Showing 138001 words to 141000 words out of 232912 words

Chapter 47 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1263

gyada tana murmushi tace
"Sannu da zuwa."
"Yauwah ya makarantar da jarabawa?"

"Alhamdulillah."
"Ince tai sauki."
Murmushi ta saki tace
"Sosai Ummi."

"To Allah bada sa'a."
"Amin nagode."
Ta fada tana mko mata kudi
"Na menene?"

"Dazu Yaa Farouk ne ya kai ni shine ya ban wannan kudin."
"To angode."

"To Ummi ki amsa."
"A'ah ki ajiye a wajen ki."

"To ni ki ajiyen."
"To nawa ne?"

Kirgawa tayi ta fada mata tace
"Dubu biyar ne."
"Angode."
Ta amsa ta saka a cikin dorowa Maryam ta mike tace
"Me za a dafa?"

"A'ah ke da zaki karatu."
"Ummi gobe ba jarabawa ko da dare nayi."

"To kije kiyi abu mai sauki."
"To Ummi."
Ta juya ta fita. Ummi ta shirya ta sauka tare suka gama abincin suna gyara kitchen su Aliyu suka dawo. Da gudu Haidar ya rumgume Ummi ya sake ta yayo wajen Maryam ta dauke shi tana fadin
"Haidar."

Ya hau mata dariya ta dire shi tana fadin
"Na kusa daina daukar ka nauyi kake karawa wallahi."
Ummi tace
"Haidar din."

"Allah Ummi baki ji yadda ya kara nauyi ba."
Dariya Ummi tayi tace
"Dan dai baki saba ba amman da ace nacewa ne dashi da kullum yana goye a bayan ki fa."

"Ai nagodewa Allah."
Ummi ta dauki Haidar suka fice Maryam ta karasa aiki.

Aliyu ta sama a falo yace
"Ummi ya gidan?"
"Alhamdulillah ya aiki?"

"Alhamdulilah."
Yai shiru yana so ya tambayi ya exam kuma baya so can yace
"Ina Maryam ya jarabawar tata?"

"Bari ta fito ta fada maka."
"A'ah Ummi kema ai nasan ta fada miki...."

Sallamar Maryam ce ta sa yayi shiru ta shigo tace
"Ina yini Yaa Aliyu."
"Lafiya lou."

Tai hanyar sama. Ummi tace
"Zo ki fada masa ya jarabawar mana."
"Ummi alhamdulillah."

"To Allah bada sa'a."
Ya fada ta amsa da Amin itama ta haye sama.

Haka suka cigaba da jarabawar acan ta hadu da wata yarinya Jawahir yar minister ce tana son Maryam duk da Maryam bata sake da ita ba amman ita ta makale mata har number Ummi ta amsa a wajen Maryam dan suna gaisawa bini bini in ba exam kuwa ta kira ta su gaisa.

*
Sati uku sukai suna jarabawa suka gama tayi jamb sai zaman jiran result. Haidar kuwa lokacin ya yaye kan sa sam ya daina shan nono sai kayan da Aliyu ke siyo masa ga tafiya ko ina yana iyawa dan a lokacin ya shiga shekara daya, yaron gwanin sha'awa ga farin jiki gashi duk abinda aka saka masa kyau yake masa ga fara'a ga kyau kamar shi yayi kansa. Maryam ma in yana bacci ta zuba masa ido ko in yai wani abu dan sosai yake kama da Abban sa. Shiyasa take jin wani son sa a zuciyar ta na daban.

Satin da suka gama jarabawa Ummi ta siya mata waya mai kyau da tsada ai kuwa Jawahir ta fara kira ta bata number sannan ta fita nunawa Inna. A falon Inna ta samu Farouk yana cin abinci ta shiga da murnar ta tana ganin sa tai kasa da kan ta ta karasa wajen Inna tana fadin
"Inna kinga wayar da Ummi ta siyon."

Amsa Inna tayi tana fadin
"Kai masha Allah. Allah yasa rai akaiwa."
"Amin."

Farouk ya dago yace
"Ni ba za a nuna min ha."
Mika masa tayi ya amsa yai danne danne sannan ya mika mata yace
"Allah sanya alheri bari na saka miki kati."

