Showing 96001 words to 99000 words out of 232912 words
Chapter 33 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
son da kake min kan su."
"See dis girl ke har kina da bakin magana, ni dake wa yafi son yara, ni ne ma na fi jin wannan tsoro kar daga kin haihu a daina ji da ni kuma."
Kallon sa tayi tace
"Ba mai kwace maka fada ta a wajen na."
"Bare ni, zance musu wannan ita ce duniya ta."
Tai murmushi sai kuma ta jingina da kujera tana fadin
"Yaya ciki na"
"Ko mu fara zuwa clinic din dai?"
"No muje in mun dawo ma biya."
Haka suka karasa wajen, a ciki ma shi ya dinga dibar mata kayan da zata bukata amman ita ta rasa me yake damun ta, da aka je biya ma fita tayi dan ji tayi wajen gaba daya yai mata zafi, dakyar ta samu take daga kafar ta wajen motoci ta nufa, tana dafe da cikinta cikin tsananin azaba a take jikinta ya hau rawa kaman mejin sanyi sakamakon iskan gurin dake busowa kasancewar ta hada zufa a jikinta, cigaba tayi da tafiya a daddafe, ta kusa da karasawa wajen motar maranta tai wani irin murdawa wanda ya haddasa mata tsala wani kara mai karfi nan tayi baya ji kake tim ta fadi a kasa, a daidai lokacin ya fito ya hangota cikin wani irin masifar firgita Haidar ya kwalla mata kira daga inda yake at once ya nufi gurin da wani mugun gudu, amma koda ya isa gurin sam bata numfashi.
Jijjigata yake cikin rikicewa yana ambaton sunanta amma ina ko motsi batayi, cikin hanzari ya mike ya ciccibeta ya nufi motarsa da ita, a baya ya shimfideta sannan shima ya shiga kanta ya daura akan cinyarsa yana cigaba da ambaton sunanta.
Gaba daya ya rasa ma me zai mata can idanunsa suka sauka akan goran faro water dake gaban motar, cikin rawar jiki ya mika hannunsa ya dauko goran ya bude bayyi wata-wata ba ya kwara mata gaba daya ruwan akan fuskarta. Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke sannan tafara bude idanunta a hankali, sam bata fahimci inda take ba kokarin tunano abunda ya sameta take Sai ko taji muryan Haidar.
"Yaa Haidatrrr!"
Ta fada cikin wata irin murya sai kuma ta kama hannun sa ta matse jin mararta yayi wani irin murdawa wanda ya haddasa mata rumgume shi sosai, kai ta hau jujjuya tana salati cikin wata murya mai ban tausayi, ta kara damke hannun sa tana jujjuya kai.
Haidar kuwa ya kara rikicewa ya rasa me zai yi mata sai kalman sannu kawai yake jera mata ko tambayar abunda ke damunta ya kasayi, yama rasa wanne taimako zai bata. Maryam cikin kuka da tsananin azaba take cewa
"Dan Allah ka taimakeni ciki na wayyoo Yaa Haidar..." Abunda kawai take iya nanatawa kenan da alama ma bata cikin hayyacinta, shiko sai a lokacin hankalinsa yafara dawowa jikinsa har ya fahimci kome ke damunta nan ko hankalinsa yadada tashi don yasan Period zata fara kila, Allah yasa kar yana zuwar mata a wannan wahalar.
Don haka cikin muryar lallashi yace
"kiyi hakuri bari in kaiki Asibiti.!"
Cikin sauri ya gyara mata kwanciya sannan ya fito ya koma mazaunin driver, da mugun gudu yaja motar ya fice daga cikin super market din.
Tuki yake yana kallonta At once kuma yana kalon hanya ko zayi katari koda da chemist ne tunda tsakaninsu da Asibiti akwai nisa gwara kawai yakaita chemist a mata su bata ko da pain relief ne, Maryam na kwance a baya babu abunda take sai kuka da ambaton sunansu Abbi sosai takejin azaba wadda bata taba jin irin ta ba shikam tuki yake yana jera mata sannu, kasancewar dare yafarayi don lokacin karfe 10 saura hakan yasa kafa yafara daukewa, sai da sukayi tafiya mai nisa sannan suka samu clinic, cikin sauri ya fakin motarsa ya nufi cikin clinic din.
