Showing 144001 words to 147000 words out of 193749 words

Chapter 49 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4407

baki ka??an, cikin sanyayyan salo ya ri)?o )?ugunta ya ha??ata da jikinshi, hakan ya haifar musu da kusanci sosai har numfashinsu na gauraya, goshinshi ya ??ora akan nata goshin, hakan yasa hancinsu ma ha??ewa wuri ??aya, rusuna idanunta tayi saboda kunya data kamata dan cikin idanunta yake kallo.

Cikin fitar da kowace kalma yace " *Ke zam-zam ??ita ce, ba iya waraka na samu ta dalilinki ba, hada tsadadden farin cikin da dukiya da matsayi basu sama min ba*, dan haka kika ci wannan sunan mai girma wato *zam-zam*."

Ha??a bakinshi yayi da nata ya sumbata har saida ya lashe man data shafa sannan ya saki ya sake kallonta yace" Ko dan darare biyu da suka gabata, ai dole ki ci sunan nan *Leemat*."

Hannunshi na hagu data ciza ya nuna mata yace" Ga kuma wannan shaidar da na samu daga kyakyawan bakinki."

Da fari hannun ta kalla, duk da yana da duhun fata amma ta kan iya hango shatin ha)?oranta wajen har ya ??an fasa, amma kuma kunyar daya tsumbulata ciki yasa ta fa??awa jikinshi ta nutsa kanta a cikin babbar rigarshi, murmushi ya saki tare da shafa bayanta ya karkata kanshi ka??an ya ra??a mata a kunne" Kenan ni ban cancanci wani sunan ba sai *mugun sarki?*"

Fashewa tayi da dariya ta sake tusa kanta a jikinshi, shima ?bar dariyar yayi yace" Uhum! Ina jinki, saka min sunana ko kuma mu koma ??aki yanzun nan."

Cikin shagwa?a ta shiga diddira )?afafunta tace" To ba na saka maka ba tun ma kafin na zo gidan nan."

Tsareta yayi da idanu alamar yana jiran )?arin bayani, turo baki tayi idanunta )?asa tace" Ummmm! *?awisu*."

Waina idanunshi yayi yace" Me ye ??awisu kuma?"

Cike da yarinta ta shiga gaba wuyan rigarshi tana fa??in" To ai ??awisu halitta ce mai daraja, kuma kaga tana da wuyar samu a ko ina, shiyasa ma sai wanda suka gawurta suke iya kiwonta, sannan ga kyau da kwalliya..."

Kallon cikin idanunshi tayi tana farin da ya sakashi )?ura mata idanu tamkar ya cinye fuskarta ya huta tace" To ni da na sameka bayan ana goranta min cewa na jima banyi aure ba, ka ga dole ka zama *??awisuna*, duk da ana cewa budurwa ne allurar cikin ruwa, amma ni kaine *allurata* da Allah ya bani nasarar dam)?arka da hannu bibbiyu."

Wani faffa??an murmushi yayi yace" *Deeyah*, kina so na ci gaba da mulkin garin nan kuwa?"

Jinjina kai tayi a snyaye tace" Ina so, ko dan a kirani da *sarauniyarka*."

Girgza mata kai yayi yace" Ki daina fasa min kai haka, za ki sa a kasa gane wannan sarkin, oya muje, yanzu na san ana jiranmu a falon Ummina."

Rusunawa tayi gwanin ban sha'awa tare da cewa" Yadda sarkina ya so."

Rumgumata yayi jikinta a nutse suka shiga takawa harsuka isa bakin )?ofa, hannu yasa ya sake jawo mata hular ita kuma tana fa??in" Wai shi sarki dole ne ya iya wannan takon )?asaitar?"

Ba tare daya kalleta ba yace" A jini yake, ban fahimci haka ba saida na mallaki hankalina."

Cike da tsokana tace" Amma dai yau zan matsa maka )?afafun nan, dan nasan suna maka ciwo."

Murmushin daya saki mai ??an )?arfi yasa dogaran dake tsaye wajen corridor suka farga da sarki na fitowa, suna isowa suka rusuna suka gaisheshi tare da bu??e musu )?ofar, Saleema ce ta fara shigewa dan ya saketa sannan shi ma ya shige.

