Showing 72001 words to 75000 words out of 193749 words

Chapter 25 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4380

kai ya sake yi yace "Hadeeya ba kowace waye bace ta ke da birgewa, kin ganni nan? Kin san da tun kafin a haifeki na ke karatu, na )?etara )?asashe duk dan neman ilimin duniya, amma ha??uwata da Saleema da ba ta fi kwana goma ba na san wasu abubuwa da ya kamata a ce na san wannan karatun na sallah tun ina da shekara goma a duniya, ta ya zan yarda na auri wacce ba za ta umarceni da na tashi na gana da ubangijina ba? Idan na aureki Hadeeya duk wuta zamu shiga, kinga kenan ba anfanin zamanmu tare."

Ko da ya gama fa??a mata ya fice da sauri yana kiran lambar abokinshi *Zeid*, dan shi dai kam baya jin zai iya kwana ba tare da an shirya tsakaninshi da Saleea ba, kai shi idan ta kama ma )?ofar gidansu zai kwana har sai ya ga dariyarta, dan Allah ya sani yana )?aunar yarinyar fiye da yanda yake son kanshi.

Lallai Hadeeya ta ga ba)?ar rana, dan kuwa shagalin nan rai ?ace aka idashi da ita, Ardiya ta fahimci hakan musamman da ta ga fitar Mu'az ba fara'a da yanayin tashin hankali, amma sai ta ha??e komai da niyyar idan aka watse hankalinsu ya kwanta ko da tsakiyar dare ne za su tattauna ta ji me ye matsalar.

*Bai* matsa a )?ofar gidan ba saida Zeid ya zo ya sameshi a ki??ime saboda fa??a masa da ya yi ba lafiya ya zo da wuri, yana ganinshi ya fito a motar ya tunkareshi, hannu ya mi)?a mishi yana fa??in "Yawwa abokina, ka ga fa Saleema ce ke hushi ni, kawai daga ta ganni da Hadeeya muna hoto."

Sai kuma ya sassauta murya yace "Dan Allah ka kirata ka bata ha)?uri, ka ga ni ina ta kira ba ta ??aga min waya, wallahi a tsorace na ke."

Da yanayi irin na haushi haushi dan bai ??auka dalilin da ya sa ya kirashi kenan ba ya girgiza kai yace "Yanzu Mu'az dama saboda yariyar nan ne ka kirani?"

Cike da tabbaci yace "E mana, ba ta kai a kiraka saboda ita bane?"

A hassake Zeid yace "Ba ta kai ba..."

Sai kuma ya gyara tsayuwarshi yace "Mu'az, wai sai yaushe za ka fahimci yarinyar nan wahalar da kai kawai take? Ni ban ma gane maka ba wallahi, sam ban ga abin damuwa a jikin yarinyar nan ba, me ye ka gani a tare da ita da yake ??a??aka a )?asa ne? Ita ba kyau ba, ba hasken fata ba, ba ilimi da..."

A matu)?ar hassale Mu'az ya matso daf da shi kamar zai ha??eshi ya nunashi da yatsa yace" Kar ka soma Zeid, idan ba za ka taimaka min ba kawai ka tafi, amma ba zan juri jin wannan ba)?a)?en maganganun na ka ba."

A fusace ya juya ya koma motarshi ya bu??e ya zauna, Zeid da ya ga rashin kyautawarshi numfashi ya sauke sai kuma ya tako a hankali ya bu??e motar ya shiga ya zauna mai zaman banza ya rufe, shiru motar ta ??auka a )?alla na mintuna biyar, a nutse Zeid yace" Me ta ga kana ma Hadeeyar? Kuma gaskiya za ka fa??a min dan ka san na fi kowa saninka."

Saida ya galla masa harara ta gefe idanu sannan ya ??auke kanshi, kamar ba zaiyi magana ba dan har da rumgume hannaye kafin kuma yace" A ganinka zan mata lalata ne?"

Wani shashashan kallon ya watsa mishi yace" Na ??auka kai ka fa??a min ka samu sabuwar ?bar shilar da za ta rage maka zafi."

