Showing 57001 words to 60000 words out of 232912 words

Chapter 20 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1282

na fara girma so da kulawar kake bani daga Ammi sai kai na fara sani daku kadai na shaku, Yaya ku ne jigo in akace mutuwa akan ku nasan zan shiga wani hali dan Allah ka daina kawo mutuwa akan ka kaji?"
Hannun ta ya kamo yasa dayan na share mata hawayen dake zubowa yace
"Naji *Matar Haidar* ba zan kara ba mutuwa ba yanzu ba sai na zama tsoho matata ta zama tsohuwa sannan mu mutu tare a burne mu ga kabari na ga nata haka yayi?" Kai ta gyada yace
"To smile now!"
Murmushi ta dan saki yace
"No ban yadda da wannan ba."

"Kai Yaya muje rana nayi kaga har 11:16 kai da kace 10 zamu fita."
"To ba kece ba!"

"Ni kuma? A'ah ni ba ruwa na."
"Oh ko?"
Ya tada motar suka bar wajen. Aisha suka dauka da Rukayya ya kaisu wajen da za ai musu gyaran kai da lalle ya biya komai sannan ya tafi ya barsu.


*Allah ka yafe mana kasa mu cika da kyau da imani Amin*


*Antty*


ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 19

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

*HML Layuza Kabir Adam. Allah ya sanya alheri da albarka, Allah ya bada zaman lafiya ya kawo zuri'a mai albarka. Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




Tin lokacin ake gyara amarya har karfe shida da ya dawo sannan aka gama mata, amman fa ba karamin kyau tayi ba, gashin nan nata mai tsayi ya kara tsawo sai sheki yake, haka nan lallen ja da baki kamar ajikin ta aka hallice shi dan yadda ya dace da kafar yai kyau sosai da sosai. Lokacin da ya shiga ya *same ta ana kankare bakin kasa motsi yayi sai ido da ya zuba musu ana gamawa ya karasa yana kallon kafar tata mai taushi fara tas sai zanen lallen da yake akai mai kyau da daukar hankali.
" *Matar Haidar* kinyi kyau!"
Mikewa tayi tana fadin
"Wash nagaji wallahi!"

Hannun ta ya kamo yana fadin
"Sannu ai kwalliyya ta biya kudin sabulu."
Kallon sa tayi ya sakar mata murmushi ya matso kusa da ita ya kai bakin sa kunnen ta yana fadin
"Ai da zaki yadda da mun tafi gidan mu nai miki tausa na gasa miki jikin ki yadda zakiji dadin sa sosai ko?"

Dan hararar sa tayi yace
"Ni kike harara ko?"
Waya ta dauka ta kira su Aisha akan su fito, suma duk sunyi kyau abinsu. Nan suka fita ya bude mata mota ta shiga ya zagaya ya shiga a hanya ya siya musu kayan motsa baki sannan suka karasa gida suna zuwa ana kiran sallah magariba dan haka sukai ciki shi kuma yai alwala ya tafi masallaci.



9:45pm yana kwance akan gadon sa wayar sa tayi kara hannu yasa ya dauka. Ahmad ne ya kai kunnen sa yace
"Kada kace min komai!"
Dariya Ahmad yayi yace
"To nayi shiru ya shirye shirye?"

"Alhamdulillah!"
"Gobe sai kamu ko?"

"Yes!"
"Wallahi naso nai attending bikin nan amman Allah bai yi ba please am sorry my friend!"

"In ban hakura ba ka fada min ya zanyi zan zo na dauko ka ne. Ka sani da nasan da haka da, da wuri zan zo na taho dakai ace biki na ba babban aboki kai abun ba dadi sam."
"Ga Alkasim nan."

"Duk da haka amman kai ma i need you by my side, ina da damuwa Ahmad!"
"Meya faru? Wacce damuwar kuma ce zata dame ka bayan nasan *Matar* kace kadai damuwar ka, kuma a iya sanina ita ba zata samar maka da damuwa ba sai dai tai maka maganin ta!"

