Showing 141001 words to 144000 words out of 232912 words

Chapter 48 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1245

yake shirin ruguza miki rayuwarki, ki kula, ki sani ba kowa ke da gaskiya ba wani yana son ki ne dan wani abu naki ko makamantan su, dan haka ki kiyaye ki ajiye wasa ki nemi wanda kike so baki sani ba ko shima yana son naki."

Ido ta lumshe yace
"Zaki ce baki da lafiya na cikaki da surutu ko? To gwara na ja miki kunne tin yanzu."
Yana fadin haka ya kashe wayar bata ji komai a ranta ba dan tasan kusan gaskiya ne amman ita to wa take so da zataje ta fada masa har shima kuma ya amshe tan? Juyi tayi kawai bacci ya dauke ta.

Tana kwance a falo akan doguwar kujera Ummi na kusa da ita akai knocking mai aiki ta leka sai ta dawo ta durkua tace
"Ummi wai Muhammad ne."

"Je kice ya shigo"
Ta koma ta fada sai gata ta shigo dauke da manyan ledoji guda biyu, Ummi ta gyara yafen mayafin ta Maryam kuma ta mike zaune, tana gyara hijab din ta.

Muhammad ya shigo sanye da Shadda Ash kala har da hula ba karamin kyau yai ba kamshin shi ya cika dakin, zama yayi a kasa ya gaishe da Ummi, Ummi ta amsa yai mata ya me jiki sannan ta mike. Mai aiki ce ta kawo masa ruwa da lemo.

Maryam na zaune kan ta a kasa tace
"Ina yini?"
"Lafiya lou My wife ya jikin?"

"Da sauki."
Ta fada taba rufe fuskar ta da hijab din jikinta, murmushi yayi yana kallon ta yace
"Allah kara sauki."

Ya matso yana fadin
"Magana nazo muyi."
Dagowa tai ta kalle shi, yadda yake zaune a gaban ta kamar dalibi da malama. Tace
"To ka tashi ka zauna akan kujera."

"A'ah nan ya isa."
Ta langwabar da kanta. Yace
"Me yasa kika kasa fada min?"

"Ba zan iya ba bansan ta ina zan fara ba."
"Amman ai kinsan ina son ki."

"Na sani amman kasan rayuwar nan, wani akan abu kadan zai iya rabuwa da wacce yake so."
Kai ya girgiza yace
"Sai dai in baya son ta."

"Ko yana son ta sau nawa akayi."
"Ba son gaskiya yake mata ba, ni kuwa son ki nake yi da gaske, ban da buri da ya wuce naga na mallake ki da ana bude zuciya da kinga abinda yake ciki wallahi Maryam da gaske ina son ki."

Dagowa tai tana kallon cikin idon sa, sam a da bataji tana son sa ba kamar a yanzu da ya amshe ta a yadda take amman me sai take tantama dan Aliyu ya sake saka mata tsoro dazu.

"Tunanin me kike dear?"
Kai ta girgiza tana fadin
"Ba wai ban yadda da kai bane, amman tabbas nasan tausayi na ne ya rinjaye ka."

"Kar kice haka Maryam duk inda so yake to da akwai tausayi a cikin sa, amman ni da gaske son naki nake kuma ina tausayin ki, in kin ban dama ko yau zan turo magabata na ai mana aure Maryam sai ki yadda cewa da gaske ina son naki."

Kai ta dauke daga kallon sa yace
"Baki yadda ba ko?"
Kai ta girgiza tace
"Na yadda da kai."

Murmushi yayi yace
"Yauwah my love ina yaro na."
"Yana wajen Mami."

Matsowa ya kuma yai yace
"Banga kin sake dani ba, please ki ban dama in nuna miki yadda nake son ki da kaunar ki."

"Na baka dama ba tin yau ba tinda har na baka damar zuwa ga magabata na."
"Nagode My love kwana biyun nan nasha wahala na rashin ki dan Allah ko da zamu samu sabani kada ki kara hukuntani da kashe waya ko kin daukar wayata ta kinji?"

Kai ta gyada yace
"Yauwah to dago ki min murnushin ki mai kyan nan."
"A falon Ummi dai muke."

"Ai dakin Ummi nane ni fa ban san wani sirika ba."
Tai murmushi tace
"Wato sirikin zamani ne a dakin sirikar sa ma soyayya zai yi."

