Showing 93001 words to 96000 words out of 193749 words

Chapter 32 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4413

hakan yasa ma)?aunata sukan rayu har abada duk tsanani, amma masoya su kan rabu da dalili mara ma'ana saboda babu )?auna."_

Kallonta yayi yace" Ba zan ta?a yarda da soyayyarki ba Hadeeya, dan na san babu )?auna a cikinta..."

?agowa yayi daga jinginar da yayi ya kalleta yace" Ki fara sanin yadda zaki )?aunaci ?bar uwarki kafin ki so wani, kada ki kuma kirana a waya bare ki je inda na ke, idan ba haka ba zan ajiye sanayya a gefe ??aya na miki abinda ban ta?a kwatanta yi wa wata mace ba."

Murfin motar ya jawo zai bu??e yace" Kada kiyi biyu babu, )?ofar abokina a bu??e take, idan aure kike so dan biyan bu)?atarki bismillah, namiji ne shi har da )?ari."

Shigewa yayi motar ya barta nan tsaye, Zeid na ganin haka ya tako da sassarfa ya zagaya ya shige motar bayan ya kalli Hadeeya da mamakin yadda take tsaye kiskirim kamar wacce bata motsi, yana shiga Mu'az ya ja motar suka bar unguwar ba tare da sake waiwayarta ba.



______________



Kowa rayuwarsa yaci gaba da yi da taimakon mai hura musu numfashi, sam Mu'az bai san da labarin fara soyayyar Hadeeya da Zeid ba sai da ya ji wai za'a kai ku??i gidansu Hadeeya, yayi mamaki sosai kuma daya tuntu?i Zeid da maganar ya nuna masa kawai ya share wasa ne fa, amma a ranar da aka tabbatar masa an kai har ya ga hotunansu a status ??in abokansu sai ya sake mamaki sosai, amma tunda ya fahimci ba'a son sa da maganar ne sai ya yi kamar bai sake ji ba. Zeid kuma a ganinshi Mu'az baya sonshi da Hadeeya ne tun farko, shiyasa yake ganin zai iya yi masa bu)?ulun tona masa asiri a rabashi da ita, shiyasa yasa aka gaggauta komai kafin ya farga har ya tura ku??inshi, a yanzu kuma ya san ya gama sace zuciyar Hadeeya da kalamai da nunamata )?ololuwar soyayyar da ba zata iya rayuwa babu shi ba. Ita kanta Hadeeya sai yanzu take jin tana so, inda Ardiya ba dan ta so ba akayi hakan, dan ita ta so ta samu Mu'az, amla da Hadeeyar ta ce uta fa ga wanda take so yanzu kula ubanta ya goya mata baya sai t zuba musu idanu kawai, a yanzu harinta na gaba Hameeda ce, gaba??aya za ta saita makamanta ta tsaya tsayin daka har sai ta ga ta samu wanda ya fi mijin da Hadeeyar ta kawo mata a matsayin suruki.

Kwanan Saleema biyar a gidan Lubna ta dawo gida, tana so ta ma mahaifinta maganar ta koma makaranta, saidai tsoron abinda zai faru ya hanata fa??a, dan bata manta dukan da ta sha ba har saida ta yi jinya a ??akin Mamanta. Dan haka kullum take zaune ??aki da litattafanta tana karatu wani lokaci kuma da Al)?ur'aninta.




*Bayan wata biyu*



Ba tare da mamaki ya bar fuskarta ba ta ??auki katin da ta gani a ?bar jakar kyauta da aka bata tun masarauta, wacce tunda ta zo ita dai bata bu??a ba mahaifiyarta ce ta ga abinda ke ciki kula ta mayar, yanzun ma tana canzawa kayanta wurin zama ne ta ga katin, zaro idanu tayi tace "Lahhh! Wallahi lambar Maman nan ce sarauniya."

Jujjuyawa ta fara yi da niyyar ??aukar waya ta kira, sai kuma ta tuna ranbonta da waya tun ranar da Mu'az ya dinga kiranta tana kashewa har ta kashe wayar gaba??aya, dama ba damunta tayi ba shiyasa bata kuma damuwa da ita ba tunda ta kai ta aje, da sauri ta nufi kayan Mamanta ta shiga binciken neman wayar, tana ganinta ta ??auka da sauri ta fito falon tana )?walawa Hamdeeya kira. A tsakiyarsu Ardiya ta sameta da )?awayenta sun cika falon da kaya saboda za su je gyaran ??aki, tsaye tayi ta mata alama da hannu tace "Zo."