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Ahmad nasani amman akan tane dai."
"What happened?"

"Ahmad you know my problem....."
"Me kenan?"

"My health problem mana, about my feeling...."
"I think this problem has already gone..."

"Ina fa kasan *Matar* tawa akwai tsoro, sam taki bari na rabe ta ko dan rage zafi, dan Allah yadda muke da ita nan ai yaci ace komai ya wakana ta saba da komai amman ina? Tin na farkon nan fa, ko hannun ta na rike zata fara ba kyau fa."
Ido ya lumshe yace
"Am suffering, dan ranan Alkasim ne ya kaini asibiti abin yana son yafi karfi na, ina da kyankyami i can't go for any girl, ita kuma taki ta ban hadin kai, kullum sai tace sauran kwana kaza, i know sauran kwana kaza, but am afraid....... The thing is getting worse wallahi kwana biyu ban bacci bakaga ba duk na rame bani da nutsuwa kullum aba ta a tsaye ga marata a daure kamar dutse...."
Ya karashe maganar cikin rauni. Sosai abokin nasa ya shiga tausayin sa.

Can yace
"Kasan me?"
"A'ah!"

"Ya kamata ka daure ta da jijiyoyin jikin ta, i know Maryam Love's you and she will not allow you to suffer, so you have to used this change and have her."
"Tayaya kai na ya kulle Ahmad!"

Nan ya masa wasu maganganu wanda na kasa gane ko me ya fada masa amman dai naga Aliyu yai murmushi yana fadin
"Thank you so much friend i really appreciate with your help, please kai ma ka daure kai aure ka daina bin matan waje."

Murmushi yayi yace
"Zanyi aure matan waje kuma ana rage zafi ne kai bagashi nan ba sai wahalar da kai take amman ni kam da na fita na samu yar Baby zata dan kawar min da sauran sha'awa ta."
"Ahmad please ka daina wannan rayuwa. Ba kyau fa. Na sha fada maka ba auren yarinya zakai ba kana yaudarar su, ni Maryam Matata ce kuma kaga yanzu dai remain few days to go...."

"Insha Allahu friend tsokanar ka kawai nake insha Allahu kan ka gama amarci ka samo mana Baby nima zan zama ango inji abinda kaji, naso ma tare za ai dan kar kazo kana isa ta da...."
"Ya isa dan Allah. Kai dan iska ne wallahi."

"Naji amman ka fini jaraba ko?"
"Nima Allah ya dauran amman na kusa ka daina ce min jarababbe tinda da na damu *Matata* a gefe kuma ba zakaji wani problem dina ba zatai min maganin shi nasani."
"To *Angon Maryam* ana dai bi da yarinyar mutane a hankali kaga yarinya ce sosai."

"Kaci gidan ku naga *Matata* ce nafika son ta da tausayin ta dan haka shut up your mouth, ka kyale ni na kwanta nayi tunanin matata ma."
"Uhmm ko dai ka kirata ta dan rage maka zafi ko ta waya ne."

Ido ya zaro yace
"Wa wallahi sai dai ta hargitsani kuma kar kasa yanzu ido na ya rufe na shiga har cikin gida na nemi matata ba zan iya ba."
"Ah haba dai ina kunyar ka take ne yanzu?"

"Kaga please bari naje nai waya da *Matar Haidar* "
"To Haidar *Angon Maryam* sai anjima."
Ya kashe wayar.

Tana kwance a tsakiyar Aisha da Rukayya ya kira ta mikewa tayi ta koma kan resting chair dake dakin, dariya sukai suka ce
"Yanzu Yaa Haidar ba zai bar mu muyi hirar karshe ba,."

Tai murmushi takai wayar kunnenta tace
"Bakai bacci ba?"
"Tayaya zan iya bacci *Matata* na nesa dani."

