi ya dago ya kalla yace
"Ummi ni ina da shawara akan Maryam."
"Ina jin ka."
"Mai zai hana ta zana jarabawa daga nan mu sama mata addmision dan shine kadai gatan ta a duniya."
"Na jima da yin wannan shawarar amman ganin tana shayawar shiyasa na dakata."
"Haidar bai da matsala, kuma kinga an kusa zana weac ana ta registeration har anyi kan lokacin fara makaranta ta fara ko yaye shine tayi tinda kinga bai fiya damuwa da maman ba."
"To shikenan Allah taimaka yanzu ya za ayi?"
"Gobe zan turo a dauke ta aje ai mata komai."
"Shikenan Allah yayi albarka."
"Amin Ummi."
Ummi ta mike tace
"Haidar ko zamu tafi?"
Aliyu ya kamkame yana shigewa jikin sa. Ummi tace
"Zaka zo ka samen."
Ta fita.
Haka akai ciki hukuncin ubangiji akai mata registeration wanda Aliyu ya dauki mai mata lesson kan a fara exam wata daya da registeration suka fara exam sannan aka saka ta wata isilamiyya dake unguwar da taje akai mata interview komai ta wuce yan makarantar dan haka suka samu Aliyu sukai masa bayani kan cewa da za su same ta a matsayin malama zasuyi murna. Wannan yasa Aliyu ya sanar da Ummi, Ummi ta samu Maryam, Maryam tace ba matsala dan haka ta fara zuwa suka bata aji tana koyar wa.
*
Ranar da zata fara exam da safe Maryam ta fito daga dakin ta shirye cikin goggagun uniform din makarantar da zata zana jarabawa, sakowa tayi daga bene, kitchen ta shiga gun Ummi, Ummi dake juye ruwan shayi a flask ta juyo tace
"Yan makaranta an fito?"
Murmushi tayi tace
"Eh Ummi, nazo na karasa."
"A'ah bari ai na gama."
Ummi ta karasa ta mika mata flask din ta fita dashi dining Ummi ta fito da flask din da ta zuba dankali da kwan da ta suya. Maryam ta hada tea ta zuba dankalin ta ci.
Maryam na gamawa ta kai plate din da cup kitchen, ta dauraye ta samu Ummi a sama ta shiga ta dauki hijab din ta ta fito tace
"Ummi zan tafi."
Ummi dake aiki a system ta dago tace
"Ki duba gaban dressing mirror a daki na akwai duba daya ki dauka."
Dakin ta juya ta shiga ta dauko sannan ta fito tace
"Ummi sai na dawo"
Ummi tace
"Ohk Allah ya tsare kiyi addu'a kafin ki fita, driver na waje."
Fita tayi ta nufi can parking space din Farouk ta gani a jikin motar sa yana worming din ta, tinda ta fito yake bin ta da kallo har ta karaso, kai tai kasa dashi tace
"Ina kwana Yaa Farouk?"
"Kin tashi lafiya yau sai makaranta ko?"
Tai murmushi ta gyada kai."
Driver ne ya karaso ya gaishe da Farouk sannan ya kalli Maryam ya gaishe ta, amman sai taki amsawa ta gaishe shi. Farouk ne yace
"Bari na kai ta, kazo daukar ta."
"Ok ranka ya dade."
Ta kalli farouk zatai magana ya daura mata hannu a kan leben sa yace
"Shiiii!"
Tare da mata nuni da ta zagaya ta shiga. drivern ta kalla tace
"Yaa Aliyu ya baka time table din ai ko?"
"Eh ya bani dazu da zai fita."
"Yauwah sai kazo dauka ta."
Ta karasa ta shiga shima ya shiga ya fitar da mota.
Suna tafe a hanya yana dan jan ta da hira har suka karasa makarantar har cikin school din ya shiga da ita sannan yai parking ya zaro kudi a aljihun sa ya mika mata yana fadin
"Allah bada sa'a."
"Amin."
Ta amsa ba tare da ta amshi kudin hannun sa ba yace
"Ki amsa mana?"
Kai ta girgiza tace
"Ummi fa ta bani."
"Na Ummi daban nawa daban amshi kinji kanwata ba kyau maida hannun kyauta baya."
Amsa tayi da hannu biyu tace
"Nagode!"
Ta rufe kofar ta juya ta nufi wajen wasu dalibai da ta gani dan tambayar exam hall. Tana zuwa ta tambaya daya a cikin su tace
"Muma can zamuje muje."
Suka dunguma suka karasa karfe tara suka shiga kowa ya zauna a sit din sa tara da rabi aka fara raba booklet suka fara exam. Da yake da Biology ce awa biyu aka bayar karfe sha biyu har sun fito. Da motar gida tai tozali ta karasa wajen Driver na gani ya taso ya bude mata ta shiga suka kama hanyar gida.
Ummi na wajen aiki amman har ta gama girki dan haka tana komawa ruwa ta watsa tai alwala tai sallah lemo kadai ta sha ta rufe sashen su ta tafi bangaren Inna.
Inna na kitchen ta shiga jiyo muryar Maryam tace
"Gani nan shigo daga ciki."
Maryam ta karasa tana fadin
"Hajiya Inna me ake soya mana?"
Cincin take soyawa Maryam tai murmushi dan bata taba ganin tsohuwa kamar Inna wacce ta iya komai daga na zamani har na gargajiya ba abinda bata yi in tana sha'awa bata fiya son kayan shago ba da kanta take fi yin komai. Maryam tace
"Inna ina yini?"
"Lafiya lou yau ina kika shiga na jiki shiru naje bangaren na same shi a rufe."
"Ai yau muka fara jarabawa shiyasa."
"Ayyaho Allah ya bada sa'a."
Ta fada tana tsame ragowar cincin din ta zuba a collender tace
"Ina Haidar din shi kuma?"
"Ai Inna ni yau banga Haidar ba ma kwata kwata. Kila Yaa Aliyu ne ya fita da shi."
"Dan kar yazo waje na ya fice dashi to wane aikin kirki zai da yaro dan Allah."
"Nima dai ina mamakin ta yadda yake aiki da Haidar."
"Hmmm ai dan kar yazo min nan ne nima ban neme shi ba suje can su karata sai fa nai wata ban saka yaron nan a ido na ba ko zai zo gaishe ni bai zuwa dashi."
"To kiyi hakuri Inna zan kawo miki shi anjima."
"A'ah A'ah bar mishi tinda bai so yazo waje na."
Suka zauna suna hira har akai la'asar Maryam ta koma dan tasan Ummi ta dawo a lokacin ai kuwa ta dawo tana sama tana watsa ruwa dakin Ummi ta shiga rike da kudin da farouk ya bata. Ummi ta fito tace
"Yan makaranta an dawo?"
Kai ta