Showing 105001 words to 108000 words out of 193749 words

Chapter 36 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4412

idan bata wanke kanta ba, cike da tausayawa Fareeda tace" Allah sarki! Ke kuma jarabawarki kenan? Karki damu ?bar uwa, ki ci gaba da addu'a watarana sai labari, in sha Allah mahaifinki zai amince ki koyi ??inki, ke dai ki yi ta masa biyayya."

Ajiyar zuciua Saleema ta sauke tace" In sha Allah, nagode sosai."

Da haka suka yanke wayar, suna gamawa kuma ta aje wayar ta tofa addu'a ta shafawa mahaifiyarta sannan ita ma ta kwanta gefe.


Fareeda ma na aje wayar ta shiga labartawa Mamanta dake kusanta, ita ma cike da tausayawa tace" Ikon Allah! Shi kuma haka yake? To Allah ya cika mata burinta."

A jimame Fareeda tace" Amee..." Ba ta )?arasa fa??a ba Huzeifa dake )?ofar ??akin tun sanda ta fara bada labarin ya tsaya yana sauraro sai yanzu ne ya shigo, a tare suka kalleshi Mamansu na amsa sallamar da yayi )?asa )?asa, mamaki ne ya lullu?e fuskarta na tunanin me ya kawoshi gidan yanzu a wannan daren? Duk da dai kusa suke sosai ba nisa, amma dai a yanzu da )?arfe goma da rabi ta wuce sai take mamaki dan bai ta?a haka ba.

Mi)?ewa Fareeda tayi ta fito tsakar gidan dan ko da ta ga yayi zaune ta san magana zasuyi, kuma a yadda ta ga fuskarshi da yanayinshi ta san ba lafiya ba. A nutse Maman ta kalleshi tace "Huzeifa lafiya? Daga ina kake yanzu cikin dare? Da fa rufe gida zamuyi yanzu, dan ma wannan ja'irin bai siyo min madarata bane ya koma siyowa."

Sadda kai ya sake yi muryarshi da amon ?acin rai sosai kuma a tausashe yace "Mama, yarinyar nan nema take ta kaini bango na aikata abinda za'a zageni, har yanzu Sharhasila ta kasa gane kara nake mata ina miki biyayya bane, ni fa na fara gajiya Mama."

Girgiza kai tayi tana mamakin yadda Sharhasila ke neman zubar da darajarta har su kai )?adamin da zasu kasa tan)?warashi daga ita har Sharhasila ??in, a nutse ta sake fa??in" Me ya faru kuma?"

Numfarfashi ya dinga saukexa yana tausar kanshi kafin yace" Mama, magani take ??auka na hana samun ciki, shine na gani na mata kawai take fa??amin ita ba ta tashi haihuwa yanzu ba, ita wai ba zan lalata mata )?uruciyarta ba tun yanzu..."

?agowa yayi ya kalleta ka??an yace" Mama ni fa niyyata na korata gidansu sannan na bar mata gidan."

Da sauri tace" A'a, kada kayi haka Huzeifa, kayi ha)?uri ka ji kamar yadda kake yi kullum, ka sake mata maganar cikin kakkausar murya, idan ba ta daina ba sai ka samu iyayen na ta ka fa??a musu, wata)?ila su su tsawata mata."

Saida ya gama )?ya)?yabta idanu kafin yace" Shikenan Mama, zan ci gaba da yi miki biyayya kamar yadda na ke yi kullum, fatana ita ma ta gyaru ta san cewa ni mijinta ne ya kamata *ta min ladabi*, amma abinda Sharhasila ke so shine ni na *mata ladabin*, abinda ba zai yiwu ba kuma."

Jinjina kai tayi tace" Allah ya maka albarka, Allah ya baka wanda zasu maka fiye da yadda ka min."

"Ameen." Ya fa??a yana shirin mi)?ewa, da kallo ta bishi har ya fita daga ??akin, Fareeda dake zaune tsakar gidan da wayarta ya tsaya yana kallo, ??agowa tayi ta kalleshi sai kuma ya juya kawai ya fice, ta?e baki tayi tana ayyana "In dai matar nan ce ta kasheka wallahi, gwara ma tun wuri ka gane Mama ba zata ta?a baka shawarar da za ta sama maka ?banci ba."