"Haba Yayana ina tare dakai fa. Gani nan kusa dakai."
"Bakya kusa dani da kina kusa dani Allah ba zaki bacci ba yau."

"Me zamuyi to?"
Ta fada tana murmushi.
"Kwana zamuyi ibada!"

"Yanzu ma ai sai muyi mu ta godiya da Allah ko?"
"Wannan godiyar sai muna tare ake yin ta *Matar Haidar* ina kewar ki tare dani."

"Yaa Haidar ina tare dakai fa a cikin zuciyar ka, dan haka ka daina feeling loneliness am always with you."
"Hmmm to *Matar Haidar* me kike baki kwanta ba?"

"Baka kira ni munyi sallama ba, sannan kasan muna tare dasu Aisha."
"Sun hanaki bacci ko? To kice in basu barki kin huta ba yanzu zan zo na dauke matata."

"To shikenan. Yanzu kaje ka kwanta sai da safe kai mafarki na."
"Kullum ne ai."

"Oh bye Allah ya tsare min kai ya tashe mu lafiya!"
"Amin kema haka *Matata* "
Suka kashe wayar akan kirjinta ta ajiye ta tana murmushi, ita kan ta she miss her husband tana son taji ta ajikin sa tana samun nutsuwa. A haka bacci ya dauke ta.



Washe gari tin safe gidan ya kara haramar mutane daga gidan Ummah har gidan su Ammi babu masaka tsinke. Itama Maryam tana dakinta ita da su Aisha da Rukayya da yan uwan ta ya'yan yayen Abbi da Yayan Yaye da kannen Ammi, wasu duk sun girmi Maryam amman kuma duk suna son ta dan Maryam ta iya mu'amala da kowa ga ladabi da girmama na gaba da ita wannan yasa take zaune lafiya da kowa. kafin a kira la'asar tayi wankan ta dan Ammi tace basa son african time karfe biyar aka saka dan haka tace biyar tai mata a bakin wajen ko da ba a time din zata shiga ba ta kasance tana kusa da wajen. Tana sallah mai kwalliya da aka dauko har gida tazo ta fara aikinta. Fuska ta dauka don kwararraiyar mai kwalliya Yaya Fadima ta dauko ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan ba da fuskar mutum take canzawa gaba dayanta. Kwalliyar tai mata kyau dan mai kwalliyar ma kanta, ta yaba to daman a bace mai kyau gashi an kara mata kwalliya duk wanda ya kalle ta sai ya kara kallan ta.

A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din sai Aisha da Rukayya da wata ta karasa musu kwalliyar a lokacin suma duk sun shirya.

Wata mota ango ya turo mai kyau da tsada dan daukar amarya zuwa wurin biki. Wanda Yaa Alkasim ne ke jan motar. Aisha na gaba, Maryam da Rukayya a baya suna zuwa suka fita, Yaya Fadima ta leko tace
"Yaa Haidar yana hanya sai kace wata mace ace har yanzu bai gama kintsawa ba."


Tana cikin motar da Yaa Alkasim ya sakar mata AC taga shigowar jerin gwanon motocin angwaye wannan yasa zuciyar Maryam ta karu da bugawa.

Saitin motar da take anan aka parking motar da Aliyu yake. Yana baya zaune a hakimce yana waya. Yana yi yana murmushi yace
"Dan Allah ka barni naga Matata!"

"Aliyu wallahi kai jarabbabe ne."
"Naji!"
Ya fada yana kashe wayar sannan ya fito, yana fitowa ko ina ya dauki kamshi.

Motar da yake ya nufa, Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu karya ya yarda yana son Matar sa. Daga Maryam har Aliyu sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani hadadden material peach a jikinta da ta samu tela yayi mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada da wani yadi mai kyalkyali akayi mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata shi daga tsakiyar daurin nata da pin. Takalminta mai tsini da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har wani dan karkacewa tayi.