Sai jin karar shigowar sako tayi tana dubawa taga dubu biyar ya saka mata tace
"Nagode."
Sannan ta mike ta koma bangaren Ummi. Tana falo tana danne danne su Haidar suka dawo yayo wajen ta a guje yana fadin
"Oyoyo."
Ta rumgune shi tana fadin
"Zo ka taya ni murna Ummi ta sai mana waya."

Aliyu dai daki ya shige nan suka hau hotona ita da Haidar har Ummi ta sauko yayi wajen ta. Satin su daya da yin Jamb result ya fito ta samu 250 daman medicine ta cike ana haka wanda wata daya da gama exam shima ya fito tana da A guda biyar sai B guda hudu murna wajen Maryam kamar me? Ummi ma ta tayata murna sosai haka ta dauki dan ta tana ta juyi dashi.

Da dare Aliyu na zaune a falo Ummi ta shiga dakin Maryam lokacin Haidar yai Bacci Ummi tace
"Kin nunawa Yayan naki kuwa jarabawar?"
"A'ah Ummi."
"To kije ki nuna masa kinji."

"To Unmi."
Ta mike ta saka hijab akan kayan baccin ta sannan ta fice ta sauka kasa hannun ta rike da waya da takardar. Da sallama ta karasa ya amsa ta zauna a kasa tare da fadin
"Ina yini?"

"Lafiya lou."
Ya fada shiru tayi sai kuma ya mike zai bar wajen murya na rawa dan ganin ko kallon ta bai ba kuma yake kokarin mikewa tace
"Daman jarabawar muce ta fito shine na kawo maka."

Hannu ya mika, ta miko masa ya kalla yace
"Allah sanya alheri."
Yasa kai yai cikin dakin sa. Da kallo ta bishi wayar ta ce tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dan haka ta dauka tace
"Ya dai yan mata."

"kin dubo exam?"
"Na dubo A5 B4"

"Masha Allah nima yanzu aka dubo min amman ni da C."
"Masha Allah Allah sa albarka.".

"Amin dan Allah kice a kawo ki makarantar da na cike."
Murmushi Maryam tayi tace
"Sai yadda su Ummi suka ce."

"Ke dai bakya so mu hadu ko?"
"Bani da kawa ko daya sai ke kinga kuwa ai zan so mu hadu tare amman ban sani ba a jamb ai can aka cike in Allah yayi sai kiga nazo nan din?"
"To shikenan Allah yasa su kawo ki nan mu hade."
Tace
"Amin"
Aliyu ne ya fito ya shiga kitchen ya dauki abu tana falo suna waya da Jawahir har ya koma itama tai sama ta kwanta bayan ta tofe su da addu'a.

Basu san komai akan harkar karatun nata ba dan lokacin har an fara addmision har Maryam ta fitar da rai, Ummi kuma a lokacin tana busy dan akwai wani case dake hannun ta wanda bata zama kullum tana aiki akan sa duk da abin na ranta amman sai ta sha'afa in tana son ta tambaye shi.



A haka ne Aliyu yai tai mata ciko ciko ba tare da sanin ta ba sai kiran ta da yayi kawai ya bata admission letter da kudin registration *Page 1/2*


~Flash back finish~


*Allah jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani Amin.*



*Antty*[11/26, 18:57] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 57

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



~Cigaban labari~


Da dare, Ummi, Abba da Maryam suna zaune a falo, Maryam na kwance akan three sitter an saka mata karin ruwa, bacci take sama-sama, sai Abba da Ummi dake magana akan zuwan Muhammad, wayar Abba ce tai kara Ummi ta mika masa ya amsa, wanda karar wayar yasa Maryam ta bude idon ta a hankali, sai kuma ta mai dasu ta rufe.

Abba ya dauki wayar yace
"Muhammad ka karaso to ka shigo mana."
Da sauri Maryam ta bude ido tana kallon Abba to wanne Muhammad din? Ido ta mayar ta rufe dan wani bacci ke son dibar ta dan har da allurar bacci akai mata saboda ta samu hutu da nutsuwa dan jinin ta har ya hau.

Ummi tace
"Ai bangaren Abbi zaku ko?"
"Eh bari na kira naji ya dawo?"

