Showing 156001 words to 159000 words out of 193749 words

Chapter 53 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4417

Deeyah*, za ki ??an bamu waje, zan gana da iyayena."

Rusunawa tayi ta mi)?e ka??an cikin tattausan murya tace" Fatan lafiya mai ??orewa *uban gidana*."

?an kallon mamanshi tayi ta mata murmushi sannan ta mi)?e gaba??aya ta fita ta )?ofar da zata sadata da ?angarenta. Saida dogarin dake bakin )?ofar ya rufo musu )?ofar bayan ya ma Saleema sannu da fitowa sannan ya sake kallon gimbiya Kubra da ta bi Saleema da kallon jin haushi da tunanin me yasa zai ce ta tafi? Bayan ita ta tsayar da ita? Ai ta so ne ya yi magana a gabanta dan ta gane irin matsayinsu a gunshi.

Muryarshi na fitar da sautin ladabinshi garesu kuma a tausashe yace "Maamaa, wannan ra'ayin *mai ??akina*, ina ga kamar ba matsala a hakan, dan ina jin da??in girkin nata, game da..."

Saida ya ja numfashi ya sauke kafin yace "?wan uwana kuma, duk ranar juma'a za mu karya tare, dan ranar ba na fita sai lokacin masallaci ya yi."

Maida kallonshi yayi ga mahaifiyarshi da ita dai ba ta ce komai sai murmushin da take dokawa a yanzun saboda hukuncin nan ya mata daidai sannan ya kallesu dukansu yace "Iyayena zan fita, a min addu'a."

Mahaifiyarshi da gimbiya Zulaihat ne suka rufeshi da addu'ar amma gimbiya Kubra a )?asan ma)?oshi tace "Allah ya tsare."

Da haka ya mi)?e ya fita yana mai fatan Allah ya bashi ikon ??aukar wannan nauyi dake kanshi, dan baya jin zai iya idan zai zamana daga cikin gida ma ana kawo masa maganganun da basu kai basu kawo ba, sa'arsa ??aya da Allah ya bashi matar da take gefenshi a kowane lokaci, a sati biyun nan da suka ??auka wata sha)?uwa ce ta sake shiga tsakaninsu, gaba??aya jin ta yake har )?asan zuciyarshi, ta ko ina baibayeshi take da farin ciki, sai dai har yanzu bakinshi nauyi yake wajen furta mata kalmar so, duk dai yana fata ita ta fa??a amma abun mamaki yarinyar ba ta rawa da kanta game da shi, hasalima ko tambayarta yayi tana sonsa sai ta bar wurin idan waya ce kuma ta kashe.



*Ranar Juma'a*



Irin kwalliyar da ta fito da ita cikin wata irin shiga ta rashin ??a'a yasa mahaifiyar ta ta sakin baki ta nunata da hannu tace "Sharha, ke kuma ina zaki je yanzu da rana tsaka? Rana yau babu aiki."

Dakatawa tayi tana )?ara duban kanta a ecran ??in wayarta tace "E Mama, amma kin manta ranar mata ce yau? Akwai wasan da za'a yi ne a mess (gidan rawa)."

A zabure ta zuba idanu tace "Yanzu kenan can ??in ne za ki je?"

"E." Ta fa??a tana shirin ficewa, cikin ??aga murya mamanta tace "Sharha karki fita a gidan nan, kinga kullum rigima muke da mahaifinki wai na hanaki aure ko, ki dawo gida wannan ba wajen zuwanki bane."

Juyowa tayi ta yatsina fuska tace "To wai mama me ye a mess ??in? Yau fa duk )?awayena da sauran manyan mata za su ha??u ne, sai kuma ni na kasa zuwa."

A hassale tace "Saboda bai dace da ke ba, kar fa ki manta ba budurwa ce ke ba, aurenki na fari ya dace ya zama silar )?ara hankalinki, kina dai gani ??anki ma neman rasashi kike, kuma kullum abinda Huzeifa ke fa??a shine baya so kina kusanta kanki da ??an nan saboda bai yarda da tarbiyarki ba, kenan kin fi so a dinga ganin laifina?"

A wani zabure tamkar za ta cijeta tace" Haba Mama bari wannan maganar, Huzeifa kuma wallahi nan kusa ka??an zai dawo hannuna ko ya )?i ko ya so, Sudeis kuma ba mai rabani da shi ai tunda ni na haifi abuna."

