Showing 228001 words to 231000 words out of 232912 words

Chapter 77 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1222

fara tana tafa hannu tace
"Yau ni kake cewa Maryam matar kace ko? Ai na sani ba sai ka kara fada min ba tinda gashi nan har ciki nagani a tare da ita...."

Da sauri Maryam ta mike ta nufi kofa tana fadin
"Mun tafi Inna."
"To ku gaida gidan."

Ta karasa wajen Yaa Haidar suka shiga mota, kallon ta yayi yace
"Inna tafiya neman magana."
"Kai Yaya ai gaskiya ta fada."

Hararar ta yayi ya tada mota, gidan Sitti suka nufa suna zuwa Basma ta rumgume Maryam tana fadin
"Oyoyo Anty Maryam."

Falo suka shiga suka gaishe da Sitti, da Momy. Tasleem dake zaune rike da waya ko kallon su batayi ba, Yaa Haidar ya dan kalle ta ya dauke kai yace
"Ke baki iya gaisuwa bane."

Baki ta turo, Sitti tace
"Gata nan tin safe da ta fita ta dawo take cicin magani ko magana ta kasa."
Maryam ta dan saki murmushi, Sitti tace
"Ya gajiyar biki?"

Maryam tace
"Tabi jiki Sitti."
Ta mike sukai ciki ita da Basma, tana daki Jawahir ta kira ta tana fadin
"Wai ba zaki zo bane."

Ido ta zaro tace
"Wa A'ah aci amarci lafiya ya gajiya."
"Ban sani ba."
Ta kashe wayar, dariya Maryam tayi sukai waya dasu Aisha da Rukayya da su zasu d'aga yanzu. Sai yamma suka tafi gida. Tasleem kuwa ko marmarin kallon Maryam da Yaa Haidar bata son tayi dan in ta kalle su a yanayin da ta gansu da safe take kara ganin su, haushin su take ji gaba dayan su.


ο»ΏBayan an gama biki kowa ya koma ya cigaba da rayuwar sa, wanda Maryam lokacin ba inda take zuwa kullum tana gida duk lokacin da Yaa Haidar yaji kewar ta ko yana waje aiki gida zai karaso yazo yaga matar sa tai masa abin dadi ya koma dan har abinci take aika masa bama in ta san zai kai yamma a asibiti.

A haka suka cigaba da rainon cikinta sosai take samun kulawa daga gare shi da Ummi, watan cikin ta biyar Yaya Fadima da matar Yaa Muhammad suka zo duba ta, taji dadin zuwan su sosai, kwanan su biyu suka juya tayi kewar su.

Kullum cikin yiwa Ammi magiya tazo amman tace me zatazo tai mata ga Ummin ta nan, haka Mami suna waya sosai, haka da Haidar karami ma suke waya ya saba dasu gaba dayan su.


A haka suka cigaba da rainon cikin su har ya shiga wata tara wanda a lokaci kuma cikin sai ya safa rigima abu kad'an kuka da shagwaba, sam bata iya ko bacci in bata tare da Yaa Haidar haka duk inda yake zata nemo shi ta kwanta a jikin sa yana massaging jikin ta da mata kalamai masu dadi har bacci ya dauke ta.

Tin da satin haihuwar yazo suka koma wajen Ummi ta cigaba da kula da ita wanda kwana su biyu da safe bayan ya tafi aiki nakuda ta fara da sukaje aka duba ta akace da sauran, Aliyu na tare da ita daga baya hannun ta ya kama tana tattakawa in abun yazo zata duke a wajen sannan su tashi su cigaba a haka har haihuwar tazo gadan gadan aka shige da ita aka fara taimaka mata bata jima ba ta haifi babyn ta katuwa da ita kyakyawa mai kama da Abban ta sak.

Lokacin da Yaa Haidar ya dauki Babyn kuka ya saka yana mai godiya da Allah da ya nuna masa jinin sa kan ya koma ga Allah, Haidar karami ma sai murna yake Momyn sa ta samo masa kanwa.

