Showing 36001 words to 39000 words out of 193749 words

Chapter 13 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4402

ya tsaya cak yace" Oh! Yi ha)?uri, na tuba Allah."

Sai kuma ya ??ora da" Kin san wani abu, al)?awari na ma kaina zan daina duk wani abu marar kyau, saboda ke."

Ha??e fuska tayi idonta har sun ??an rarako tace" Saboda ni? Me yasa sai ni?"

Saida ya cire duk wasa ya mayar gefe cike da kamala sannan yace" Saboda ke kika tunasar da ni mahimmancin sallah, hakan yasa na fara bibiyar wa'azizzikan malamai, hakan kuma ba )?aramin tasiri ya yi gareni ba, dan na )?ara jin tsoron ubangijina."

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace" A ta)?aice dai tsoron ha??uwarka da Allah yasa za ka daina?"

Jinjina kai yayi yace" &?warai."

Sanyayyan kallo ta masa mai ban sha'awa tace" Allah ya ??oraka a hanya madaidaiciya, Allah ya baka ikon gyara duk wani kure da ka san kana yi a rayuwarka, Allah kuma ya baka lada a kan ya)?i da zakayi da tsohuwar ??abi'arka wajen )?ir)?iro sabuwar ??abi'a."

"Ameen, nagode matata." Ya fa??a yana kallonta da )?auna kamar a ce an ??aura musu aure ne.

Da mamaki ta sake kallonshi tace "Me yasa ka ke kirana da matarka? Bayan kuma ka san ba haka ba ne."

?aga gira yayi yace "To ai ina sonki, kuma na fa??awa su Abba sun san da maganar, har ma ya min al)?awarin zai je ya ga Abbanki, kin ga kuwa kin zama matata."

Hankali tashe ta marairaice tace "Dan Allah Yaya Mu'az ka rufa min asiri, aure da soyayya, ni sam ban ma san su ba, dama-dama ma auren tunda ta hanyarshi aka haifeni, dan Allah kar ka ruguza min burina, sannan ka ga ina karatu kuma Abba ma ya ce ba yanzu zai aurar da mu ba sai mun cimma wata )?wa)?warrar matsaya a rayuwa."

Yana tu)?i yana kallonta da mamakin dama tana dogon surutu haka wanda bai shafi nasiha ko karatu ba? Sai kuma ya ??auke kai ya ta?e baki yace" Matata kar ki damu, idan mukayi auren za ki ci gaba da karatunki, burinki kuma ki zayyane min shi yanzu, ni zan cika mi shi da yardar Allah."

Girgiza kai tayi tana kallonshi tace" Ni dai dan Allah ka dakatar da almarar nan da ka ke rerawa, sam bana son aure a yanzu saboda wasu dalilai na."

Ba alamar wasa ya kalleta yace" Fa??i biyu na ji."

Rumgume hannaye tayi tace" Ba na sonka, sannan ina da burika."

Da hannu ya mata alama ya )?an)?ance ido yace" Fa??a min buri ??aya na ji."

Wani murmushi tayi mai kama da kuka amma ba tace komai ba, cikin kulawa ya kalleta sosai yace" Uhum! Ina jinki?"

Iska ta feso daga bakinta ta ha??e kukan da ya taho mata tace" Babban burina shine nima mahaifina ya yi alfahari da ni, ko sau ??aya ne ina so ya furta min cewa *ina alfahari da ke*, zan so ya dafa kaina ya saka min albarka, sai dai ban sani ba ko zan cimma haka, dan na yi iya )?o)?arina wajen koyawa kaina fahimtar karatu amma abun ya gagara, ban san me yake damun kaina ba, gashi yanzu za..."

Shiru tayi ta kalli Mu'az kamar a tsorace, dan gani take ta yi su?ul da baka sosai wajen fa??in abinda ke ranta ga wanda ba wata sha)?uwa ba ce tsakaninsu, goge hawayenta tayi ta ??aure fuska a dole ita ba komai kawai, lura da haka yasa Mu'az bai ce mata komai ba saboda a karatunshi ya karanci l'homme et le monde (mutum da duniyarsa) yasa ya bata damar hucewa kafin ya ce mata komai.