"To menene a ciki?"
"Ah babu."
Yai murmushi yace "kema zakiyi a dakin Ammi"

Gaban ta ne ya fadi jin ya ambaci Ammi, dakewa tayi tace
"Dan kai baka da kunya nima bani da ita?"

"Eh saboda zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin....'
"Ban dani.'

Yai dariya yace
"Har dake."
Ta sunkuyar da kanta. Farouk ne ya shigo, ganin Muhammad zaune a gaban Maryam ya bata masa rai, fuska ya hade yai kicin kicin, ya karaso, duk suka juyo ya zauna a kusa da Maryam yana fadin
"Ya jikin my sister?"

Ta dago tana fadin
"Da sauki Yaya ya aikin?"
"Alhamdulillah zan dawo na biya na siya miki fura since yesterday Abbi na min dan biki wai bansan me kike so ba."

"Kai amman nagode daman tin dazu nake tunanin me zanci baki na ba dadi."
"Ah ai suya zakici bari ai magarib zan kawo miki."

"Thank you swt bro."
Ya mike yana fadin
"Ummi fa?"

"Tana sama."
Har ya juya tace
"Yaya kaga fa."
Ta nuna masa Muhammad dan kallon sa yayi yace
'Ai banganshi ba."

Ya dan daga masa hannu yace
"Ya kake?" Muhammad ya dago ya kalle shi yana fadin
"Alhamdulillah ya aiki?"

Gaba yai yana fadin
"Alhamdulillah!"
Ya juya yai sama. Maryam ta kalli Muhammad dake danna waya fuskar sa ba yabo ba fallasa, tace
"Ya dai?"

Ya dan dago ya kalle ta yace
"Ni me yasa baki fadan kina son wani abu ba."
"Ni ba wani abu fa nake so ba."

"Gashi nan shi da yake dan uwanki, kin fada masa."
"Kai dear rigima."

"Ba wani rigimi, please ki dauken a matsayin Yayan ki, abokin ki, kuma mai sonki, komai kike so ki fada min kinji as bro, friend and ur love kar kiji kunyar komai am always there for you."

"Thank you so much dear."
Ya dago ya dan kalle ta tai saurin dauke idon ta yai murmushi yace
"Bari na tafi magariba nayi."

"Nagode sosai a gaishe da su Ammi."
"Zataji insha Allah."

Ya mike yace
'Kicewa Ummi na tafi."
Kai ta gyada ya juya ya fita, furar ta dauka ta dauki spoon ta fara sha, Farouk ne ya sauko yace
"Yan mata kin gama zancen?"

Baki ta dan turo tace
"Ni ba zance nayi ba."
"To me kikai?"

"Dubani fa yazo oh baka sanshi ba ko? Abokin Abdul ne kuma yayan Jawahir."
Baki ya tabe yace
"Ko?"

Kai ta gyada yace
"Yayi kyau."
Ya fita a dakin. Roba daya ta sha ta ajiye sauran a firij ta hau sama dan tayi alwala.

Yadda take samun kulawa daga yan gidan nasu da Muhammad yasa nan da nan ta warware dan kowa na kokarin ganin ya dauke mata kewa da damuwa, Aliyu yana kira da safe da dare, duk da in ya kira ba wani hira suke ba karkari su gaisa ya tambayi Haidar tana ganin su zasu sha hira na rabin awa har na awa daya.

Duk da haka tana da damuwa wacce in ka titsiye ta ba zata fada maka ba abinda ke damun ta ba, dan tin tafiyar Aliyu take jin ta wani iri, a haka sukai exam wanda ita kanta tasan ba zata samu abinda ta saba samu ba dan ba karamin damuwa take ciki ba bata iya zama babu tunani da haka suka gama jarabawa suka samu hutu.

Kana ganin Maryam zakaga ta kara ramewa saboda rashin nutsuwa, wannan yasa Ummi tace taje gidan Sitti ko ta samu sauki, ai kuwa zuwan ta gidan ya dan rage mata damuwa dan Sitti na mata nasiha da bata nishadi haka nan da Najwa ta ganta a damuwa zata sa su fita zaga gari sune wannan park din sune wancan wani lokacin Abdul da Muhammad ne suke kai su. Matsalar ta daya tin da tazo gidan Sitti basuyi waya da Aliyu ba wani lokacin tana zaune suke waya da Sitti sai sun gama zata hau tambayar ya yake? Sitti ta kanyi murnushi tace
"Kira ki tambaye."