Tana kwance Yaa Haidar ya karasa gadon da take rike da Baby, zama yayi a gefen ta yana nuno mata fuskar Babyn ido ta lumshe ya shafa kanta yana sakar mata kiss a goshin ta yace
"Sannu *Matar Haidar* Allah miki albarka ya baki lafiya, ina son ki *Ummu Haidar* "

Ido ta lumshe tana mai karajin son mijin ta, Najwa da ta shigo tace
"Yaya a gadon asibitin ma sai kunyi soyayya."
Ummi ya kalla dake waya ya dan harari Najwan yace
"Bar nan marar kunya."

Baki ta turo tace
"Bani 'yar tawa to."
Ta amsa ta basu waje, Yaa Haidar kuwa sai addu'a yake wa Maryam da kalamai masu dadi wanda yasa take jin wani sanyi da dadi a cikin zuciyar ta.

A ranar aka sallame su suka koma gida, d'akin ta aka gyara suka zauna ita da Babyn ta, da dare wajen goma ya shigo dakin nasu, tana zaune rike da Babyn da ta gama shan mama ta mika masa ya amsa ya saka a kafada yana shafa bayan ta sannan ya sauke ta ya ajiye ta akan gadon, Maryam ya janyo jikin sa yana shinshinar wuyan ta dake tashin kamshi, yace
"Kamar ba mai jego ba."

"Kai Yaya."
"Uhmm ni bama wannan ma yau a ina zan kwana?"

Dariya ta dan saki tace
"Ka tafi d'akin ka nima baka ga a inda nake ba."
"Anya zan iya kuwa?"

Kofar d'akin aka budo Ummi ta shigo da sallama, turus tayi, Maryam ta janye daga jikin sa da sauri, Ummi tace
"Ka tashi ka tafi ka barta tai bacci ta huta."

Kai ya hau shafawa yana fadin
"Ummi korata zaki."
"Ai dare yayi Dr."

"To bari naiwa Baby bye bye."
Ya dauki babyn yai masa addu'a ya ajiye, Ummi ta fita, Maryam da ta juya musu baya ya janyo yana daura ta akan cinyar sa, sauka tayi tace
"Yaya kada Ummi ta dawo fa."

"Amman ai mayi sallama ko?"
Bakin sa ta kama ta dan tsotsa sannan ta sake shi tana fadin
"Sai da safe."

Kamo ta yayi ya hade bakin su sai da ya jima yana kissing nata sannan ya sake ta, ya gyara mata kwanciyya yai musu addu'a sannan ya sauka ya tafi dakin sa.


*
Ana ya gobe suna yan Kano suka sauka, zo kuga murna sun tahowa da Baby da maman Baby kayan barka masu yawa da kyau da tsada, ranar suna Babyn taci sunan Ummi Aisha suke kiran ta da Humairah haka akai taron suna lafiya, Maryam ta samu kayan barka daga yan uwan ta, dan jin ta take tafi kowa gata yan uwa ne da ita ga na Kano gasu Yaya Hannah da suka zame mata suma yan uwa masu son ta da kaunar ta, haka nan Yaa Abubakar ya dauke ta tamkar kanwar sa ta ciki d'aya duk wata sai ya turo mata kudi tare dayiwa Haidar siyayya haka zai kira su gaisa yaji me take so, akai akai kuma yake sa Anty zuwa ta dubo ta, dan haka itama ta dauki shi tamkar su Yaa Alkasim, tana kara girmama shi tare da son sa da dan uwan sa da d'an dake tsakanin su, haka Mami ma da tazo barka ta kawo musu kaya masu yawa da tsada, ita kuwa me zatace ga yan uwan Yaa Haidar, ai ba abinda zatai musu sai addu'a shima Allah ya jikan sa ya kyautata makwanci. Ta yadda ita da Haidar ba wanda ya kai su gata da yan uwa masu son su. Bayan suna da kwana biyu su Yaya Fadima suka koma.


*
Sosai Maryam take jin dadin jegon ta dan Ummi ba karamin kula da gyara ta take ba, cikin satin su na biyu suka kara kyau ita da Babyn sukai jajir abin sha'awa dasu.


