Showing 48001 words to 51000 words out of 193749 words

Chapter 17 - BAIWATA BOOK COMPLETE BY SAMIRA HARUNA.doc

19 Sep 2025

4387

ni zan ??auki matakin da ya dace."

Ha??a idanu sukayi da Alhaji Yusuf dan ya san da shi yake, shi ma kuma ya kalleshi ne dan ya san ya ji kuma ya fahimta, mi)?ewa tayi a rikice ta juya ta bar falon na mahaifinta. Mu'az da ya bita da kallo tana fita a )?ofar ya kalli Alhaji Yusuf yace" Abba zan iya magana da ita?"

Jinjina masa kai kawai yayi dan takaicin na Saleema ya hana shi magana, shi kawai gani yake yarinyar nan kamar ma sauya masa ita aka yi a asibiti, sam yarinya kamar wacce ta zo a zamanin Kakarshi Hajia Zarah.

Tana kaiwa tsakiyar falonsu ta tunkari ??akinsu ta ji muryarshi a bayanta yace "Saleema."

Cak! Ta tsaya jikinta ya )?ara ??aukan kyarma, ba ta juyo ba har saida ya zo daf da ita ya tsaga gabanta, kallonta yake sosai kamar zai ha??iyeta, kamar an mintseneshi sai kuma ya dur)?usa gwiwarshi ??aya a )?asa yana kallonta yace "Saleema, ban san me kike so na fa??a miki ba bayan wanda na fa??a miki a gida, kamar yadda na fa??a miki ke ce mace ta farko dana fara jin ina so, Saleema kwana uku ka??ai kukayi a gidanmu, amma rayuwar gidan gaba??aya ta canza, a wadanan kwanakin na maida komai na wa zuwa ga Allahn da ya halicceni, kwana na ke ina neman gafararsa akan abin da na aikata a baya, Saleema na kasance..."

Saida ya sadda kanshi sannan yace" Ina biyan bu)?atata da duk macen da ta birgeni, amma fa ba zina na ke aikatawa ba..."

Baya Saleema ta ja ka??an tana kallonshi da kyau, hakan ya sa shi mi)?ewa da sauri kamar zai ri)?ota yace" A'a ba yadda kike tunani ba ne, ina nufin ba na jima'i da mace, amma dai mu kan yi...wasa da junanmu har bu)?ata ta biya, Saleema ina ganinki na ji na aje komai gefe ina kuma so na yi aure da wuri."

Tafin hannunshi yasa shima ya ??an shafe gumin da ya fara tsatsafo mishi gaban goshi yace" Yanzu idan ki ka )?i amince ya zanyi? Saleema ba zan iya auren macen da bana so ba dan kawai maganin sha'awata, idan ba ki amince dani ba kamar kin yerje na ci gaba da aikata ?arnar da nake aikatawa a baya."

Duk da hawayen da ke mata anbaliya saida ta kalleshi tace" Kenan nima *auren sha'awa* ne za ka yi da ni?"

Girgiza kai tayi ta ha??e hannaye tace" Ka ga dan Allah ka janye )?udirinka a kaina, ka sake tunani ka bincika za ka samu wacce ta yi daidai da kai, ni...ni fa na sani wannan ??in ha)?)?ine dake hawa kan duka ma'aurata, amma yanda ka ke nuna min ya sa ni jin tsoron lamarin fiye da yadda kake tunani."

Numfashi ya sauke cike da sacewar gwiwa yace" Shikena Saleema, ba zan tilastaki ba, amma kamar yadda kika ce kiyi shawara da Mama, zan ji daga gareki zuwa gobe."

Ra?ata yayi ya wuce ya barta nan tsaye, saida ta ji ya rufe )?ofar sannan ta )?arasa ita ma ??akin ta samu mamanta zaune bakin gado tana shan magungunan ta. Ganin alamar ta ci kuka yasa hankali tashe ta aje kofin hannunta ta jawo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita, cike da kulawa ta kalleta tace "Hajia, me ya faru? Me ya sameki kike kuka? Wani abu ya miki?"

Girgiza kai tayi ta kwantar da kanta kan cinyoyin mahaifiyarta tana ci gaba da rusa kuka, dadda?ata ta fara yi ta sake cewa "Fa??a min me ya faru? Dukanki ya yi ne?"

