Showing 129001 words to 132000 words out of 193749 words

Chapter 44 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4423

su kuma su ja ma ?barsu.


*A* hankali ya sauke sanyayyan numfashin da babu wanda ya san yayi saboda fuskarshi da aka rufe da na??in farin rawani, sosai ya shiga damuwar al)?awuran da ya ??auka yanzun nan da nauyin jama'a da ya hau kanshi, shin zai iya saukewa? Shugabanci abu ne mai nauyi da kuma wuyar sha'ani, shin zai iya sauke ha)?)?in al'ummarshi? Ba ma wannan ba! Wani nauyin na daban da mahaifiyarshi ta jagoranta aka ??aura mishi, shima zai iya saukewa? Ta ya ma akayi baya jin wannan tashin hankalin kamar sauran lokuta idan za'a ??aura masa aure? Bai san komai ba game da yarinyar, fuskarta? Kamanninta? Sunanta kanshi bai sani ba har yanzu, abu ??aya daya sani shine *ita ta bashi magani*, hakan yasa a yanzun ya bata sunan *zam-zam*.


_Aunty Safiya ga fa sunan._

Ya gaji da zaman nan jama'a a cikin manyan kayan, sai dai har yanzu ba)?i ke shigowa, a haka wai wan??anda ke kusa ne da zasu iya zuwa, a bar maganar wanda zasu taso takanas dan tayashi murna da addu'a. A hankali ya sake lumshe idanu ya gya??a kanshi tamkar yana masa ciwo ya amsa gaisuwar mataimakin gwamna yana jin yadda fadawan ke amsa masa da cewa "Sarki ya amsa, sarki na godiya." Wannan sha'ani ne mai wuyar gaske, abun ne ya zamar masa biyu, ba gaira ba dalili yana zamanshi Ummi ta sakashi tunanin wacece ita? Ya za ta kasance? Fari' cikinsa ko ba)?in cikinsa? Fatanshi ??aya ne ta kasance tamkar ruwan da ta bashi ya sha, ma'ana zam-zam maganin kowace cuta. Yawan tunanin haka yasa shi jin )?aguwa da duhu yayi ko a je ??auko masa *sirrinsa*, ba dan ya )?agu ba sai dan ya ga wacece kawai.



______________


A hankali mutane suka fara cika gidan, dan abun a bazata ya zo ma kowa ba wannan tunanin, hakan yasa duk wanda ya ji sai ya hanzarta zuwa dan tabbatarwa. ?ai??aikun mutanen dake )?ofar gidan ne suka fara mi)?ewa kasancewar yamma tayi sosai tsaye suna kallon sarautar Allah, yadda motocin suka tsaya da yadda gimbiya *Kubra* ke fitowa jakadiyai na take mata baya, ga dogarai guda hu??u a gabansu sai ??aya dake ta faman shelantawa gimbiya ce da kanta ta zo ??aukar surukarta gimbiya, har falon suka dinga rakata saida aka mata nuni da ??akin maman Saleema ka??ai dogarai mazan suka jira da sauran hadiman, sai gimbiyar da jakadiyarta da kuma amintacciyar jakadiyar gimbiya Ramlat suka shiga.

Aunty Lubna da sauran matan dake ??akin ne suke mi)?e suna mata sannu da zuwa, kujera ta musamman suka nuna mata ta zauna cike da gadara da )?arewa komai kallo ta )?asan idanu, duk da har yanzu ba ta ga abinda za ta kushesu da shi ba, dan ta ??auka gidan ?bar talakawa futuk za su shigo, jakadiyan ne suka zauna )?asa kusa da )?afafunta, a nutse cike da shan )?amshi ta kalli Lubna da take )?o)?arin ganin ta kar?esu yadda ya dace, a ta)?aice tace "Barkanmu ko?"

Da fara'a Lubna ta amsa da "Barkanmu ranki shi da??e."

Wani malalacin murmushi tayi tace "Umm...ke ce mahaifiy..." Sai kuma tayi shiru, gane tambayar yasa ta saurin cewa "A'a, gata nan."

Ta nuna mata Safiya da kanta ke sadde, ??an ??aga kai tayi alamar "Oho! Na gane." Cike da girmamawa Safiya ta sake cewa "Ranki shi da??e."

