Showing 150001 words to 153000 words out of 232912 words
Chapter 51 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
na biyo ki bakya nan."
Wayarta ya amsa, ya kashe, juyowa tayi tana kallon sa ya hade rai ya ajiye wayar, wata unguwa suka shiga wacce ta gama haduwa duk zagayen ta a garin bata taba zuwan ta ba ta hadu sosai, bakin wani katon gida mai kyau suka karasa yai horn mai gadi ya bude suka shiga, parking yai ya fito ya rufe kofar ya zagaya ya bude mata, ta sauko tabi bayan sa ya nufi kofar wacce take da tumbprint din sa, hannu ya saka a kofar ta bude suka shiga wani hadadden falo ne wanda yake dauke da kujeru orange da lemon kala, haka labulaye da center carpet sai kamshi dakin yake ga wani sanyi mai dadi, kujera ya samu ya zauna ya kalle ta yace
"Wa yasa ai miki wannan kwalliyar?"
Shiru tayi yace
"Ba magana nake ba?"
"Sitti ce tace sai nayi."
Mikewa yayi ya dauko lemo a firij, ya zauna yana kallo TV yana shan coke kallo ta yayi yace
"Zauna man."
Kamar ba zata zauna ba ta dan zauna a gefen kujerar ta zauna ya dauki waya yana dan danne danne a haka ya gama shan lemon ya dan shafa cikin sa sannan ya dago yace
"Yunwa nake ji, ki shiga ki samar min wani abunda zan ci."
Mikewa tai tace
"A ina zan dafa maka?"
Ki shiga waccan kofar akwai wani corridor ki bi nan ne kitchen."
Ta juya ta shiga, wani falo ta kara shiga wanda yafi wanda suka zauna kyau, tana mamakin gidan wanene nan, corridor tayi ta shiga kitchen din, yai kyau, babu ce kawai babu, dan yai kyau a gyare wajen yake ta bude firij taga akwai wasu kayan amfani, kaza ta dauka ta wanke ta daura akan wuta ta dauki dankali ta yanka ta daura masa farar taliya da miyar kaji da dankalin turawa tana gamawa ana kiran magariba ta fito ta tada baya nan a kitchen tai alwala ta fito a tada sallah a falo tana zaune ya shigo ta dauko masa abincin ya dauka ya fara ci, ya dago ya kalle ta yace
"Ke bazaki ci ba?"
Kai ta girgiza yace
"To."
Ya cigaba da cin abincin sa sai da ya gama sannan ya zauna yana kallon ta, ta dago tace
"Yaya don Allah ka kai ni gida."
Banza yai mata har sai wajen bakwa da rabi sannan ya tashi yace
"Muje."
Ta mike yabi bayansa suka shiga mota, yana zuwa gida ta bude mota ta fita, zata wuce yace
"Ungo wayar ki."
Ta juyo ta amsa ta bar wajen da sauri ranta a matukar bace, tana shiga ta fara neman layin Farouk yana dauka tace
"Yaya kana ina?"
"Ina gidan Sitti."
"Please kazo ka dauke ni Yaya anan zan kwana."
"Meyasa kika koma gida?"
"To ba Yaya bane."
Tai magana kamar zatai kuka yace
"To gani nan zuwa."
Ya kashe waya sallah kawai tayi Farouk ya kira ta, tai wa Ummi sallma ta tafi.
Suna zuwa ta shiga dakin Najwa yan matan amarya ne a wajen Najwa na zaune kan sallaya ta karasa ta zauna, Najwa ta kalle ta tace
"Ina kika je ne?"
"Ba Yaya bane ya dauke ni kawai."
"Wane Yayan?"
"Wanne kuwa? Yaya dai."
"Wai shi Yaya mai yake damun sa ne."
"Uhmm."
"Ace ba zai barki ki sake ba, haba kina da saurayi amman yabi ya kankane?"
Wata kawar Najwa Hauwa tace
"Amman ba thesame father suke ba ko?"
"Yes cousin ne Yaya na fa."
"Ah son ta yake amman ko?"
Wani kallo Maryam ta bi Hauwa dashi da mamaki tace
"Yaya ne fa... Yayana ne shi"
Hauwa tayi dariya sosai tace
"Baya takura miki akan samari?"
