Showing 66001 words to 69000 words out of 232912 words

Chapter 23 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1233

dai lafiya ko? Dan sai kuka take!"

Shiru yayi Aisha tace
"Hello!"
"Aisha muna asibiti ne kada ki fadawa kowa Aliyu bai da lafiya amman insha Allahu komai zai zama normal ki kular min da kanwata please."

"Ayyah Allah bashi lafiya. Insha Allahu!"
Ta kashe wayar ta tsaya tunanin shakuwar Aliyu da Maryam wanda bashi da lafiya ma sai taji a jikin ta ko da yake ba yanzu suka fara ba haka suke ko a gida.

Alwala tayi ta fito, ta fito ta samu Maryam ta daga hannu tana addu'a. Sallah ta tayar tana idar wa Yaya Zainab ta shigo tace
"Aisha ku taso har wasu sun tafi ma! Ku taso."
Maryam ta yunkura zata tashi tana mikewa tayi baya zata fadi da sauri Aisha da Anty Zainab suka kamo ta. Zainab ta rike ta suka fita. Bangaren Abbi suka shiga dakin shiru sai kamshi yake.

Abbi ne zaune sai Inno da Hajja kakakanin Maryam sai Ammi da wasu daga cikin Yaye da kannen Abbi da Ammi duk suna zaune. A kasa aka zaunar da Maryam. Aisha ta tsaya a kofar falon Abbi.

Wayarta ta dauka ta kara neman layin Alkasim bayan ya dauka tace
"Ya jikin nasa?"

Cikin muryar damuwa yace
"Har yanzu shiru fa, ba wanda ya fito a cikin su."
"To fa wai ciwon har haka ne."

"Sai dai sun fito zamuji."
"To Allah kara sauki."

"Amin!"
Ya fada a sanyaye ya kashe wayar. Abokan sa ne suka fara kira suna masa tsiya wai sun tafi sun bar su ina angon suna ta kira bai dauka ba. Hakuri ya basu yace gasu nan yanzu insha Allah. Zama yayi ya dafe kai kawai dan ya rasa yaya zai yi ma.

Yanzu wa zai fadawa a gida wanda hankalin sa ba zai tashi ba. Abbah ya fada a ransa wayar sa ya dauka ya fara neman layin Abbah. Yana dauka yace
'Abbah kana ina ne?"

"Ina hanya zan koma gida lafiya?"
"Ka tsaya gani nan zuwa kana dai dai ina?"

"Ina zoo road."
"Ok!"
Ya mike ya fita. Napep ya hau ya isa yana zuwa ya samu Abbah a tsaye a bakin motar sa.

"Lafiya Alkasim ina Aliyun?"
Kai ya dan sosa yace
"Abbah muna asibiti baya jin dadi ne."

"Me yake damunsa?"
Abbah ya fada cikin damuwa.
"Cikin sa ke ciwo tin dazu muke asibiti har yanzu likitocin basu fito ba."

"Ya salam muje to muje!"
Suka nufi asibitin Alkasim na tuka motar suna zuwa likita ya fito daga dakin da sauri Alkasim ya karasa yana fadin
"Doctor ya jikin nasa?"
Dagowa yai ya kalle su sai ya girgiza kai yace.......


*
Maryam ce zaune kan ta a kasa hawaye na zubo mata. Abbi yace
"Ba abinda zance miki Mamana sai dai ina alfahari dake, Allah yai miki albarka. Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah yasa ki shiga a sa'a yadda kikai min biyayya Allah ya baki masu miki. Kiyi hakuri da rayuwar aure nasan Aliyu na son ki kuma zai rike ki da amana ki masa biyayya domin daga yau zai zama sirrin ki cikon rayuwar ki, zai zama jigo kuma garkuwa gareki. Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka."
Duk yan dakin suka amsa da amin.

Haka kowa ya tofa albarkacin bakin sa, sannan suka saka mata albarka da addu'ar gamawa da duniya lafiya. Alkur'ani da littafan addu'a da carbi Abbi ya bata. Ta amsa tana hawaye da yaki tsayawa.

A gaban su Abbi da Ammi ta durkusa tace
"Abbi da Ammi ku yafe min dan Allah ku yafe min."
Abbi ne ya kamo hannun ta yace
"Mun yafe miki Mama nah, Allah yasa ki shiga a sa'a baki taba bata min ba Mama nah."

Ammi ta rumgume autar ta tace
"Allah miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya. Allah ya baki ikon yin biyayya da daukar ko wacce irin jarabawa. Allah ya baki hakuri Amin. Allah miki albarka."