A da)?ile tace "Ina miki murna." Da fara'a ta amsa da "Nagode, nima ina muku murna."

Wani kallo ta watsa mata kafin ta ??auke idanunta ta mayar )?asa inda jakadiyar gimbiya Ramlat take, da idanu ta mata alamar su gabatar da abinda ya kawosu, jinjina kai tayi sannan ta kalli Lubna tace "Ina gimbiyar take?"

Washe baki Lubna tayi ta nufi hanyar fita tace "Uhum! Bari na kirata."

Mi)?ewa jakadiyar tayi tace "Gyara kalamai akan gimbiya, mu zamu je inda take, ki kaimu gareta."

Da mamaki Safiya ta kalli jakadiyar inda Lubna tayi saurin fa??in "To, Allah ya huci zuciyarki, sake abun farko ne bamu san komai a kai ba."

Gaba tayi jakadiyar ta bita, suna fita a )?ofar ??akin da Saleema take a nan jakadiyr ta yi alama da hannu biyu daga cikin hadiman da suka tsaya dan jiransu a nan suka nufota, tare suka shiga ??akin da Saleema take kwance ta )?udundune hawayenta sun tsaya cak! Tunda aka ce an ??aura mata aure da sarki, sarki? Sarki fa? Ita? Ita a wa? Hmmmm! Ta rasa akan me za ta yi tunani, dan haka take kwance sakamakon ciwon da kanta ke mata.

A ta)?aice alwala da sallah magriba ka??ai suka barta tayi da kanta, hatta da cire zip na riga wata hadimar ce ta cire mata, tana ji tana gani amintacciyar jakadiyar nan ta mata ??aurin )?irji da farin tattausan towel suka shiga ban??aki wai za ta tayata wanka, ko wankan me? Sarautar Allah.

A )?alla dai sun ??auki awa ??aya da rabi a ban??akin, ba dan a ce )?arya take ba sai tace har madara matar nan ta mata wanka da ita, bayan ta tambayeta zuma bata mata illar komai ta ce e, sannan ta shafe mata jikinta da ita ha??e da madara gari, hatta da turaren jiki na wuta a ban??akin ta mata kafin suka fito aka shiga shiryata. Tun yamma Hadeeya ta zo gidan amma tana zaune falo tana ta fama da cin dabino da )?aramin cikinta ke sakata ga kuma ?barta mai shegen la)?uwa bata yarda da kowa sai ita, tare da Hameeda wacce suka tafi Abuja da mijinta sai jiya suka zo suka taso dan zuwa su ga Saleema, shiri ne na gayu jikin Hameeda, amma suna dosowa )?ofar za su shiga ba tare da su kula da hadimai biyun dake jikin )?ofar ba suka tsaresu tare da fa??in "Kuyi ha)?uri ba zaku shiga ba, ana shirya sarauniya ne."

Da mamaki suka kalli junansu sai kuma Hameeda cike da sabuwar rashin kunyar data koya ta fitsara da jin yanzu tana auren mai ku??i tace "Sai me? Kunsan su waye mu? &?annenta ne fa, su waye ku da zaku hanamu shiga duk inda muke so a gidan ubanmu?"

?aya daga cikinsu ce ta ha??e fuska sosai tace "Ba zaku shiga ba, umarni aka bamu kuma dole mu cika."

Hadeeya ce tace "To nan ai ba gidanta bane, ku bari har ta je can ??in idan kun ga )?afarmu sai ku mana iskanci."

A hassale Hameeda ta kama hannun Hadeeya tace "Zo muje dan Allah, can su )?arata da da)?i)?iyar tasu da basu ma san w..."

A razane, a kausashe ??aya daga cikin dogarai dake tsaye ri)?e da bulala cikin )?a)?)?arfan murya yace "Keeee! Gyara kimtsi ?bar matsiyata, ki iya sarrafa harshenki ko jikinki ya gaya miki, sarauniya ba abar wasar uban kowa ba ce."

A tsorace Hadeeya ta ja baya tna kallonshi sai Hameeda da ta harareshi ta )?asan idanu tace "Mu fa )?annenta ne ba ?ba?ban matsiyata ba."