Girgiza kai tayi cikin kuka tace "Mama ki tayani da addu'a, maganar aure Abba ya min kuma da Mu'az, bana jin komai da ya danganci a game da shi, ina tsoron kar Abba ya tilasani na auri Mu'az."


Girgiza mata kai tayi tace "A'a Hajia, Abbanku bai da wannan tsarin a rayuwa, ba zai tilastaki ba in sha Allah, amma ki zauna ki nutsu kiyi tunani, idan kin ga ya miki sai ki amince, idan bai miki ba ba wanda zai miki dole."

Share mata hawayen tayi tace "Yanzu tashi ki wanke fuskarki ki zo ki ci gaba da karatunki."

Jinjina kai tayi tana shashe)?ar kuka ta shiga ban ??aki, da kallo ta bita har ta shige cike da tausayinta da kuma fatan kar ya mata auren dolen, dan bata san me yasa yake hassala akan lamarin Saleema ba wasu lokuta? Mi)?ewa tayi ita ma ta fita daga ??akin dan ba lokacin baccinta bane yanzu.



*Washe gari*



Gidan Alhaji Auwal dai ba'a yi baccin arzi)?i ba musamman ma Alhaji da amarya, tunda ya fa??a musu Mu'awwaz zai auri Nafissa suka rikice ita da Mu'awwaz ??in, da kuma ta fara kawo masa hauka ya nunata da yatsa yace "Ke baki isa na fasa abin da mahaifina ya ke so baa, in ma za ki ha)?ura ki ha)?ura ki lallashi ??anki, da yake iskanci a garin nan kina ina? Ba kallon yaro kike masa ba? To ki nutsu daga ke har shi, idan har kuka ce za ku bijere min wallahi mataki zan ??auka a kanku da zakuyi mamakina a rayuwarku."

Bugu da )?ari saida ya kalleta sama da )?asa sannan yace" Kin fi kowa sanin ba tare muka zo duniya ba, sannan ??anki ba shi ka??ai na haifa ba bare na ji takaicin rasa me gadata bayan raina."

Cike da hauka da hargagi da kuma jin cewa ita ce hasken gidanshi ta cire ??an kwalinta ta jefar, yalo-yalon gashinta ba)?i mai tsayin gaske ya bayyana, cikin ??aga murya ta fara bubbuga )?irji kamar wata dangin inyamurai take fa??in" Ahaji ni ka ke fa??ama haka? Akan me za ka yanke mana wannan hukuncin? Laifi muka maka ne? ?an nawa za ka ha??a da mai aikin gidan nan )?azamar yarinya saboda ka tsanemu, wallahi ba ka isa ba, Mu'awwaz Hameeda zai aura ?bar Ardiya ko kana so ko baka so."

A nutse ya jinjina mata kai yace" To shikenan mu zuba, zan nuna miki na isa har na yi yawa."

Cikin bala'i da masifa tace" Ni dama tunda yaran nan suka zo na ga ka canja, wannan na san ba zai rasa nasaba da yarinyar nan da na ga kana wani shige mata kana mata kallon )?auna, gwara ma ka fito fili ka fa??a mana gaskiyar abin da ka ke shiryawa, dan na san gaba ka??an za ka ce mana aurenta za ka yi."

A tsawace Alhaji Auwal ya kalleta yana nunata yace" Ke *Gaishata* (team amare) ???iki san me bakinki zai dinga fa??a min, wallahi kika min hauka nan bar min gidana za ki yi, yarinyar da kike magana a kai ita ta zama fitilar da ta haska mana gidan nan shekara da shekaru, daga ke har Rabi cikinku wacece ta ta?a ce min na gyara tsakanina da mahaifina? To ki sani da zan iya samun wata kamar Saleema wallahi zan aura na ga idan kin isa ki hanani, shi kanshi ??an na ki da kike ??aga murya a kai ba dan shawarar da ta bamu ba da wata)?ila a kawo miki gawarshi ?ban iskan gari sun kasheshi."

Rara)?o idanu tayi tace" Saleema? Ita ce ta bayar da shawarar a aura masa ?bar aiki? Na sani dama wannan yarinyar ce ta canza maka tunaninka."

