Showing 81001 words to 84000 words out of 193749 words

Chapter 28 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4418

fizge ta kalleshi tace "Ka daina ta?ani."

Marairaicewa yayi yace "Soffee, dan Allah kada ki bari damuwa ta samu muhalli a gangar jikinki ma bare ruhinki, kin fi kowa sanin illar da hakan zai haifar mana."

A gatsalce ta kalleshi tace "Me wai? Cikin jikina? Kai ma ai kasan ba mai zama bane, kamar yadda ba)?in cikinka na baya ya yi sanadiyar zubewarshi, yanzu ma haka ce za ta faru, da haka na gane ba sona kake ba, rayuwata kake nema *Isuhu*."

Kecewa ya yi da dariya ya ??an ja baya ya nuna kanshi yace" Isuhu? Ni?"

Ba alamar wasa tace" E ??in, ko )?arya na yi ba sunanka bane, na fa??a Isuhu."

Gumtse bakinshi yayi yana dariya yace" Shikenan na ji, yanzu dai dan Allah kiyi ha)?uri, ke ma kinsan abinda ta yi bata kyauta ba, ni fa ubanta ne, ta ya za ta kai )?arata ga wani? Kenan ni ban isa na yanke hukunci a kanta ba?"

Fashewa tayi da kuka ta ja baya har saida ta zauna bakin gadon tace" Shine sai ta wannan dukan za ka nuna mata kuskurenta, wallahi ban yarda ba, haka kawai za ka dinga narkar min yarinya kamar wata jaka."

Dur)?usawa yayi gabanta yace" Shikenan na ji, daina kukan to, fa??a min ya kike so na yi? Na miki al)?awarin zan yi amma bana son damuwarki."

Kallonshi tayi tace" Ka amince ta koyo abinda ranta yake so."

Ha??e fuska yayi tare da kawar da kai yace" Ban da shi, ki nemi wata alfarmar."

Ha??e kukanta tayi tace" Shikenan, amma ka manta da nima matarka ce."

?an )?aramin tsaki yayi ya kawar da kai yace" Soffee, bana so fa, ki daina irin haka kamar wata yarinya, ta ya zatayi laifi na hukuntata kuma ki dinga hushi dani? Dan kinga ina damuwa ne da damuwarki?"

Mi)?ewa yayi tsaye ya karka??e rigarshi yace" Ki ci abinci a kan lokaci, kada ki ci ??an??ano dayawa, sannan ki sha magungunanki a kan lokaci, ki samu isashen bacci, dan Allah ki min wannan alfarmar ko dan abinda ke cikinki."

Har zai tafi sai kuma ya tsaya cak, ba tare da ya juyo ba yace" Kada ki sake ki harareni idan na juya."

&?eyarsa ta kalla dan magana ta gaskiya har tayi haramar hararen tashi, amma jin haka sai ta kasa binshi da hararar, saida ya fice ta daki gadon da hannu tace da fa??in" Ba zan yi ??in ba, ba zanyi ko ??aya da ka fa??a ba."




*08:20 na dare*



Kiranta yayi ya ce su ha??u a gidan cin aminci na *Kebab*, ba gardama ta ce masa za ta zo yanzu, duk da ta san dare ne kuma mahaifinta na gidan, amma a ganinta da ta ce masa za ta je kar?an wasu takardu an wuce wurin, addu'a zai mata har da guzurin ku??in adaidaita. A gaggauce ta shiga shiryawa, Ardiya dake zaune da na'ura gabanya ana ta faman lissafi ta kalleta tace "Wai ina za ki je na ga kina ta shiri? Ko ba)?o kikayi a waje?"

Turaren da take murzawa a hannayenta ta shafa a wuyanta sannan ta juyo ta kalleta tace "A'a, fita zanyi."

"Ina?" Ta fa??a tana )?ura mata idanu, saida ta ??auki wayarta a hannu da jaka ta rataya tace "Mama Yaya Mu'az ne ya zo na zo mu ha??u yanzu."

A hassale Ardiya tace "Ke saurara bana son iskanci, wai me ye tsakaninki da shi? Ke baki da zuciya ne? Ba ki ga kayan Yayarki ya kawo jiya ba?"

Sassauta murya Hadeeya tayi sosai ta zauna kusa da ita tana daddana wayarta tace "Momma kinga, wani abu nake shiryawa, ban san ko zaiyi aiki ba, amma dai na tabbata zai kawo tsaiko a auren nan."

