Showing 114001 words to 117000 words out of 232912 words

Chapter 39 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1252

su ba kinga kuwa dole ya saka ido sosai akan ta dan kar abun da ya faru baya ya sake faruwa."
"Haka ne Allah ya raba lafiya!"

"Amin. Abbi na son ya shigo yaganta but late yake dawowa ya fita da wuri amman yace na duba ta Allah bata lafiya."
"Amin Yaya!"
Ta mike tace
"Ni zan koma sai da safe!"

Mikewa Ummi tayi tabi bayan ta. Lokacin dan har bacci ya dauke Maryam. A bakin kofa suka samu Aliyu yana jin motsin su ya kara waya a kunne. Ummi ta karasa tace
"You better stop this pretending!"

Kai yayi kasa dashi ya nufi kofa ya shige da sauri, Dariya Ummi da Mami sukai. Sannan suka cigaba da tafiya suna tattaunawa akan aiki daga baya suka dawo maganar Maryam. A bakin gate din Mami suka tsaya suna cigaba da hirar. Suna tsaye motar Hajiya Mama ta shigo aka shige akai parking sai da ta jima a cikin mota tana kallon su sannan ta fito fuska a hade. Zata shige ciki.

Ummi tace
"Sannu da zuwa Hajiya Barira!"
Ko kallon ta batai ba ta shige. Mami tace
"Ai maganin ki!"

"Yaya ni ba zan iya gaba da ita bayan babu kyau."
"To ai sai kiyi tayi."
Ummi tai murmushi tace
"Bari na wuce sai anjima!"

"To sai anjima!"
Mami ta fada tai ciki Ummi ta nufi sashen ta.


**
Washe gari Ummi a gida ta zauna da Maryam dan yau da amai ta tashi zuciyar ta tai ta tashi da Aliyu yai mata allura ya dan lafa bayan ya tafi aiki kuma sai abun ya kara gaba ga ciwon ciki ga kirjin ta da take ta kuka dashi. Wannan yasa ba shiri Ummi ta dauke ta suka nufi asibiti.

Yana zaune a office yana tunanin ko a wane hali Maryam take ko ya jikin nata. Wayar sa ta hau kara dauka yai ya duba yaga Ummi ce take kiran sa. Dauka yayi yace
"Ummi ba dai jikin nata bane."
"Gamu nan karasowa asibiti!"

"Sai kun karaso!"
Ya fada ya mike yafita ya fara zagaye parking space yafi minti ashirin a wajen duk motar da zata shigo sai ya kalla dan yadda ya kafe bakin gate din da kallo. Yana tsaye motar Ummi ta karaso da tai parking ya karasa ya bude baya inda Maryam ke kwance dafe da kirji tana juyi. Ummi ta fito ta zagayo ta kamata wasu nurse biyu suka karaso da kujerar tura mara lafiya aka daura ta akai office din Aliyu suka nufa gaba dayan su.

Kan suje har wasu likitoci sun shiga suna jiran su suna zuwa aka rufa akan ta. Allura sukai mata ta samun relief sannan suka farai dubata.

Aliyu na tsaye ya kasa komai dan sam ya rasa me zai sun dauki kusan rabin awa kowa ya tafi yin gwaje gwajen da zasuyi da Maryam. Ummi da Aliyu na zaune duk sun kasa magana. Sai bayan wajen awa daya suka dawo da ita aka kwantar. Doctor Hauwa ce ta pkaraso tana fadin
"Doctor gaskiya jikin ta ba kwari Sam rashin cin abincin ta yana neman illata ta da babyn cikin ta ga ulcer da take da ita. Daga ita har babyn are suffering!"

Ta mika masa result din ya amsa yana kalla, Doctor Lukman ne ya shigo da file a hannu ya samu waje ya zauna Yana fadin
"Doctor Ina yan uwan ta yarinya nan she is in danger fa, abun yai yawa ga ciki, ga hawan jini, ga ciwon zuciya sannan babban illa ne ga mai ciki fa..."

Ya fada cikin damuwa da halin da Maryam take ciki. Kai Aliyu ya dafe ya amshi file din yace
"Thank you all doctor Allah saka. Zan dau hutu na yau insha Allah zan kula da komai, komai zai zo da sauki."
"Allah Kara sauki!"