?aga bulalarshi kamar zai tsala musu, amma tayar da sallah isha'i da aka yi kuma a lokacin ake son fita da matar sarki ba tare da kowace ijiya ta samu damar ganinta ba, sai kuma ya dakata daidai lokacin da aka bu??o ??akin da suke ciki.




*Alhamdulillah.*
20/06/2022 ?? 22:07 - MOM LATEEF???i: ???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??
*BAIWATA*
???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ??A惙@?
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
=??? *[G. M. N. A]* =??? ??Id???g???


_Bismillahir rahamanir rahim_


_42_




Jakadiyar gimbiya Kubra ce ta fito da sauri ta sanar da su sarauniya na fitowa, da sauri sauri hadiman suka isa bakin )?ofar suka tsaya su kuma dogaran nan biyu ??aya ya fita da sauri dan dolenshi ya tabbatar babu kowa a kan hanyar wucewarsu kamar yadda a fada aka bu)?aci da a )?ara wasu mintuna kafin tayar da sallah, ana so a lokacin da za'a shiga da ita gidan ya zama kowa na sallah a lokacin tunda ba za'a barta har dare ya tsala ba, ??aya dogarin dake magana da su Hadeeya ??aga bulalar yayi yana bubbugata gefe da gefe, da gangan, da saninshi ya tsala wa Hameeda dan ??azu ma ya so duka mata dan ta gane girman da Allah ya ba ?bar uwarsu. &?ara ta saki tare da dafe cinyarta da ya tsulama bulalar tace "Kammm!"

?akin aka )?ara bu??ewa jakadiya na gaba sai gimbiya Kubra sai sauran a bayansu, su Hadeeya dake tsaye dogarin ya daka ma tsawa da "Gwiwa )?asa talakawan gimbiya, )?arya kuke ku ha??a tsayi da uwar marayu."

A razane suka zube gwiwoyinsu )?asa Hameeda da ta ji kalar bulalar nan harda sadda kanta tayi idanunta na cika taf da hawaye, wannan dogarin daya fita tare da hadimai biyun da suke jira suna jiran fitowarsu ne suka )?araso, sula duk zagaye gabanta da bayanta sukayi, hakan yasa aka saka Saleema tsakiya wanda duk baza idanun Hadeeya ta kasa ganin ko da kayan jikinta bare ta ga fatar jikinta.

Gashi tafiya suke tamkar wa??anda basu da lafiya, tafiya kamar marasa kuzari, har ita kanta Saleema da kanta ke lullu?e cikin alkyabbar da aka rufe jikinta ruf da ita take ganin yaushe zasu kai da wannan tafiya? Ita kam da sun bata ma damar ganin Mamanta, dan rabonta da ita tun kafin sallah la'asar da suka sakata tsakiya ita da Abbanta suka mata nasihar da har yanzu haway take dan ji tayi tamkar za ta rabu da su ne na har abada. Suna kawowa daidai falo Gaishata na fito daga ??akin Ardiya za ta tafi gida sai Ardiya dake bayanta zata rakata, sun wuni suna gulmar suna jajanta lamarin, ga takaicin Kabil wanda da ta fa??a masa ma Saleema fa tayi aure ya ja mata tsaki a wayar ya kashe bai tanka mata ba, ranta ya ?ace sosai da abun nan da ya mata, da gudu ??aya daga cikin dogarawan ya shiga bu??e babbar rigarshi yana zazzaro musu idanu yana fa??in "Kawuna )?asa, )?asa, maza."

Jikinsu ne ya fara rawa basu san sanda suka dur)?ushe )?asa ba Gaishata gaba??aya ma zaune tayi tana sadda kanta )?asa jikinta sai rawa yake, dan tsawar da ya musu ta tsorata ta, Ardiya ma kanta na )?asa sai "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Take karantawa.

Saida suka ga fitarsu suka ??aga kawunansu, take abinda Ardiya ta fa??a kwana biyu da suka wuce ya dawo mata, wato izgilin da ta yi ne take ganin ai abu ne da ba zai faru ba, sai gashi yana faruwa da uta yanzun nan, Saleemar da suka rayu tare, ita ce yanzu har ake kakkarewa idanunta ma suka kasa ko da hango suturar jikinta in ba sanyayyan )?amshin da ta bar masu a ??akin ba.