Hannu ya zura mata dan ya san ya sake ya shiga motar nan to komai zai iya faruwa, hannunta da ya sha ja da bakin lalle da abin hannu ta daura akan nasa ya dago ta, ta fito a hankali, tana gama fitowa aka fara daukar hotuna kamar me.

Nan aka fadawa MC isowar ango da amarya ya saka kida na musamman kawayen amarya masu anko suka fito sukai musu iso bayan su kuma abokan ango ne. A hankali take tafiya wanda shima yake taya ta yin irin takun da take so ba karamin dace da burge kowa sukai a wajen ba.

Yaa Rabi'a da Yaya Hauwa matan Yaa Muhammad da Yaa Ibrahim sai Yaa Ummulkusum da Yaya Zainab da Yaya Fadima da sukai ango iri daya suka karaso suna musu liki da 1-1k tin kan su karasa wajen zaman su. Bayan sun zauna ne aka bude taro da addu'a sannan aka kira Innah kakar Amarya da zuwan ta kenan itama ta karaso ita da kawar ta dan kama ango da amarya. Nan suka kama su aka cigaba da taro kamar yadda aka tsara.

Haka aka cigaba da gudanar da taro anci ansha an raba gift na kasko turaren wuta da humra da turaren wuta da muhuci da sauran su. Amarya dai kan ta a kasa ango ta kuwa sam ya kasa dauke idon sa akan ta. Da suka fito fili ma an musu liki daga dangin ango har dangin amarya kowa yayi rawar gani.

Ana magariba taro ya watse Yaa Alkasim ya mai da Maryam da Aisha da Rukayya, Ango kuwa anan sukai magariba sannan suka wuce daya daga cikin gidan da Abbah ya basu dan saukar bakin sa na nesa. Gida ne babba akwai komai a ciki, abinci kuwa Mamah ke akai musu kala kalar abinci.




Washe gari dinner tin yamma aka farai mata kwalliya sai da akai magariba aka gama sallah tayi sannan ta saka kayan ta aka kara gyara mata kwalliyar ta. Kayan ta na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne baki sai adon golding yellow a jikin sa. Riga da siket aka yi mata. Fadar irin kyan da tayi bata baki ne domin amarya ta fito a amaryar ta tai kyau sosai da sosai. sai dai ace masha Allah kowa ya ganta sai ya furta masha Allah.

Tini aka dauke kowa aka tafi dasu sai ita da Aisha da Rukayya da suke jiran zuwan ango. Mota biyu ce suka zo daukar amarya daya Ango ne a ciki wacce za a dauki amarya daya kuma Ba kowa su Aisha za a dauka da Rukayya wanda Yaa Alkasim ke tuka motar.

Wani abokin sa ne a gaba yana jan motar shi kuma yana baya tinda suka fito daga gida ya kasa dena kallon Maryam, kunya ya bata ma kan ta a kasa, ta dan dago ta kalle shi, Itama yayi mata kyau sosai yana sanye da golding yellow din shadda tai masa kyau sosai da sosai. Wani kyau na musamman taga yai mata. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai gidansu. Ya mika hannu ya kamo hannun ta mai taushi wanda a tare duk suka lumshe ido.

Janyo ta jikin sa kawai yayi ya daura kan ta akan kirjin sa, ido ta lumshe shima haka a haka suka karasa wajen dinner basu san an zo ba sai da sukaji rufe motar da abokin sa yayi. Ido ya bude yaga sun iso wajen. Dago ta yayi ya gyara zaman babbar rigar sa sannan ya kamo hannun ta yace
" *Matar Haidar* gobe ne fa!"

Kasa tayi da kan ta, yai murmushi yace
"Ina son ki, ina kaunar ki, kada ki taba mantawa da Ni Haidar naso ki, kada ki taba mantawa da duk duniya bani da tamkar ki, kece sirri na."

Knocking glass akai ya saukar da glass din kasa yace
"Ya akai?"
Waya Alkasim ya miko masa yace
"Ahmad ne yace yana kira baka dauka ba."