Kanwar Ammi Anty Hauwa ta kamata ita da Yayar ta Anty Asibi suka mike Bayan su Kannen Abbi Anty Aisha da Anty Mariya suka fita. Gidan Mamah suka shiga har falon ta akai musu iso.

Tana zaune itama da ka ganta zaka san akwai abinda ke damun ta amanar Maryam aka bata ta dauke ta amshe amanar Maryam ta saka mata albarka sannan ta bata kaya cikin wata jaka wanda tarkace ne turaruka da kaya da kudi a ciki. Aisha ta amso suka fito. Mota biyu ce ta rage Aisha ta shiga gaba. Maryam da Anty Asibi da Anty Mariya a baya dayar kuma Anty Aisha da Anty Hauwa suka shiga suka nufi gidan Maryam da har an fara dawo da yan ganin gida sai kadan daga yan uwa dan ana magariba aka fara kai su.

Har dakin ta aka kai ta. Yan kawo amarya na ta yaba kyau da girma hadi da tsaruwar gidan wanda iyayen ta kuma suka zuba kaya masu kyau tsada da tsari wanda gidan ya kara fito kowa sai yaba shi yake dan wasu cewa suke ai wannan ita ce aljannar duniya.

Haka suka zaunar da ita suka tafi aka bar Aisha da Rukayya sai Zarah yar Anty Hauwa da Yaya Fadima kan abokan ango su taho suka zauna suna kara gyara gidan.

Maryam kuwa alwala tayo ta tada sallah tana sallah tana kuka ta idar ta jima tana addu'a ta rasa faduwar gaban me take yi. Aisha ta kira tace
"Aisha ki kira min Yaa Haidar!"
"Wayar sa a kashe fa."

"Ikon Allah dan Allah ki kira Yaa Alkasim ni dai ki kira shi ya nemon shi ya hadani dashi dan Allah."
"Toh!"
Ta dauki wayarta, ta fara neman layin Yaa Alkasim.




*
Doctor yace
"Yana cikin wani hali ba abinda yake ambata sai sunan Allah da *Matar Haidar* yana fadin a kira masa ita, in da hali kuzo da ita ko in ya ganta zai samu nutsuwa."

Abbah ne ya kalli Alkasim yace
"To bari naje na taho masa da ita."
Ya juya ya fita. Doctor ya juya zai koma dakin Yaa Alkasim yace
"Ya jikin nasa?"

Cikin karaya yace
"Da sauki amman yana bukatar addu'ar ku."
"Insha Allahu!"

Wayar sa ce ta hau kara ya zaro yaga Aisha ce. Dauka yayi yace
"Aisha!"
"Na'am Yaya daman Maryam ce tace na kira ka....."

Wayar Maryam ta amshe tana fadin
"Yaya ina My Hayyat ya shiga ka fada min ina ya tafi ya barni, dan Allah ka nemo min shi"
"Haba Maryam ki nutsu mana menene na kuka ina aka ce miki ya shiga? ai yana nan."

"To ka hadani dashi yana bandaki in ya fito zan fada miki."
"Ok!"




*Allah ya yafe mana kasa mu cika da kyau da imani. Allah yasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




MS Indabawa
*Antty*

💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 23

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*




Aisha ta amsa ta mike ta fita tace
"Ya jikin nasa?"
"Da sauki yanzu Abbah zai zo ya dauko Maryam din yana son ganin ta."

"Yah Alkasim mufa muna gidan ta ma har an kawo ta gidan ta."
"Au yau ne fa za a kawo ta ko wallahi na manta ma kwata kwata."

"Allah ya kara sauki sai anjima."
Ya kashe wayar. Kira ne ya shigo daga abokan sa ya dauka
"Wai kuna ina ne?"

"Muna asibiti fa. Aliyu ne ba lafiya."
"What? Wanne asibitin?"
Nan ya fada musu sannan ya kashe wayar.


Abbah gidan su Maryam ya nufa kai tsaye yasa ai masa magana da Abbi. Har sitting room aka kai shi Abbi ya fito yana ganin sa suka kara musabaha yace
"Daman kai ne?"

"Wallahi nine."
Suka gaisa sannan Abbah yace
"Dan naka ne fa ba lafiya, "

"Aliyu! me yake damun sa?"
"To yana asibiti ma dai yanzu nima Alkasim yake fada min likita ne yace nazo na dauko masa Maryam da sai kiran sunan ta yake yi."