Daukar ta yayi ya shiga nurse na ganin sa suka gangaro gado suka shiga da ita, gefen ya tsaya sai sannu yake ta faman jero mata, ita kam ta rike hannunsa gam kaman jinjirin da ya rike nonon uwarsa.
Cikin kankanin lokaci yafara bata taimakon gaggawa, dan karamin ruwa ya saka mata yayi rushing dinsa a jikinta sannan ya mata allurai har guda biyu duka a jijiya cikin kankanin lokaci abun yafara sauka kafun kace me bacci yayi awon gaba da ita. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya. Kallon Haidar yayi sannan ya umarcesa da suje waje, Koda suka fito ya bashi kujera ya zauna sannan yafara mishi bayani kamar haka
"Karka samu damuwa yanzun munyi mata duk abunda ya dace wannan bacci da take zai iya daukanta daga yanzun zuwa nan da awanni koma fiye da hakan sannan kada a tasheta sai idan har itace ta tashi da kanta, hakan zai taimaka mata wajen samun saukin ciwon sosai, sannan inaga kafun lokacin jinin zai iya fitowa..!"
Jinjina kai Haidar, wani Dr ne ya hango Aliyu ya karaso yana fadin
"Dr AS kai ne anan."
Hannu ya mika masa sukai musabaha, dayan likitan da ya duba Maryam yace
"Shima likita ne?"
Kai dayan ya gyada yai murmushi yace
"Amman na tsaya maka bayani ai zaka iya kula da ita kuma kasan abubuwan dake kawo ciwon kila ko sanyi, ko kuma tana daga cikin jerin masu tsananin sha'awa da take bukatar namiji nan kusa kasan dai matsalolin?"
Kai ya gyada yace
"Kuma kaga wannan ne na farkon ta."
"Ikon Allah, to ya kamata a dauki mataki dan kar tana shan wahala."
"Insha Allahu."
Dayan yace
"Mara lafiya ka kawo?"
"Eh wallah."
"To Allah sauwake kai me ya hanaka duba ta?"
"Na rikice na kasa gane mema zan mata."
"Ko dai madan din ce."
Sukai tafa suna dariya. Bayan tafiyar sa ya koma dakin da maryam take Ammi ya kira ya sanar da ita suna asibiti nan ta hau tambayar me ya faru, bai boye mata komai ba ya fada mata, Ammi tace suna ina zata zo yace ba sai ta zo ba.
Yana zaune har wajen sha biyu sannan ta farka ya karasa da sauri yana fadin
"Sannu *Matar Haidar* "
Dagowa tayi tana kallon sa fuska cike da damuwa ta kalle shi yace
"Sannu tana miki ciwo har yanzu?"
Kai ta gyada yace
"Bari ina zuwa, "
Ya fita nurse ya tura mata, shi kuma ya fita mota ya dauko mata pant da pad har da wata riga dan daman kamar yasani ya siyo mata su, ciki ya koma ya bawa nurse din ita ta taimaka mata ta gyara jikin ta Maryam na gane me ya faru da ita sai ta hau kuka a haka ta fito tana kuka, da sauri ya karaso ya durkusa a gaban ta yace
"Me kuma ya faru Baby?"
"Yaya abin ne yazo fa."
"Wane abun?"
Ya tambaya dan bai sa me take nufi, tace
"Abun da ka gama ja min yi dazu."
Ya saki murmushi yana fadin
"Please yanzu fa kin kara girma."
"Ni bana son girman."
Ya mike yace
"Bakya so ki haifa min Baby ko?"
Baki ta turo tana yamutsa fuska kamar zatai kuka tace
"Yaya ni ka kaini Ammi ciki na ciwo yake har yanzu."
Ta fada tana yarfe hannu, mikewa yayi yace
"Muje to."
Yaje ya biya kudi sannan suka tafi gida, a mota ma shiru tai masa kawai dan ciwo take ji sosai wannan yasa ko motsi bata so tayi.