Tana gama fa??a ta fice a gidan da sauri dan kar ma ta sake jin wani abu daga mahaifiyar ta ta, da kallo ta bita tana girgiza kai cike da takaici tace" Allah ya shiryeki, Allah fito miki da wani mijin, amma Huzeifa kam ba zai ta?a maidaki ba har abada, na farko ma da yayi biyayya ya wa mahaifiyarsa da muka je mata da tayin aurenki, na tabbata ba zai wannan kuskuren ba tunda yana da hankali."


_______________



?an )?wan)?wasa )?ofar tayi ta ??an ??aga murya tace "Yalla?ai towel ??in."

Bu??o )?ofar yayi ya zuro hannu zai kar?a sai kawai ya ja tare da hannunta hakan yasa ta fa??a ban??akin ba tare da ta shirya ba, zazzaro idanu tayi sai kuma ta li)?esu gam tace "Wayyoooo Allahna! Na shiga uku."

Towel ??in da har yanzu ke hannunta bai kar?a ba ta rufe fuskarta da shi, hannu yasa ya fizge towel ??in ya jefashi kan bahon wanka tare da mata ra??a a kunne cewa "Yanzu *Ade* ni ne ke da shiga ukun dan an ganni haka?"

Da a sauri ta girgiza kai tare da )?arga rintse iddanunta tace "Haba yalla?ai, wai kai baka jin kun..."

Tsaretan da yayi da idanu yasa ta yin shiru ta sadda kanta, tallabo ha?arta yayi yace "Bu??a idonki mana ki Kalleni."

Girgiza kai tayi tace "Um um, gaskiya ba zan iya ba."

"Me yasa?" Ya fa??a yana murmushi, )?ara sinne kanta tayi tace "Kawai dai, ka fara ??aura towel ??in sannan."

Rumgumota yayi jikinshi tare da )?o)?arin cire mata yaloluwar rigar dake jikinta wacce tun safe ta so cireta ya ce sam bai yarda yana son kallonta a haka, )?asa yayi da hannayen rigar take ta zube kuma dama babu komai a jikinta sai rigar kalar ja yadin nata mai rawa, da sauri ta bu??a idanunta ta kalleshi a cikin )?wayar idanunshi tace "Abdul, na yi wanka fa."

Sake ri)?ota yayi sosai yace "Um! Wankan juma'a zamuyi."

Hannu yasa kan ribom ??in dake kanta ya cire shima yayi fatali da shi, zura hannunshi yayi ya sake kunna ruwan suka shiga sauka a kansu, idanunshi ta sake kallo kamar yadda shima yake kallonta yace "Gimbiyar dake kallon sarkinta babu k..."

Da sauri tasa tafin hannunta na dama ta rufe masa baki tana murmushi tace "Shiiii! Ba dan ba dan ba da na ce..."

?war harara ya aika mata yace "Da kin ce fitsararren sarki ko."

Waro idanu tayi ta )?yal)?yale da dariya tace "Ya akayi kasan abinda na so fa??a kenan?"

Sai kuma ta ??ora hannunta akan )?irjinshi da ruwa ke sauka tana shafawa tace "Yalla?aina."

A )?asan ma)?oshi ya amsa da "Ummm!" Amma kuma hannunshi na dama na shafar damtsenta har zuwa nonuwanta, cikin ra??a tace "Lokacin masallaci fa zai yi."

A nutse ya juyata ya zamana bayanta yake kallo tare da ??ora ha?arshi akan kafa??arta ya saka duka hannayenshi akan mararta ya dafe tare da rufe idanunshi yace " *Halee*, yaushe za ki mana ajiya ne?"

Da rashin fahimtar tambayarshi tace" Wace irin ajiya kuma?"

&?ara matsa mararta yayi yace" A nan mana." Murmushi tayi tace" To ajiya ba kullum ina yi ba? Sau uku fa zuwa ha??u nake cin abinci a rana."

Bu??a idanunshi yayi yace" Haleema, wai me yasa kika fiya wauta ne?"

Turo baki tayi tace" Wata)?ila dan na kasance ?bar fari gaba da baya."