Tunda suka doso falon bayan jakadiya ta sanar da sa)?on shigowar mai martaba uban talakawa Saleema ta sake daidaita tafiyarta da jikinta sosai, karatun da sukeyi da dattijuwar jakadiyar nan ne har yanzu bai fita a kunnenta ba, ta yarda cewa nuna ragwantaka a farkon lamarin nan da kuma raki kan sa wa ya ficewa namiji a rai har ya dinga shakkar ta?aka, dan hakane ita duk wahalar da take ji yayin al'amarin nan da zaran an ida take iya )?o)?arinta wajen nuna ba abinda ke mata ciwo, amma har yanzu daga )?asanta har mararta ciwo suke, dan tana tare da rashin sabo a fanni, Allah Allah take su rabu ta koma ??akinta ta sake shigewa ruwan ??umi dan daga jiya zuwa yau ta fahimci bata da masoya sama da su.

Kanta sadde yake yayin da yake ri)?e da hannunta, abun mamaki shine duka wa??anda ke zaune kan kujera zubewa sukayi )?asa duk da bata ga fuskokinsu ba, ba yadda suka iya girma ne kuma Allah ya bashi, idan a ke?e suke zasu iya zamansu, amma tunda a cikin mutane ne har iyayen kansu su kan rusuna ne dan girmama wanda Allah ma ya girmama ta hanyar jarabtarshi da mulki. Gimbiya Ramlat kanta zaune take a kan wani darduma da ke zagaye da wani )?ton fillow irin wanda ake ??ora )?afafu, inda ta ga hannun gimbiya Ramlat na nuni tare da cewa "Zauna ?bata."

A hankali ya saketa ta zauna kusa da ita duk da )?asa ta so zama amma ta ri)?eta, ta dai ji ya zauna amma ba ta san ina ne ba, gaisuwa ce ta sarakai kowa abun a jiinsa yake, hakan yasa iya gaisuwar ba ta wuce "Barka da safiya." Sai kuma )?annenshi da suke gaisheshi da "Allah ja zamanin mai mara??awa."

Ta hanyar lumshe idanu da yatsu biyu kawai yake amsawa, saida falon yayi shiru na wasu da)?i)?u kafin gimbiya Ramlat tace "?wata, nan duka ahalinki ne, zan iya bu??e fuskarki dan ki ga ?ban uwanki su ma su ganki?"

Shiru tayi ba ta ce komai ba cike da kunya, a hankali gimbiya Ramlat ta ??an ja hularta baya ka??an fuskarta ta fito, murmushi ta sakar mata ta nuna mata maza da matan da kuma iuayensu dake zazzaune kasancewar litinin ce kuma ba)?uwa ce ita akwai bu)?atar su san junansu tace "Ga su, sai ku gabatar mata da kanku."

Wanda ya fara nuna kanshi ne yace "Abdul Karim, ni nake bi wa mai martaba sarkin mara??awa."

Nuna wata kyakyawar matashiya yayi yace "Ga matata..."

Cikin nutsuwa da sanyin murya matashiyar ta ??ago kai tace "Rufaida, ina miki barka da zuwa ahalin masu adalci."

Murmushi Saleema ta sakar mata bayan ta mata kallo ??aya ta kalli wata matashiya ita ma data nuna kanta tace "Ni kuma Sarah, ina miki barka."

Wata matashiya ce ita ma ta yatsina fuska ta kalli Saleema tace "Izza, Izzatu, barka." Ta )?arashe tana hararenta sama da )?asa. Tsaf a idanun Saleema, hakan yasa ta shiga taitayinta da tunanin ita kuma me ye tsakaninta da ita to? Daga fara ganin juna yanzu sai harara.

...Da haka suka dinga gabatar da kansu har )?ananan, saida suka gama tsaf har iyayen kafin Saleema ta sadda kanta a ta)?aice tace "Nagode muku."

Daga haka ba ta sake cewa komai ba, shiru ne ??akin ya ratsa inda gimbiya Kubra da ?barta ke mamakin iskanci irin na wannan ?bar talakawa, su yanzu duk da ba dan ita suka zo ba, amma dai hada dalilin ganinta, shine zata amsa musu duk gabatarwar nan da wai *nagode muku*! Gyaran muryar da Abdus-samad yayi a sanyaye ne yace "Amm..."