Suna zuwa ya bude mota yace
"Baby mun karaso."
Ta dago ta kalle shi tace
"Yaya kafata ta rike ba zan iya ba."
Kallon wajen ya fara sai kuma ya zura hannu a aljihu ya fara neman layin Alkasim yana dauka yace
"Kana ina ne?"
"Ina compound kazo."
Ba bata lokaci ya fito yana fadin
"Lafiya?"
"Please daukar min ita mu shiga ta kasa tafiya."
Tin da Maryam ta shiga shekara goma Aliyu ya daina daukar ta da taba ta, in har ya taba ta bai fi ta kamo hannun sa ba shima yana janye wa haka tinda ta kai lokacin ko tazo zata rumgume shi yake dakatar da ita wannan yasa su Ammi basa kara damuwa da shakuwar tasu saboda sosai suke kiyaye hakkokin dan da ta girma ma bata zama ba hijab a gaban duk yayyen ta wannan kuma tarbiyyar Ammi ce.
Kamo ta yayi, Haidar ya kwashi kayan sukai ciki anan falo ya ajiye ta Ammi ta mike tana fadin
"Mata ana ciwo."
Ta sagwabe fuska tace
"Ammi kamar zan mutu fa kinji ciki."
Sai ta fara hawaye Yaa Haidar ya durkusa yace
"Haba my jaruma, bar yin kuka zata daina kinji."
Ya mike ya shiga kitchen sai gashi ya fito da ruwan tea a cup sai ruwan dumi a bowl, tea ya bata ta amsa ta sha daya kuma ya bata karamin towel yace ta gasa marar tata, Ammi ta dauke ta sukai dakin ta gasa marar tayi wannan yasa ta dan ji dadi har bacci ya dauke ta.
Tin asuba ta tashi, Ammi ta koya mata yadda zata saka pad ta saka ta fito ta saka wasu Pakistan riga da wando sannan ta saka hula ta haye gado, dan har lokacin marar ta yana tai mata ciwo, tana kwanciyya bacci ya dauke ta.
Karfe takwas ya shigo sashen Ammi, ba kowa a falo, kitchen ya leka ya samu Ammi ya gaishe ta yace
"Maryam ta tashi?"
"Kila ta tashi har yanzu tana can tana raki."
Dakin ya shiga ya same ta kwance akan gado, kan gadon ya karasa ya zauna daga gefen ta yace
"Dear."
A hankali ta motsa tana bude idon ta, ganin Yaa Haidar yasa tai maza taja abin lulluba, murmushi Yaa Haidar yayi yace
"Morning My Love."
"Morning too dear."
Ta mike tace
"Yaya...."
"Sannu my love ya jikin?"
Fuska ta shagwabe tace
"Uhmm ba sauki Yaya har yanzu ciwo take min, kafa na ma ciwo take min."
Ta kara yamutsa fuska tace
"Amai nake ji Yaya."
"Sannu kinji yanzu zan samo miki pain relief dan ba a son ana shan maganin ciwon marar nan."
"Yaya ko mutuwa zanyi ne?"
Kai ya hau girgiza mata yace
"Wa yace miki daga ciwo sai mutuwa."
Ido ta runtse tana cije baki tace
"Yaya..."
"Sannu Baby kin ci wani abu?"
Kai ta girgiza ya mike ya fita bai jima ba ya dawo da ruwan tea ba sugar ta mike zaune ya fara bata tea din tana sha a hankali bayan ta gama Abdullah ya kawo maganin da Haidar ya ake shi ya siyo bata yayi tana kuka tana komai ta sha maganin, ranar ko aiki Haidar bai je ba sai zama jinyar Maryam ai kuwa sai shagwaba take masa daga tace zataci wannan sai wancan kuma in an kawo ba abinda take ci a ciki, har dare haka sukai ta fama.
Kwanan ta biyu ya dauke sai kuma shagwaba da ta dadu, haka Aliyu yake biye mata yai ta lallabata Ammi dai sai zuba ido tayi, dan har da Mami a daure musu gindi. Ummah kuwa a duniya ba wanda ta tsana kamar Ammi da Mami, ji take kamar ta kashe su.