Dungure mata kai yayi yana ci gaba da shafa mararta yace" Kamar ni kenan, ai ba sai kin gaya min magana ba."

?war dariya tayi tace" Ni dai ban ce ba." Kama kafa??unta yaui ya juyo da ita tana sake fuskantarshi ya tsurawa fuskarta idanu, ita ma kan fuskarshi take kallo dan har yanzu ba ta yi kasadan kallon )?asan nan ba dan ba zata iya ba, ba alamar wasa a tare da shi yace" Da gaske fa nake, yaushe za ki min albishirin kina da juna biyu ne?"

Waro idanu tayi ta dafa marar ta ta tace" Ni kuma? Ciki? Um um!"

Ta fa??a tana ma)?ale kafa??a, tsura mata idanu ya sake yi yace" Me yasa? Saboda ba kya sona?"

Rarraba idanu ta fara yi tana kakkawar da kai, a dake ya juyo da ha?arta ya sake tilasta mata kallon fuskarshi da ya ??an ha??eta yace" Uhum! Ba kya son haihuwa dani ne?"

Da sauri ya girgiza masa kai sai kuma ta ??auke kanta dake kan hannunshi ya tallabe mata ha?a ta ??an kawar da kanta tace" Abdul ka gane mana...ni fa."

Zuba mata idanu yayi yana ci gaba da kallonta, jayewa tayi ka??an sannan ta juyo ta kalleshi tace" Abdul ba zan )?i kar?an ajiyarka komai nauyinta, anya kuwa ka san irin tanadin da nake mana? Kullum fa cikin tsara mana rayuwarmu nake musamman ma wacce za ta zo mana nan gaba, ranka shi da??e indai naka ne zan iya..." Hannu ta sake ??orawa a mararta tace" Zan iya da izinin Allah, tunda har na yarda na fara rayuwar aure da kai, ??aukan cikinka da haifeshi ba zai gagara ba in sha Allah..."

Sai kuma ta saki murmushi tana rausaya kanta tace" Kai dai kawai ka ta yi mun addu'a Allah ya rabamu da ma)?iyanmu sannan ya kawo masu albarka."

Jawota yayi jikinshi yana murmushi yace" To ki ce kina sona mana."

A hankali ta girgiza kai tace" Um um! Kai dai kayi ta addu'a ka yi nasarar sace zuciyar gimbiyarka kawai."

Yadda tayi maganar da yanayin kuri yasa shi murmusawa yace" Kenan har yanzu ban samu ba?"

Jinjina kai tayi alamar e, tallabo ha?arta yayi ya daidaici bakinta ya ??ora nashi a hankali ya shiga fara tsotsar bakin na ta.

*Dake* juma'ar da ta gaba sarki da kansa ne yayi hu??uba, hakan ya jawo cikar masallacin dake gaban gidan sarkin yau, duk girman masallacin nan masha Allah ya cika da ??an mutum har filin dake zagaye da shi wanda wasu lokuta da yamma samari ke cikawa suna ball. Kuma anyi sa'a yau ma tunda ya fita ta )?ofar dake cikin gida ya shiga masallacin tun bai fara hu??ubar ba labari ya kawowa mutanen waje yau ma shi ne da kansa, hakan yasa wurin ya ??auki shiru duba da za'a fara fiyayyen zance (Na Allah da Manzonsa).

Tunda ya fara hu??ubar da harshen larabci yana magana kan dan)?on zumunci masallaci ke amsawa saboda lafiyar amsakuwar, sai dai kuma a tausashe sosai yake maganar a yanayin dake lula lallai jinin sarauta ne, har saida ya dakata na wasu sakanni tare da zama kamar yadda sunna ta koyar kafin ya mi)?e ya fara da harshen hausa, cike da gamsuwa da kalamanshi da kuma jinjina hikimarshi ta wa'azantarwa kowa ke sauraro kuma suna ??aukar abinda yake tunatar da su ??in. Saida ya zo rufewa yana addu'a ne kowa ya gane lallai shi ??in sarki ne ba irin sauran ba, sarki ne da ya san akwai na gaba da shi, domin kuwa addu'a yake daga zuciyarsa muryarsa na rawan dake nuna kowane lokaci zai iya fashewa da kuka gaban mahaliccinsa sarkin sarakuna, kafin daga bisani a )?ar)?are aka tayar da sallah.