Har gimbiya Kubra da ba haka ranta ke so ba dole ta sake sadda kanta duk qka )?ara nutsuwa dan jin bayaninshi, ci gaba yayi da fa??in "Sakamakon ba)?in da har yanzu ke kai da kawowa, ba zamu samu damar tattaunawa ba kamar yadda aka saba..."

Shiru yayi yana sauke numfashi a hankali kafin yace "Zamu ha??u sati na sama in sha Allah."

A tsanake ya shiga )?o)?arin tashi, shiru ??akin ya sake ??auka kowa kanshi )?asa, saida ta ji mi)?ewarsa da kyau har ya ??an fara takun nan nasa dake saka ta jin tausayinshi ta ??aga kanta a hankali saidai ta fi ??aga idanunta fiye da kanta, hakan uasa idanunsu ha??ewa dana juna.

Da idanunshi ya mata alamar _"Na fita."_

Lumshe idanunta ta fara yi alamar _"To."_ Sannan ta warasu sosai sama, sai ta ??an daga yatsarta manuniya ta nunashi alamar _" Allah ya tsare min."_ Nunashi da tayi ya tabbatar masa _" Shi. "_ Kenan take nufi, a sau)?a)?e ya lumshe idanu sannan ya )?arasa fita daga falon ya bi ta hanyar da yanzu dogarai na nan suna jiran fitowarshi.

Saida ya fita Izzatu ta mi)?e da sauri ba girmamawa ta kalli mahaifiyarta gimbiya Kubra tace "Mama ni zan shiga ciki, sai kin taho."

Juyawa tayi ta tafiyarta, a hankali gimbiya Kubra ta bi bayanta kafin da ??ai-??aya duk su bar falon, daga Saleema sai gimbiya Ramlat kadai aka bari, hakan yasa gimbiya Ramlat kamo hannayen Saleema cikin nutsuwa tace "Saleema, ya ba)?unta? Fatan dai kina jin da??in zaman gidan namu?"

Murmushin ya)?e kawai tayi, yo ita gidan da ko gama sanin gabanshi ba ta yi ba, har yanzu daga falonta zuwa ??akinshi ka??ai ta sani, bayan nan ko a yankata ba za ta kai kanta ??akin da ake mata gyaran jiki ba zuwa ??akinta, gida uwa ??akin kurege, can )?ofa nan ??aki, a da tana jin ana cewa gidan sarki )?ofa takwas ke akwai ta shiga kawai, amma yanzu da ta shigo sai take tunanin anya ba ta fi haka ba? Ta yiwu kawai shaci-fa??i ne na mutane ko kuma dan a rikita munafukai.

Ita ma murmushin tayi ta jinjina hannayenta da kyau tace "Saleema, akwai abinda na so fa??a miki tun ranar da aka kawoki, ama ban samu dama ba, shin zamu iya yin magana yanzu?"

A nutse kanta sadde tace "Ranki shi da??e zamu iya yin magana, ba sai kin ji son ra'ayina ba."

Murmushi tayi tace "Hakane, amma da fari ki daina ce min ranki shi da??e, ko dai baki ??aukeni tamkar uwa bane?"

A hankali ta girgiza kanta tace "Tamkar uwa nake kallonki, a gafarceni, zan kiyaye in sha Allah."

Jinjina kai tayi tana murmushi tace "Saleema, kinga nan gidan sarauta ne, babu abinda muka rasa na daga dukiya ko iko, daidai gwargwado Allah ya mallaka mana, tun fil'azal kakannin wannan masarauta ?ban kasuwa ne da aka sansu akan harkarsu, kuma ?ba?ba da jikoki basu yada wannan gadon ba, babu abinda zaki nema a nan ki rasa, sai dai akwai abu ??aya da bamu da shi a gidan nan."

A hankali ta so ??aga kanta ta kalleta sai kuma ta )?i hakan saboda suna kusa ne sosai, lura da haka yasa gimbiya Ramlat ci gaba da fa??in" Hakane Saleema, akwai abu ??aya da ba lallai ki sameshi a nan ba, wannan abun shine *ha??in kai* na ?ban uwa, kin gani Alhamdulillah muna da yawa, sai dai yawan na taron tsintsiya ne ba shara, abu alkairi ba zai sameka ka waiga ka ga ??an uwanka na gidan nan a kusa da kai ba, Saleema wasu mutane na ??aukar duniyar nan da zafi sosai, mulki, mulki sai ya sa ka nesanta daga ??an uwanka, kinga mijinki...?"