Ba wanda ya sake magana har suka isa kasuwa shagon Alhaji Ibrahim, wanda Saleema ce ta san shi a nan suke siyan duk wank abu da ya shafi atamfa, leshi, shadda da sauransu, zaune take kan benci daga baki-bakin shagon, shi kuma ya na tsaye ya rumgume hannaye yana kallon duk wani motsinta, ita kam hankali na kan kayan da ake ta fito mata da su tana dubawa dan za?en wanda ya mata. Mu'az da ya kula da wani matashin da ke yawan kallon Saleema gyara tsayuwa ya yi yace "&?anena, sassauta mata kallon nan haka ka j, ka yi ha)?uri ka bar min ita ta wa ce, ka ga ni ma ba kulani take ba bare kai."

Tunda ya fara maganar ta ??aga kai tana kallonshi tana kallon matashin, sai da ya gama ta girgiza kai ta kalli yaron shagon da kunya ta kamshi yana ta sosa )?eya tace" Yawwa wannan na ke so."

Nuna masa duk wanda ta za?a ta yi sannan ya jinjina kai yace" Bari na fa??awa Alhaji."

Shigewa ya yi ciki ita kuma ta kalli Mu'az tana sauke numfashi, shi ma kallonta yake da fara'a a fuskarshi yace" Ban san me yasa ba, amma dai haushi na ke ji idan wani na kallonki."

Fuskarta a ha??e tace" Ka daina wasar nan mana, na fa??a maka komai fa yanzun nan, sam ni da kai ba mu dace ba."

Sam babu alamar ya ji zafin maganarta ko makamancin haka, sai ma murmushi da ya sakar mata yace" A gaba za ki so ni, lokaci kawai ki ke bu)?ata na baki, kuma na baki daga nan har a ??aura mana aure."

?auke kai tayi ta kalli mai shagon dake fitowa yana mata murmushi suka gaisa, nuna masa kayan ta yi ya lissafa ya fa??a mata tare da mata ragi sosai saboda sanayya, godiya ta masa bayan ta biya ku??in yaronshi ya ??auki kayan ya na saka mata a mota. Ba su yi nisa ba aka fara kiraye-kirayen sallah magriba, faka motar ya yi gefe ya kalleta yace "Matata, za ki iya jirana na yi sallah?"

Bu??a baki ta yi za ta yi magana sai kuma ya langa?e kai yace "Dan Allah madame, kar ki hanani, ke ce fa ki ka nuna min mahimmancin sallah kan lokacinta, shiyasa na ke )?o)?arin kamantawa yanzu."

Sakin fuskarta tayi daga ??aurewar da ta mata ta saki murmushi tace "To shikenan, a sakamu a addu'a."

Bu??a motar ya yi zai fita yana fa??in "Tunda na ganki na ke addu'ar samunki, kar ki damu matata, addu'ata ta ki ce."

Saida ya rufo mata )?ofar kawai ta saki wani sanyayyan murmushi tana girgiza kanta, gyara zamanta tayi sosai tana hangenshi bakin )?ofar masallacin yana alwala, irin yanda yake sauri saboda an kusa tayar da sallah, amma kuma a nutse yake kamar ba jikinshi ke kazar-kazar ??in ba, ba ta gushe tana kallonshi ba har suka kabbara sallah.


______________



Da sallama dattijuwar ta shigo ??akin, a sanyaye ya amsa yana tashi zaune, cike da ladabi ya kar?i kwanon hannunta yace "Mama da kan ki? Ina su Fareeda?"

Saida ta zauna tana fuskantarshi kafin tace "Suna can suna aikin da aka saba, ka san asabar ??in nan uta ce ta farkon hutun makaranta da aka shiga, dan haka akwai bukukuwa da dama."

Jinjina kai ya yi yace "Hakane, amma Mama ai da ba ki kawo min da kanki ba."

Irin kallon nan na manya ta aika masa tace "Na kawo maka da kaina ne saboda a gabana na???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ke so ka ci ka bani kwanon."

Cike da kunya ya sosa )?eya yace "Mama, Allah za..."

