Showing 21001 words to 24000 words out of 228147 words

Chapter 8 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10398

ta masa? Sam bata iya kallon cikin idannuwansa, dan bakinta ta murguda a kasan zuciyarta kuwa fadi take" wai shi hala dan daudu ne da yake saka kwali?

Kara bin fuskarta da ta sada ya yi da ido, lebensa dake cikin rawaninsa ya datse da hakorinsa na sama
A kasan zuciyarsa ya furta" wani rashin jin maganar kika shirya da ya saka ki sakin murmushi Majanune?
Dubansa ya maida wajen Dayabu, sai kuma ya lumshe idannuwansa yana ayanna ya zama wajibi a koya mata biyaya da bambancin sarkinta da yan iskanta! Irin yanda ta tsinke fuskar Zinaria da mari a gaban sarkinta ta yi rashin kunya mai tsauri!


Muryoyin dogarai da jakadiyoyin dake kofa na shaida karasowar Zinaria ya saka NAJEEBA kara janye kafamfafuwanta domin ita ta fi kusanta da hanya ta kuma tabata idan har ta shigo ta ganta a bakin hanyar nan zata baje tafiyarta ta yanda zata taka mata kafa ne ita kuwa ta kara mata na biyu a gaban ubanta!













Za ina tsalake ranakun posting idan har baku daukaka comment dinku ba😔
[31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



9



Cike da wata irin kasaita da alkyaba a jikinta ta sanyo kai, bayanta kuwa jakadiya ce, sai bayi mata uku du suka duduka sannan suka dukar da kawunansu kasa

A hankali ta ringa takawa har ta karasa kusa da Anmy ta samu waje saman luntsumemiyar kujerar dake nan ta zauna hakan ya kasance Zahrau na zaune kusa da kafarta ne

Sai da ta sada kanta a hankali ta gaishe da Anmy, sannan ta juya ta yiwa sarakan gaisuwar tare domin ba wanda zata fara gaishewa ta bar daya dan rabonta da mijin nata kusan kwana uku kennan

Sarki SHAHEED ne ya dubi dogaran dake tsatsaye kansu dan su san maganar tasu ce

Da yatsunsa ya yi masu nuni kan su fita

Da sauri suka ringa zagayowa sai su zube har kasa su kara neman afuwa sannan su fice a haka har ya zama daga su sai su a dakin

Kanta dake kasa ta dan dago ta dubi mahaifinta dake dan nesa da ita

A hankali ta saki kukan da ta aura harma ya zama abokin yinta ba dare ba rana kan rasuwar yaron nata

Mahaifinta yana gannin yanda Anmy ta girgiza kai ta sada kanta hakan ya saka shi yin gyaran murya yana kallonta

A nitse ya ce" shin baki yarda ba a maido maki yaronki ne ZULAIHAT?

Da sauri ta sada kanta dan a kausashe ya yi maganar wace ke nuna ransa ya baci da irin kukan nata, wanda ya tabata kafin ya zo sarakuwarta da mijinta ba zasu kasa rarashinta ba harma su nuna mata adu'a ya fi bukata ba kuka ba

Muryarsa ya kuma budewa a dake wanda hakan ya saka yan matan Anmy baki daya dagowa suka zuba masa ido wanda idan sarki baba na magana haka du kowa kansa yake sadawa

Da sauri Anmy ke saka kafarta tana dan zungurinsu, ta hakan suke tunnawa sunna mayar da dubansu kasa
Sai dai Zahrau haka kawai ta kara kure rawaninsa da kallo kafin ta sada kan nata

Cikin wata kakausar muryar ya ce" wannan ai aikin banza ne bayan kema kin san idan yanzu wanda ya halice ki ya yi kiranki koda duka duniya ne gatanki bamu isa mu tare maki ko mu hanna ki ba ko a dadaure ko a nitse sai kin amsa dan shi ya amsa zaki auri kuka ki ringa yi masa kina hanna shi sukuni a inda yake, shin a kanki aka fara rasa yaro ne ZULAIHAT?