Sallama Muhammad yayi ya shigo, su Ummi suka amsa masa ya karaso ya durkusa ya gaishe da Ummi da Abba suka amsa Ummi tace
"Zauna mana."

Kan sa a kasa yace
"Ummi nan ma yayi."
Ya zauna a gefen carpet, Maryam ya saci kallo yaga yadda idon ta ke motsi alamar ba baccin take ba bude idon ne bata so, Ummi ya kalla saboda Abba na waya yace
"Ummi bata da lafiya ne?"

"Eh bata jin dadi."
"Allah sauwake."

"Amin mungode."
Abba ya gama waya yace
"Tashi muje."

Muhammad ya mike yabi bayan Abba, har cikin babban falon sa suka karasa, ya zauna akan carpet, Abbi yace
"Ah Muhammad yi zaman ka akan kujera."

"Nan ma ya isa."
Ya fada yana gaishe shi. Abbi ya amsa sannan yai gyaran murya, zai magana kenan Farouk ya shigo, ya gaishe da su Abbi sannan ya mikawa Muhammad hannu ba yabo ba fallasa suka gaisa, gyara zama yai shima akan carpet, Abbi yace
"Muhammad mun kira ka ne akan Maryam, hakika wani lokacin ina manta alakar mu da ita domin mun dauke ta tamkar yar cikin mu, zan iya ce maka tafi wasu ya'yan namu a wajen mu, yarinya ce mai ladabi da biyayya wacce take da addini da ilimi, mai son kyautatawa kowa bata da hayaniya bare fada tin zaman mu da ita a gidan nan na sama da shekara hudu ban taba jin wani yace tai masa abu na batanci ba sam, kullum cikin kyautatawa mutanen gidan nan take, duk wanda ya samu Maryam ya dace kuma ya samu babba rabo. Ba ina fada maka haka bane dan na yabeta ko in kara maka son ta ta yadda zaka kara kwadaituwa da ita ba, sai dan naga kai ma kana da hankali in har haka zata faru zamufi kowa jin dadi dan fatana kenan Maryam ta samu me rike ta tamkar tana hannun mu bana son tai maraicin komai da kowa."

Abbi ya dakata Muhammad kan sa na 'kasa sai yanzu ya gane cewa Maryam ba yar gidan nan ba kila yar kanin su ko wansu ce, kila iyayen ta ne suka mutu. Maganar Abba ce ta dawo da shi daga tunanin da yake,
"Mun tsinci Maryam shakara hudu da wani abu da suka wuce a garin Bauchi lokacin munje wani aiki da mai daki na akan hanyar mu ta dawowa muka bige ta wannan dalilin yasa muka kai ta asibiti, dole mu tsaya akan ta muga yanayin jikin ta wanda a dalilin haka muka kwana a asibitin duk da cikin dare ne amman da mai daki na ta bukaci ta kira gida sai muka gane bata da kowa, ko kuma nace tamkar ta rasa komai na tunanin ta, dan bata tuna kowa sai mutane biyu a rayuwar ta da muka tambaya ina suke kuma bata sani ba, gashi kuma bata magana, a wannan halin da muka same ta muka sa likita ya bincika mana lafiyar ta wanda anan muka gane matsalar ta na da yawa tana da ciwon zuciya, ga damuwa, kuma rashin magana ma razana ita ta dauke mata ita sai abu na karshe shine tana da cikin watanni wajen uku."

Da sauri Muhammad ya dago, Abba ya gyada masa kai, sannan ya cigaba da magana
"A gaskiya a halin da muka ganta ba zamu iya barin ta ba dan tana fama da laulayi kuma tana bukatar kulawa wannan yasa mai daki na ta bukaci mu taho da ita, haka muka zo da ita gida mukaci gaba da kulawa da ita ta sha jiki wanda daga baya Allah ya bata lafiya har ta haifi yaron ta Aliyu Haidar, a haka mukaci gaba da rayuwa da ita kuma har yau bata tuna komai game da bayan ta, muna jin dadin zama da ita dan mun dauke ta tamkar yar cikin mu, bana baka labarin nan ne dan ka taimaka mata ba, in har kasan wani abu ya taba zuciyar ka, ko son da kake mata ya ragu, ko ka fara zargin wani abu dan Allah ka janye tin bata fada tarkon son ka ba, da farko ya kamata mu sanar maka to matsayin ta a wajen mu ya mantar damu dan ji nayi tamkar Najwa aka zo nema aure, bana son Maryam tai kuka akan wani abu a rayuwa, kullum addu'a Maryam ta tuno gida dan dole wata rana za ta so sanin asalin ta, duk da mu bamuce mu ba nan asalin ta bane muma asalin tane kuma gatan ta, na fada maka wannan saboda aure kazo nema a aure ba a karya."