"Uhmm ko waya baya so tayi dasu ba, ya hanata kula su sam."
Najwa ta fada, Hauwa ta kuma dariya tace
"Wai amman kinji Yaya ne, to haka kawai bazai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki waya, idan babu wani abu a kasa"
*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakhawan karshe. Amin*
*Antty*
[11/28, 13:42] Maryam S Indabawaπ₯°: ππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 61
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Maryam ta hade rai, Hauwa tai dariya, Maryam tace
"Kai ke wallahi baki san Yaya bane ko ke bai miki haka ba?"
Ta fada tana mai da tambayar kan Najwa.
"Ya min amman ba kamar naki ba."
"To ai ni dan muna tare ne."
"Uhmm cewa fa yayi kar ta tsaya kula samari ta riki karatu dan Allah kalli wannan budurwa mai kyau wai ita za a cewa kar ta kula samari."
Dariya suka sheke da ita Basma tace
"Uhmm kalli fa yadda Affan ya rikice daga ganin ta."
Dariya Hauwa tayi tace
"Tabb, lallai Yaya Aliyu"
Maryam dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Hauwa tace
"Toh wallahi son ki yake...."
Maryam ta zaro ido ta koma baya da sauri tace
"Don Allah ki daina cewa haka plsease, wallahi Yaya na ne fa, ke ai Najwa kinsan Yaya fa"
Najwa tayi wani murmushi tace
"Tinda ba ciki daya kuka fito ba ai an gama Maryam, ki daina tinda manyan yan soyayya suka gane to da wata a kasa fa. Ni daman na fara zargin sa dan yadda da kika zo hutun nan ya adabe mu da zarya har sai da kika koma sai muyi sati nawa bamu gansa ba amman kina nan kullum yana nan kuma bai son ya barki ki je ko ina ke kulawar Yayan tai yawa. Yadda Yaya yake miki ma ai bai mana ba, ke dai ce ban san lokacin da zaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai Yaya ne. A'a ba Yaya ba..."
lokaci daya hankalin Maryam ya tashi wai Yaya son ta yake, ji tayi ta kasa nutsuwa sai kara tabbatar wa suke Hauwa na kara zuga Najwa, Maryam tace
"Wallahi ku daina cewa haka ba kyau, ni ai Yaya yafi karfi na wallahi ba ruwan sa."
Dariya kawai Hauwa take don Maryam tayi mugun bata dariya, haushi suka bata ta mike ta bar dakin, dakin Sitti taje ta zauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, Sitti ce ta shigo ta zauna a gefen ta tace
"A'ah Yaushe kika dawo."
"Yanzu."
Ta fada tana kwanciyya akan gado, Sitti tace
"Meyake damun ki?"
"Ba komai Sitti bacci nake ji."
"To kinci abinci ne?"
Kai ta girgiza tace
"Na koshi."
Bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci a jikin ta ta kwanta akan gadon Sitti.
*
Washe gari yini da safe duk yan mata na dakin Najwa, Maryam kuwa na dakin Sitti kwance Najwa tayi tayi ta fito taki dan tin jiya bata kara komawa wajen su ba Basma ce zaune suna hira jefi jefi, wayar Maryam ce tai kara ta dauka ta kai kunnen ta tace
"Asslamau alaikum."
"Wa'alaikum salam."
"Ya kk ya gida?"
"Alhamdulillah."
"Jiya kuma sai kika gudu."
"Kai nane yake ciwo."
"Ayyah ya kike ji yanzu?"
"Ya daina."
"To sannu ya anjima fa? Nazo na kai ki?"
Kai ta gyada tace
"To in mun shirya zan maka magana."
"Shikenan sai anjima."
Sukai sallama, ta kashe wayar, Basma tace
"Wai da Muhammad za ayi ne? Affan na damu na fa."
"Ke kyale wani Affan dan Allah."
"Uhmm shikenan."
Ta koma ta kwanta.
Biyar har an fara kwashe yan tafiya wajen yinin bikin sauran yan matan suna waje suna jiran motoci, yau Maryam bata bi Najwa ba dan tin jiya ma bataje wajen ta ba da zasu tafi makeup tazo su tafi amman taki tace ba inda zata.