Sai dai tai murmushi kawai, satin ta biyu ta koma gida suka fara shirin komawa makaranta, wanda a lokacin bikin Najwa saura wata daya, satin su biyu da komawa suka fara rabon katin bikin Nawa duk bata da lokaci dan wani lokacin daga makaranta suke wucewa ga shirye shirye da suka faman yi.


Najwa taso Maryan ta dawo gidan Sitti har ayi biki amman tace sai an fara zata taho wannan yasa ta ma daina kiran ta da yake sun gama rabo, ko an kawo musu dinki bata kira ta fada mata balle ta nuna mata, ita kuma Maryam har da rashin kiran Aliyu da bata so tayi kewa dan ko banza in tana gida zai kira kuma zasu gaisa ko da kuwa Haidar zai wa magana, kuma in ya kira Ummi bai samu ba zai kira ya aike ta, to ita ta rasa meyasa take so taji ya kiratan, dan in suka kwana biyu basuyi wayar ba tai ta damuwa kenan, gashi in ta zauna tai ta tunanin sa, tana zaton ko dan yadda yake taimaka mata ne dan duk da baya gari duk wata da kudin, zuwa makaranta da na shopping dinta ita da Haidar har extra yake dada nata to ita kuwa me zatace da Aliyu in ba godiya ba, wannan yasa kullum bata da aiki sai tunani wani lokacin bata sanin ta fara tunanin sai an kirata bata amsa ba.

Jawahir tai fadan har ta gaji dan wani lokacin ma ko lecture suke haka take zubawa allo ido tai ta tunanin da bata san tushen sa ba. Shiyasa yanzu take a kare ko da yaushe Ummi tayi fadan tayi nasihar amman duk a banza sai abinda ya dadu in kana son kaga farin cikin ta to taga kiran Aliyu har zumudin dauka take yi.

Ranar da zasuje lalle tana zaune a daki tayi nisa cikin tunanin da take Najwa ta shigo, tsayawa tayi a bakin kofa tana kallon ta, tafi minti biyar amman bata sani karasowa tayi ta zauna a gefen ta sannan ta dago tana fadin
"Yaushe kika shigo?"

"Kina can tunani tayaya zaki sani."
Tai murmushi sallamar Jawahir suka jiyo suka amsa ta shigo, Najwa tace
"Akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar min."

Jawahir tace
"Abinda nake fada kenan kullum ban taba boye mata komai ba amman ita ta fiya zurfin ciki."

Shiru tayi tana tunanin me za tace masu can dai tace
"Najwa da Jawahir ba haka bane."
Murmushi Najwa tayi tace
"Kin fada soyayya to saboda me kike tunani ko ba wanda kike so bane ya kawo kansa."

Kallon ta Maryam tayi,
"Yanayin ki na nuna wani kike so kin kasa fada rashin shi ke saki a damuwa. Haka ne?"
Jawahir ta fada, gaban Maryam ne ya fadi shin da gaske ne halin da take ciki to wa take so din. Dafata Najwa tayi tace
"Menene ki fada mana."
Hawaye suka soma zubawa a idon Maryam dan ta rasa madafa.



*Allah ya jikan musulmai Allah kyautata namu zuwa yasa muyu kyakyawan karshe Amin.*



*Antty*
[11/26, 18:57] Maryam S IndabawaπŸ₯°: πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 58

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Wayar ta ce tai kara da kamar bazata dauka ba sai kuma ta janyo ta ganin sunan dake kan wayar yasa tai saurin goge idon ta tare da danna received ta kai kunnen ta
"Assalamu alaikum."

Taji yai sallama ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya ta, dan a duk lokacin da zataji muryar Aliyu ita kadai tasan me take ji, a hankali ta amsa da
"Wa'alaikum ssalam."
Ido ta runtse tai shiru, shima shiru yayi sai can yace
"Me ya samu muryar ki?"

Shiru tayi yace
"Kuka kikai ko?"
Kai ta girgiza kamar yana ganin ta. Yace
"Karya kike kinyi kuka."

Mikewa tai ta fita yace
"Ummi fa?"
"Tana gidan Sitti."

"Ke fa?"
"Ina gida."

"Ke da wa?"
"Ni da Najwa zamuje lalle ne."