Jikin Muhammad sosai yai sanyi ya rasa me ma zai yi ya rasa tunanin da zai yi zuciyar sa kuwa sai dukan uku uku take, Farouk kuwa ransa ne ya baci, dan me za a zo a fadawa wani na waje wannan bayanin dan yaje ya yayatata kila ya guje ta kila yaje yai mata wani sharri shi in ta shine sam ba za ai wannan abun ba shiyasa yaso ya aure ta ko dan rayuwar ta ko dan gudun wannan alamarin amman ina tayaya bayan Mama ta lalata komai tayi Allah ya isa a duk lokacin da ya aikata haka dole ya hakura ba dan baya son ta ba sai dan samun ya rabauta amman yana ji yana ganin sam ba zai taba yadda wani ya wulakantata ko yaci zarafin ta ba tabbas sai inda karfin sa ya kare.

Dakin ne yai shiru kamar ba kowa a ciki, Abbi yace
"Kaje kai tunani Muhammad ba ai maka dole ba kai kazo neman auren ta haka ba zamuce kada ka janye ba kaje kai tunani sosai akan lamarin."

Kai ya russuna sannan ya mike yace
"To Abba, amman ni ina ganin ba wani tunani da zanyi, duk da haka ina son ta."
Kai Abbi ya girgiza yace
"Kaje dai kayi sosai kaga in da yiyuwar abun."

"To shikenan ina godiya Allah ya saka da alheri."
"Amin Amin."
Ya durkusa yace "zan tafi."

Abba ya kalli Farouk yace
"Raka shi Umar."

Farouk ya mike Muhammad yabi bayan sa a haka suka karasa har wajen motar sa, Farouk ya kalli Muhammad yace
"Muna son kanwar mu ba zamu lamunci bacin ran ta ba, a dalilin ka ciwon ta ke son tashi, in har kasan haka zaka cigaba da sa rayuwar ta a matsala to kada ka soma shiga cikin rayuwar ta dan ba zamu lamunci wannan ba."

Wani Murmushi Muhmmad yayi yace
"Da da cuta nazo ga Maryam bazan fito ba, hakika ina son ta kuma ita ce rayuwa ta kuma damuwar ta ta wace dan haka kar ka damu akan wannan fata na ka tayani addu'a Allah ya bani ita dan naga alamun ita din mai sa'a ce gwana ce kowa so yake."

Yana fadar haka ya shiga cikin mota yace
"Nagode Bro in-law."
Ya daga masa hannu ya fice, Farouk yabi sa da wani banzan kallo sannan ya koma wajen su Abba. Suna zaune suna tattaunawa Farouk ya zauna yai kasa da kai yace
"Amman Abba sai naga kamar bai dace a fada masa ba tinda bamu san irin son da yake mata ba kada yaje ya yayata mana yar uwa kasan mutane."

Murmushi Abba yayi yace
"Kada ka damu, ina ji a jikina Maryam daga babban gida take kuma koman daren dadewa zata koma gida kuma gaskiya zatai halin ta naji na yadda da ita dari bisa dari so komai zai faru da ita kadaddar ne Allah bata ikon cinyewa."
"Amin."
Ya fada, Abba ya mike yace
'Bari naje sai da safe, "

Abbi shima ya mike yace
"Muje naga jikin nata."
Farouk ya mike yabi bayan su..

Tana zaune, dan ba a jima da cire mata karin ruwan ba, gaban ta bowl ne na farfesu, da Ummi ta kawo mata, amsa sallamar su Abba tayi suka shigo suka zauna, Abbi yace
"Ya jikin 'ya ta?"