Haka rayuwar Maryam da Haidar take duk wanda yasan Haidar to yasan Maryam haka duk wanda yasan Maryam yasan Haidar, soyayyar su mai tsafta ce dan ko hannun ta bai tabawa, zabin su iri daya burin su daya koman su daya wannan soyayya ba wanda bai san ta ba daga family din Haidar har Family din Maryam both side.
Lokacin da ta shiga SS 3 ne aka tsayar da ranar auren su, a lokacin shakuwar Haidar da Maryam ta kara tsanani, dan ko ciwo Maryam tayi Haidar yana gida yana ji a jikin sa ma in period din ta yazo sosai take shan wahala tai ta suma a haka yake kullum yana hanyar zuwa makarantar su dan bai da shamaki da zuwa wajen ta a ko da yaushe, suna second term kan su fara aka kawo lefen ta da sadaki wanda aka saka sati daya da graduation bikin, Shin don mene ne Maryam ba zata so Aliyu ba.
Hakika Maryam na son Aliyu so ba na wasa ba kuma tabbas ya cancanci a so shi domin mutumin da ya kwashe shekaru goma sha yana kula da ita, kulawar da iyayen da suka tsuguna suka haife ta basu yi mata ita ba domin duk abinda su Ammi zasuyi mata kan suyi ya riga yayi tin tana karama yake dawainiyya da ita yake bauta mata, yana dadada mata, yana faranta mata, In har bata so Aliyu ba, tabbas ta zama butulu ce cikin butullun ababen halitta wanda zuciya ba ta aiki a jikinsu.
A wannan tsukukun kuma Aliyu yafara wani matsifaffen ciwon ciki wanda in ya tasar masa shima har suma yake yi, lokacin duk sai ya fara ramewa da ka kalle shi zaka san bai jin dadi.
Ajiyar zuciya Mami ta sauke tana me cigaba da tunanin wani abu da ya fado mata.
Tabbas abun da ya fara daurewa Mami kai shine tin da suka shiga third term zasu fara exam ba a kara yo waya akan Maryam tayi ciwom mara ba wanda a da duk wata sai an dawo da ita gida ko asibiti ta kwanta wannan yana nuni da tin kusan lokacin kenan Maryam ta samu sauki, wanda ba zata manta ba akwai wani dr da ya taba fada musu samuwar lafiyar Maryam sai tayi aure ta tara da mijin ta.
Da sauri Mami ta mike tuna wasu abubuwa a wadan nan lokutan, sune Haidar ya kara sa son Maryam a ransa wanda yasha fadawa Mami shi a daura musu aure kan tayi graduation amman Mami tace zataiwa Abba magana Abba yace ya bari saurin me yake ne ai an kusa a wannan lokacin ya janye batun sa sai dai wani kalamai da ya taba fadawa Mami shine
"Nifa Mami Maryam ta gama zama matata buri na kawai ku bani abata mu tafi duk wannan shagalin da za ayi bidi'a ne."
A lokacin bata damu da kalaman sa ba dan sai take ganin kamar ba wani abu bane kawai zumudi ne, sai kuma ranar daurin auren su da ya kira ta akan yana son suyi wata magana tabbas basu samu dama ba dan Abba ya aika tazo daga nan da ta koma kuma bata ganshi ba inda bata kara ganin sa ba sai gawar sa da aka kawo mata, shin me yake son ya fada mata, hakika zuciyar Mami ta karaya dan ta tabbara daga Maryam har Haidar ba mazina ta bane daya a cikin su ba zai taba yin zina ba amman to me hakan yake nufi tayaya Maryam ta samu ciki, tayaya? Shin cikin wa Maryam take dashi? Bata so ta sa aranta cewar Haidar da Maryam sun aikata zina dan haka tai sauri ta mike ta shiga daki ta fara wani abu da zai dauke mata wannan mummuna tunanin.