Zaune take a dakin ta tana bawa Humairah mama, taci kwalliya sai kace mai shirin zuwa wajen biki, sai kamshi take yi, Yaa Haidar ne ya shigo bakin sa dauke da sallama, amsawa tai tana mai sakar mata murmushi shima ya sakar mata ya karaso ciki ya zauna a gefen su yana rumgume ta a jikin sa, ido ta lumshe tace
"Sannu da zuwa Yaya."

Babyn ya cire daga shan Maman ya ajiye a gefe ya daga Maryam ya daura a cinyar sa yana shafa kirjin ta, ido ta lumshe ta kwantar da kanta a kirjin sa.
"Wai wannan wankan dole ne?"
Ido ta bude a hankali tace
"Haba Honey, kwana nawa ya rage."

"Wallahi na gaji Baby kuma naji Ummi na fadin zakije Kano?"
Kai ta gyada tace
"Zanje Ammi da Abbi suga Humairah."

"Dan Allah ki bari in mun koma gida sai muje muyi kwana biyu mu dawo."
"Duk yada kace Yaya."

"Yauwah yar aljanna shiyasa nake son ki."
Ya kama lips din ta yana tsotsa. A haka suka dan ragewa junan su zafi.


*
Ana gobe arba'in ya samu Ummi zaune a daki, ta kalle shi tace
"Jibi fa tafiyar su Maryam banji kana shiri ba."
"Ummi ai nace a bari in mun koma da sati sai muje tare ko?"

"Aliyu ba dole nake so nai maka ba amman kana gani tinda Maryam taga yan uwan ta bata taba zuwa tai kwanaki cikin yan uwan ta ba, ni da ta tawa ce ka barta ta tafi jibin, daga can taje Adamawa ta nunawa su Malam Babyn kaga suma zasuji dadi itama haka amman ace bata da damar da zata gida ta dade taga yan uwan ta."
"Shikenan Ummi."

"Yauwah Dr Allah maka albarka."
Ranar da sukai arba'in washe gari suka daga Kano har da Haidar karami da suka samu hutu, kwanan ta biyu a gida duk suka tafi Adamawa, satin su daya acan wanda taga gata sosai da soyayyar yan uwan ta sannan suka dawo gida Kano taje gidan duk yan uwan ta yini suma sun zo gida sun sha hira sosai suka kara gyara yar uwar tasu, wanda satin ta biyu Yaa Haidar ya sauka, kwana sa biyu suka juya gaba dayan su, gidan Ummi suka sauka sai dare sannan suka wuce gidan su.

Tin a mota yake rawar kafa, Maryam dai sai dariya take masa, yan d'an harare ta yace
"Allah ban kara yadda da wannan tafiyar mai tsayi in har ta zama dole to sai dai ayi dani."

Tana dariya tace
"Nima zanso na kasance a tare da miji na."
"Ba wani nan kina can kinawa Ammi shagwaba naga dai ke ba auta bace."

Ido ta zaro tace
"Wa yace maka. Ai i will always be Ammi's Autah."
"Kin girma fa ya'ya biyu."

"Allah yaya ko goma ne am Ammi's Autah, and i will always do what u ever i want to both you and them."
"Allah ya kawo goman."

"Yaya da yawa fa."
"Ni ina so ai."

"Allah ya kawo mana masu albarka."
Ya fada yana shafa kan Humairah dake bacci.

Bayan sun shiga gida. Ta kwantar da Baby, tare suka shiga wanka tin acan suka fara shan soyayyar su wankan da ba ai bama suka fito. A ranar soyayyar da aka jima ba ayi ba ita aka sha aka yi nanuwa juna yadda sukai missing junan su, sai da suka gamsu da junan su, suka nutsu, suka kara yadda da soyayyar juna su, sun yadda in ba daya daya yana cikin garari wanda suke addu'a Allah ya barsu tare.