Kanta a kasa tace
"Da sauki Abbi."
Farouk yazo ya zauna kusa da ita yana fadin
"Yar gatan Ummi ni ina nawa?"

Ya dauki spoon ya dauki tsoka ya kai bakin sa, ido ya lumshe yace
'Uhmm dadi."
Abbi yace
"Kai baka kawo mata ba kazo kana cinye mata ko?"

"Yanzu zanje na kawo mata ta fada min me take so?"
Kai tai kasa dashi, Abbi yace
"Yakamata kasan me take so ai ba sai ka tambaye ta ba."

Abba yace
"Ai kasan in mutum bashi da lafiya yana canja abinda yake so ko?"
Abbi yace
"Haka ne 'ya ta me kike so?"

Kai ta girgiza, Tace
"Ba komai Abbi."
Ummi ce ta fito daga kitchen suka gaisa da su Abba ta zauna tana fadin
"Kici ko kyaji dadin bakin ki."

Farouk ya dau spoon ya kara ci yana fadin
"Bari na bata."
Ya dauki guda daya ya mika mata ta amshi spoon din ta kai bakin ta ta fara ci, su Abbi sun jima sannan suka tafi.

Maryam ma sama tayi tana shiga taga wayar ta tai haske dauka tayi taga missed call din Muhammas guda goma, sai message guda biyu zama tayi ta fara karantawa na farko ya rubuta
"Kin ban mamaki Maryam da kika kasa gane da wa kike tare, na fada miki ina son ki kuma da gaske nake son ki ba da yaudara ba kina zaton wani abu zai raba mu ba abinda zai sa son ki ya fita a raina ko yaya kike ko me kika aikata bare wannan bansan kaddarar da ta baro ki da gida ba kuma ban sa a rai na cewar marar kyau bace ina kallon ki da son gaskiya ba zan taba saka zargi a tsakanin mu ba ki sani Muhammad na son ki da duk zuciyar sa da rayuwar sa."

Hawaye taji yana zubo mata bata taba jin son sa irin na yanzu ba dayan sakon ta bude ta fara karantawa
"Wallahi ba yaudara a zance na ki bani dama zan zame miki duk abinda kika rasa zan kasance dake a duk runtsi dan Allah ki bani dama."

Sai na ukun da yake fadin
"Ki dauki waya ta dan Allah Baby."
Ido ta runtse hawayen dake idon ta ya hau zubowa, kwanciyya kawai tayi dan zuciyar ta ta fara raya mata wani abu kar taje tausayin ta kawai Muhammad yake ji shiyasa ba zai barta ba ita sam bata so. Da irin wannan tunanin bacci ya dauke ta.


*
Washe gari da safe tana kwance bayan tai wanka ta canja kaya, Ummi ce ta bude kofar ta shigo rike da tray ajiye tayi ta karasa tana taba jikin Maryam, ido ta bude, mikewa tayi tace
"Ummi."

Ummi ta kamata ta mikewa tace
"Ya jikin?"
"Da sauki.'

Ta dauko tray ta mike mata cup, amsa tayi ta kurba ta bude bowl din da ta hada mata dankali a cikin kwai, fork ta dauka ta bata ta amsa taci sai da ta ci da yawa sannan ta ajiye plate din, magani ta dauko, Maryam ta bata fuska, Ummi tace
"Please kike daurewa daughter bana son ina ganin ki a haka."

Amsa tayi ta runtsa ido ta sha, Ummi ta hau shafa mata baya, lamo tayi a jikin Ummi sai da ya tsarga mata, sannan ta kwantar da ita ta mike ta fita, tana fita wayar Maryam ya hau kara da farko ta zata Muhamamd ne amman tana dubawa taga Aliyu ne, dauka tayi ta kwanta, muryar sa tajiyo yai mata sallama, wanda sai da ya haifar mata da faduwar gaba, dan yadda taji muryar tata har cikin kwakwalwar ta tsigar jikin ta ta tashi, ido ta lumshe tana amsawa, yace
"Ya jikin naki?"
"Da sauki."

"Allah kara sauki."
"Amin."
Sukai shiru sai kuma yace
"Kan na tafi na farai miki magana akan Muhammad, kinga abinda kika jawowa kanki ko? Kina zaune lafiya kin dauko wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login