Dakatar da shi tayi da hannu tace "Ka ga Huzeifa, ka ci abincin nan yanzu ko ranka ya ?ace."

Sunkuyar da kanshi )?asa ya yi tare da talla?e ha?arshi, bai san ta ya zai kwatanta ma mahaifiyarshi ba ya sha'awar cin komai ba? *Allah sarki, Allah ji)?an Babanmu*! Wannan zazza)?ar murya ita ke masa amsa-kuwa a kunnuwa, sahihiyar fuskarta mai cike da kamala da haiba, tsintar kanshi ya yi da murmushi shi ka??ai a zaune.

Mahaifiyarshi da ta )?ura masa idanuwa ta na jiran ya ci abincin ta ga shiru, a )?arshe sai ganin ta yi ya ?ige da murmushi shi ka??ai, cike da kulawa tace "Huzeifa."

Zunbur ya kalleta dan ya manta a gabanta ya ke, da sauri ya kalleta ya ??an rarraba idanu yace "Ah...ahhh, na'am Mama."

A tausashe tace "Me ya ke damunka?"

Girgiza kai yayi kanshi )?asa yace "Ba komai Mama."

&?ara gyara zama ta yi sosai tace "Huzeifa, kada wannan jarabawar ta sa ka illata kanka, ka daina cin abinci gaba??aya, kullum karatu ba ka da lokacin hutu, ??an lokacin da ba karatun ka ke ba kuma ??inki ka ke yi, kana ganin hakan ya yi dai-dai? Ba ka tsoron ulcer ??inka ta tashi?"

Kallonta ya yi a ladabce yace" Ki yi ha)?uri Mama, in sha Allah zan kiyaye, ai komai ya zo )?arshe tunda an gama."

Cike da tabbaci tace" An gama, amma jiran tsammanin sakamakon shi yake jefaka a halin tunanin nan, me zai hana ka bar wa Allah za?i, idan ka yi nasara ka gode masa, idan ba ka samu ba ka gode masa ka kuma duba wata hanyar ka bi."

Ajiyar zyciya ya sauke ya jinjina kai yace" Hakane Mama, in sha Allah zan yi yanda ki ka ce."

"Allah yasa." Ta fa??a tana kallon kwanon abincin tace "Maida hankali ka ci abincin."

"To Mama." Ya fa??a yana jawo kwanon dan ba ya son yin musu da ita, saida ta ga ya fara jefa abincin ka??ai ta bar ??akin tana sake jadadda masa za ta zo ??aukar kwanon da kanta, maza ya cin ye duka kafin ta dawo.

&?arar da wayarshi ta yi yasa ko amsa mata baiyi ba ya du a wayar, wani iska ya feso daga bakinshi ganin Sharhasila ce, )?urawa lambar idanu yayi da tunanin ya ??auka? Dan tun da ya fara zana jarabawar nan bai kirata ba saboda zafi da kanshi ya yi, yau ne ya gama yake tunanin zai je gidan dan su ha??u saboda )?ara )?aratowar lokacin bikinsu, gashi kuma ta kira bai san dalili ba.

?auka ya yi ya kara a kunne yana sallama, a ta)?aice ta amsa wa "Alaika salam, Baby shine ka manta da ni ko kirana ba ka yi?"

Lumshe idanu yayi kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya numfasa cikin nutsuwa yace "Ban manta da ke ba, zan zo gidan yau."

Cike da shagwa?a da kuma sakarci tace "Ka ga ni zan zo, zan zo gidan na ku, ina son ganinka ne."

Waro idanu yayi a sau)?a)?e yace "Gidanmu kuma?"

Turo baki tayi ta amsa da "E, gidanku, na yi kewarka Baby."

Dafe gaban goshonshi yayi yace "Ba sai kin zo ba, ni zan zo anjima, kin ji?"

Cikin shagwa?a tace "Ka yi al)?awari?"

"Na yi." Ya fa??a a tausashe, murmushi tayi wanda saida ya ji sautinsa a kunnuwa tace "To Baby ka taho mana da ice cream, ni zan ba ka wani abu idan ka zo."