Suka juya suka fita. Ummi ta mike ta koma gaban gadon da Maryam take bacci, Ummi tace
"Son ina tsaro kar mu rasa yarinyar nan ba tare da taga iyayen ta ba."

Wani kwarin gwiwa yaji duk da zuciyar sa na karyewa shima wani lokacin a hankali ya mike ya karasa gaban Ummi ya kamo hannun ta yace
"Kada ki karaya Ummi na. Ki cigaba da addu'a zan tayaki da kula da ita sai yadda karfi na ya kare insha Allahu zata tashi da kafafun ta da bakin ta zata koma gida cikin aminci da izinin Allah."

Hannun sa ta matse a nata tace
"Allah ya yadda ya bamu sa'a!"
Ta fada hawaye na zubo mata. Ya saka hannu ya goge mata ido sannan ya ja mata kujera ya zaunar da ita yace
"Bari naje na amso magungunan da suka dace sai nazo mu tafi gida ko?"

"Ok!"
Ya fita. Ta kamo hannun Maryam tana kallon ta hawaye na zubo mata na tausayin ta. Yarinyar ta kuma ramewa gaskiya tana wahala. Hannu ta daura akan ta tana shafawa a haka Aliyu ya dawo ya same su. Ya karasa yace
"Bata tashi ba?"

"Eh!"
"Mu bari ta tashi sai mu tafi ko?"

"Eh!"
Ya koma kan kujera ya zauna yana kallon su. A haka aka kira sallah ya tafi masallaci Ummi tayi anan. Yana dawo ya samu Maryam zaune akan sallaya.

Zama yayi yace
"Ummi ta tashi kenan?"
"Eh har tayi sallah!"

"Zamu iya tafiya?"
Kai ta gyada ta mike ta kama Maryam ta zaunar akan kujera sannan ta ninke sallaya. Ta kama hannun ta suka fita Aliyu na binsu a baya.

A haka suka karasa parking space ya amshi key din motar Ummi ya bawa messenger sa akan ya kawo masa gida ya shiga tasa su Ummi a baya suka tafi gida. A main parking space yai parking ya fito ya zagayo wajen su Ummi ya bude musu kofa. Ummi ta fito rike da maryam. Dai dai fitowar Hajiya Mama daga gate din su kenan. Kallon su ta tsaya har Ummi tai gaba Aliyu ya mara musu baya da ledar magani.

"Wacece wannan kuma?"
Ta fada tana kankance ido ta ina zata san su waye wannan. Ciki ta koma da sauri ta dauki waya ta fara kiran Farouk. Yana dauka tace
"Kana ina?"

"Mama ina hanya akwai abinda kike bukata ne?"
"Da ka dawo kazo kaji ko?"

"To Mama."
Ya kashe wayar yana fadin
"Allah yasa lafiya dai!"

Da sauri ya shigo gidan ya nufi sashen su. Dakin Mama ya nufa ya same ta tsaye a bakin kofa tana safa da marwa da sauri ya karasa yana fadin
"Lafiya dai ko Mama?"
Juyowa tayi ta zauna akan kujera sannan ta kalle shi tace
"Zauna mana!"

Zama yayi ya zuba mata ido, tace
"Wata yarinya ce a gidan nan?"
"Gidan nan kuma Mama? yarinya kuma?"

"Eh a sashen Aisha take!"
Shiru yayi yana nazari. Mama tace
"Naga kamar bata da lafiya!"

"Ohhh wata yarinya ce!"
Ya fada yana ya mutsa fuska.
"Yar wajen wacece?"

"Mama gaskiya ban san ta ba duk yayan su Anty Umma na san su amman wannan ban san daga ina take ba."
"Ina son na san wacece ka tambayar min Aliyu!"

"Wanne Aliyu Mama? Kinsan Hamma ba magana yake so ba bare nai masa magana ya ban amsa wallahi ba zai fadan wacece ba."
"To ya za ai ina son nasan wacece?"

"Amman Mama saboda me? Ina ruwan ki dasu?"
"Ban sani ba."