"Ikon Allah! Ai yanzun nan aka kai ta sai muje mukai ta naga jikin nasa ko?"
"To ba matsala."
Suka mike suka fita tare. A kofar gida suka tsaya Abbi yace
"Bari naga ko su waye a ciki!"

Ya dauki waya ya fara neman layin Ammi, dauka tayi yace
"Su waye a gidan Mama nah?"
"Fadima suna can."

"Shikenan!"
Ya kashe wayar ya fita a motar Abbah ma ya fita suka nufi gidan knocking sukai Mai gadi ya bude su Abbah ya gani ya bude da sauri yana fadin
"Barkan ku da zuwa!"

"Yauwah!"
Suka gaisa sannan suka nufi cikin gidan a bakin kofa Abbi yai knocking, Fadima ce ta fito tana ganin Abbi ta matsa yace
"A'ah ba shiga zamuyi ba ina Mama nah?"

"Tana ciki!"
"Je ki taho min da ita kuma kuzo ku tafi gida kawai."

"Lafiya Abbi?"
"Lafiya lou."
Ta juya tai shiga. Maryam na zaune akan sallaya ta shiga ta nufi wajenta ta kamo ta tana fadin
"Taso!"

Mikewa tayi tace
"Su Yaa Haidar ne?"
"A'ah Abbi da Abbah ne!"

"Ina Yaa Haidar me ya faru me ya faru?"
"Ke ki nutsu ba komai Abbi yace dai kizo."
Ta kamata ta fita da ita. Bakin kofa suka hadu dasu Abbi ta nufi Abbi da sauri tana fadin
"Abbi ina Yaa Haidar dan Allah yana ina?"

Hannunta ya kama yace
"Ki nutsu yana nan kinji ko?"
Hawaye take kawai dan hankalinta ya dada tashi, ya kalli Fadima yace
"Zan turo Abdullahi ya dauke ku, ku rufe gidan kunji!"

"To Abbi!"
suka fita Maryam rike da hannun Abbi jikin ta sai rawa yake a baya ya saka ta ya kalle ta yace
"Kina ambaton Allah kinji?"
Kai ta gyada ya juya ya koma gidan driver ya tada motar ya kalli Abbah dake kallon Maryam cike da tausayi yace
"Wane asibitin zamu?"

Fada masa yayi ya tada motar suka nufi asibitin sam Maryam bata cikin hankalin ta da zata san ina ma suke tafiya sunan Allah kawai take kira tana hawaye har suka isa Abbi yai parking ya fito ya rufe ya budewa Maryam kofa amman sai ta tsaya kallon sa hannunta ya kamo yace
"Taho Mama nah!"

Ta kama hannun sa suka fito harabar asibitin ta kalla ta kalli Abbi tace
"Abbi me ya faru? Me yasamu Yaa Haidar?"
Tayi maganar murya na rawa saboda kukan da yazo mata mai karfi. Kama hannun ta yayi yace
"Ki daina kukan nan dan Allah!"

"Na daina Abbi!"
Tai maganar da kana kallon ta kasan bata cikin haiyacin ta. Abbah yai gaba Abbi na bin sa rike da hannun Maryam har suka shiga reception din suka nufi corridor da dakin da aka kwantar da Aliyu. Alkasim ta gani da sauri ta sakin hannun Abbi ta karasa wajen sa tace
"Ina Yaa Haidar din?"

Dakin da yake ya nuna mata da sauri ta nufi dakin ta bude doctor ne da nurses tsaye akan Aliyu suna jin an budo kofa suka juyo suna kallonta da sauri tayi ciki ganin Aliyu kwance akan gado daga shi sai farar singlet da dogo wando a jikinsa.

Da gudu ta karasa ta dago kan sa tana fadin
"Yaa Haidarrr! Yaaa Haidarrr!! Dan Allah ka tashi ka tashi ga *Matar ka* tazo ga *Matar Yaa Haidar* kaji *Mijinah* dan Allah ka tashi *Mijin Maryam* !"

A hankali ya bude idanun sa da sukai rine dan azabar ciwo murya a hankali ya rike hannun ta daya ya daura kan cikin sa dayan ya rike yace
" *Matar Haidar* ki yafe min mutuwa zanyi *Matata* mutuwa zanyi na barki...."
Ya kasa karasa maganar jin wata rumguma da tai masa hawaye na zuba a idon ta tana kuka tace
"Bazaka mutu ba, Bazaka mutu ka barni ba, bazan iya rayuwa ba kai ba dan Allah ka daina fadin haka dan Allah Yaa Haidar ka tashi mu tafi gidan mu Yaa Haidar kaji ka tashi."