Cike da rashin gaskiya yace" Hakane na fa??a, amma kafin na fa son Saleema ne, yanzu babu wannan tunanin a raina game da ita, ka yarda dani abokina."

Iska Zeid ya huro daga bakinshi yace" Ba maganar yarda tsakanina da kai Mu'az, yanzu fa??a min me yasa ka kirani?"

A take yace" Ha)?uri nake so ka bata, ka fa??a mata wallahi ba abinda take tunani bane, kuma yanzu ma haka na ma Hadeeya kashedi za ta fita harkata."

Da wani kallon tuhuma ya kalleshi yace" Za ka daina kiranta kenan?"

Matse fuska yayi yace" Ni fa dama ba ni ke kiranta ba, ita ke yawan takura min da kira."

"Sai ka ke ??agawa ko? Duk da kasan maganar aure ce tsakaninka da Yayarta." Ya fa??a yana kallonshi, da alamar saranda ya ??aga hannaye yace "Na ji kuma na ??auki laifina, amma dan Allah ka je ka bata ha)?uri komai ya wuce."

Girgiza masa kai yayi yace "Mu'az ba zaka iya da rigimar yarinyar nan ba, ka san matsalar auran mace ?bar islamiyya?"

&?ura mishi idanu Mu'az yayi da alama )?arin bayani yake nema, ??orawa yayi da "Haka za ta dinga gwara maka kai kamar wani ??anta, su fa irin yaran nan komai a gurinsu ba daidai ba ne, kowane motsinka sai ta nuna maka ai ba kyau Allah ya hana, kaza haramun ne kaza haramun ne, ga takurar tsiya da na cin sababi musamman kan abinda ya shafi addini, ka ga ka auri] ar islamiyyar nan? Wallahi ka daina baccin asuba kenan saboda saita tilasta maka bin jam'i, ga su da ganin kowa ??an wuta, haka kawai za ta ga komai ba daidai ka ke yi sai yadda take yi ne daidai."

Tsaf! Ya zuba masa idanu har ya gama maganarsa, numfasawa Mu'az yayi yana murmushi yace" Gaba da gabanta, duk lalacewata ka fini iskancewa, tunda ni ina son na daina duk abinda na ke, hakanne ma ya sa na ke son auren wacce take da ilimin addini, maganar tashi sallah asuba kuma ai tun zuwanta gidanmu ta koya min, yanzu haka daga waccen ranar da ta je zuwa yanzu ban ta?a rasa jam'i a kowace sallah ba."

Kallonshi yayi sosai yace" *Zeidul-Abidin*, mun samu rayuwar nan ba da wayo ko dabararmu ba, kar mu yi saken zuwa lahira babu guzuri, dan hakan shine asara ma fi girma da zamu tafka, mutuwar nan dai ba sallama take wa mutum ba, sannan ba ta turo sa)?on kar ta kwana, to idan dai mutuwa za ta zo mana bagatatan a halin da muke ciki yanzu, da wane ido zamu kalli ubangijinmu, wanda Saleema ta fa??a min cewa kowane yaro yana zuwa duniya ne da al)?awarin da ya ??auko tsakaninshi da ubangiji kan ba zai ta?a ha??ashi da kowa ba, sannan zai bauta masa iya iyawarsa, ka ga haka...?"

Ya fa??a yana nuna masa dun)?ulallen hannunshi na dama sannan yace" Ta ce min dalilin da yasa kowane jariri ke zuwa da dun)?ulallen hannu kenan, wannan al)?awarin da ya ??auko ma mahaliccinsa, amma awanni ka??an, kwana ka??an sai ka samu jaririn da bai san waye shi ba ya saki hannunsa saboda kawai ya sha)?i iskar duniya, da haka zai ci gaba da mantawa da wannan al)?awarin, abinda zai sa ka tuawa kuma shine zama a gaban masu ilimin da zasu sake tunatar da kai wannan al)?awarin, idan har muka bi ta son zuciyarmu Zeid, ina ga ba anfanin zamanmu muna amsa sunan musulmi, kawai mu koma maguzanci zai fi dacewa da mu."