"Haidar fa?"
"Yana wajen Inna."

"To sai anjima."
Sukai sallama ya kashe wayar dakin, Ummi ta shiga ta wanke fuskar ta sannan ta fito ta koma daki.

Jawahir da Najwa suna hira ta shiga tace
"Muje ko?"
Suka mike suka fita. Daga lalle saloon suka wuce sai dare suka koma gida.

Da sukaje gidan Sitti ba masaka tsinke saboda yan uwa da abokan arziki, yan garin su duk sun zo duk da washe gari za a fara biki, Maryam dai na daki duk ta takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane. Suna zaune sukaji an shigo da sallama, dagowa sukai suna amsawa wata kyakyawar yarinya ce ta shigo sanye da wata doguwar riga maroon kala sai dan mayafi da ta yafa hannun ta rike da waya da jakar ta, Najwa ce ta mike a guje tana fadin
"Tasleem oyoyo."

Dagowa Maryam tayi tana kallon ta, Tasleem ta huging Najwa tana fadin
"Amarya ta sha kamshi."
Sai ta kalli yan dakin, hannu ta daga musu tace
"Sannun ku."

Maryam tace
"Yauwah sis ya hanya?"
A share ta amsa da
"Ahamdulillah."

Jawahir ta mike tace
"Ni tafiya zanyi."
"Waye zai kai ki gidan?"

"Yaa Muhammad."
"Nima gida zan tafi."

Najwa ta juyo tace
'Saboda me?"
"Gidan ya cika ni gwara na koma wajen Ummi kema kizo mu tafi."

"Amman nan yafi in na tafi can ma sai na dawo nan."
"Shikenan gobe nazo."
Ta mike tace
"Jawahir muje ku ajiye ni."

Babu yanda Najwa bata yi da ita kan ta zauna amma taki, lokacin da taje wajen Sitti sallama ta zauna Sitti ta kalle ta taga yadda take yamutsa fuska, Sitti tace "Ko dai za ki wuce gida ne?"

Kai ta gyada Sitti tace
"To waye zai kai ki?"
Kai tayi kasa dashi tace
"Muhammad ne zai kai Jawahir gida sai ya ajiye ni."

Sitti tace
"To tashi ki je, sai da safe."

Tunda Maryam ta fito Muhammad ke kallonta, ta sunkuyar da kai tace
"Ina yini"
yace
"Lafiya lau."

Jawahir ta shiga gaba ita kuma ta bude baya ta shiga ta zauna tare da jinginar da kanta tana sauke numfashi a hankali, lokaci lokaci Muhammad ke satar kallonta sai ya sakar mata lallausan murmushi, ita dai sai dai ta sauke idonta, dai dai gate din gidansu yayi parking, a hankali ta kallesa tace "Nagode"

Ta kalli Jawahir tace
"Thanks Sis sai goben."
"Allah kaimu."

"Amin."
Ta juya ta shiga gida, tana shiga taji sako ya shigo wayar ta bata duba ba ta shiga gani tayi har Ummi ta rufe kofa knocking tayi, Ummi ta sauko tana tambayar waye. Tace
"Ummi nice."

Budewa tayi tabi Maryam da kallo tace
"Daga ina?"
"Ummi ba zan iya kwana ba."

Hanya Ummi ta bata tace
"Allah ya shirya ki duk fa yan uwan ki ne."
"Ummi ni ba haka bane yasa na kasa ba, kawai gida nake so."

"To ai shikenan."
Ta wuce sama, wanka tayi ta fito ta kwanta wayar ta taji tai kara ta dauka ta kai kunne yace
"Dear kinga yadda kikai kyau kamar kece amaryar."

"Kai ina wani kyau."
"Hmmm wallahi baki gani ba, gaskiya ina jin ba zan iya jimawa ba tare dake ba, ina son ki Baby, ina son kasancewa dake, please Baby ki so ni ko daya bisa darin da nake son ki ne."

"Kana son kana dawo da abu baya, kullum ina fada maka ina son ka ina sonka."
"Na sani amman bai kai kwatan nawa ba yadda nake jin ki ko?"

"Meyasa kake boyewa Jawahir?"
"Saboda ina son nai mata surprise nan gaba kadan lokacin da za a zo tambayar aure a lokacin zata san wacece matata nasan zataji dadi sosai."

"Uhmmm."
"Eh ko ya kika ce."