Ma)?ale kafa??a tayi alamar ba zata zo ba, harara ta dalla mata tace "Za ki zo ko saina takaki?"

Tana turo baki ta taso ta nufota Ardiya kuma ta harari Saleema, hannunta ta kama zasu fita farfajiya, daf da zasu fita wata gogaggiya kuma wayayyar] ar )?walisar mata ta shigo ??akin, )?amshin turarenta daya daki hancin Saleema, daga sama har )?asa ta kalli yanayin shigarta da suturarta mai tsadar gaske, irin ajin matar da shan )?amshi, dole ta tabbatar babbar mace ce, kauce mata tayi ta fara wucewa tana gaisheta a ladabce, a yatsine ta amsa mata wanda hakan ya ma Saleema zafi, duba da ba wasu shekaru ne a kanta, ba zata fi ashirin da bakwai zuwa da takwas ba, girma ko dukiya a ganinta ba su zaisa ta wula)?antata ba, sharewa kawai tayi ta fita a ??akin dan ba ita ce gabanta ba.

Ardiya na ganin amaryar gwamna Alhaji Nasir ta mi)?e tana wasar baki da mata sannu da zuwa, ??an murmushi kawai ta mata amma ba ta amsa ba, duk matan nan dake ??akin suna ta hayaniyarsu suna kuma gaisheta ba wanda ta amsa ba, kallon Ardiya kawai tayi a sanyaye a kuma sha)?e tace "An kawo kayan?"

Da sauri Ardiya ta juya kan kujerar data tashi ta ??auko ledojin guda biyu tace "An kawo, gasu ma, duba ki gani Madame."

A yatsine tace mata "Karki damu, ina sauri ne, dreba na jirana."

Take mata baya Ardiya ta yi har suka fita a farfajiyar tamkar wacce ke maula a wajenta sam ta manta da na ta ajin da kuma wayewarta.

Saleema na tsaye tana jiran Hamdeeya da ta aika siyo mata kati matar ta fita, da kallo kawai ta bita kafin ta ??auke kai sanda jami'i biyu suka take mata baya sai mace ??aya ita ma jami'a ga kuma ?bar abi yarima a sha ki??a. Tana nan tsaye Hamdeeya ta kawo mata sa)?on ta kar?a ta koma ciki, zaune tayi a tsanake ta shiga saka katin har ta gama sannan ta shiga saka lambaobin tana jin gabanta na faduwa sakamakon kiran da za ta aikawa wannan babbar lalba ta babbar mace.

Sosai ta )?ame tana jiran a ??aga kamar wacce za ta ??auke numfashi, saida wayar ta yi kamar za ta yanke aka ??aga, a hakan ma dan an kira )?aramar wayar sarauniya Ramlat ce, alamu ne na wanda ya kira makusancinta ne sosai, dan ahalinta kadai take ba wannan lamba, da ta ga ba)?uwar lamba sai ta ??aga dan tasan duk yadda aka yi ita ce ta bayar da lambar ko kuma wani ahalinta ne ya kira da wata lambar. A matu)?ar nutse ta fara da "Assalama alaikum."

A tausashe, a rarraba ta amsa mata da "Wa...alaiki..salam."

Numfashi Saleema ta sauke tana sakin murmushi ta ma rasa me za ta ce da jin wannan murya, abun mamaki da bata taba tsammani ba sai ta ji matar tace "Saleema, ke ce?"

Fada??a fara'arta tayi tace "E, ni ce, barka ranki shi da??e."

A yanzun sai ta ji yanyin maganarta ya canza, ma'ana daga da)?ilen nan zuwa sauri sauri ka??an tace "Saleema, me yasa ba ki kirani tun tuni ba? Na yi ta dakon kiranki amma shiru, kina lafiya?"

A tusashe da ladabi tace "Lafiya lau, a gafarceni, waya ne bana Abbana baya so na ri)?e sai yanzu ya yarda."