Kai yai kasa dashi. Tace
"Tashi kaje ina son ka samon wacece yarinyar nan ko a wajen Innar kuce!"
Mikewa yayi ya mike ya fita. Ya nufi sashen inna yana fadin
"To ita Mama dan Allah ina ruwan ta da su bayan ba shiga harkar su take ba."

Inna na zaune tana cin gashin naman da tayi Farouk ya shigo da sallama. Dagowa tayi ta amsa tana fadin
"Umaru har ka dawo kenan!"
Zama yayi yace
"Eh ya gidan?"

"Lafiya ni kuwa su Aisha sun dawo daga asibitin ka kira min su dan Allah muji ya me jikin?"
"To Inna amman wai wacece yarinyar nan?"

Gyara zama tayi tace
"Aisha ce ta samo ta kasan Aisha da tausayi fa."
"Bangane ba Inna!"

"Kai fa haka kake da tambaya kamar dan jarida in kai shiru ma ai zan fada maka kasani. Ba ranan Aisha da Shehu sunje Bauchi ba?"
Kai ya gyada yace
"Eh yafi sati nawa da dawowar tasu ma."

"Yauwah to acan suka same ta."
"Kamar yaya kenan wai Inna?"

"Suna cikin tafiya suka kade ta daga nan shine fa ta suma to da tafarka kuma ba lafiya haka sukai jinyar ta na kwanaki wanda a jinyar suka gane ta samu matsala ta manta iyayen ta da komai. Abun dai kamar aljanu kamar asiri ga ciki mutum biyu take iya kira daga mijin sai mahaifiyar ta. To fa shine suka taho da ita Aisha ke dawainiyya da ita yarinyar kirki mai hankali da nutsuwa. To kaji Aliyu ke ta dawiniyya da ita. Yau dai jikin yaki yi tin safe take amai wannan yasa Aishan suka tafi asibiti har yanzu ban sani ba ko sun dawo."
Baki Farouk ya tabe, ya zaro waya ya fara dadananawa. Wayar ta Inna ta miko masa tace
"Ni dai nasan wayata da kudi bare ka wulakantani nace ka kira min Aisha kaki, danno min a wayata."

"Nifa bance ba zan kira ba!"
Fara neman layin Ummi yayi lokacin tana zaune Aliyu na sakawa Maryam ruwa. Wayar ta ce tayi kara Aiyu ya miko mata ta amsa ta kai kunnen ta.

Inna ya mikawa, Inna ta rafka sallama Ummi ta amsa tana fadin
"Inna barka da rana!"
"Yauwah Aisha ya jikin Maryam din?"

"Inna da sauki mun dawo ma yanzu."
"To madallah bari nazo naga jikin!"

Tashi tayi ta mikawa Farouk wayar dan ya kashe mata tare da fadin
"Tashi muje mu duba ta?"
"Inna muje kuma? Kije dai!"

Wani kallo tai masa sannan ta mike tace
"Sai kaje wallahi ka duba ta kila baka tabai mata sannu ba."
Ta yafa mayafi ta kalle shi tace
"Tashi muje!"








*Allah ya jikan mu, ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*



*Antty*
*Antty*[11/20, 12:32] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 46

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Ya mike ya fita tabi bayan sa tare da rufe dakin ta da key. Bangaren Ummi suka nufa ba kowa a falo wannan yasa Inna ta nufi sama tana fadin
"Suna sama kenan. Ni benen nan sam bana son sa ciwon kafa kawai zai saka mutane mu da bamuyi rayuwa dashi ba yaya bare ku da baku da abin yi sai gini da bene kamar tsuntsaye."
"Ke inna kin fiya mita wallahi ina ruwan ki to ai ba bangaren ki akayiwa benen ba."

Lokacin suka karaso bakin kofar ta tura kofar tare da sallama. Aliyu dake zaune ya mike ya nufi kofa, Inna na shigowa ya fice Farouk ya sama bakin kofa ya shige sa ya sauka, da kallo ya bisa. Inna tace
"Kana ina Umaru?"

Ya shigo dakin yana ya mutsa fuska, Inna ta zauna gefen Maryam, tan fadin
"Sannu ya jikin?"
Da hannu tai alama da sauki. Inna ta juyo ta kalli Farouk ya hade fuska yace
"Ya jikin?"