Ta fa??a da yanayin tambaya ta tsareta da idanu, sadda kanta tayi cike da kunya ta ??an ??aga kai ka??an, ??orawa tayi da" Karki ??auka yana cikin farin ciki ne da wannan nauyi dake kansa, ba kuma zai fi kowa arziki ko matsayi bane, Saleema a halin yanzu mijinki tamkar *tsokar naman da aka jefata a tsakiyar kuraye ne*, a lissafinki ya zasu farauci wannan tsokar?"

??oyayyen numfashi Saleema ta sauke kafin tace" Wawaf da zasu daka a kanta abun )?ayatarwa ne wajen kallo, sai dai abun tausayi ne ga su kurayen, dan kuwa duk kurar da ta samu ba zata anfaneta da maganin yunwa ba, bayan cutar da kawunansu da zasuyi, dan akwai yiwuwar su kashe kawunansu wajen ??aukar wannan tsokar."

Murmushi tayi tace" Da kyau Saleema, to wannan kujerar da mijinki ke zaune a kai ita ce tsokar naman, kinga kuwa ba za'a sameta ba sai babu kowa a kai, idan kuma ya zama akwai wani mahaluki a kant? Hakan yasa suke kawar da duk wanda ya nemi shan gabansu."

Ajiyar zuciya ta sauke kamar za ta yi kuka ta sassauta murya sosai tace" Saleema, abu biyu zan fa??a miki da zai taimaka miki wajen zamanki lafiya a gidan nan, na farko ri)?e sirrinki, duk tsanani duk wuya kada ki ta?a fa??awa wani abinda ya shafeki ko ya shafi ke da mijinki, komai girman mutum ko matsayinsa a gun mijinki, dan wasu zasu iya anfanin da matsayinsu a gareshi su shiga jikinki, idan bakiyi sannu ba za'a dinga tuntu?arki rayuwarki ko zamanki da mai gidanki, ta haka kuma za'a samu )?ofar da za'a shiga a cutar daku."

Numfasawa tayi tace" Na biyu kuma shine, ba kowa ne dake miki dariya ba kema zaki yage masa baki, wani dariyarsa iya la??ansa ne kawai, Saleema a cikin mutane sama da ??ari da zaki zauna da su, bai fi kaso talatin ba da zaki iya samun dariyar gaskiya daga garesu ba, sauran duk za'a miki ne dan kawai ba yadda zasuyi, idan kika zama mai lura da saka idanu zaki fahimci haka, amma sai kin zama mai takatsantsan da lamarin kowa a gidan nan, abu na )?arshe da zan fa??amiki shine..."

Numfashi ta ja ta sauke sannan tace" Kada ki zama mai bawa hadiman gidan nan yarda akan abinda ya shafeki da kula wanda ya shafi sarkinki, bakinki da su ya zama abinda kawai su ne zasu iya yi miki, amma in dai zaki iya da kanki to kiyi, Saleema... *kada ki yarda hadimai ne zasu gyara miki makwancinki*, bawai zan hanaki hutawa ba ko hanaki kiyi ikonki yadda ya dace a matsayinki na *matar sarki*, amma dai a nan kusa ya kamata ki zama mai kula sosai, domin kuwa nima na yi irin wannan sakacin, wanda shi ya kaini ga halin da muka samu kanmu a ciki har ya zama silar shigowarki rayuwarmu..."

?an tsagaitawa tayi kafin tace" Ruwan wankansa, takalmin )?afarsa, da ku??in da suka fito daga gareshi, da su aka ha??a aka masa sihirin da ya fi shekara takwas dashi a jiki..."

Hawaye ne suka wanke mata fuska tasa hannu tana sharewa tana ci gaba da fa??in" Ba dan iyayena masu hali bane, da mun yi bara saboda larurar *Abdus-samad* sai da na dinga siyan da kadarori dan na sama mishi lafiya, ba dan Allah ya azurtamu da ka??autashi shi ka??ai ba, da mun yi shirka kamar yadda wasu malaman ke nuna mana sai ta hakane zai samu lafiya, shiyasa na ??auki lamarinki da mahimmanci Saleema, shekarun da aka ??auka da ku??a??en da aka kashe, ashe maganin na nan kusa da mu ga wata yarinyar da ba wanda ya santa...abun al'ajabi."