Sai kuwa ta )?arasa inda Mu'awwaz yake kanshi sadde ya ma rasa me ke masa da??i ta finciki hannunshi tana fa??in" Muje kai, in dai ni na haifeka bbu wanda ya isa ya aura maka wannan kucakar."

?akinta suka nufa suna kusan shiga Alhaji Auwal yace" Ji ni da kyau, mahaifina lokaci )?an)?ani ya ??ebo ma auren, ranar juma'a da za ta zo za'a ??aura auren a masallaci, idan ki ka ce ba za'ayi ba kuma kika kaini bango, to ki sani sa'ilin da surukarki za ta shigo gidan, lokacin ke kuma za ki tattara kayanki ki barmin gida. "

Mu'awwaz ya kalla da ya juyo ya kalli mahaifin na shi yace" Kai kuma ka sani ida har ka yi yun)?urin yin wani abu to za ka gami da ?acin raina, dan sai na rabaka da komai da yake nawa, duk wani da??i da kake ji da dukiyata sai na tabbatar ka kai )?adamin da zaka iya yin barar abinci sannan zan ha??aka da hukuma su hukuntaka."

A fusace ya juya ya barsu tsaye sun shiga zulumi da ki??imar da basuyi tsamlanin zai yi ikrarin ambatar musu ita ba. Sakin hannun Mu'awwaz tayi ta kalli Hajia Rabi da ita dai tunda suka fara ??aga muryoyi ta ce su yi ha)?uri Gaishata ta daka mata tsawa ta zuba musu idanu, nuyya ce ta yi ko zai kafta mata mari ba za ta tashi ko da tsaye ba bare ta damu. A hassale Gaishata ta wurga ma Hajia Rabi harara sannan ta banka )?ofar ??akin ta shiga har hawayen takaici da ba)?in ciki na ziraro mata da tunanin me za ta wa Saleema ta huce ma?



_____________



Wajen Saleema kuma maganar saukar da za'a yi ne kawai a gabanta, yanzu haka wayar Mamanta ce a kunnenta cikin nutsuwa tace "E malam ta kawo min, ga takardar ma a hannuna."

Daga ?angaren malamin yace "Yawwa Saleema, to kin gani yanzu kwana uku ya rage, kuma abinda kika bu)?ata za ki yi magana a kai ranar babban abu ne da ya dauki shafuka har uku, a haka ma a komai na saka miki ba, farkon za ki ga mu)?addima ne, na san wannan kin haddaceshi ba tun yau ba, abu ma fi mahimmanci shine ki haddace ko da rabin shafi na farko, tunda kinga minti biyar ne ake ba wa kowane ??alibi dan karatu."

Numfashi ta sauke tare da kallon Khairat dake gabanta tace" To malam, nagode sosa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i."

Kamar yana gabanta ya mata murmushi yace" Ba komai Saleema, kuma ina fata ba za'a samu matsala daga wajen mahaifinki ba?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace" Malam ko da akwai matsala ma ni zan kar?eta, sanin lahirata ya fi min komai, idan na bi ta mahaifina zan tashi ne babu duniyar kuma babu lahirar, to idan haka ta faru wace riba na ci ta zuwana duniya?"

Cike da jin da??i da kuma jinjina nutsuwar yarinyar yace" Hakane Saleema, Allah ya miki albarka, Allah ya ma karatunki albarka, in sha Allah wata rana mahaifinki zai yi alfahari da ke."

A sanyaye tace" Allah ya sa malam, nagode."

Da haka suka rabu Khairat ta koma dan dama takardar karatun da zata gabatar ta kawo mata, Saleema kuma shiryawa ta yi ta fita kasuwa ta siyo kalar yadin hijabin da zasuyi anko uta da sauran ??alibai, ba ta dawo ba saida aka ??inko mata shi yanda take da bu)?ata sannan ta dawo. Ko da ta shigo ta samu Mamarta da )?anwarta *Lubna*, gaisawa sukayi sosai cike da mutumtawa da kewar juna kafin tace mata "?war mamanta kenan, gashi dai daga )?arshe kela za ki yi saukar nan, burinki zai cika."

Murmushi Saleema tayi sannan ta kalli Mamanta tace "Mama, kar fa ki fa??ama kowa tunda kinga ba taro za'ayi ba."

Harara Safiya ta dalla mata tace "Kina tsoron ya sani amma ki ka dage sai kinyi?"