Shi ma Zeid zuba mishi idanu yayi har saida ya gama, dan gaskiya abinda ya fa??a gaskiya ne kuma ya ratsa zuciyarsa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da murmusawa yace "Gaskiya nima ?bar islamiyyar nan zan nema, gashi lokaci ??aya har ta mayar da kai sheikh Mu'az."

Harara ya watsa mishi yace "Kai fa ??an iskane."

Shi ma hararanshi yayi yace "Na kaika ne?"

Girgiza kai yayi yace "Na ji yanzu zan shiga har ciki na bata ha)?uri, amma Mu'az dan Allah dan girman Alla kaaa fita harkar )?anwarta."

Cike da tabbaci yace "Na daina wallahi, kuma ba zan sake kulata ba."

Jinjina kai yayi yacce "Allah yasa, dan gaskiya ni tsoro ka ke bani, kuma tunda ka fa??a min tsarinka a kansu na ji dama hankalina bai kwanta ba, dole dama a samu irin haka."

Cike da jin haushi yace "Na ce na daina ko? Ni dai yanzu ka shiryani da ita dan Allah."

Bu??e murfin motar yayi ya fita ya tunkari shiga gidan, haka ya dinga kutsa ?ban mata da samarin da har yanzu ra)?ashewa ce a gabansu har saida ya isa )?ofar shiga babban falon ya dakata, su Ardiya dake zaune nan wajen ya gaishe da su a mutumce suka amsa, dake bata san shi ba ko da ya tambayeta Saleema ta kalleshi daga sama har )?asa, a ranta ta ayyana "Kaiii!"

A ganinta me ye tsakaninshi da Saleema, irin shaddar dake jikinshi mai )?aramin ??inki, gashi kyakyawa dukda duhun fatarshi, abu ga dogo ga iya ??aukar wanka, sai kawai ta sakar masa murmushi tace "Ko dai kaine surikin na mu?"

Cike da kunya ya girgiza kai yace "A'a, ni abokin Mu'az ne, na zo bata sa)?o ne."

Ha??e fuska tayi ta galla masa guntuwar harara ta )?asan idanu ta nuna masa tace "Shiga tana ciki."

Shiga yayi da mamakin ita kuma matar nan me ke damunta? Ta ya za'a ce ba ta san Mu'az ba da maganar dake tsakaninsu da Saleema? Sa'ar da ya ci ta ha??ewa da Hamdeeya ya saka ta kirawo masa Saleema dake ??akinsu kwance, sai dai ta daina kuka yanzu saboda bata son Mamanta ta fahimci wani abu.

Hijab ??inta ta sako dan bata san ko wanene ba, hasalima ba'a ta?a mata irin wannan kiran ba, a falon ta same shi zaune kan kujera duk da ana shige da fice tsakanin falon da ??akin Ardiya, kujerar nesa da shi ta zauna tana ??an sakin fuskarta saboda ta sanshi lokacin bikin Mu'awwaz sun ha??u, cike da girmama juna suka gaisa kafin ya fara da abinda ya kawoshi, cikin nutsuwa ya gyara zamanshi yace "Saleema, abokina ya fa??a min abinda ya faru ??azun, ya shiga damuwa sosai da tashin hankali, har yanzu yana waje bai bar nan ba, shine na ce bari na zo na baki ha)?uri, sannan na fa??a miki ba abinda kike tunani bane, ba komai tsakaninshi da )?anwarki sai mutumci da girmamawa, ina fatan za ki fahimceni sannan ki yafe masa?"

Da mamaki da kuma shanye damuwarta tace" To! Na fa??a masa ina hushi da shi ne? Ni ai ban ??auka da zafi haka ba, kuma ya min bayani na fahimta, ba komai."

Da kallon tuhuma ya bita yace" Kin tabbata ba komai?"

Da tabbaci tace" Na tabbata, har zuciyata nake fa??a maka haka."

Da sigar zolaya yace" Kenan yanzu zai iya turowa mu ??aura muku aure mu huta da irin wannan )?ananen matsalolin?"

Cike da kunya ta sinne kanta ta rufe fuska da hijabi, murmushi yayi cike da jin yarinyar ta birgeshi saboda kunya ya sake cewa "Kenan baki ha)?ura ba har yanzu?"

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a wallahi na ha)?ura."