Bai jira ta basa amsa ba ya juya ya fita. Inna tace
"Ja'iri yazo ya cikani da tambaya akan ta dan me ba zan ce yazo ya duba ta ba shi ko tausayin ta ma bai ji?"
Ummi tace
"Kinsan Farouk ai kyankyami gare sa."

"Mene abun kyankyami a gun Maryam?"
"Amai yaji tanayi kinsan sa ai!"

"Oh ni yasu aman ma sai kyankyami menene a cikin sa. Allah ya kyauta to."
Inna ta kalli Maryam tace
"Kinga har tai bacci Allah sarki me taci?"

"Ba abinda taci!"
Mikewa Inna tayi tace
"Bari naje na samar mata abu kan ta tashi."

"To Inna muna godiya!"
Ta fita, a falo ta samu Aliyu zai fita tace
"Wai me kake gani game da jikin yarinyar nan ni dai da zaka bi tatawa da an gwada na hausa."

"Dan Allah Inna kiyi hakuri kar kice zaki ta bata abubuwa ki barta haka nima ina kula da ita kuma naga abun nan ciki ne in lokacin karshen wahalar yai ai zai wuce amman gamje gamjen nan duk bai da amfani sai yazo ya haifar mata da wata matsala kuma."
"Hmm ai shikenan amman da haka uwar ka har ta haife ka shin me ita ya same ta, a lokacin wallahi ba asibitin da muke zuwa duk yadda Suleimanu yaso na hana kuma ya hanu sai ni ke bata na gida kuma da ta tashi haifar ka duk gidan nan ba yaro kato mai lafiya kamar ka amman wai kai ke kushe maganin gargajiya anya kuwa Ali, wai kai bokan turai wannan sun sauya kane kawai."

Bai tanka mata ba har ta gama ta fita ya koma ciki ya zauna a falo yana danna waya. Sitti ya gani akan allon wayar tana kira dan murmushi ya saki ya kai wayar kunnen sa yana fadin
"Matata!"
"Hmm Ali kenan ya gidan ya aiki?"

"Ina yini Sitti?"
Ya dai dai ta magana cikin girmamawa.
"Alhamdulillah ya gida da aiki?"

"Alhamdulillah!*
"ya mai jikin?"
"Da sauki Sitti but wallahi Sitti tana wahala sosai ba abinda take ci fa."

"Ya kuke barin ta haka ina Hajiya Hauwa ita ba zata dan mata wani abu da zataji dadin ci ba."
"Haba Sitti, me Inna zata iya zata bata abinda zai cutar da ita ne tana girka komai ta bata bayan yarinyar tana bukatar abun gina jiki ne amman ita tana bata traditional thing wanda ba abinda zai kara mata."
"Ai nasan za a rina Ali. Nasan zaka aikata haka amman banda abin ka mu a da din aka ce maka cimar mu bata kara lpy a jiki ne? Ku kuke ganin bama hada abun da zai gina mana jiki amman wa ya kai mu cin abun da zai gina mana jiki. Kaga mu bama rabuwa da kayan lambu wanda kai kan ka ko a likitan can kasan yana daya daga abinda aka fi so muci sosai. Duk abinda zamuyi sai mun saka wake ko yar gyada a ciki banda nama da kifi to me kuma za a fada mana in har kana so yarinyar nan tana samun abinda zataci ka lallaba Inna tasan me zata bawa masu irin matsalar ta kaji ko?"
"Sitti....."

"Kai shiru kawai kaje. Shin da ta zauna babu mai gina jikin babu mara gina jikin ba gwara ko yaya ne ta samu taci ko ba zai amfaneta da komai ba rashin cin abinci matsala ne shi kadai zai iya jefa mutum a halaka bare ga ciki ga ciwo dan Allah Aliyu ka bari ana bata wani abu nasan halin ka."
"Shikenan Sitti."

"Yauwah Allah maka albarka ai da ina nan waje na za a kawon ita, kai yanzu ma ko zaka kawon ita!"
"Zan duba in gani Sitti!"

"To shikenan!"
"Ya jikin?"

"Nifa yanzu ba abinda ke damu na."
"Masha Allah Allah kara sauki."

"Amin Allah yayi albarka."
"Amin Sitti sai anjima."