Gyara zamanta tayi dangalgal tace ma Gaishata "Je ki kawai, munyi waya daga baya."

Harara Gaishata ta watso mata tace "In fita wa??ancen mahaukatan su zaneni, shela fa na ji suna yi kar wanda ya fito wai gimbiya za ta fita."

Sai kuma ta ta?e baki tace "Humm! Da bari mukayi ma ta auri Mu'az ??in, ko ba komai ba zata mana wuyar gani ba."

A hassale Ardiya ta mi)?e tana fa??in "Ki tafi kawai, ni har yanzu ba da??in jikina nake ji ba."

Gaishata ma mi)?ewa tayi tana ??aukar jakarta data saki ta ta?e baki tace "Hawan jini ma kamaki zaiyi idan baki cir..."

A zabure ta matsa kusan Ardiya suna neman )?amkame juna saboda busar sarewar da akayi daga waje wacce ke nuni da fitowar sarauniya waje, a haka aka bu??e mata mota ta shiga ita da gimbiya Kubra sai jakadiyar gimbiya Ramlat da ke gaba zaune, a nutse motocin sukayi jerin gwanonsu suka fita a gidan saleema ba ta ko ji motsin Mamanta ba bare auntynta Lubna da har lokacin tana nan ita ma.

Su Hameeda ne suka taso daga inda suka dur)?usa ranta ?ace na bulalar nan da aka tsula mata, kusan Mamanta ta tsaya tace "Momma ni na tafi gida, wallahi da na san kayan takaicin da zan tarar kenan da ban zo gidan nan ba."

Juyawa tayi za ta fita tace "Aikin banza kawai."

Da kallo suka bita har ta fita, Hadeeya ma ??akin Mamansu ta nufa tana fa??in "Nima dai bari na kirashi ya zo ya ??aukeni, banga anfanin zaman ba."

Da kallo Ardiya ta bita tace "Ke shikenan abinda kika za?a ma rayuwarki kenan, ciki ne fa da ke."

Da sauri tace "To wai Momma ya zanyi, tunda yana son abunshi ba shikenan ba."

Da mamaki ta ri)?e ha?a tace "Kuma dan yana so shikenan sai kiyi ta biye masa? Shikenan rayuwarki ce."



_______________



Sanda suka iso masarautar anyi tsakiyar sallah isha'i, hakan yasa gidan ke shiru sosai, tunda aka ce ta fito ta zuro )?afafunta da addu'ar shigowa gida "Bismillahi wa'lajna, wa bismillahi karajna, wa'alallahi Rabbina tawakkalna."

Kamata sukayi suka shiga ta )?ofar sirrin da sarki ke kai kawo a cikin suka dinga kutsawa har suka isa falonta na biyu a sabon wurin da ya zama mallakinta yanzu, gimbiya Kubra ce ta kamata ta zaunar da ita tare da cewa" Zauna ko."

Saida ta zauna sannan hadiman suka zauna a )?asa.
Shigowar gimbiya Ramlat yasa hadiman suka rage yawa a falon, sam ta kasa yarda da irin wannan shigewa da gimbiya Kubra take musu, hakan yasa ta mi)?ewa ba tare da tayi maganar da take son yi da Saleema ba ta kalli jakadiyarta amintatta tace "Jakadiya, kinsan abinda ya dace kiyi, zamu baku wuri ki shiryata, idan kun ida sai ki jira umarnin mai gado."

Cike da ladabi ta amsa da "Angama ranki shi da??e."

Kallon gimbiya Kubra tayi da bata da niyyar tashi, amma da ta kalleta da idanu ta nuna mata mu tafi, dole ta mi)?e tana murmushi suka fice jakadiyarta na binta a baya tana ayyana "Idan ba yau ai akwai gobe."

Suna fita jakadiyar ta taso ta rufe )?ofar sannan ta dawo wajen Saleema, a nutse ta fara cire mata alkyabbar nan, kamata tayi ta tashi suka shiga wani ??aki, kan wani gado gado mai shinfi??e da leda ta zaunar da ita ta juya bayanta ta cire mata zip ??in rigarta. Tana ji tana gani ta sake tu?eta zigidir kafin a saka mata wata yar riga ba)?a wace aka fara yi mata darzar fatar jikinta da ita, ??akin wani irin ??umi ne yake da wanda da farko ta ringa zufa sosai sai daga baya zufar ta tsane a jikinta a lokacin da ta ke mata wata irin lindar da ta kusan fitar da ita daga hayyacinta.