*Washe Gari*



Sosai Fareeda ta sake mamakin ganinshi da safiyar nan, musamman da ya )?ura mata idanu da alamar bakinshi akwai magana, amma kuma kamar mai tsoro ko shakkar furtawa, har suka gama gaisawa da Mama ya karya kumallo dan Sharhasila ta rigashi fita saboda haukan da ya sauke mata jiya, ko kwana basu yi gidan nan dan daya sake tuntu?arta kan maganar sai ta nemi yi mishi iskanci, dan haka kawai ya sauke mata kalar na shi haukan ya gwara kanta a bango ya mata mur)?usar tsiya, shine fa take ta hararenshi tana gunguni gari na wayewa ta bar masa gidan. Yana gama karyawa ya fito zai fita ya sake kallon Fareeda dake wanke kayan Mama kafin lokacin islamiyya ya ida ta tafi, saida ya yi hanyar fita yace "Ke zo nan."

Kallonshi tayi sai kuma ta ta?e baki ta aje wankin ta saka hijab ta bi bayanshi, shago ta saleshi har ya zauna kan kujera amma ya buga tagumi, a ladabce tace "Yaya gani."

Shiru yayi kuma bai kalleta ba kamar baisan da zuwanta ba, ya ??an jima kafin ya ??ago ya kalleta, cike da kakkawar da kai yace "Kirata zan yi magana da ita ne."

Da mamakin da ya jefata a ciki ta kalleshi da kyau tace "Wa fa Yaya?"

Wata harara ya watso mata da yanayin masifar da yarinyar can ta fara koya masa yace "Ban gane wa ba? Jiya ba ke na ji kunyi waya da ita ba?"

Kya?une fuska tayi alamar za ta fashe masa da kuka tace "Wallahi Yaya ni..." Sai kuma tayi alamar tuna wani abu da fuskarta sannan tace "Oho! Saleema?"

Harara ya wurga mata mai nuni da kin fahimta kenan sannan ya ??auke kai, murmushi tayi tace "Wayar na gida, bari in ??auko."

Bai ce mata )?ala ba har ta je ta dawo ta mi)?a masa wayar tace "Yaya ba ku??i a tawa, ko zaka kira da ta ka?"

Kar?a yayi yana jan tsaki ya ciro wayarshi a aljihu ya shiga loda lambobin Saleema, yana sakawa ya danna kira, jim ka??an ta fara )?arar dake nuni da kiran ya shiga, gabanshi ya ji ya fara fa??uwa haka kawai, hakan yasa shi ??aga kai ya kalli Fareeda dake tsaye ya mi)?a mata wayar daidai lokacin da Saleema ta ??aga ta yi shiru dan jin wa zaiyi magana.

Da sauri Fareeda ta masa alamu da "Ka yi magana."

Ha??e fuska yayi ua sake nuno mata wayar, girgiza masa kai ta sake yi tace "Yaya ka yi magana."

A ??an hassale yace "Ke ba'a son iskanci, kar?i."

Saleema da ta ji abinda aka ambata da mamaki daga ?angarenta tace "Me? Wanene kai? Me kuma na maka?"

Da sauri ya kalli wayar sannan ya kalli Fareeda ya wurga mata harara, da gudu ta fita a shagon dan zai iya katse kiran ya sha)?i wuyanta, ganin haka uasa shi ??ora wayar a kunne a tausashe yace "Hello!"

Cike da tsiwa tace "Uhum!"

Cikin rashin sanin abinda zai fa??a mata yace "Ba ki iya sallama ba?"

Da mamaki ta bu??e baki tace "Malam wai waye kai?"

?an gyaran murya yayi ya sake tausasawa yace "Ba ki ganeni ba?"

Cike da )?aguwa tace "Ta ya zan ganeka bayan ban sanka ba? Ni muryarka ma kama ta min da ta *alhudahuda*."


Tsuru yayi da idanu yana kallon wuri ??aya, sai kuma ya numfasa yace "Ni ne."

A mugun razane ta kalli lambar ta furta "Kai! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Huzeifi?"