"Yayi."
"Bari na barki kiyi bacci, saboda gobe nasan kila da wuri zaki tashi, zakuyi kamu ko?"

"Eh."
"Allah kaimu."

"Amin."
Sukai sallama ta kwanta. Da wuri kuwa ta tashi.

Washe gari kamu, da safe yan UK suka sauka, su Momy, da ya'yan ta Yasmeen da Basma, Yayar Ummi ce, dan haka a gidan Ummi suka sauka dan gidan Sitti a cike yake da mutane, duk da Maryam da Basma basu taba haduwa ba amman Basma na ganin ta ta rumgume Maryam tana fadin
"Sister."

Sama suka nufa, a daki suka zauna suna hira tamkar wanda suka taba ganin juna wanda iyakar su waya ne ko vedio call, a gida suka yini dan sai yamma mai make up tazo har gida Basma tayiwa, Maryam da farko cewa tayi ba zatayi ba sai da Momy ta sa baki sannan tace ai mata light make up. Ta saka wani jan material, dinka riga da siket duk yanda mutum ya kai ga hassada ba zai kushe Maryam ba a wannan rana takalmi da jaka bakake tayi amfani dasu, fitowa sukai dan su Ummi duk sun riga da sun tafi.

Waya Maryam tayiwa Jawahir take fada mata an kwashe kowa suma yanzu suna hanya, compound suka fita dan ta kira driver ya kai su, suna fitowa gaban ta yai wata mummunar faduwa saboda hango Aliyu da tayi a compound din gida, Basma dake waya ta karaso tana fadin
"Waye zai kai mu?"

Kasa magana Maryam tayi, dan kallon Aliyu dake sanye da wando jeans baki da riga fara ta kama jikinshi yai kyau annuri ne ke fita a fuskarshi yana da kyau na karshe fatar shi ta kara zama smooth giran tashi kuwa kamar wacce aka dasa, ji tayi kamar ta juya sai kuma ta dake tunda bai ganta ba. Wata mota ce ta shigo compound din Basma tayi gaba, Aliyu taiwa magana sannan ta karasa wajen motar da ta shigo ta tsaya, gaba Maryam tayi zata wuce.

Wanda ya ke driving ne ya fito yana kallon Najwa, kofar da take ta mai zaman banza ma aka bude wani kyakyawan saurayi ne ya fito, gaisawa sukai da Basma, har Maryam zata shige Basma tace
"Sister meet Fauwaz."
Juyowa tayi ta dan kalle su, tace
"Sannun ku da zuwa."

Suka fara gaisawa dayan da yake abokin Fauwaz ya zuba mata ido, kai ta dauke ta kalli Aliyu wanda yayi wani kicin kicin da fuska kamar ba zata gaishe shi ba sai ta daure tace
"Ina yini?"

"Lafiya."
Ya amsa a ciki tare da mikawa Fauwaz hannu yana fadin
"Ashe kana gida."
Ya mikawa dayan hannu fuska a hade suka gaisa,

Gefe Maryam tayi, Aliyu ya nufi motar sa yana shiga ya fara dailing number wayar, wayar Maryam ce ta hau kara, kallon wayar tayi, ganin Aliyu yana kiran ta yasa ta dago tana kallon sa, kai ya dauke kamar bashi ke kiran ta ba, a hankali ta fara tafiya har ta karasa, batai magana ba yace
"Zagayo ki shigo."
Ba musu ta zagaya ta bude motar ta shiga,
"Kira Basma mu tafi."
Ya fada ba tare da ya kalle ta ba.

Waya ta dauka ta kira wayar Basma, karasowa tai Aliyu yace
"Shigo mu tafi."
Fuska ta shagwabe tace
"Please Yaya ka barni na tafi dasu kaga danni suka zo."

"Ku biyo motata."
Tace "Ok."

Ya tada mota ya fita, sukabi bayansu har hall din da ake bikin yai parking zata fita ya saka lock, juyowa tayi ta kalle sa, kai dauke yace
"Naga kamar kanki yana rawa ki kula, nasan Muhammad ya zo ko? Abokin Abdul ne bana so kinji ko?"

Kai ta dauke ba tare da tai magana ba, hannun ta ya kamo ta juyo da sauri dan wannan ne karo na farko da Aliyu ya taba ta ba cikin wani lalura ko taimako ba, wanda daga ita har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login