Tana )?arashe fa??a ta rintse idanu sakamakon )?aryar da tayi, a ganinta ta ce bata ga lambar ba sai yanzu kamar bata daraja kyautar da ta mata bane, sai dai abunda Saleema bata sani ba hakan ma da ta yi )?arawa kanta girma da kima tayi da kuma kankaro mutumcin mahaifinta har take ganin jajircewarsa akan tarbiyar yaranshi. Cike da jin dadi tace "Hakan ya yi kyau, kuma ina goyon bayansa."

Ba wata hira suka yi mai tsayi ba, illa dai daga )?arshe kafin suyi sallama sarauniya Ramlat ta nemi Saleema da cewa "?wata, muna barar addu'arki, kada ki manta da mu a cikin addu'o'inki, Allah ya yaye mana matsalolinmu."

Cike da tabbaci Saleema tace" In sha Allah ranki shi da..."

Katseta tayi da" A'a, ki kirani da Ummi, nima Umminki ce."

Jinjina kai tayi tace" To Ummi, in sha Allah, Allah ya yaye duka damuwa."

Da haka sukayi sallama Saleema na mamakin matsalar da matar ta ambata, wace irin matsala kuma? Suna gidan sarautar? Ba rashin ci, ba ta sha, ga mulki da iko a hannu, ga dukiya daidai gwargwado, ga hadimai zagaye da su wanda ko wanka sai ka so ne za ka yi saboda kasancewarka ??an adam, to me ye zai damesu a rayuwa kuma? (wata ??aukakar matsala a rayuwa, rayauwar talauci in da godiyr Allah da wadatar zuci da??i gareta, Allah ka bamu wadatar zuci da godiya a gareka).


*Bayan* sallah magriba Mamanta ta dawo a gajiye, kayan data shigo da su ta jawo tana dubawa, Safiya dake shafawa )?afafunta mai bayan wankan da tayi ta kalleta tace "Ki ware mana leshen nan daban da safe sai ki kai mana ??inki."

Kallonta Saleema tayi tace" Mama an samu ne?"

Cike da gajiya tace" Na sameshi da )?yar."

Da ??an mamaki tace" To amma Mama ina zamu ??inki yanzu? Kayan da zamu saka nan da kwana uku?"

Murmushi tayi tace" Ba kwana uku ba, biyu ne, krki damu kanki da wannan, ban zo gidan nan ba saida Lubna ta ha??ani da wani mai ??inkinta, kuma ya tabbatar a kai masa za'a samu."

Turo baki tayi tace" Allah yasa kar ya ?ata mana lokaci, dan ni bana juran ?acin rai daga ma??inka saboda abu ne da ni ma zan iya yi, dama ce kawai ban samu ba."

Murmushi kawai Safiya ta sake yi ba ta ce mata komai ba, gu??ar amaryar data kara??e gidan yasa suka kalli juna Safiya tace" Ki tashi ku tafi, ina ga wanka ne zasu tafi."

Girgiza kai tayi tace" Um um Mama, a dawo lafiya."

Da sauri Safiya ta )?arasa shiryawa ta bi bayan masu tafiya ta bar Saleema a gidan, ta riga da ta yi niyya ne ba zata halarci komai na bikin ba tunda ta ji Zeid ne zai auri Hadeeya, ta san dole zata iya ha??uwa da Mu'az, ita kuma mantawa take so tayi da shi na har abada, duk da hakan ma na neman gagararta, amma dai za ta koya wa kanta )?arfi da yaji.

Ka??aixin da ya yi yawa a ??akin yasa baccin ??aukarta a gadon mahaifiyar na ta, Safiya ma na dawowa ta sameta bata tasheta ba, saida ta sake watsa ruwa tayi sallah isha'i da ta samesu a hanya tayi shaf'i da wutiri, tana tsaye gaban madubi tana ??aure gashinta da )?aramin ribom ya turo )?ofar ??akin ya shigo, ta madubi ta dinga kallonshi har saida ya isa kusanta.

Ba tare da tunanin komai ba ya ri)?o )?ugunta ya kwanta a gadon bayanta ya lumshe idanu, da sauri ta shiga ?am?are jikinta tana hangen inda Saleema ke kwance ta madubi, cikin ra??a tace "Sakeni mana, idan fa ta tashi ta ganmu?"

Cikin sanyayyar murya yace "To sai me, ba mijinki bane ni?"

Da )?arfi ta )?wace kanta tana juyowa ta fuskanceshi tace "Ai dai da kunya, ko Hamdeeya ba zan so ta ganmu haka ba bare Saleema data mallaki..."