"To kada ka manta fa."
"Insha Allahu!"
Suka kashe wayar jingina kai yayi da jikin kujera tare da lumshe ido.


2012
```Ba abinda ya fado masa sai Maryam matar sa lokacin da tana da ciki. Farkon cikin ta da wani matsanan cin ciwon kai ta fara wanda sam bata fada masa ba dan Maryam akwai dauriya duk dawainiyyar sa bata daina ba ta yadda ya gane tana da ciki in ta gama girki kauri gas sai yasa tai ta amai amman a haka take masa komai. Wannan yasa ya dauki jinin ta awon farko ya nuna tana da ciki murna gun Aliyu ba a cewa komai haka su Ummi sai dai tin daga lokacin lafiya tai kaura daga Maryam dan sai ta daina cin komai ko ruwa ta sha sai amai wannan yasa ya mai da ita gida wajen Ummi suka kula da ita ba karamin damuwa Aliyu yai akan cikin Maryam dan shi kan sa daina cin abinci yayi dan sam ba zai iya ci Maryam bata ci ba.

A haka Inna ta fara mata dure duren abincin ta wanda wani da tayi cokali biyu zata dawo dashi amman sam Inna bata daina duk da bata so amman in Inna ta kawo amsa take ta ci ko da zata dawo dashi. Kwana suke basu bacci ba saboda zazzabi wani lokacin ciwon ciki duk magungunan da zai bata ba sauki. Ummi tace
"Aliyu ka kwantar da hankali kila in cikin yai kwari zata samu rangwami!"

Aliyu kan ce
"Ummi har yaushe wata uku zuwa hudu muna fama da abu daya."
Inna ta shigo da kwano a hannu tana fadin
"Haka fa kowa yai fama ba akan ku aka fara ba da zaka na tada wa mutane hankali."

Maryam dake zaune ta mikewa kwanon ta amshi maza kici zakiji dadin bakin ki. Amsa tayi amman kasan ranta bata so dan bakin ta sam ba dadi kuma tasan da taci zata dawo dashi amman a haka ta amsa ta fara ci tana ya mutsa fuska Aliyu kuwa kamar yai me dan Ummi ta hana sa ne amman da ba abinda zai bari taci mikewa yayi ya fice a fusace. Inna tace
"Ana musu gata basa gani dan kan uba gaba yazo yana godiya ai."

Ummi tai murmushi Maryam ta mike da sauri ta nufi bandaki Ummi tabi bayan ta yana falo yaji kakarin ta da sauri ya shigo kamar zai kuka yace
"Kinga ko Ummi tana zaman zaman ta an janyo mata amai."

Ya kamo Maryam suka fito suka sauka zuwa dakin sa. Inna ta girgiza kai tace
"Ni ba muguwa ba ce ai in abinda kake tunani kenan."


Irin wannan yasa ya dauke matar sa suka bar kasar gaba daya. A can shi ya dinga kula da ita kullum sai karin ruwa a haka cikin yai wata biyar wanda daga nan ta samu sauki sai kuma kwadayi da ciye ciye cikin lokaci kan ta sauya tamkar batai laulayi ba tayi kyau tai kiba ga cikin da ya dan fito yai mata kyau. Wacce kulawa ce Aliyu bai bata ba komai take so shi yake mata ya daura rai akan cikin nan in ya zauna yana hira da cikin kamar me hira da mutum.

Cikin watan ta tara su Ummi suka matsa ya dawo ba yadda ya iya haka suka koma lokacin cikin ta ya kara girma kamar zai fado kasa. Da suka koma kowa yai murna ganin su da jin dadi yadda Maryam ta warke a haka suka cigaba da rayuwa wanda satin su biyu da dawowa da safe nakuda ta taso mata Aliyu na bacci ya jiyo numfashin ta a bandaki da sauri ya shiga ganin halin da take ya kira farouk bai sanar da kowa ba suka tafi asibiti sai da sukaje ya kira ya fadawa gida ai kan kace me aibiti ya cika da yan gida, Maryam ta sha wahala dan tin safe har rana tana fama kai abu kamar wasa har dare wajen bakwai sauran likitocin suka samu Aliyu akan ya kamata ai mata CS dan karfin ta ya fara daukewa yaron ma ya daina motsin dan ya galabaita shi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login