Amsa yayi yace
"Dan jaraba me kuma zan masa."
Ya kai kunne yace
"Menene?"

Dariya Ahmad yayi yace
"Ni nasan in kana tare da *Matar Haidar* ne kadai kake min wannan abun saboda bani da mahimmanci a gun ka in kuna tare ko? Ba komai kun karasa wajen ne?"
"Yess yanzu zamu shiga!"

"Ok a shiga lafiya ayi taro lafiya a gama lafiya nima na gama da wannan garin anjima zan tafi dayan in na siyi sim zan kira ka da na sauka insha Allah!"
"Allah ya tsare ya kai ka lafiya."

"Amin Ango tafiyar awa goma sha ce nasan zamu sauka a wata kasar kan mu karasa ban sani ba ko zan samu nai maka wishing Happy marriage life but i wish you all the best and may Allah bless your union, Happy Marriage life once again!"

"Thank you so much!"
Yai dariya yace
"sai washe gari tariya zan kira naji ya kuka kasance."

"Dan iska kasan wa zaka tambaya ba dai ni ba."
Ya kashe wayar yana bude kofar juyowa yai ya kalle ta yace
"Wannan dan isakan ne."

"Kai Yaya, Yayan nawa!"
"Oh ni kuma menene naki?"

" *Miji na* , *Jigonah* "
Ido ya lumshe yace
"Muje kar kisa nayi abinda zakice -Ba kyau fa- "
Ya fada yana kwaikwayar muryar ta in zatace ba kyau fa.




*Allah ka jikan mu kasa mu cika da kyau da imani*



*Amin*

ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 20

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


*HML KHADIJA SANI DAUDA AND MY SIS HASSANA, ALLAH YA SANYA ALHERI YA BADA ZAMAN LAFIYA YA KAWO ZURI'A MAI ALBARKA. AMIN*

Ya fita ya kamo hannun ta haka suka karasa wajen aka shiga da ango da amarya yau sosai wajen ya hada manyan mutane dan abokan Aliyu duk sun zo yau dan gobe daga juma'at za a daura aure dan haka an kara samun ba'ki masu kwana.

An gudanar da biki yadda ya dace cikin nustuwa, girma da ilimi kowa abin ya burge shi, an yanka cake an sha rawa da hutu kamar ba gobe. Suna daga zaune ta hango Yaa Alkasim sit din su daya da Aisha suna ta hira murmushi tayi tace
"Allah tabbatar da alheri zan so ki zama cikin zuri'a ta."

Rukkayya ta gano da abokin Aliyu suma zaune tace
"To ni kam da Yaa Ahmad nai miki kamu Allah ya hada kowa da rabon sa."

"Tunanin me kike *Matar Haidar* "
Kallon sa tayi tana murmushi nan masu huta suka samu abin yi, tai kasa da kai tace
"Tunanin *Miji na* nake"

"Gani wane tunani na zaki, ki ta kallo na kawai!"
Ta kara dagowa sai tayi saurin yin kasa da kan ta a kunyace.


Sai wuraren sha daya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Aliyu ya dubi Maryam wacce duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Key ya amsa wajen Abokin sa. Yace
"Ka tafi zan mai da Matata daga nan a gida zan kwana sai da safe kawai."

"Allah tashe mu lafiya."
Sai da yaga tafiyar kowa sannan ya dawo cikin hall din wanda Maryam ce kadai a ciki. Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji dan yadda yake dan murza hannun nata cikin yanayin tsokanar mutum.

Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin direba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan cinyar sa. A haka ya tayar da motar ya soma tuki cikin nutsuwa.

Shiru tayi jin yadda yake mata tsoro da fargaba dan tini wani lokaci da ya wuce da haka ta faru, dan haka kanta ta jingina a jikin kujera kawai ta zubawa titi ido. A hankali yace
"Tunanin me kike yi ne"

Ta dan rufe idonta ta bude tace
"Babu komai"
muryar nan tata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login