Mi)?ewa yayi tsaye yace "To indai hakane mu je yana jiranki a waje."

Zaro idanu tayi tace "Yanzu kuma?"

Da mamaki yace "E, me ye to?"

Shiru tayi tana tunani a ranta, katseta yayi da fa??in "In dai ba ki je ba zan sameshi na fa??a masa kin )?i ha)?ura ya zo da kanshi har ??akin ya sameki."

Da sauri ta mi)?e tsaye tana fa??in "To shikenan zan je."

Gaba ya yi ita kuma tana binshi a baya har suka fita daga gidan, yana ganinsu ya fito da zumu??i yana washe mata baki, saida ya )?araso ta tsaya ya )?ara gyara tsayuwarshi yace "Babyyy, kin yafe min?"

Sadda kanta tayi )?asa ba ta ce komai ba, sake matsowa yayi daf da ita ya marairaice yace "Matata, ki yafewa mijinki mana, ba zan )?ara ba."

Cikin kunya ta ??an ??ago ta kalleshi tace "Ni fa dama ba hushi na yi ba."

Le)?a fuskarta yayi yace "In dai hakane to ki min murmushi ko na ji sanyi a raina."

Numfashi ta sauke kafin ta ??an murmusa, dafe )?irjinshi yayi yana kallonta yace "Na ji da??i Baby, kuma dan Allah kada ki )?ara irin hushin nan dani, zan iya mutuwa fa."

?war dariya kawai tayi ba tace komai ba, a hankali ya dinga jan ta da hira tana ??an amsa mishi sama sama, dan a takure???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? take jinta duba da basu ta?a tsayawa a nan ba, sai take ganin duk wanda ya wyce kallonsu yake, sun kai minti sha biyar kafin ya mata sallama zuciyarshi fes na farin cikin ba zata kwana da ?acin ranshi ba ya bar gidan.




*Alhamdulillah.*
09/06/2022 ?? 22:49 - MOM LATEEF???i: ???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??
*BAIWATA*
???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ??A惙@?
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
=??? *[G. M. N. A]* =??? ??Id???g???


_Bismillahir rahamanir rahim_


_27_





?an nesa da shi ta zauna kanta a )?asa tana jin yana rufe jaridar dake gabanshi, gilashin dake idanunshi ya cire ya aje kafin ya sake maida hankalinshi kanta yace "Ina jinki?"

Saida ta )?ara sinne kai tana )?arfafa kanta cikin nutsuwa tace "Abba, dama...da...dama ina zan fara koyon ??inki ne, dan Allah Abba ka barni na fara?"

&?ura mata idanu yayi na tsawon lokaci, sai kuma ya numfasa tare da mi)?ewa ya ??auki makullenshi da wayarshi ya nufi hanyar ficewa a ??akin yana fa??in "Bana son sake jin maganar ??inkin nan a bakinki, idan ba haka zan ?ata miki rai fiye da tunaninki."

Da sauri ta juya ta bishi da kallo ta )?ofar baya da zai fita tace "Abba dan Allah?"

Cak! Ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, )?an)?ance idanu yayi ya nunota da yatsa yace "Saleema rainani kikayi kenan? Dan kinga abinda kika aikata ba da sanina ba ban ??auki mataki a kanki ba, shi ne yanzu za ki zo min da maganar banza?"

Gyara tsayuwa yayi cike da bata tabbaci yace "To bari ki ji, wallahi idan kika )?ara maganar ??inki a gidan nan, ba ke ka??ai ba har mahifiyarki sai ta gane shayi tsurar ruwa ne."

A mugun tsawace yace "Tashi ki bani wuri."

A zabure ta mi)?e da sauri za ta bar ??akin, muryarsa ce ta sake dakar kunnuwanta yana fa??in "Aurenki nan da wata ??aya, kuma zan tabbatar shi kanshi Mu'az ??in bai barki kin zubar mana da mutumcinmu ba ta hanyar fara ??inki."