?innn! Ta kashe kiran dan wallahi kunya ta kamata tare da tsoron me zai ce mata, wayar ya bi da kallo ya tallabe ha?a yace "Wai ita ba ta girma ne? Me ye haka kuma?"

Sai kuma ya yi wani sakaran murmushi yace "Alhudahuda? Ni ko?"

Jinjina kai yayi ya soka wayar aljihu da tunanin anjima zai sake kira dan maganar da yake so suyi mai mahimmanci ce, haka kawai ya ji yana son taimaka mata daga labarin da ya ji Fareeda na ba Mamansu, sai dai bai sani ba ko hakan zai mata.




______________



Cikin kuka )?ashirban ta amsa da "Na'am."

A gigice ta ??ago wayar ta kalla dan tabbatarwa wayar Hadeeya ta kira? Sa yanayin tashin hankali ta sake maida wayar a kunne tace "Ke Hadeeya lafiya? Me aka miki kike kuka?"

Cike da sangarta da kuka kamar ranta zai fita tace "Momma ba komai, Zeid ne ya ce zai yi ba)?i anjima kuma yana so in masa girki, ni kuma ban san yadda zanyi ba kuma ban iya girki mai yawa ba, shiyasa na kiraki."

Wata )?a)?)?arfar ajiyar zuciya ta sauke ta dafe gaban goshi ta gyara zamanta a kujerar ofishinta tace" Yanzu Hadeeya akan wannan ne za ki ??aga min hankali? Me yasa ba kya tsoron sakani damuwa ne?"

Cikin shashe)?ar kuka tace" To ba shi bane da na ce ban iya ba ya yi ta min fa??an sababi har da zagina, kuma Momma..."

Hankali tashe tace" Kuma me? Zeid ??in ne ya zageki?"

Cikin kuka tace" E Momma, ni dai ki fa??a min yadda zanyi kawai."

Ajiyar zuciya ta sauke dan wasu lokuta Hadeeya mamaki take bata, shin soyayyar Zeid ce ta mata yawan da ga damuwa )?arara amma take ?oyewa? Ko kuma dai wata muguntar yake mata da take mugun tsoronshi? Cikin nutsuwa tace" Ki kira Ummeeta mana ta je ta kama miki, ko kuma wata daga cikin )?awayenki, Hameeda dai ba iyawa za ta yi ba dan kinsan ita ko jikinta ba son tashi take ta gyara ba, idan ma na tura miki ita aikin banza ne saidai ku taru ku lalace."

Hankali tashe Hadeeya ta sake fashewa da kuka tace" Allah ya sawa)?e min na kira )?awayena, Momma ni yanzu ma na hana kowace )?awa zuwa min gida, dan in suka zo sai Zeid ya yita kallonsu yana musu hira da basu kyauta idan zasu tafi, Momma ranar fa Ummeeta ke fa??amin ta ga lambarshi a wayar wata )?awarmu Habiba, ni kawai ba zan kira kowa ba."

Rintse idanu Ardiya tayi a ranta ta furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" A zahiri kuma sai tace" To ita Ummee a ina ta san lambarshi da har take iya ganewa a wayar wasu? Hadeeya dama mijinki ??an iska ne?"

Ranta ne ya sosu matu)?a dan duk lalacewarshi a haka dai ta koyi sonshi kuma tana masa fatan shiriya, rai a jagule tace" Mommaaa! Ni dai ki taimaka min."

Ta?e baki tayi tace" Hadeeya bana so ki zama sakaryar mace da namiji zai dinga juyawa, wallahi ki murje idanunki ki nuna masa ke fa ba kanwa lasa ba ce, kada ki yarda yayi anfani da yarintarki ya dinga cuta miki, ki zage dantse in zaki iya idan ba haka ba wata rana kukan jini zaki yi nake fa??a miki."

Numfasawa tayi sannan tace" Ban san wa zai aika miki ba kuma sai dai in ni zanje mu yi aikin tare."

Da sauri Hadeeya tace" Ke fa Momma?"

Banza ta mata dan ta gama ?ata mata rai, kamar wata wacce ba ta yi karatu ba? Kamar ba wayayya ba za ta zauna tana wani shan wahala a hannun namijin da gasu nan birjik a gari, tana cikin tunanin haka kawai tayi saurin cewa" Yawwa kina ji?"