Kar?an wayar ta sake yi tana kallon videon Hadeeya kuma na fa??in "Ba na nuna miki ba jiya, to ai shima na tura masa kuma na ce masa zan ??orashi a tik tok, shine ya tsorata ya ce kar na zubar mata da mutumci, nafa??a masa idan bai amince da aurena ba sai kowa ya ga tsiraicinta, shi ne ya ce zai kirani muyi magana."

Zuba mata idanu tayi na wasu da)?i)?u, sai kuma ta washe baki da yanayin jin da??i ta nunata da yatsa tace" Kinga anfanin boko kenan, ?bata mai basira."

Hannu ta bata suka tafa hakan yasa suka fashe da dariya, tsagaitawa Ardiya tayi tace" Kin san me? Ba za ki je ba yanzun, Hadeeya ke yarinya ce, dan a haufe Mu'az ya haifeki dan baiyi aure da wuri bane, na tabbata akwai abinda ya shirya miki, shiyasa ya nemi da ku ha??u."

Da mamaki tace" To Momma ya zanyi kenan? Idan fa amincewa zai yi?"

Girgiza mata kai tayi tace" Ba ma haka bane, zai yi wuya ya amince a sau)?a)?e haka, kinsan me?"

Ta fa??a tana mi)?o mata wayar tace" Tura masa sa)?o cewa ba za ki samu damar zuwa ba, da sauri Hadeeya ta shiga yin abinda ta umarceta da shi, tana turawa tace "Yawxa na tura."

Kar?ar wayar Ardiya tayi ta kasheta gaba??aya sannan ta kalleta tace "Kada ki kunna wayar nan har sai gobe da safe, kuma idan ya kiraki karki ??aga, idan ya turo miki sa)?o ki duba amma karki mayar masa."

Da mamaki Hadeeya tace "Amma Momma me yasa? Idan ya yi zuciya ya shareni fa? Ni fa gaskiya Momma ina sonshi."

Da fara'a tace "To ai auren na shi nake son jawo miki, idan ya ga kina rawar )?afar nan zai ji haushinki, sannan zai ga kin fi shi matsuwa, amma idan kika shareshi bayan ke kike ri)?e da wannan makamin, dole zai ci gaba da nemanki, dan ba zai so ki tona sirrin future iyalinshi ba."

Tintserewa sukayi da dariya suka kuma tafa hannu, jinjina kai Hadeeya tayi tace" Shiyasa nake sonki Momma."

"Nima haka." Ta fa??a tana mi)?a mata wayarta, kar?a tayi ta fita a ??akin zuwa na su dan dama kayan kwalliyar mahaifiyarta yasa ta shigowa ??akin, tana ganin fitarta ta ri)?e ha?a da yatsu biyu ta jinjina kai tace "Mu'az kenan, in kana tunanin yi mata wayo, to ai ni na girmeka, ka ga ba zaka min wayo ba, ka jira ka??an, lokaci zai ha??aka da matarka."

Sai kuma tayi murmushi ta ci gaba da aikinta zuciyarta fari tass tana jin sun gama samun abinda suke so.


*Mu'az* na ganin sa)?onta da sauri ya shiga aika mata kira amma take ake fa??a masa wayar kashe, ranshi da yayi )?ololuwar ?aci jefa wayar yayi kan kujerar mai zaman banza ya taka birki, ri)?e ha?a yayi yana tunanin duk yadda aka yi akwai mai taimakawa yarinyar nan kan lamarin nan, amma yarinya kamar Hadeeya da wuya ta iya haka, shi da ya so su ha??u sai sun ci abinci a hanyarsu ta komawa ya kakkafta mata marin da zai gigita tunaninta sannan ya kar?e wayar gaba??aya, dan dama bar mata wayar da Saleema tayi bai mata ba, dan ta fara masa rigima ne kawai ya rabu da ita, gashi da wayar da ta bata take neman wula)?anta ta, shi kam bai ta?a ganin ?ban ubanta ka irin wannan ba. Gashi a halin da ake ciki yanzu ba zai so yayi garaje, dan yin haka zai iya jawo kowa ya san abinda ya fara shiga tsakaninsu da Hadeeyar, duk da zai iya murje idanu ya nuna shi bai yi da wata manufa ba, amma Saleema ta fi )?arfin ya mata haka, ya na jin kunyarta sannan yana darata yarinyar fiye da kima, baya )?aunar duk wani abu da zai ??aga mata hankali bare ta shiga damuwa, uwa uba a ce ta dalilinshi ne.