Kuka ne ya )?wace mata da ya sakata rufe bakinta ta juya da gudu ta koma ??aki inda ta baro Mamanta, tana shiga ta fa??a kan gadon kusa da Mamanta, Safiya dake zaune da carbinta a hannu tana ja ta kalleta ta ta?e baki tace" Da na fa??a miki wahalar banza za ki yi ba ki yarda ba, mahaifinki ba mutane ne da ake shawo kansu ta sau)?i ba, ki ma ha)?ura in za ki ha)?ura, ni baki ganni ba? Sha'awar abincin siyarwa nake, har ??an uwana ya sa ma min aiki a wani gurin cin abinci da zan dinga yi musu sinasir da wainar shinkafa, a gida zan yi su zo su ??auka su bani ku??ina, amma haka ya ba??awa idanunshi toka ya ce ba da shi za'a yi wannan zubar da mutumcin ba."

Da sigar tambaya tace" Da ya nuna baya so me kika ga na yi? Ha)?ura na yi ya ce shi zai dinga bani albashi duk wata, kuma gashi yana bani sai in mantuwa ya yi, ke ma ki ??auki hakan a matsayin )?addarki, idan kikayi aurenki wata)?ila Mu'az ya taimaka miki."

Sai lokacin ta ??ago kanta tana ta shashe)?a tamkar za ta mutu tace" Mama Abba fa cewa ya yi wai har Yaya Mu'az ??in zai fa??a masa kar ya saki ya taimake ni saboda zubar da mutumcinsu ne, Mama me yasa Abba baya so na? Na ??auka na yi abinda zai yi alfahari da ni, amma har yay bakinshi bai iya nuna min irin )?o)?arin da na yi ba, me yasa?"

Shiru Safiya tayi ta ci gaba da carbinta dan in ta ce za ta yi magana za ta iya yin kuka ita ma, dan gaskiya ba ta jin da??i ha)?uri kawai take. Ta na laziminta wata dabarar ta fa??o mata, da sauri ta kalli Saleema da ta sake maida kanta )?asa tana kuka tace "Kinga tashi zaune, ki saurareni."

A sa?ule ta tashi zaune tana ta sharar hawaye, cikin nutsuwa Safiya tace "Kina ji, mahaifinki yana ganin girman surukinki wato Alhaji Auwal, ki kirasa ko ki je gidan ki fa??a masa, na tabbata idan shi ne ya masa magana zai barki ki yi abinda ranki ya ke so."

Da sauri ta fara share hawayen inda fara'a ta maye fuskarta sa?anin yanzun da take kuka tace" Hakane fa Mama, ban yi wannan tunanin ba, kuma kinga ko da ma ba zai yarda ba hakan zai bani damar na fara koya bayan aurenmu."

Murmushi Safiya tayi tace" Ni ma yanzu tunanin ya zo min, Allah ya bada sa'a."

"Ameen." Ta fa??a tana sauka daga kan gadon ta nufi inda ta li)?a wayarta caji, da mamaki Mamanta ta kalleta tace "Ba dai yanzu za ki kirashi ba?"

A shagwa?e tace "E mana Mama, da gaggawa ai ya fi."

Da alamar nusarwa tace "Amma kinsan da gaggawa aikin she??an ne, ki bari zuwa yamma ko dare lokacin yana gida, amma yanzu na san duk inda yake yana wata sabgar."

Cike da rashin jin da??i ta jinjina kai ta cire hijabinta ta jefo kan gado sannan ta zo ta zauna, sai take jin kamar ta ??aga hannu sama ta yi addu'ar Allah ya kawo yammar nan yanzu dan ta kira Alhaji Auwal wanda zuciyarta ke raya mata tabbas yanzun kam Abbanta zai amince dan baya tsallake maganar mai gidan na sa kuma amini ta wata fuskar.



______________



Shigowarshi ??akin kenan daga wanka yana son fita kunnuwanshi suka jiyo mishi abinda sam bai ??auka a shekaru da ilimi irin na Sharha za ta aikata haka ba, da kunnuwanshi ya ji tana fa??a ma )?awarta da bakinta cewa "Ai )?awata ki bari kawai, jiya na )?ara son mijina fiye da yadda kike tunani, ashe wannan shiru shirun da sanyin nan kamar marar lakka ha??e da gemun nan irin na ustazai, ashe dai kayan aiki ne a cikin tattausar suffar nan."

Dariya tayi na wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login