A sanyaye Hadeeya tace" E." ?orawa tayi da" Bari na kira Autynku (Safiya) sai na sa ta tura miki wannan ?bar zaman banzan da ba komai take a gida ba sai shiga madafa."

Cike da jin da??i Hadeeya tace" Yawwa Momma ya ma fi, tunda ita ?bar uwata ce ai ba zai kalleta ba ma."

Ta?e baki Ardiya tayi tace" Hummm!" Sannan tace" Kina zuwa makarantar kuwa? Ko ya hanaki?"

Da sauri tace" A'a Momma ina zuwa, ai bai isa ya hanani ba tunda al)?awari ya muku zan yi karatuna har na samu aiki."

Jinjina kai tayi cike da garga??i tace" Kuma ki kula da kyau, ina sake jadadda miki kada ki kuskura ki ??auki ciki yanzu, wallahi kina yin wannan kuskuren kin gama ta?ewa yarinya, dan laulayi ba zai barki karatunki ba, idan kika haihu reno ya hanaki ta?uka komai, kafin ki farga Hadeeya kin zama matar gida mai ciki da haihuwa kawai, wannan jar fatar taki da )?walisa duk zasu zama labari."

Shiru Hadeeya tayi ba tace komai ba, yo ta ya za ta yarda ta fa??a mata yanzu haka ciki ne jikinta, kuma akan ta nuna bata so ne tun jiya yake daddaga mata bala'i, duk iskancinshi da lalacewarshi yana son haihuwar, saida ya yi kamar zai cinyeta ??anya dalilin haka har ya ce mata idan ta cika ?bar iska ce ta cire cikin dan Allah ta gani, shi kuma da ba ita ba har uwarta sai ya yi shari'a da ita daga nan har duniya ta na??e. Ba ta san ya zatayi ba yanzu? Ta yi shiru ne kar Mamanta ta ji? Ko kuma ta fa??a mata duk fa??an da zata mata dai ba zata daketa ba ai. A qanyaye ta amsa mata da "To Momma." Sukayi sallama dan bata so maganar ta yi tsayin da za ta sakata fallasa kanta.

Da zuciya ??aya Safiya ta tura Saleema gidan Hadeeya dan ta taimaka ma ?bar uwarta, saidai tuni Safiya ta sa ma ranta cewa Hadeeya ciki ne da ita, dan ko zuwanta na )?arshe gidan ta kula da ??an dabinon dake bakinta tana ta tsutsa, to amma tunda komai nasu a ??aki sukeyi ba'a bari kowa ya ji, sai ba ta nuna ta sani ba kawai tana mata fatan in ma shine to ta sauka lafiya, dan cikin na yanzu wanda ya ta?a yi ma ya suka )?arata da haihuwar nan bare sabin shiga. Haka Saleema ta isa gidan a adaidaita sahu, tun shigarta take cin karo da abubuwanda basu kwanta mata a rai ba har ta shiga falon.

Hadeeya na kwance kan kujera da waya tana latsawa, kusa da ita daga )?asa kuma ledoji ne ba)?a)?e da kallo ??aya ba zaka san me ye a ciki ba, )?arewa falon kallo tayi sannan ta )?arasa shiga da sallama, da sauri ta tashi zaune da fara'a a fuskarta saidai bata amsa ba, tashi tayi ta fito farfajiyar ta tofar da yawu kafin ta koma, kallonta Saleema ke yi kamar ba ta ta?a ganinta ba, yadda jar fatar nan ta wani ko??e ita ba dan ace ta zuga abun ba sai tace kamar yaushi yaushi ta gani a jikinta na rashin gyara da kula da kai, sam jikinta ba alamar tana kula da shi, haka kuma yanzun haka ba alamar da ta nuna ta yi wanka, idan ma tayi to jikinta bai ga mai ba bare maganar kwalluyar da aka )?ware wajen ??aukarta a gida.