Safiyar yau ko da suka tashi da aikin gyaran jikin ?barta ta farka, da fari ta so dam)?a komai hannun ?bar uwarta Lubna, amma dake tana so Alhaji Yusuf ya ga tana ta aiki da jikinta sai ta zage damtse ta fito farfajiyar gidan, wajen hura wutar gawai kanta tasha wahala dan abu ne da baka saba ba, kuma da ta tabbatar yana gidan haka take komai da )?arfi )?arfi wai a dole ya gani ko ya ji haushi, dan ta san ya damu da ??an cikinta sosai. A tsanake ta shiga tu)?a sabulunta da zallar madarar ruwa peak (mai neman )?arin bayanin yadda ake ha??a sabulu na gyaran jiki, na amarya, na mai jego, ki garzaya ki biya ku??in littafin *ni zan ladabi* na Sajida, zaki samu cikakken bayanin yadda zakiyi, abun armashi kuma shine zaki iya yinshi a matsayin sana'a, da ??ari biyar kacal yar uwa ki gyara rayuwarki), tana cikin aikin ya fito zai fita, ya jima tsaye yana kallonta amma ta yi kamar ba ta ganshi ba tana ta aikinta, girgiza kai yayi ya wuce kawai dan ya kula magana take nemanshi da ita.

Tana gama tu)?a sabulunta ta saka mishi kurkum mai haske da ja saboda kalar fatar Saleema sannan ta juyeshi a bokiti ta kai ??aki ta aje inda babu rana, sai da ta gama ha??in )?wan da za ta shafa mata a jiki saboda duhun fatarta tana bu)?atarta ta ga fuskarta na )?yalli da she)?i yasa za ta ata wannan ha??in, tana gama ha??awa ta tasheta a baccin da ta koma bayan sallah asuba, saida ta fara bata sabulun Anakonda wanda shima ta sakashi a cikin ha??in sabulun nan ta ce ta yi wanka, dan zai taimaka sosai wajen cire mata datti da wata tsohuwar fata, bayan ta fito ta tsane jikinta sosai sannan ta zauna kan leda ta fara shafe mata jikinta da farin )?wan (shi ma dai wannan ha??in zaku sameshi a wannan littafi na ni zan ladabi, iya katin waya ma ya isheki ki dogara da kanki yar uwa, kar kuyi sanya).



*Bayan sati biyu*





Shirye shirye matu)?a sun kankama, lokaci na gabatowa sosai inda amarya ke ??aukar gyara, dake tana da fata mai nutsuwa da taushi sannan ga taimakon Glyc?rine, sai hakan yasa duk abinda aka ma fatar yana kar?a a )?an)?anin lokaci, sai ga Saleema dake da ba)?ar fata idan ka kalleta sau ??aya za ka so ka sakata gaba kayi ta kallo, )?yal )?yal take tamkar sabuwar shadda mai mai)?o, haske take da walwali ga sanyayyen )?amshi na dadda??an humrar *Raudha* (ma'ana dausayin aljanna, idan baki samu ta ki ba yar uwa ki nema ki sha )?amshi a farashi mai sau)?i).

Tun lokacin kuma Hadeeya ke ta yawo da hankalin Mu'az, ta )?i yarda su ha??u bare ya nuna mata fin )?arfin da yake da niyyar yi mata, kuma magana ta gaskiya yana jin kunya sosai ta fa??i abinda ya mata, dan haka duk shirin nan da ake hankalinshi a take yake, idan ya kirata sai ta ga dama take ??auka, mamakin irin amsoshin da take bashi yake, shi yasan tabbas da sa hannun wani wanda ya fi ta wayo da sanin ta kan duniya, gashi Saleema tun da aka saka ranar sau ??aya suka ha??u. Dan haka yau ya shirya tafiya amma da biyu, tunanin ganin sahibarsa da kuma ganin Hadeeya ya ga me take ji da shi, yau kam sai ya kar?e wayar ta ko wane hali.

Ko da ya sanar da ita zai zo bata yi yun)?urin komai ba saida ta kira Hamdeeya, tana zuwa ta dafa kafa??arta tace "Kina ji )?anwata, ki je ki fa??awa Abba Yaya Mu'az zai zo anjima."