Rufe idanu yayi yana mamakin wauta irin ta Sharhasila, "To." Kawai ya fa??a yana ??auke wayar daga kunnenshi ya aje ya ci gaba da cin abincin.


*Ga mai son shiga grp ??ina ya tuntu?i wanda ke musu post zai samu kanshi a ciki in sha Allah.*




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 ?? 22:41 - MOM LATEEF???i: ???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??
*BAIWATA*
???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ??A惙@?
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
=??? *[G. M. N. A]* =??? ??Id???g???


_Bismillahir rahamanir rahim_


_16_




Fitowarta kenan daga wanka tana tsane jikinta da babban towel, su Hadeeya ta samu suna ta mitar aikin da sukayi na gyaran ??akin Papi wanda har kayan abinci sai da Alhaji Auwal ya sa aka canza musu wuri aka maidasu madafa, Ummee haushi kamar zai kasheta da tana aikin, yanzu haka duk a gajiye suka kwanta har )?arfe 11:00 ta yi.

Kayan baccinta ta saka ta zauna bakin gado tana addu'o'in da ta saba yi, ta shafe jikinta kenan za ta kwanta aka )?wan)?wasa ??akin, mi)?ewa tayi da niyyar bu??ewa dan Hameeda tsaki ta ja tana fa??in "Daren ma ba za'a bari mu huta ba."

Ta kai hannu za ta ??auki hijabinta aka turo )?ofar, ido hu??u sukayi da Mu'az da yayi turus yana kallonta daga )?asa har sama, bakinshi bu??e ya kasa furta ko a, hankali ya lalubi idanunshi ya rufe dan in ba haka ba zai mutu a tsaye. Sa'a ??aya ta yi saurin rarumo hijabi ta rufe jikinta ba tare da ta sanya ba, sosai kunya ta kamata ta sadda kanta )?asa, riga da wando ne jikinta na bacci, rigar ta na da hannaye iya damatsenta, saidai ta fito mata da surarta, haka ma wandon duk da bai kamata ba, amma tsayinshi iya bakin gwiwoyinta ne.

Hadeeya da ta mi)?e zaune ce tace "Yaya, lafiya?"

Bu??a idanunshi ya yi ya kalleta sai kuma ya yi gyaran murya yace "Ughym! Umm..ammm...! Dama jarabawarku ne ta fito, na zo na ji lambobinku ne dan na duba muku."

Da sauri Hadeeya ta taso tana fa??in "Yawwa, Yaya ni lambata 4452..."

Saida ya saci kallon Saleema da ta wanka masa harara ta ja tsaki ta koma ta zauna kan gadon kafin ya turawa abokin na shi lambar da sunan Hadeeya ya duba masa, cikin )?an)?anin lokaci aka fa??a masa Hadeeya da Ummee sun samu har ma da Hameeda da ita ta zana jarabawar ne kawai amma ba ta kai ga ajin ba (candidate libre), cikin )?an)?anin lokaci ??akin ya hargitse da ihu da shewa na ?ban matan, da gudu suka fita dan sanar da iyayen da har yanzu suke zaune a falo suna kallo suna hira.

A hankali ya tako ya zo gabanta cikin sanyin murya kamar mai tsoronta yace "Saleema, lambarki?"

A zafafe tace "Ba na bu)?ata malam, ka ga shigo mana ??aki da ka yi ma ba tare da an baka izini ba ya isa, dan haka kar ka hassalani dayawa."

Kawar da kai tayi tana sake ha??e fuska sosai ita dole ya ?ata mata rai, dur)?usawa ya yi niyyar yi dan ci gaba da bata ha)?uri, haka kawai ya ke jin ranshi ba da??i saboda ranta ya ?ace, da sauri ta jaye )?afafunta dake kusa da shi tana ??an galla masa harara, mi)?ewa yayi tsaye yace "Ki yi ha)?uri Saleema, na shigo ne dan na ga baku jima da shigowa ??akin ba bare a ce har kun kwanta, amma ai na )?wan)?wasa )?ofa, kuma sai da na ??an jinkirta kafin na shigo, tunanina hakan ya ba wa wacce ke farke damar kimtsa jikinta."