_Muna ta bankwana fa, *Matar Haidar* yana ta hade kayan sa._

*Baki na ya kasa rufuwa ido na ya ciko da kwalla saboda soyayya, hakika zanyi miss naku, more especially Amina Yar'adua, Shaheedah, Jamila. Amina Yar'adua your comment makes me laugh even if am not in the mood, i so much love you Mamanah, i will miss your comment i hope u will be with me in my coming books, i really appreciate with your love, ban taba jin kewar irin wannan ba, ina fatan ta alheri ce, to ban sani ba ko shine last book dina, kila ba zan kara wani rubutun ba zan mutu, in haka ta faru please wanda na bata wa wanda na sani da wanda ban sani ba ya yafe min, ni na yafewa kowa dan wannan soyayyar taku tana sani naji zuciya ta ta karye har hawaye ya zubo min. Ina son ku da kaunar ku. Allah ya sada mu da alheri Amin. Please in na mutu kuyi min addu'a Allah ya yafe min ya jikan mu baki d'aya.*

*I will miss you readers* 😒 😒 😒


*Allah jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe.*



*Antty*
[12/15, 18:56] My Airtel: ο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 89-90
*Epilogue*

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


*JAN HANKALI*
*BAN YADDA WANI KO WATA YA COPY KO YA JUYA MIN LABARI, KO YA KARANTA MIN A KO WANNE CHANNEL BA TARE DA IZINI NA BA. NAGODE*

6 years later
Masha Allah rayuwace mai dad'i da zaman lafiya suke ciki gaba daya familyn kowa sai sam barka duk da wani lokacin akwai wasu kalubale da Allah kan jarabci bawa amman Alhamdulillah komai yana zuwan musu da sauki baya fin karfin su saboda sun rike Allah da bauta masa ba dare ba rana haka nan sun kyautatawa iyayen su da yan uwan su, a tsakanin su baka taba jin wani fada ko sabani kowa yana son dan uwan sa duk inda suka hadu zaka kamar su cinye junan su ya'yan na da zumunci da son junan su.

Cikin wannan shekarun Aliyu ya kara zama babban mutum dan har asibitin sa ya bude wanda yake aiki tare da matar sa duk da ita bata fiya fita aiki ba bama da ta cigaba da karatu har ta zama babbar likitan mata wanda ake ji da ita ba a iya Abuja ba har a Nigeria baki daya dan ma ba aiki take sosai ba in kaga ta shiga asibiti to an samu masu bukatar taimakon ta sosai wanda dole sai ita sannan take shiga asibiti ta. Sosai suka samu cigaba daga asibitin nasu dan yadda suke da kwararun likitoci.

A cikin wadan nan shekarun Maryam ta sake haihuwar Baby girl sau biyu, ta farko aka saka mata suna Maryam din suke kiran ta da Islam sai ta biyun ta aka saka mata sunan Mami suke kiran ta da Sajida, Najwa ma ya'yan ta uku maza biyu mace daya sai Aisha ma ya'yan ta uku mata biyu namiji daya, Rukayya ya'yan ta biyu mace da namiji inda namijin yaci suna Yaa Haidar, Anty Nusaiba matar Yaya Abubakar ma ta sake haihuwar ya'ya biyu duk maza, Yaa Farouk da Jawahir ma ya'yan su biyu mace da namiji daya sunan Mama ya saka mata sai namijin yasa suna Abba Usman.

*
Zaune take a falon Ummi sanye cikin wata atamfa fara ce wacce akai mata ado da blue and orange kala dinkin doguwar riga ne wanda yaji stone tai kyau ta sha dauri ga sakar gold wuya da hannun ta, Maryam ta kara kyau ta ciko ba rama a jikin ta ta kara haske kana ganin ta kasan kwanciyyar hankali ta zauna mata, Ummi ce ke zaune a gefen ta tana kallon tana murmushi, yadda take magana kamar zatai kuka, tana fadin
"Dan Allah Ummi ki sa baki yaki ya barni naje sam kuma Ummi kusan shekara fa rabo na da Kano, in ba irin hakan ce ta faru fa bai fiya bari na naje ba."
Tai maganar cike da shagwaba wacce har yanzu taki ta barta.