Sai kuma ta mike da sauri tana daura hannun ta akan marar sa tace
"Irin wancan ciwon ne Yaa Haidar fada min Yayahh irin wancan ne?"
Kai ya hau girgiza mata yana cije baki tare da fadin
"Ciki na ke ciwo ba marata b....."

Ya saki wani dan kara yana fadin
"Ya ilahi! ya mujibadda'awati!"
Ya fada cikin daga sauti sai kuma ya fara salati yana tasbihi ga Allah. Can kuma sai ya lafa gumi ya hau zubo masa ta ko ina duk da AC dake dakin.

Mayafinta ta saka tana goge masa gumin tana fadin
"Sannu! Sannu Yaa Haidar!"
Ta kalli Doctor din tace
"Dan Allah kuyi masa wani abu cikin sa ciwo yake."
Ta fada tana shafa cikin tana tofi tana shafawa a cikin.

Ruwa ta gani a roba ta dauko ta bude tayi tofi sannan ta kai bakin Yaa Aliyu ta bashi sosai yasha sannan ta daura kan sa akan cinyar ta tana shafa gashin kansa dayan hannun na cikin nasa sai da ya samu ya fada masa sannan yace
"Allah miki albarka *Matar Haidar* "
"Sannu Yaa Haidar! Ya kake jin cikin?"

"Da sauki!"
"To ka daina cewa zaka tafi ka barni ka manta abinda kace tare zamu rayu, mu tsofa, sannan mu mutu tare ga kabarin ka ga nawa."

Ta fada hawaye na zubo mata. Hannu yasa ya share mata yana fadin
"Haka naso *Matar Haidar* amman kinsa kowa akwai abinda Allah ya tsara masa, muna tamu Allah yana tashi kuma kinsan na Allah shine gaskiya, duk yadda mukaso abu sai kiga watakil ba namu ne alheri ba na Allah ne alheri kuma kullum alheri muke nema a gurin Allah. Kuma rabon wani shi ke kashe kashe wani, kuma kaddara ta riga fata. Fata na ki kasance cikin farin ciki ko bana raye."

"Wane farin ciki zan shiga babu kai....."
"Ki daina cire rai da jin dadi, ki daina kina zaune zaki samu me kular min dake wanda zai baki farin ciki fiye da nawa."

Kai ta hau girgizawa tana fadin
"Ka daina fadar haka Yaya babu wanda zai soni fiye da kai dan Allah ka bari zan haifa mana yaran da kake so ba Baby boy kake so ba, zan haifa maka shi mai kama da kai in saka masa sunan ka kaji ko baka so?"
Duk da ya fara jin dawowar ciwon sai da ya sakar mata murmushi sannan yace
"Ina so mana *Matar Haidar* ko bana raye zaki haifa min yaro *Ummu Haidar* "

"Zama ka rayu damu, har da mai kama dani ko baka so?"
"Ina so mana *Ummu Haidar!* "
Duk nurses din dake dakin kallon su suka tsaya cikin tausayi da burgewa. A hankali Doctors din suka fita wanda Abba da Abbi suka yi kan sa da sauri.

"Ya jikin nasa?"
"Da sauki!"

"Amman me yake damun sa?"
Abbi ya fada. Yaa Alkasim yace
"Zan iya ganin sa."

Kai ya gyada ya kalli Abbi yace
"Za ai masa sceening anjima na rasa gane ciwon cikin nasa mun masa allurai da sa masa ruwa dai yanzu Allah ya bashi lafiya."
"Amin mungode!"

Ya tafi suka shiga dakin. Suna shiga Maryam ta fara kokarin tashi Aliyu ya riko hannun ta kan ta tayi kasa dashi. Abbi da Abbah suka karaso suna kallon sa duk ya rame sai yanzu suka ga ramar sa sosai.
"Sannu Aliyu ya jikin?"

"Alhamdulillah Abbi!"
"Allah kara sauki!"

"Amin!"
Abbah ya dafa kan sa yace
"Sannu Aliyu!"

"Yauwah Abbah!"
Wayar Abbah ce ta hau kara ya dauka yace
"Hajiya lafiya dai ko"

"Lafiya Alhaji amman rabo na da Aliyu tin safe fa? Yana ina ne ko ya tafi ba sallama."
"Muna asibiti ne bashi da lafiya fa."

Da sauri ta mike tana fadin
"Me yake damun sa? Yana ina? Ya jikin nasa? Innalillahi wainna illahir rajiun! Ku na wane asibitin?"
"Ki nutsu jikin da sauki."