Da sauri Hamdeeya ta tafi dan isar da sa)?onta, tana zuwa ta sameshi zaune yana kallon labarai a tashar canal3 wanda ba ya wuceshi kowane dare, tsaye tayi gabanshi tana wasa da wuyan rigarshi tace" Abba, wai Saleema ta ce in fa??a maka Yaya Mu'az zai zo."

Cike da kulawa da ba wa wacce ta turo sa)?on mahimmanci yace" Yanzu?"

Gira ta ??aga masa alamar e, jinjina kai yayi yana jin rashin jin da??i sosai, dan tunda ya daki yarinyar ko ganinta wuya yake masa, kullum tana ??aki ita da mahaifiyarta wacce ita kanta yanzu abinci ka??ai take dafawa ta aje masa a teburinshi idan girkinta ne, girkin da yake sakata a baya idan girkin Ardiya ne ta daina, kai tsaye take ce masa ya kira mai kwanan ya sakata mana, sai dai wani lokacin tana ganin rashin dacewar hakan sai kawai ya ga ta turo masa abinda yake da bu)?atar. A tunaninshi wani abun take bu)?ata, dan hak ya maida Hamdeeya ta tambayota, tana zuwa ta ce mata "In ji Abba wai me kike so?"

Murmushi Saleema tayi na jin da??i tace "Ki ce dama na fa??amasa ne dan ya sani."

Da gudu ta juya dan isarwa ita ma, tana zuwa tace "Wai ta fa??a ne kawai dan ka sani."

Jim! Yayi yana kallon Hamdeeya da ta kawo sa)?on, zai ya shiga tunanin a farfajiyar gidan da zata zauna zance shine sai ta fa??amasa? Kuma fa wanda zai aureta ne nan da wasu kwanaki, tabbas ta sh fa??a masa irin haka, saidai a ganinshi yanzu ai tana shirin zama matarsa ne, me ye na fa??a masa ko da barin gidan ne zasuyi?! (Kashhhhh??F0%??]?j?_u?a??en tunani).

Maida Hamdeeya yace yayi da sa)?on ya ji ba komai, lokacin ka??ai ta mi)?e dan yin wanka ta shirya duk da dai ba wata kwalliya take ba dama a ??abi'arta.



*Bayan ??an lokaci*



Sanyayyan murmushi ta saki tare da sunkuyar da kanta tace "Kunya fa kake sakani ji idan kana kallona haka."

Tsadadden murmushi ya sakar mata tare da sake gyara taguminshi yana ci gaba da kallonta yace "Baby, so nake nayi ta kallonki har na mutu, ina ma ace gobe ne ranar ??aurin auren nan, da..."

Kallonshi tayi tace "Da me za ka yi?" Da fara'a ya ??auke tagumin yace "Da na yi tsalle na rumgumeki."

Waro idanu tayi tace "Lahhhhh! Da girmanka?"

Cike da tabbaci yace "To miye? Ba kin kusa zama matata ba?"

Nitsar da kanta ta sake yi )?asa ba tace komai ba saboda kunya, gyara zama yayi yace "Kinsan wani abu? Ranar da aka ??aura aurenmu, idan aka kawo min ke gidana, abu na farko da zan fara tarbanki dashi shine tattaciyar madara, kinsan me yasa?"

Girgiza kai tayi tana murmushi, ??orawa yayi da "Na ji wani wa'azi ne cewa haka Manzon Tsira ya yi lokacin da Nana Aisha (R. A) ta tare gidansa, kinga kenan nima zan yi koyi da wannan sunnar, washe gari kuma sai na kawo miki kazarki, lokacin za ki iya ci da kyau ki )?oshi, dan an fa..."

Gum! Ya tsuke bakinshi sakamakon tahowar Hadeeya ta inda yake fuskanta cike da salo na lalacewa da son rikitashi, riga ce mai )?ananen hannaye jikinta ta kamata sosai, sai wando jeam ba)?i wanda ya tsaya mata iya gwiwa, kanta ba ??an kwali sai dogon gashinta data zubashi kwance, )?afafunta sanye da takalmi )?afa ciki, wayar hannunta ta shiga jujjuyawa tana kallonshi tana sakin murmushi, kuma ba kowa ya turota da wannan salon ba sai uwarta.