Haidar, da kannen sa Humaira, Islam, da Sajida, suka shigo a tare cikin shiga iri daya, dogayen riguna ne a jikin su, red and white kala wanda kansu an musu kitso jelar ta fito ta kasan hular dake kan su iri daya hatta takalmin su iri daya ne, in kaga Humaira da Islam sai ka zata yan biyu ne dan basu da nesa sosai, Sajida ce yar shekara uku, Haidar ma wando ne jeans da har riga a jikin sa, sai takamlmi baki yaran kyawawa dasu abin sha'awa dukkan su leda ce a hannun su. Sajida ce ta nufi wajen Maryam ta hau an cinyar ta tana fadi
"Momy kinga abinda Dady ya siyo mana."

Janye ta tayi dan ita so take taji abinda Ummi zata fada dan tana son taje Kano ta hadu da yan uwan ta, wanda Matar Yaa Abdullah ce ta haihu take son zuwa sunan.
"Daughter ki bar damuwa zan masa magana shikenan?"

Kai ta gyada tana sakin murmushi, Sajida ta makale mata daukar ta tayi tana fadin
"Menene Sajida?"
Ta rumgume yarinyar da take kama da ita sak, dan Haidar kama yake da Abbin sa haka Humaira da Islam kamar su daya da Abbin su, Sajidar ce tayo ta gaba daya kamar ita haka su Ammi ke fadi. Yaa Haidar ne ya shigo dakin da sallama cikin shiga ta alfarma sai tashin kamshi yake, amsawa suka ya zauna akan kujera yana fadin
"Ku fito mu tafi gida."
Sajida, Maryam ta ajiye tai sama dan hado kayan su, da kallo ya bita sannan ya kalli Ummi yace
"Ummi yar taki sai rigima take ji fa."

"Ai Aliyu in ma tayi ba matsala tinda kai ka jawo."
"Ni kuma Ummi?"

"Dole fa kana barin ta tana shiga yan uwan ta, dan ma ka same ta mai hakuri ne, in wata ce ba zatana wata biyu bataje gida ba amman ita daga nan zuwa Kano ace kai ta hana ta zuwa sai ta shekara bataje ba, gaskiya Aliyu kana barin ta tana zuwa sai kace wata uwa duniya."
"Ummi saboda makarantar yara ne fa."

"Yanzu ai hutu suke, ka barta taje ta shiga cikin yan uwan ta."
"Shkenan Ummi, amman in ta tafi ni kuma fa.

"Kai meyasa baka da hakuri in dai akan Maryam ne, duk tsiya fa in taje ba zatai sati uku ba."
"Ummi ba zaki gane bane, wallahi kwana daya in nayi babu ita ni kadai nasan me nake ji, shiyasa sam bana son tai nesa dani amman tinda kinsa baki shikenan amman sati daya Ummi."

"Sati daya yai kadan Aliyu ka barta tai sati biyu kaga hutun su Haidar da yawa."
"Ummi...."

"Dan Allah Aliyu."
"Ummi an gama Allah ya kaimu shikenan."

"Allah maka albarka."
"Amin."
Saukowa tayi da jakar ta da jakar kayan su Haidar ta ajiye tace
"Bari naiwa su Inna sallama."

Ta fita ta nufi sashen Inna acan sukai sallama ta shiga taiwa Mama da Mami sallama ta fito a compound ta same shi da yaran Ummi na tsaye, ta karasa ta rumgume Ummi tace
"Ummi mungode sai da safe."
"Allah bamu alheri amman in kun dawo su Islam zasu zo suyi mana kwana biyu?"

"Abinda nace kenan sai su karasa hutun su."
Yaa Aliyu ya fada
"Shikenan ku gaida gidan."
Suka shiga mota suna dagawa Ummi hannu, sai da suka fita a gida ya kamo hannun ta yace
"To kiyi murmushi mana *Matar Haidar.* "

Juyowa tayi ta saki murnushi, ya kai hannun ta bakin sa yai kissing yace
"I love you."
Murmushi kawai ta sakar masa, har suka karasa gida. wanda yaran duk sunyi bacci, Sajida ta dauka ta shiga da ita ta canja mata kaya, Ya Haidar ya shigo Humaira da Islam itama ta canja masu kaya, addu'a tai musu sannan ta nufi dakin Haidar da shima Yaa Haidar ya kwantar dashi, addu'a tai masa sannan ta fita, bayan ta kashe masa fitila.

Fita tayi nufi bangaren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login