Biyar da rabi ta fito zuwa compound din gidan Sitti sanye take da less cream kala wanda akaiwa ado da coffee, ita tai kwalliyar ta kuma sosai tai kyau batai wani shafe shafe mai yawa ba amman ita kanta sai da ta kalli kanta ta kuma kalla dan tayi kyau, coffe kalar mayafi ta yafa, da wani half cover takalmi da jaka, sai dankunne da sarka da ta saka golding sosai tai kyau kamar ita ce amaryar.
Suna tsaye ita da wasu yan mata motar Muhammad ta karaso, wayar ta ce ta hau kara ta zata shine tana dubawa taga Najwa ce dauka tayi tace
"Kina gida ne?"
"Eh ke kina ina?"
"Mun fito yanzu zamu karaso akwai wata friend dina da zasu karaso yanzu please ki samu wani ya kawo mana su."
"Ok."
Ta kashe waya, Muhammad ne ya fito ya karaso, yana murmushi, ya karaso yace
"Amaryar Muhammad."
Tai kasa da kai yace
"Gaskiya ina kishi kar wani ya kalle min kyakyawar matata kinga yadda kikai kyau kuwa?"
"Kai Muhammad kai dai maganar ka kenan."
"Ai gaskiya ce shiyasa nake nanatawa kullum."
Murmushi tayi yace
"Zamu iya tafiya?"
Kai ta girgiza tace
"Akwai wasu da zan baka ka kai mana su, in Yaa Farouk bai zo ba sai ka dawo ka dauken amman yanzu please dear ka kaisu."
"An gama ranki ya dade suna ina?"
Nan ta shiga ta kira su, suka zo suka tafi a bakin mota yace
"Zan dawo fa."
Tace
"Toh."
wata hadaddiyar mota ta kunno kai harabar gidan duk mutanen dake gurin sun raja'a ga ganin motar, baka ce wuluk haka gilashin ta, kai ta dauke zata juya, jakarta ce ta fadi ta durkusa ta dauko tana juyowa taga Yaya Aliyu ya fito cikin wata shadda yar gaske sai maiko take, yayi wani irin kyau wanda duk wanda ya ganshi sai ya kyasa.
Idon 'yan mata kuwa kamar ya fado dan kallon da suke masa, ta ganban ta yazo ya wuce ya shiga dakin Sitti bai jima ba ya fito, tana tsaye suna magana da wasu yan mata ta kai su wajen wata mota aka zuba su kenan ta juyo suka hada ido kai ta dauke ta nufi cikin gida wayar ta ce ta hau kara tana duba taga Aliyu ne dagowa tayi tana ganin sa bai magana ba kuma bai daina kallon ta ba karasowa tayi tana tsayawa ya shiga tare da bude dayan gefen yai mata nuni a hankali ta karasa ta shiga ta zauna motar ya tayar wannan yasa ta rufe kofar dan kada ta fadi in ya ja,
Sanyi da kamshi dake cikin motar su suka saka ta lumshe ido, cikin isa da jan aji ya tashi motar ba tare da ya dube ta ba cikin gwaninta ya fisgo motar da gudu sai da suka hau titin wayar ta, ta dauka ta saka a silent dan kar Muhammad ya kira, dagowar da zatai taga sun dauki hanyar gidan da ya kai ta jiya, tsoro ne ya kamata da fargaba kar fa ya hanata zuwa wajen yinin nan, amman bari taga gudun ruwan sa, har ciki suka shiga ya bude ya fita kamar jiya ya dawo ya bude mata kofa, kallon sa tayi tace
"Yaya wajen yini fa zani."
Kai ya girgiza yace
"Ba inda zaki dan nima ba zani ba, bana son hayani gwara kema ki saba da rashin son ta, bama wannan ba kina so kije maza suyi ta kallon ki a haka ko? Kinga yadda kakai kyau."
Kai ya girgiza, cike da damuwa take kallon sa tace
"Yaya nayi gayyata kuma wasu daga kawayen Najwa ni suka sani ba dadi."
Kallon ta kawai yake ta dago suka hada ido da sauri ta kawar da idon ta yace
"yunwa nake ji banci komai ba Unmi batai mana girki ba yau, mu shiga ki min abinci."