Sosai take bin duk wani sa)?o na jikinta tamkar wanda zasu canza mata fatarta daga ba)?a zuwa fara, ruwa mai ??umin gaske mai ha??e da ruwan turaren nan mai tsadar gaske suka wanke mata jikinta tas, babban towel ??in da ta bata ta ??aura yasa Saleema kallonta a nutse tace "Mama, ina so zanyi sallah isha'i."

Jnjina mata kai tayi tace "Shikena, kiyi alwala idan kin idar sai mu ida."

Da kallon son tambayar har yanzu ba'a gama ba kenan? Ta bita kafin ta ??aura alwala ta fito ta bata doguwar riga ta saka sannan ta kabarta sallah. Daga yadda dattijuwar ke zaune ya nuna mata kamar ita take jira, dan haka da ta sallame ba ta samu damar )?arasa Azkhar ??in da ta saba ba ta tashi suka koma ??akin.



Rigar ta sake kamawa za ta cire mata, kamar za ta fashe da kuka ta kalleta tace "Mama, yanzu ma cirewa za'a yi?"

Murmushi dattijuwar ta mata tace "Da alama ba sai na koyar dake tausasa harshenki ba, dan alamu sun nuna kin iya magana da babba, sai dai yalla?ai sarki ne, sarkinki, idan zakiyi magana da shi idanunki a )?asa, sannan muryarki ta fi haka kwanciya, idan zai yiwu ki dinga magana tamkar muryarki na ?arin kuka dan tsoro, amma fa ba kowane lokaci ba, haduwarku ce ta farko wannan, ki kula sosai wajen magana da yalla?ai, ki sani wata maganar ma ba da baki zaki furta masa ba, ido kawai sun isa su sanar masa da sa)?onki, matar sarki kike yanzu, dole ki koyi wannan sarauniyata, musamman idan kuna tare da mutane, ya dace ki fa??a masa abinda kike son fa??ane da idanunki da kuma yanayin fuskarki."

Zaunar da ita ta sake yi bakin gadon ta zagaya bayanta, kanta da suka kwance mata tun a gida ta shiga warwarz mata yalwatacciyar sumarta tana rabata, wani dandanan man kai ta dinga shafa mata tare da dun)?ule mata shi tamkar kitso, saida ta gama ta zagayo gabanta tana kallon fuskar Saleema da uta dai ta ??ora hannayenta ta rufe )?irjinta sannan tace "Motsinki, tafiyarki, yanayin gudanar da duka lamuranki, dole a samu nutsuwa da aji a ciki, ko daga ke sai yalla?ai ne, ba kowane lokaci zaki bu)?aci bu??a bakinki ba, tambayarsa kawai zakiyi da idanu kuma ya fahimci me kike nufi, haka idan kina son ganar da shi wani abu ne dake kusa dashi, zaki iya yin fari da idanunki na sai kin ce uffan ba."

A sanyaye ta sake fa??in " A yanzu ke ??in kin zama uwar talakawa, nauyi mai girma ne ya hau kanki tare da nauyin da ya hau kan yalla?ai, akwai bu)?atar ki zama hutunsa a cikin gida, ke ce za ki tarbeshi idan ya ??au zafi saboda nauyin al'umma, ke ce zaki tarbesa a duk halin da ya shigo miki, mulki babban lamari ne da idan Allah ya baka ba yana nufin ya fi sonka bane a cikin bayinsa, alamu ne na babbar jarabawa ake maka, akwai abubuwa dayawa na tashin hankali da zasu faru da shi a waje ya dinga shanyewa, amma ke matsalarki, ba lallai ne ya iya shanyeta ba, damuwarki )?arara za ta bayyanar da tasa damuwar har ta fara shafar mulkinsa, dan kuwa a gabanki ne zai iya fitar da ?acin ran da ya wuni yana sha)?a, a gabanki ne zai iya fitar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login