Tsurawa Saleema idanu tayi da ta gyara kwanciyarta, juyawa yayi shima ya kalli Saleema sai kuma ya kalleta yace "Ke fa yarinyar nan har yanzu Baby kike ??aukarta ko? To da tayi aure ya zakiyi?"

A ta)?aice ta )?arasa ??aure gashinta tace "Na yi laifi ne? Ita ??aya gareni."

Hannunta ya kama da niyyar janta su fita yace "Muje ??akina to."

"Me zan maka?" Ta fa??a tana kallonshi, janta yayi yana fa??in "Muje zaki gani."

Binshi kawai tayi dan ta san kwanan zancen, kamar yadda shima yau ??in yayi niyya idan har bata biyoshi ba to ko zasu yi abun kunya a gaban ?bar da take ??auka Baby.



*Washe Gari*


Duk kai da kawowar da ake gidan bai hanata shieyawarta tsaf ba ta fita dan kai ??inkinta da na Mamanta na ankon leshen da zasuyi iya su kawai gidan bayan wasu ankon da duk mahaifinsu ya yi wanda Saleema har yau take jin tamkar ta masa kuka, dan kuwa duk wanda aka fito Ardiya tqaye take ta fara amsar ku??in na ta dana yaranta, hakan yake sa shi ita ma ya bata da mahaifiyarta dan ba zai iya waresu ba, a )?alla ita dai ranar da ya basu ku??in ankon dana ??inki da sauran bu)?atunsu na shigar bikin iya su biyar kawai ban da Hadeeya dake amaryar saida ya zube musu ku??i tsabarsu har jaka ??ari hu??u, saida ta masa )?wallan tausayi ganin hidimar ba ita kenan ba fa. Yanzu haka wannan leshen ita kawai da Mamanta saba'in da biyar ya basu, kai ita dai gaskiya tana tausayawa maza. ???i

Kwatancen da Safiya ta ma drebansu tun jiya ya dinga bi har saida Saleema ta fara shinshino anya kuwa ba shagon nan bane zai kaita? Ai kam tana ganin an ??auki layin ta tabbatar da zatonta, tunda ya faka motar take le)?en shagon kawai sai take jin kunyar shiga saboda dalilin maganar da sukayi ne ta ce zata koyi ??inki har Abbanta ya daketa. Saida dreban ya juyo yace "Hajiar Alhaji nan ne fa."

Da sauri kamar wacce ya gaurawa mari tace "Uhum." Bu??e motar tayi a nutse ta ??auko kayan ta fito sannan ta rufe )?ofar, )?etara titin tayi ta shigo shagon da sallama, ganin babu Alhudahuda yasa ta sauke ajiyar zuciya ta )?arasa shiga ciki.

?aya a cikin matasan dake ??inki shagon ta samu kuma wanda sukayi al)?awari da Mamanta, dan haka ba ta tsaya komai ba tana mi)?awa ta biyashi rabin ku??inshi ta tafi da tabbaci jibi ta dawo ta kar?a, kamaar wacce bata da gaskiya haka ta yi saurin komawa mota, tana shiga ta rufe kenan ta ga tsayawar motonshi zai shiga shagon, kamar dama shine bata son gani sai kawai ta sauke ajiyar zuciya, ba ta dain kallonshi ba har ya shiga shagon su kuma suka bar wurin.



*Ranar Kamu*


A jigace ta zauna kan kujerar robar tana kallon yadda ta gama tsara wurin zaman amarya da ango, murmushi tayi dan ita kanta tayi mamakin yadda ta iya shirya wurin yayi kyau haka, ba wai ziga kanta take ba, ta tabbatar yayine tunda har Ardiya da ta sakata aikin ta ce yayi kyau sannan ta ce mata sannu da aiki, da baiyi ba tun a fuska za ta gane. Ta gaji sosai, dan lamarin bikin na gidansu mamaki yake bata, shekaran jiya an yi Guitar wanda hakan al'adar Ardiya ne kasancewarta buzuwa, haka aka kwana ana ka??a jita mata da maza ana rawa da tsalle tsalle da iface iface (kwate tarhanine, tagmasss???i). Jiya kuma partyn )?auyawa aka yi, haka gidan nan ya hautsine mata suka dinga canza halittarsu da shigarsu suka zama )?auyawa kata'in, yau kuma ga kamu wanda shine )?arshe dan gobe za'a ??aura aure kowa ma ya huta.