Sake marairaicewa ya yi yace" Saleema, ni fa ba kowace mace ke birgeni ba, ba kuma kowane tsiraici na ke son gani ba, tunda na ke a rayuwata ban ta?a jin ina son wata ?ba mace ba sai ke, ke ce mace ta farko da na ji ina so na yi rayuwar aure da ita, ke ce macen da na ji ina sha'awar ta zama uwar ?ba?bana, Saleema..."

Yanda ya kira sunanta yasa ta ??aga kai ta kalleshi, ci gaba ya yi da cewa" Tabbas )?arya na fa??a idan har na ce surarki ba ta birgeni, amma ki sani na yi tarayya da mata da suka fi ki kyau da wayewa, sai dai ba su min ba saboda sun rasa *aji*, a gareki ne na fahimci duk wata mace mai aji, to tana tare da *kamun kanta*, wallahi abu ??aya ya sa na ke sonki da aure, wannan abun kuma shine *tarbiyya*, ina da ya)?inin tarayyata da ke za ta zama tsanin hawana hanya madaidaiciya, kamar yanda na ke da tabbacin zuri'ata indai ta tsatsonki za su fito, to za su zama abun alfaharin kowa, sannan na zama uba ma fi dacen ?ba?ba a duniya."

Da sauri ya dur)?usa gabanta yayi tsugunno irin na maza yana kallon fuskarta kamar yadda ita ma take kallonshi da )?yar take )?yaftawa yace" Saleema, ki nemi za?in ubangijinki a kan lamarina, kar kiyi gaggawa dan ni ma ba zan yi ba, duk da kuwa ina matu)?ar son yin aure saboda wani babban dalili, idan har kika ji kin gamsu za ki aureni, to ki sanar da ni a ko da yaushe, ni kuma na miki al)?awarin fa??a miki komai a game da ni, har da ma wanda iyayena kansu ba su sani ba, dan bana so mu fara zama na gaskiha ba tare da kin san wannan abun ba, dan gaskiya ba na jurar matsala daga abun da na ke so, musaman ma..."

Saida ya yi )?asa da kanshi kafin yace" Musamman ma ke, wallahi zan iya miki kuka idan kina hushi dani."

Da sauri ya ??ago ya kalleta yace" Kin gane? Ni kwata-kwata ban saba da rayuwar wahala ba, ban ta?a jin abu ya birgeni lokaci ??aya ba kamar yadda kika shiga raina, an reneni cikin gata da bani duk abin da na ke so, dan Allah Saleema kar ki hana min kanki a karon farko na rayuwata."

Bu??a ido tayi da kyau tana kallonshi, ??an jan hijabinta tayi ta )?ara rufe )?afafunta da take jin ta kamar a tsirara, ba tare da ta ??auke dubanta gareshi ba tace" *Aku*, aku sarkin surutu."

La)?ace mata hanci yayi yana dariya yace" Ke ma da kin aureni za ki koyi surutu."

Da sauri ya mi)?e tsaye yana sake fa??in" Yanzu bani lambar ta ki kema na sa a duba miki?"

Girgiza kai tayi tace" Gaskiya a'a, ina ji a jikina ma ban ci ba, ba sai ka wahalar da kanka ba."

Da mamaki yace" Me yasa? Ya za ki cire rai haka?"

Cike da jimami tace" Ka share kawai, nagode da kulawarka."

?aga kafa??a ya yi yace" Shikenan, bari na canza kaya sai na je na dubo miki."

Da mugun sauri ta mi)?e tsaye har tana sakin hijabin ya zube )?asa ta yi ram da rigarshi tana fa??in" A'a, a'a dan Allah kar k..."

Sai kuma ta saki rigarshi ta ja baya tana dur)?usawa ta ??auki hijabin kanta )?asa cike da kunyar abun da ta aikata, ganin ta yi shiru babu ma alamar za ta ce )?ala sai kawai ya fita shima ya na ji a ranshi lallai lallai dole ya dinga nisantar yarinyar nan dan gudun samun matsala, dan in dai zai dinga ganinta a haka, sannan har wani dalili ya sa su ha??a jikinsu, to fa tabbas komai na iya faruwa a yadda yake tsananin son yin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login