*A minti ashirin* aka gama sallah bayan ya juyo wa??anda ke bayanshi suna ??an gaisheshi, ido hu??un da yayi da malaminsa dattijon arzi)?i yana zaune ya jingina a bango da alama ba yanzu zai fita a masallacin ba yasa shi mi)?ewa a nutse, da sauri dogarai suka mi)?e suka rufa masa baya suna baza manyan rigunansu, wani kallo ya aiko musu daya nuna baya bu)?atar rakiyarsu, hakan yasa suka zube )?asa dan cikin masallaci suke ba filin fada ba.

&?arasawa yayi gabanshi tare da neman guri ya zauna sukayi musabiha, sosai suka gaisa da dattijon mai dattako yana tambayarsa al'umaran rayuwa, ta)?aiciyar nasiha ya masa da "Ka ji tsoron Allah, ka tuna akwai )?iyama, wuta gaskiya ce haka ma aljanna gaskiya ce, Allah ya tayaka ri)?o da hannayenka, Allah ya ??oraka akan ma)?iyanka."

"Ameen, nagode sosai." Ya fa??a yana sadda kanshi )?asa kafin ya fara tattara alkyabbarsa zai tashi, a nutse ya mi)?e gaba??ayansa ya shiga takawa a lokacin da mutane ke ta fita a masallacin. Kafin ya isa ga dogarai dake jiranshi wani )?a)?)?arfan matashin da zai wuce shekara talatin da biyar ya tunkaro tamkar za su yi sa?ani, sai dai suna daf da juna kuma babu wanda ya hanashi tunkararshi dan ??akin Allah suke kuma mutane na ta fita ne ta )?ofofi ukun dake cikin masallacin bayan ta shigowar sarki.

&?aramar wu)?ar da suka ha??ata da mummunar gubar da tana ta?a mutum sai dai idan Allah ya tsare kawai ya zaro daga aljihun rigar yadinshi ya cireta a cikin gidanta ya nufi soka masa ita a ciki duk da an bashi tabbaci ko ya yane ya tabbatar dai ta yanki jikinshi, da zarar gubar ta shiga jininshi to an gama. Tuni Abdus-samad ya ankara da wannan balagaggen namiji, da salo irin kwarewa ya yi saurin ra?e jikinshi hakan yasa hannun mutumin wucewa a banza ya soki iska, kafin ya ankara da ina ya soka wu)?ar Abdus-samad ya ri)?i wuyan hannunshi da mugun )?arfin da ya saka shi sakin wu)?ar lokaci ??aya ya nemi dur)?ushewa har ya saki wani gunjin )?ara yace "Ahhj! Hannuna..."


Da gudu dogarai sukayo kansu ??aya dogarin dake bakin )?ofa tsaye ya rigasu fita da gudu shima ya shigo yana zaro labceciyar wu)?arshi daga gidanta yana fa??in "...





*Alhamdulillah.*
26/06/2022 ?? 22:54 - MOM LATEEF???i: ???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??
*BAIWATA*
???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ??A惙@?
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
=??? *[G. M. N. A]* =??? ??Id???g???


_Bismillahir rahamanir rahim_


_51_




Da gudu shima ya shigo yana zaro labceciyar wu)?arshi daga gidanta yana fa??in "Kai )?aramin mugu, hattara dai maza bisa kanka."

Da sauri Abdus-samad ya ??aga masa hannu alamar ya dakata tare da )?urawa mutumin idanu wanda tuni dogaran nan suka mishi wata matsa da hannayenshi suka mur??e sosai sun hanashi damar ko da numfasawa yadda yake so, sauran mutanen da basu gama fita bane suka dawo suna kallon ikon Allah ana ta salallami, dogarai hu??u ne suka zagaye gabanshida bayanshi da kuma gefenshi dama da hauni ??aya daga ciki na fa??in "Ranka shi da??e muje ciki, a barmu da shi zai gane kurensa."