Gaisawa sukayi a sama sama dan ba wani sakewa ne dama a tsakaninsu ba, hakan ba dan babu soyayyar ?ban uwa ba ne, kawai daga iyayensune ne matsalar, hakan yasa har yau babu sha)?uwa idan ba su da suka fito ciki ??aya ba. Ledojin dake gabanta ta nuna mata tace "Aunty Saleema kin ga naman nan yanzu ya kawo, sai ko duba ki ga me ya dace muyi? Bayan la'asar ne zasu zo."

Mi)?ewa Saleema tayi ta dur)?usa wajen ledojin ta fara dubawa, nama ne har kala uku, kayan ciki, naman rago, da kuma naman zabi, kallon Hadeeya tayi tace" Me kike so a yi?"

Turo baki tayi tace" Aunty ai wannan aikin ya mana yawa mu biyu, ki ??auki wanda kike son yin aiki da shi, sauran sai a saka a fridge a ajiye, na dinga aiki dashi daga baya."

Kallonta Saleema tayi tana mi)?ewa tsaye tace" Haka ya gaya miki?"

Girgiza kai tayi a hankali tace" A'a."

A sanyaye tace" Dan haka zamu iya, in sha Allah."

Cire hijabinta tayi ta aje kan kujerar sannan ta kwaso ledojin ta fito da su waje, madafa ta shiga ta ??auko kayan aiki da duk abinda za ta bu)?ata, a tare ta ??ora silalar naman ragon da na kayan ciki bayan ta saka musu komai da ta ga mahaifiyarta na yi, kafin ta shiga gyara zabin nan ba tare da ta yanyankasu ba ta cire wuya kawai da wajen yatsun, wankesu tayi sosai kafin ta aje dan su tsane.




*Alhamdulillah.*
13/06/2022 ?? 17:25 - MOM LATEEF???i: ???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??
*BAIWATA*
???a%??]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??Hq>%? ?]so??_? ?]Hq??



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ??A惙@?
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
=??? *[G. M. N. A]* =??? ??Id???g???


_Bismillahir rahamanir rahim_


_36_




Silalar kayan cikin ta sauke ta tsane ruwan ta aje kayan cikin daban dan bata bu)?atar ruwan, naman ragonta ma daya dahu saukeshi tayi a wuta sannan ta ??ora silalar zabin nan guda uku bayan ta saka musu dafaffen )?wai a ciki da albasar data yanka da fa??i tare da tarugu babba guda ba tare da ta yankashi ko sa?awa ba, sannan ta yanka dankalin turawa kamar za ta soya sai ta saka a ciki shima, hakan yasa zabin suka zama )?osassu tamkar girmansu ne a haka sannan ta ??inki bakinsu da zare da sabuwar allura, komai na kayan )?amshi ta saka musu tare da ??an??ano, basu jima a wuta ba ta sauke dan bata bu)?atar su silala su ragargaje, Hadeeya dake ??aki kwance )?afafu a mi)?e tana kallo tana shan iska ta samu tace "Hadeeya wurin gashinki yana yi?"

Waro idanu tayi tace "Kai! Ban ta?a aiki da shi ba aunty."

Juyawa tayi cike da takaicin abubuwan da take ta gani a gidan )?anwar ta ta da kuma mamakin kiranta Aunty da take wanda ba ta haka idan ba wani abu take so a wurinta ba, ko da ta bu??a wurin gashin )?ura ce bajaja, hakan yasa ta dagewa ta shiga gyara wurin ta wanke duk abubuwan na gashi, kafin su tsane ta shiga soya miyarta ta kayan ciki ba tare da tayi aiki da ruwan silalar ba, dan sune suke ?ata miyar ka ga tayi kauri sosai har mai tsantseni ya kasa ci, sannan su yi mai)?o gana ci hannunka na daskarewa tsabar mai. Ta na zuba kayan cikin ta shiga )?o)?arin gasa zabinta data sake linde jikinsu da ha??in mai da da ??an moutarde da jajjage, ta kunna oven ??in dan ??orawa kawai ya )?i yi, haka ta yi juyin duniya amma ya )?i yi, )?arshe ha)?ura tayi dan ta san rashin aiki da shi ne ya kawo haka. Tukunya kawai ta ??ora a wuta ta zuba mai isashe dan ta soya.

Shigowarshi kenan ya ji gida ya gauraye da )?amshin girki, abu ne da bai ta?a ji ba tunda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login