"To amman kana wanne asibitin?"
Nan ya fada mata ta mike da sauri ta fito compound kanwar ta Hajara ta biyo ta tana fadin
"Lafiya Yaya?"

"Aliyu ne ba lafiya!"
"Me ya same shi?"
Ta fada tana bin bayan sa. Dirver ta kira yazo ya tafi dasu.

Alkasim yana gaban gadon abokan su suka kira sun zo suna wane dakin? Fada musu yayi dan haka da suka karaso sun kai su goma sha suka shigo dakin gaba dayan, su Abbah suka gaisar sannan su Abba suka fita.

Sukai wa Aliyu sannu suna masa tsiyar, Alkasim yana ta kare shi dan shi sai murmushi yake musu suna musabaha da dai dai da dai dan su.


Abdullah ya dauki su Yaya Fadima ya mai da gida. suna shiga Fadima ta nufi dakin Ammi. Ammi ta kalle ta tace
"Har kun dawo?"

"Eh Ammi amman fa Yaa Haidar ne ba lafiya yana can asibiti Abbi da Abba sunje sun dauki Maryam ma."
"Me yake damun sa?"

"Wallahi nima ban sani ba."
"To ina Abdullah kira min shi!"

Ta fita ta kira shi. Yazo ya zauna a gaban Ammi tace
"Kira min Abbin ku kaji suna wane asibiti?"
Wayar sa yazaro ya fara neman layin Abbi.




Suna fita Abbi ya kalli Abbah yace
"Wannan ciwon cikin yana bani tsoro anya ba za a fitar da Aliyu ba?"
"Nima tunanin da nake kenan."

"Gaskiya dai bari zanyi magana zuwa anjima muji ya abin zai kasance kalli yadda yaron ya rame lokaci daya kasan ciwon ciki ba dadi"
"Haka ne nagode Sosai Malam."

"Ba konai ai an zama daya."
Wayar Abbi ce ta hau kara ya zaro yaga Abdullahi ne dauka yayi yace
"Ka mai dasu gida?"

"Eh Ammi ce tace na tambaya kuna wane asibitin?"
Ya fada musu Abdullah ya amsa da
"Toh!"
Ya kashe wayar ya kalli Ammi ya fada mata. Nan sukai mota har biyu suka tafi asibitin.

Kusan a tare suka shigo asibitin dasu Mamah a parking space suka hadu dan haka suka nufi dakin bayan sun kira Abbi ya fada musu inda suke. Suna zuwa suka shiga dakin da yake wanda hakan yasa abokan sa sukai masa sai da safe suka tafi.

Maryam na ganin Ammin ta mike ta fada jikinta tana kuka. Ammi tace
"To menene na kukan?"
Mamah ta kamo ta tace
"Ki daina kuka zai tashi kinji!"

Ta kwantar da ita a jikin ta, ta kalli Aliyu tace
"Sannu!"
Kai ya gyada kawai yana kallon Maryam dake kuka. A haka sukai masa sannu dukka amman shi ido sa hankalin sa na kan Maryam. A hankali ta dago tana kallon sa. Ya mike mata hannu kin tashi tayi sai da Mamah tace
"Tashi kije mana!"

Ta karasa ya matsa mata gefen gadon ta zauna ya daura kan sa akan cinyarta ya kamo hannun ta daya ya daura akan cikin sa. Wani numfashi ya sauki sai kuma ya fara salati dan yadda cikin ya murda masa. Nan Maryam ta fara tofi Alkasim kuwa da sauri ya mike ya fita a dakin dan kiran likita tare suka dawo da likita yazo yace su fita, har Maryam ta mike amman Aliyu ya kamo hannun ta Doctor yace
"Yi zaman ki."

"Yi min tofi *Matar Haidar* "
Ta dauki ruwa ta karai masa tofi ta bashi ya amsa ya sha sannan ya lumshe ido ya mike zaune ya rumgume ta a jikin sa. Fita doctor yayi ya barsu su kadai a dakin.

Shiru sukai sai numfashi da suke saukewa can yace
"Allah miki albarka *Matar Haidar* "
"Amin Yaa Haidar nagode."

" *Matar Haidar* ki yafe min zan tafi na barki zan tafi wajen Manzo na, fatan na ki amshi duk kalar jarabawar da zata zo miki da kalubalen rayuwa wata rana sai labari."

Hannu ya saka ya shafa cikin ta yace
"Naso naga abinda zaki haifa min *Matar Haidar* amman nasan ba zan gani ba ki kular

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login