Kallon sa tayi ganin fuskar shi ba alamun wasa yasa tai kasa da kai tace
"Ayyah Yaya muje wajen anyi abinci sai na kawo maka."
Jingina yayi da motar sa tare da harde hannu a kirji yana kallon ta tace
"Kin taba ganin naci abincin waje bare na wajen biki?"
Shiru tayi yace
"Gwara ki sani bana cin abincin waje duk uzurin ki, sai kin min abinci kan kiyi abinda kike so."
Ya fada yana yin cikin gidan, tsayawa tayi a wajen kamar ta fasa kuka amman ba yadda zatayi tafi minti biyar tsaye ta rasa me zatayi taji wayar ta na vibrating dubawa tayi taga shine, kin dauka tayi amman sai ga wani kiran nasa nan, dauka tayi ta kai kunne yace
"Yunwa fa nake ji."
Yadda yai maganar sai da yasa tsigar jikin ta ta tashi.
Wayar ta kashe tace
"To ina ruwa na."
Sai kuma ta juya ta nufi cikin gidan, tana shiga baya falon farko na biyu ta nufa ta same shi kwance akan kujera yana kallo a TV kitchen ta nufa tana shiga ta dauki indomie ta dafa masa ta saka kifin gwangwani ta dafa wani kwan wani ta soya ta dauko ta kawo masa falo, a gabanshi ta jera komai ta koma ta zauna ya dube ta yace
"Me kika dafan?"
"Indomie."
"Ni bana cin indomie."
Ya fada yana tsure ta da ido, kai ta dauke ya janyo stool din yace
"Amman tinda kin dafa yaya zanyi?"
A ranta tace
"Kada kaci."
Ya bude kamshi ya daki hancin sa ya lumshe ido yace
"Zo mu ci."
kai kawai ta girgiza dai dai lokacin da taji vibration din wayar ta a cikin jakata ta ciro wayar har ta katse ta duba taga uban miss call ta duba su Jawahir ne da Muhammad da Basma dagowa tayi ta dube shi, sai abincin sa yake ci hankalin sa kwance, baki ta tabe tace
"Dan Allah yaya kai sauri suna jira na."
"Nai sauri muje ina?"
"Wajen bikin."
Dagowa yayi yace
"Amman ai nace baza a ba ko?"
"Yaya bikin fa Najwa ne."
"Bikin Najwa bikin ki ne?"
Shiru tayi ya cigaba da cin abincin shi sai da yayi dam sannan ya mike yai ciki.
Sai da yaji ana kiran sallah sannan ya fito ya fita anan tai sallah sai bayan ya idar ya kira ta a waya yace
"Fito mu tafi."
Ta fita suka shiga mota suka bar gidan ganin sun dauki hanyar wajen bikin yasa ta fara murna amman sai taga ya dauke hanya, ranar dai a haka suka yi ta yawo a gari har taran dare, kuka ne kawai Maryam bata yi ba dan haushi wai ace biki kamar na Najwa bata guri ai da takaici gashi ya amshe wayata ya kashe sai tara ya maida ta gidan Sitti shima da kyar dan da cewa yai gida zai kai ta sai da tai ta rokan sa sannan ya kai ta gidan Sitti.
Tana shiga ta wuce dakin Sitti ta fada gado tana sakin kukan da bata samu tayi shi ba, Najwa da Jawahir dake compound sukaga wucewar ta suka biyo ta da fada Najwa ta shigo amman ganin tana kuka sai ta sakko tana tambayata menene? cikin kuka takece mata Yaya ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani zuwa gurin yinin, Najwa tace
"Ba komai kila shima yana da dalili."
"Wanne dalili? shidai burin shi ya ga raina a bace."
Nan dai ta shiga lallashin ta sannan ta fita Jawahir ta kalle ta tace
"Wai Yayan nan ba son ki yake ba kuwa?"
"Kema zaki fara ko?"
"Allah naga takurar tai yawa."
Dan tsaki ta saki ta haye gado tana fadin
"Dan Allah Jawahir kada ki fara."
"To taso muci abinci yanzu Yaa Muhammad ya kawo."
Shiru tai mata Jawahir ta hau gadon ta juyo da ita yace
"To wai menene?"