Takawa Abdus-samad ya fara yi sai kuma ya sake kallon mutumin, girgiza kai yayi a ranshi yana mamakin yadda ma mutane zasuyi wannan rashin hankalin, to an fa??a musu haka kawai mutum ke haye kujerar ya shiga baccin asara? Ko kuma an fa??a musu suma kamar su ??in malamai da bokaye suke bibiya ne? Lallai idan haka suke tunani sun yi kuskure, dan kuwa yau zai nuna musu banbancinshi da su na nesa ne ba kusa ba, yau za'a yi ta ta )?are a gidan nan ya nunawa kow ya fa san zaman da yake da mutune, ai ba mahaukaci bane shi da zai rasa gane mai kamalta sonsa dan Allah, kamar yadda shi ba makaho bane yana gane dariyar da ta fito daga zuciya ??aya da kuma wacce ta fito dan a nuna masa kawai an yi.

Zai iya cewa ya jima bai yi saurin da yayi a yanzun ba da yake hanyar shigewa fadarsa tun da aka na??a masa rawanin nan idan ka cire gudu da yake yi a filin dawakin da ke bayan gidan shi ma ba kullum ba, tunda suka shiga fadar ta hargitse ana ta surutai )?asa )?asa kowa na fa??in albarkacin bakinshi. Daga waje kuma mutane ne ke ta cika aikinsu ta hanyar bayar da ba'asin abinda ya faru, wasu sun gani kuma suna fa??a yadda ya kasance, yayin da wasu ji ne sukayi daga sama su ma suke )?arawa a kan nasu, dan kuwa wasu har sun fara fa??in sarkin nan ashe ??an bala'i ne kuma ??an tauri, an soke shi da wu)?a amma bai ji ba kamar a jikin )?arfi aka soka.

Bai zauna kan kujerar ba yana tsaye su kuma dogarai da sauran mutanen fada kawunansu na )?asa dan ba zasu mi)?e tsaye ba idan ba tafiya ne zai yi ba sai dogari ??aya kawai dake bayanshi da bulala a hannu.

Kitir! Kitir da )?arfi dogaran suka shigo da mutumin nan dake ta son ya )?waci kanshi ya tsare sai jajaye ido yake yana fa??in "Ku sakeni."

Basu kula da tsiyarsa ba saida suka dur)?usar da shi da wata gandareriyar bulala a gabanshi ta hanyar labta masa ita a bayanshi sai da ya zabura, ja baya yayi kas??an yana kallon mutumin da shi ma a lokacin ya ??aga kai ya kalleshi, duk da fuskar Abdus-samad a rufe take amma sai ya ji kwarjini da haibarsa sun cika masa idanu, da sauri ya sadda kai yana ha??e hannaye alamar ro)?o yace "Ranka shi da??e kai min rai, ka min afuwa na tuba ba zan )?ara ba, ka yafe min ranka shi da??e."

Da wani kakkausan kallo ya dubeshi zuciyarshi na tunzurashi kan ya wanka masa marin da ba shi ba sake ji na har abada, amma kuma yana tausar kanshi kar yayi abinda bai dace ba tun yanzu a fara kiransa da marar adalci.

?aga kanshi yayi sama cike da bada umarni yace "Ku bamu waje dukanku."

Duk rusunawa suka sake yi sai dogari ??aya da yace "Allah taimaki sarkina, sarki mai adalci da ha)?uri, anya kuwa zamu iya barinku kai da shi?"

Da yanayin fara hassala yace "Ku tafi na ce."

Jikinshi ne ya )?ara ??aukan rawa yana ja baya daga zaunen da yake yace "Allah taimaki sarki mai adalci, sarki mai ha)?uri da yafiya, kai min rai ranka shi da??e na tuba, Allah ya huci zuciyarka."

Duk ficewa sukayi har da ??angaladima daya fita a )?arshe yana waiwayen mutumin da fatan Allah ya rufa masa asiri, saida suka fice gaba??ayansu suka rufo )?ofar sannan ya dubi mutumin da kanshi ke )?asa sai zufa ke ta tsatsafo masa tamkar zaiyi kwance a zaman tsabar rusuna kai.

Sandar dake hannunshi wacce aka ma kwalliya da jan abu tamkar na alkyabbar dake da ratsin ja amma fara ce tas tamkar dakakkiyar shaddarsa, ajeta yayi kan kujerarshi ta zama, a nutse ya fara warware rawanin daya ma mutumin nan shamaki da ganin fuskarshi, saida ya cireshi gaba??aya shi ma ya aje tare da hular, a nutse ya tattaro babbar rigarshi ita ma ya cireta ta sama ya aje gefe, a hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login