Hameeda ce ta fito daga ?angaren Abbansu, ganin wurin yasa ta waro idanu tace "Wow, Saleema wai da gaske ke kikayi?"

A )?asan ma)?oshi ta amsa mata da "Um." Da sauri ta koma inda ta fito tana fa??in "Kai ku fito an gyara wurin."

Jim ka??an ?ban dandazon ?ban matan dake ciki suka dinga fitowa, mi)?ewa Saleema tayi ta shiga falonsu dan ta samu ta shirya, sam bata sakewa a cikin mutane, biki ko na gidansu ne sai ta dinga ??ari ??ari da kunya. Tunda ta shiga ciki bata fito ba saida ta yi sallah magriba, lokacin ita da kanta tana jin irin hayaniyar dake tashi ta san mutanen sun gama hallara, lokacin ne ta cire hijabin ta gyara ??aurin ??an kwalinta sannan ta saka takalminta ta fito bayan ta rufe ??akin dan Mamanta na waje.

Tana fitowa falo suka ci karo da Ardiya ??auke da )?aton cake, da sauri tace "Yawwa Saleema kar?i, fitar musu da shi dan Allah."

Kar?a tayi tana jinjina kai, tana fitowa farfajiyar ta tsaya cak! Tana kallon farfajiyar, mutane ne duk zazzaune sai ?ban mata tsakiyar fili ana ta dabsar rawa, wani banbara)?wai ta ji kanta da bata sako mayafi ba, sai ta ji ba zata iya shiga filin da kayan jikinta ba, riga da siket ??in na leshe da suka matu)?ar amsar jikinta suka fito mata cas a jiki, duk da ba ta kwalliya ba kuma ??aurin kallabin ma a sau)?a)?e tayi shi, amma sai tayi kyau ga kuma gyaran da aka fara mata tun lokacin saka ranar aurenta, dake ya kar?eta musamman sabulun da har yanzu da shi suke wanka ita da Mamanta, sai take ta )?yalli ita ma kamar wata amaryar.

Juyawa tayi da sauri da niyyar komawa ??aki ta ??auko hijabi dan ba gyale gareta ba, sai kuma Ardiya ta fito tare da )?awayenta, ganinta yasa ta fa??in "Saleema baki kai ba har yanzu? Me kike jira?"

A raunane tace "Aunty hijabi zan ??auko."

Cike da takaici Ardiya tace "Hijabinme ke kuwa? Bikin )?anwarki ne fa, wa ya damu da ke a nan bare ya cinyeki."

A sa?ule ta juya ta tunkari tsakiyar filin hannayenta har rawa suke saboda akwai maza sosai a wurin suna ta shewar ganin?ban mata, da harara Ardiya ta bita tana fa??in "Kidahumar banza."

?aga a cikin )?awayenta ne tace "Wai da gaske mijinki ne ya haifeta?"

Yatsina baki tayi tace "Wai ba." Tsaki ta ja tare da )?arasawa su la filin taron suka samu wuri suka zauna. Tunda ta shiga filin idanun ma fi yawan mutane ya koma kanta, musamman da babu wanda zai ce ya ta?a ganinta babu hijabi a wurin sai yau, sai abun ya zama sabo a gurin su kansu da ita kanta, insa wanda suka samu damar ganin bayanta kuma suke sauke idanuwansu akan )?ugunta da ya matu)?ar basu sha'awa, dayawa qai suka shiga tunanin dama haka take yarinyar nan? Amma take tauye kanta ta hanyar rufe jikinta ko ina, wasu kuma na ganin ashe da babban dalilin da yasa take rufe jikinta, dan kuwa )?ugunta ba iya fa??i kawai gareshi ba har da kakkauran ??auwawun da suka isa wadatar mai kallonsu sake rinjayar ragamar idanun su ci gaba da kallonta.

Daga cikin masu kallon nan har da Mu'az da yau dai Zeid da kanshi ya lalla?oshi ya zo kamun nan, ya jima daga zaunen nan yana tsarkake zati da buwayar Allah, ya jima yana ambaton Allah ??aya, haka kuma ya jima yana godewa Allah da ya sa bai ta?a ganin haka kafin yau ba, ya kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login