"Yaya ne mana duk ya batan yau dina."
"To menene sis yanzu fushin zai dawo miki da lokacin ne?"
Kai ta girgiza, Jawahir tace
"To please forget about it, let continue celebrate the rest day."
Ta kamo hannun ta suka sauka kasa tace
"Bari na kira Basma."
Ta mike ta fita tare suka ci Basma da Najwa da Jawahir da Maryam, nama ne da wani hadin salad, bayan sun gama suka zauna hira sune har karfe biyu idon su biyu, sannan suka kwanta.
Washe gari aka daura auren su Najwa da Abdul, da safe, bayan anyi reception, suka karaso gidan Sitti, anan akai hutuna, Maryam na daki akwace wayar ta ta hau kara, tana dubawa taga Muhammad ne yace
"Ina kika buye ban ganki ba sai zuba ido nake."
"Ina daki kunzo ne?"
"Yes gamu a sitting room naga kowa ban dake."
"Uhmm."
Yace
"Common my dear zo inga kwalliyar ki ai mana picture kinji."
Yana fada ya kashe wayar ta mike ta dauki rigar ta da ta cire ta saka wata army green kalar shadda wacce tai mata kyau ta dada haskaka ta, red mayafi ta yafa a kafadar ta, ta saka wani flat red takalmi ta daura dankwalin ta ta nufi stting room tana shiga ya taso ya karaso waje ta, a bakin kofa ta tsaya ya durkusa a gaban ta ya zaro wani box a aljihun sa ya bude wani zuben gold ne mai tsada a ciki ya dago yana kallon ta yace
"Will you marry me?"
Kallon sa ta tsaya yi, ya sakar mata wani murmushi mai sanyi ido ta lumshe tana sakin murnushi tare da gyada masa kai, yan dakin ne suka hau tafi ya kamo hannun ta ya zura mata zoben ta dago hannun ta tana kallon zoben, ya mike ya karasa wajen ta nan aka hau daukar su pictures tare akai musu da amare da ango Jawahir na wajen Yaa Farouk bata san me akai ba, Hauwa kawar Najwa tace
"Wannan shine Yayan naku?"
Najwa tace
"A'ah abokin Abdul ne fa."
"Tab gaskiya shima yana son ta, ko Yaya za ayi?"
"Uhmm ita tace Yaa Aliyu ba son ta yake ba."
"Uhmm kinga banganshi ba ko? Amman duk wanda zai ji yadda yake mata wallahi yasan son ta yake."
"To ni dai dukka ina son su, zan fi son ta da Yaa Aliyu dan indai da gaske Yaa Aliyu na son ta to tabbas ba son wasa yake ba dan ko matar sa da ta rasu hadasu akai amman ita kuma ace yana son ta after so many year of lossing his wife kai da naji dadi wallahi."
Tai murmushi tace
"Allah ya zaba mafi alheri ai Maryam abar so ce."
"Gaskiya ba ruwan ta gata da hakuri sosai."
"Uhmm Allah sarki."
Wajen su tayo suka gaisa da Hauwa dan bata san zuwan ta ba anan mazajen suka tafi suka bar yan mata suna yinin su. da daddare aka kai Najwa gidan Abdul
Suna zaune a dakin Najwa Muhammad ya kira ta, ba dan taso ba ta mike ta nufi bakin gate yana cikin mota layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace
"Ina yini"
yace
"Lafiya lau Baby."
"Masha Allah an gama biki lafiya Allah basu zaman lafiya"
tace
"Ameen"
yace
"Sauran namu ko?"
Fuska ta rufe da hannu, yace
"Eh mana dan kin nace sai kin gama karatun nan naki ne amman da nima kwanan nan zamuyi mu huta ko?"
Shiru tayi yace
'Ke za a bari yar zaman daki."
Ido ta zaro tace
"Da girma na."
Yai murmushi yace
'Gaskiya ke zaki sa musu ido su kasa sakewa ko?"
Tace
"Yaushe ango zai zo ne gida nake son tafiya."
"Ah haba tin yanzu ai sai anjima kar ki damu ni zan kai ki gida da kai na."
Shiru tayi tace
"To ni dai su Ummi