&?asa yayi da kanshi yana ha??e fuska, Saleema da ta fara jiyo )?amshin turarenta juyawa tayi, tana ganinta ta girgiza kai saida ta )?araso gabansu ta tsaya tana ci gaba da kallonshi, cike da izgili tace "Ina wuni angon auntyna."

Bai ??aga kanshi ba barebya kalleta, Saleema kuma kallonta ta sake yi tace "Hadeeya wannan wace irin shiga ce? Ke ba kya tsoron ko she??anu ma su dameki?"

Dafe )?ugu Hadeeya tayi tana murmushi tace "Gaskiyarki fa Auntyna, dan haka waccen gidan ma suka dinga damuna, kuma har yanzu bibiyata suke."

A hankali ya ??ago idanunshi ya kalleta, cike da sha)?iyanci tace "Gaskiya ne Yayana?"

Ha??e fuska Saleema tayi tace "Hadeeya bana son tashin kunya, bar nan wurin."

Ta?e baki tayi ta harareta tace "Na ji, dama wannan na zo nuna ma Yaya Mu'az..."

Ta fa??a tana daddana wayar ta )?ara matsawa kusanshi, da sauri Mu'az ya ??ago sosai ya fara rarraba idanu tsakaninsu, a rikice ya mi)?e tsaye dan baya so Saleema ta ga hoton nan dole za ta ji ba da??i, a matsayinshi na masoyinta bai kamata ya bari haka ta faru gabanta ba, dan haka ya kalleta bayan ya tashi tsaye yace "Am...baby, ruwa, kawo min ruwa?"

Da sauri Saleema ta mi)?e tana jin kunyar rashin kawo masa ruwan sai lemu kawai da wasu abubuwan na ta?awa da mahaifiyarta tayi ta nufi cikin falon. Yana ganin shigarta ya dam)?i hannun Hadeeya da )?arfin da saida ta yi )?ara sai kuma ta kalleshi a tsorace tace "Yayyyya."

A haukace rai ?ace yace "Hadeeya ki bar wannan wasar, sati nawa yau ina kiranki kina wula)?antani? Me yasa baki da tarbiya? Wannan ba ?ber uwarki bace?"

Fizge hannunta tayi da nufin )?wacewa sai dai ta kasa hakan dan ba ka??an ya ri)?eta ba, ??aya hannun nata dake ri)?e da wayar ya kamo sannan ya saki ??ayan, mur??e mata hannu yayi sosai yana fa??in" Kin ??auka wayo gareki, idan ma wani ke koya miki iskancin nan to daga ke har shi ko ita baku da hankali, mahaukatan banza marasa imani."

Duk yana maganar ne yana daddana wayar ta ta dan kuwa dama ba ta saka ma waya kowane irin code. A gigice Hadeeya ta nemi )?am)?ameshi tana son kar?ar wayar, shi kuma ya juya mata baya yana ci gaba da neman video, dake waya ce ta hauka videon da ta yi daga lokacin zuwa yanzu sun fi ??ari, hakan ya bashi wahala kafin ya hango hoton a rububi, yana nasarar ganinshi bai ?ata lokaci ba wajen gogewa, duk lokacin kuma Hadeeya na ta )?o)?arin dakatar da shi tana ya bata wayarta, amma bai saurareta saima kakkauce mata da yake, idan ta yi nan ya yi can idan ya yi can ta yi nan.

Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da yin hamdala ga Allah ya lumshe idanu, juyowa yayi ga Hadeeya da lokacin ta tsaya wuri ??aya tana hararenshi, mi)?a mata wayar yayi yace "Kin yi sa'a ina farin ciki zan zama angon Yayarki, ba dan haka ba wayar na so )?wacewa gaba??aya."

Cikin jin haushi tace "Za ka gani, wallahi ba zaka zama angon nata ba, kuma zan sake samo wani video, ya zakayi idan na ??auko hotonta sanda take wank..."

Ba zato ba tare da shi kanshi zai iya yin hakan ba ya sha)?o wuyan rigarta da hannu bibbiyu irin sha)?ar da namiji balagagge ya kamata ya ma, amma yanda ya hango abun sanda ta fa??a, sai wani mahaukacin kishin da shi yasan a kan Saleema ka??ai yake da shi ya turnu)?eshi. Gaf da fuskarshi ya matso ta ta fuskar, irin yanda fuskarshi ta yi jajir tsabar ?acin rai da kuma ha??e fuskar da yayi ya sakata jin ?ari kamar zatayi fistari,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login