*Allah ya yafe mana, ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
ο»Ώο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 38
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
*
Abba na gidan tsakiya Ummi da Maryam na gidan baya, Maryam kwance akan cinyar Ummi tana ta bacci dan yanzu ba abinda take yawan yi sai bacci. Har suka Iso Kano bacci take. Suna shiga Kano, ta mike ta matsa jikin Ummi tana karkare wa kamar me tsoron wani abu. Ummi tace
"Menene Maryam?"
Jikin Ummi ta fada ta rufe fuskar ta tana girigiza kai,
"Alhaji akwai abinda zakuyi kan mu karasa airport?"
Ado Driver ya tambaya.
"Aah! Mu zarce airport kawai. Madam ko kina so wani abu!"
"A'ah Maryam ko kina son wani abu ne?"
Kai tai sauri ta girgiza kan ta a boye a jikin Ummi.
"Mu tafi airport din lokaci ma ya kusa."
Direct Aminu Kano Airport suka tafi suna zuwa suka shiga suka dan huta, Aliyu ta kira ta shaida masa yanzu zasu taho yai musu addu'a sannan yace
"Ummi ina asibiti da kyar na samu na dauko ku."
"Kada ka damu kaji."
"To Ummi zan aiko Baba Halliru sai ya dauko ku tinda naga Baba Ado ne ya kai ku nan ko?"
"Eh sun taho suma nasan nan da magariba zasu karaso."
"Allah kawo su lafiya."
"Amin!"
"Ya me jikin?"
Kallon Maryam tayi wacce ke jikin ta a dukunkune tinda suka shigo Kano take a haka wanda ta ki ta saki Ummi sam kamar wanda ke ganin wani abu.
"Gata nan!"
Ta fada tana shafa kan ta."
"Ai mata sannu!"
"Zataji!"
Sukai sallama sannan ta shafa kan Maryam tace
"My Son na miki sannu!"
Kai ta gyada kawai. Karfe uku jirgin su ya fara haramar tashi.
Karfe biyar saura suka fito daga cikin airport din cikin wasu jerin gwanon motoci wajen guda biyar biyu a gaban tasu biyu a bayan tasu an saki jiniya a haka suka ratsa babban titi suka nufi gida kai tsaye. Bakin wani katon hadadden gida sukai horn security ya bude katon gate din ciki suka shiga a jere.
Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta zauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku manya masu fenti iri daya, ko wanne sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko da na biyu, wanda na farko shi zaka ci karo da bayan shigowar ka gate din zamanin dake babban gidan ba dai girma ba wanda girman sa daya da tsaruwa a komai da na kusa dashi. Manyan gida ne masu girman gaske sai parking space gari guda dake gefe., a cikin ko wanne. Banda na main compound da yake dauke da securities room da boy quaters. Gidan ya tsaru iya tsaruwa da kyau ko ina neat sai kamshi yake ga ni'ima saboda shuke shuken da suke dashi.
Suna parking suka fito Ummi rike da hannun Maryam da ta gama galabaita saboda gajiya da tayi ga ciwo ga yunwa duk ita kadai. Second part dake cikin gidan suka nufa, hannu ta saka ta karkashin wata tukunyar shuka sannan ta dauki key. Abba ta bawa ya amsa yai bismillah ya zura key din ya bude. Kamshi ne ya dake su tare da sanyin AC. Shiga yayi da sallama Ummi tabi bayan sa rike da hannun Maryam.
Katon falo wanda yake dauke manya manyan kujeru wajen set uku maroon kala and milk, labulayen ma maroon kala ne da adon milk sai milk center carpet da center table a tsakiyar dakin. Gefen kujerun kuma side stool ne yan kananu a tsakan kanin kujerun. Can gefe kuma dan step ne wanda ke dauke da dining table da dining carbinate an saka musu wani labule mai igiyoyi milk an maroon ka. Ta gefen dining akwai kitchen, sai gefen dining da wata kofa, da matattakalar bene sannan akwai corridor dake dauke da three room two bedroom da resting room.
Suna shiga Maryam ta lumshe ido ta saki Hannun Ummi kasan tile ta kwanta tana mai lumshe ido. Ummi ta kalle ta sannan ta karasa ta kamata tace
"Ba a son kwanciyar kasa fa."
Akan