Sake ri)?e hannayenta tayi sosai tace" Ki zama mai kula akan komai Saleema, dan wannan mulkin da kika gani wasu a shirye suke da su *raba mijinki da rayuwarsa* ma."

A tsorace Saleema ta kalleta, ha)?i)?a maganganunta sun shigeta sosai kuma ta ??auki aniyar kiyayewa, sai dai maganar rasa rayuwar nan yasa ta jin fa??uwar gaba har ta fara hasasho idan fa hakan ta faru da gaske? Idan fa aka yi nasara a kansu kenan? Za ta zama mai *takabarsa* kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ta ambata a ranta, wane wace irin rayuwa ce? Me ye a mulkin da za'a so raba wani da ransa saboda shi? Sosai ta shiga ru??ani da kuma tsoron zaman gidan, dan gaba??aya ji take tamkar ko numfashinta da zai fito daga ruhinta akan idanun wasu zia sauka tsabar saka ido, tsoro matu)?a ta ji ya kamata har ta gagara tashi ta koma inda take, ji take ma kamar ba lallai ta kai ?angaren na ta ba.

A ??an rikice Saleema ta kalleta tace " *Umma*, to a ina suke cin abinci?"

Da rashin fahimtar kalamanta tace "Su wai? Kowa a ?angarensa, sai dai wasu lokuta mu kan ha??u gaba??aya a ci abinci, kuma haka tun mai martaba yana raye ne, har yanzu bamu daina ba, sai dai ba wani shau)?i a wajen cin abincin."

Saida ta ji ta dasa aya sannan tace "Su nake nufi, yalla?ai mai martaba."

Kallon tsanake ta mata cike da jin ta birgeta, ashe fa Abdus-samad take nufi da su, hakan ya birgeta sosai, kuma duk da ba amsar tambayarta ta bata ba, bata katse mata numfashinta ba saida ta dire maganar sannan, hakan girmamawa ne daya samo asali daga lafiyayyar tarbiya, murmushi ta mata tace "Daga )?aramar madafa ake fidda mana abincinmu tare da na shi."

Jinjina kai Saleema tayi tace "Nagode Umma, kuma in sha Allah zan kiyaye duk abinda kika fa??amin."

Sakin hannayenta tayi tana fara'a tace "Nagode *sarauniyata*, za ki iya tafiya ?angarenki."

Jinjina kai tayi ta mi)?e a hankali, da sauri ta mi)?e tsaye ita ma tana sake ri)?e hannayenta tace "Uhyemmm! Kuma kina ji, Saleema ??ana ba waliyi bane bare na ce ba zai miki ba daidai ba, saidai duk yadda ranki zai ?ace game da shi idan ya miki ba daidai ba, dan na ro)?eki kada ki bari wasu su fahimci sa?aninku, zaki iya hushinki a ??aki dan kema ?bar adam ce, amma da kin fito waje ki nunawa kowa lafiya lau kuke zaune ta hanyar sakin walwalar fuskarki, dan kuwa sanin sa?anin naku shi zai bada damar da wasu zasu shiga tsakani dan a farra)?u."

Murmushi Saleema tayi tace" In sha Allah Umma, zan kiyaye."

Da fara'a a fuskarta tace" Allah ya miki albarka."

"Ameen." Ta fa??a tana rusunawa sannan ta juya ta )?ofar da suka shigo ta nan ta bi dan ta hakane za ta iya gane na ta ?angaren.




*Alhamdulillah.*
20/06/2022 ?? 22:08 - MOM LATEEF???i: ???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??
*BAIWATA*
???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ??A惙@?
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
=??? *[G. M. N. A]* =??? ??Id???g???


_Bismillahir rahamanir rahim_


_47_




Jakadiyar dake gabanta ta kalla a nutse bayan ta aje littafinta tace "Madafa nake son shiga, za ki iya yi min jagora?"

Rusunawa ta sake yi tace "Yadda kike so uwargijiyata."

A nutse ta mi)?e tsaye hakan yasa jakadiyar take mata baya, daga nan take nuna mata hanyar har suka isa madafar, ba kowa a ciki dan lokacin girkin rana bai yi ba, kula an riga da an gama na safe, hakan yasa Saleema kallonta tace" Ko zan iya ganin wa??anda suke iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login