A ladabce tace "Mama ba tsoron ya sani yanzu ba na ke, wallahi ko da zai sani ne minti ??aya da gama karatuna a makaranta ban damu ba, na san dai ba zai wuce ya sake hanani wani abun ba ko kuma ya dakeni."

Dariya Lubna tayi tace "Ba ma zai dakeki ba yanzu tunda kin zama budurwa, kuma ai babu wanda ya sani a dangi, nima yanzu ne na sani data kirani ta bani ku??in nan da za'a miki wainar sadaka da kuma gallelen ragon da ta ce a siya dan a kai makarantar."

Cike da farin ciki Saleema ta rumgume Lubna tana fa??in" Kai amma na ji da??i sosai Aunty."

Da fara'a ta shafa kanta tace" Ai ke ?bar Mamanta ce."



*Ranar Sauka*


Gidan shiru yake kamar ko yaushe babu alamar wani hidima, hatta da Saleema da abun ya shafeta ita da mahaifiyarta, a ??aki suke suna kitsawa da warwarewa saboda tsaro, inda lokaci lokaci sukan yi waya da Aunty Lubna suna jin yanda komai ke tafiya daidai daga ?angarenta. Wayar mahaifiyarta ce ta yi )?ara da sauri ta ??auka da tunanin Khairat ce da take jiran ta kira ta bata malaminsu dan ta masa bitar haddata da ya ce yau da safe zai ji daga bakinta, ganin Hajia Rabi ce yasa ta mi)?awa Mamanta tace "Mama Hajiarsu Mu'az ce."

Cike da tsokana tace "Ki ??aga mana, sarakuwarki ce fa."

Turo baki tayi gaba tace "Maaaama."

Dariya Safiya tayi ta kar?i wayar ta ??ora a kunne da sallama, Saleema na jinsu suna gaisawa kafin daga bisani ta mi)?o mata wayar tace "Tana son magana da ke ne."

A ladabce Saleema ta kar?i wayar ta ??ora a kunne, a sanyaye sosai ta furta "Assalama alaiki, Mahmah."

Shiru aka yi ba amsa, da mamaki ta ??an ??ago wayar daga kunnenta ta duba sannan ta sake mayarwa tace "Hello!"

&?a)?)?arfan numfashin da ya sauke a cikin kunnuwanta ya sa ta kallon Mamanta da kyau da mamaki, cikin taushin murya kamar mai mata ra??a yace "Baby shine kika manta dani ko? Ina wayarki take? Tun da aka kawo miki nake ta kiranki amma bana samu, anya ma kin saka layin a wayar? Matata me yasa kike min wula)?anci ne haka?"

Gaba??aya sassan jikinta saida suka amsa, yanda yake maganar kamar zaiyi kuka da saurin da yake maganar sai ta ji wani abu mai kama da tausayinshi a zuciyarta, a hankali ta mi)?e tana satar kallon Mamanta har ta fice a ??akin kafin tace" Ni ban wula)?antaka ba, kuma ma ai...ni fa..."

Shirun da tayi yasa yace" Ke fa me? Har yanzu ba ki gama shawara da Maman ba ne? Saleema jiran amsar nan ta ki kinsan halin tashin hankalin da na shiga kuwa? Na rantse miki da Allah ko tashin hankalin da na shiga sanda na ke neman takardar wani aiki a wata Projet bai kai wanda na je ciki ba yanzu."

Cike da shagwa?a ta turo baki idanunta a rintse ita a dole kunya take ji kamar tana gabanshi tace" Malam ka mana shiru ko, kai bakinka ba ya gajiya da surutu? Ba na fa??a maka na amince ba."

Daga ?angarenshi da mamaki yace" Kin fa??a min? Yaushe kuma?"

Cike da yarinta da sangarta tace" Yanzu mana."

"Wayeeehuuuu!" Ya fasa mata kunnuwa da wata irin mahaukaciyar )?ara, kafin ta ce wani abu ta ji muryarshi da alama ru)?um)?ume Hajia Rabi yayi yana fa??in "Ta amince wallahi Mama, wayyo da??i, Mama kasheni kar farin ciki ya min yawa."

A kunnenta tana jin yanda suke ta murna shi da Hajia har ta gaji da tsayuwa ta kashe wayar dan alamu sun nuna farin cikin da ya shiga ya mantar da shi waya suke. Kashe wayar tayi tare da nufa ??akin su Hadeeya dan kar?o wayar nan, sam ta manta da ita a rayuwarta, tun ranar wayar ke hannun su Hadeeya amma ba ta damu ba.

&?wan)?wasa )?ofar ??akin ta yi tare da sallama, daga ciki Hameeda tace "Shigo."

Tura )?ofar tayi ta shiga tana zuba idanunta a kansu, da alama tun da suka farka basu tashi a gadon ba, dama ba su karya tare da su ba, yanzu kuma gasu kwance da kayan bacci a jikinsu kawunansu a hargitse gashi a sake sai ??aukar hotuna suke, a ganinta me ye abun ??auka kuma daga tashi daga bacci? Shin hoton hauka da ake ??auka kowane lokaci? &?arasawa ta yi ta tarawa Hadeeya hannu tace "Waya za ki bani?"

Da sauri Hadeeya ta kalleta tare da marairaicewa sai kuma ta kalli Hameeda, kamar za ta yi kuka tace "Dan Allah *aunty* Saleema ki bar min ita har a gama bikin murnar samun jarabawar )?awata, gobe ne da an gama sai na baki."

A hankalce ta kalli fuskarta da mamakin ita ce yau Hadeeya ke kira da aunty? Aunty fa? ?an ta?e baki tayi tace "To ke ba ga wayarki ba?"

Cike da sigar tausayi tace "Aunty wannan ba ta ??aukar hoto da kyau, wannan wayar fa babbar waya ce."

Hameeda dake zaune gefe ne tace "Wallahi aunty da ma zaki bar mana ita, kinga fa har ta bu??e tik tok, baki ga irin mabiyan da ta samu ba."

&?an)?ance idanu Saleema tayi tace "Dama abin da za ki yi da wayar kenan?"

Da sauri Hadeeya ta kalli Hameeda tana aika mata garga??in me yasa? Sai ka ce ta manta suna tare da ustazar gidansu ne, sai kuma ta kalli Saleema tace "A'a aunty, wa'azizzika nake ??orawa, tsaya ki gani."

Ta fa??a tana matsowa kusanta ta fara nuna mata wasu gajerun wa'azizzika tace "To kinga irinsu ne nake ??orawa, ba sa wuce minti ??aya zuwa second talatin, kinga ko ya mutum ya )?aru da ni ai ke ma kin samu lada."

Jinjina kai Saleema tayi dan sosai abun ya kama hankalinta, numfasawa tayi tace "To ki bani kwalin wayar, da alama akwai layi a ciki."

Da sauri ta sauka a gadon ta ??auko ta kawo mata, har ta juya za ta fita Hadeeya tace "Aunty Saleema ko na baki wayata sai ki saka layin a ciki?"

Ba tare da damuwar komai ba ko jin ta yi asarar abu mai tsada ba tace "To ki bani ita duka mana, ke sai ki ri)?e wannan."

A tare suka rakata da idanu a waje Hadeeya har da safe )?irji tace "Da gaske auntyna? Kin bar min ita duka?"

Yatsina fuska tayi tace "To me ye a ciki? Waya ce, dau??ar duniya, kina ?bar uwata na kasa bar miki ita."

Da gudu Hadeeya ta sauko a gadon tana fa??in "Yeeeeeeee! Auntyna nagode, nagode sosai."

Rumgumeta ta yi Hameeda da ba ta ji da??in haka ba tunda ba ita aka bar ma ba kauda kai tayi tana ??an )?aramin tsaki. ?agowa tayi suka kalli juna Hadeeya ta sake sumbatar kuncin Saleema tace "Nagode auntyna."

Murmushi Saleema tayi ta ??an shafa kuncinta tace "Da ina da irin wayar nan guda dubu, to da na dinga baki ko dan na ji sunan aunty a bakinki tare da ganin )?auna a tattare dake zuwa gareni, amma hakan ma nagode ma Allah."

Cike da kunya Hadeeya ta sunkuyar da kai tace "Ai daga yau aunty zan dinga cewa."

Murmushi kawai tayi ta tara mata hannu tace "?auko min wayar?"

Juyowa tayi ta ??auki wayar a kan gado ta bata, yo ita fa dama tun ranar ta gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login