A hankali , cikin tatausar murya Anmy ta ce" Zulaihat na neman afuwa Allah ya huci zuciyar sarki mai adalci

Dubanta ta kai wajen Shaheed wanda ya dace ya nema mata afuwa aman ya yi biris, san hararansa Anmy ta yi hakan ya sa ya kawar da dubansa daga kanta

Abih ne ya dan gyara zamansa shima a nitse ya ce" Allah ya huci zuciyar adalin sarki

DAYABUma ya kara sada kansa cike da girmama sarkin ya furta" a yiwa zinaria afuwa mai martaba

Anmy ta ringa zungurin su NAJEEBA,

Najeeba ta saki murmushi ta ki yin magana, a hankali ZAHRAU ta sada kanta ta ce" Allah ya huci zuciyar sarkin abzin

Haka su Ummu suka ringa furtawa a hankali aman cikin ikon Allah NAJEEBA sai ta sada kanta kawai tana murmushi a saman lebenta wanda bata boye ba

Da yake basu da yawa a dakin dole a fahimci wanda ya yi magana da wanda bai yi ba, gashi maganar a nitse ake yinta ba da hayaniya ba, sannan ba a tare ake yin maganar ba idan daya ya yi sai ya ajiye harma ya saka sekwani sannan wani ya yi cike da biyaya

Da sauri ta zamo kasa ta dukar da kanta ta ce" Allah ya huci zuciyar Aba

SHAHEED ya kawar da dubansa daga kanta, ya maida wajen sarki, da idannuwansa ya risinar da idannuwan nasa sosai sannan ba rufe su ya yi ba haka kuma ana gannin samansu da gashin girarsa
Hannunsa na daman ya dan daga daga ajiyen da yake ya dan dunkule shi sannan ya kara sada kansa

Murmushi sarkin garin Agadez ya yi da kansa ya iya amsa masa shima kafin cike da farin cikin kasancewarsa sirikinsa sarkin da ko cikinsu sarakunna suna maganar irin yanda sarauta ta zauna masa a jinnin jikinsa

Dubansa ya kai wajen Zulaihat a hankali ya ce" na san da kin san cewa dukan mai rai mamaci ne, sannan kin san cewa mamaci baya son kuka
Ba za'a hana ki zubar da hawayen rasa gudan jinninki ba, aman kuma ba za'a barki ki zubar har zubarwa ta dawo ta zama ba kyau
Idan kika tuna shi, ki yi gagawar yi masa adu'a
Idan soyaya ce nuna masa ta hanyar adu'a
Sannan ke kanki ki shirya naki zuwan inda ya tafi

Kanta take gyadawa hakan ya sa NAJEEBA ta kara dagowa ta tsura mata ido

Sai yau ta ji tausayinta, gaskiya ta ji tausayinta har cikin ranta
Kwana ukun nan koke koken da suke a bangaren Anmy sai ta dauke shi kawai na a ringa basu hakuri ne a hadu a lalace, tabas mutuwar Aliyu ta daketa domin yaron ba wanda ya batawa, yaro be mai shiru shiru sosai sai idan kun hada ido yakan sakar maka murmushi
To baima yi maganar ba bale ka ce ya maka ba daidai ba
Sannan koda yaushe yana wajen mahaifinsa sunna zaman fada, bai cika zama a gida ba dan mamansa bata barinsa zama a gida kulun korarsa take ya je ya koyi irin yanda ake juya kujerar da wata rana zai mulka

Idannuwanta ta lumshe ta maida kanta ta sada har ya gama sannan du suka shiga fadin godiya take da dai sauransu

NAJEEBA kuwa abinda ya fi bata daria kennan, irin yanda sha'anin sarauta yake tafia, irin yanda sarki ke zaune magana na masa wahala aman wasu na ta faman Allah ya huci zuciyarsa
To waima me aka masa da za'a ringa neman afuwar mutun? Anmy kadai take iya yiwa wannan kazagin itama sai idan ta tabata cewa ta bata mata to fa takan yi gagawar zubewa kasa ta ringa Allah ya huci zuciyar Gimbiya

Sai da komai ya nitsa Sarki ya nemi da yaran su fita

Du mimikewa suka yi, Zinaria ta fara godiya sannan ta juya ta fita
Su Ummu da zahra dukansu sai da suka yi godiya sannan suka firfito aman NAJEEBA kanta kawai ke kasa a hankali kuma cikin tafiarta wace ake gannin yanga ce ko takama da isa ce bayan haka take tun kankannuwarta bata iya sauri ba a haka ta fita a falon

Kansa kawai ya girgiza......bata nemi afuwar sarki ba, bata yi godiya ba, sannan da zata fita bata gode ba

DAYABU kansa duka abubuwan nan yana hankalce da ita harma ya gama ganewa NAJEEBAR so take ta jaza masu baki daya tashin hankalin Mai Martaba wanda hakan ba zai masu da sauki ba


Sunna tsakiyar tafia NAJEEBA ta ja ta tsaya, sai kawai ta shiga daria tana girgiza kanta

UMMU ta harareta ta yi tsaki ta ce" ke dai, ke dai akoy fitinaniya, wai ke mai martaba sa'ankine da zaki ringa kokarin kawo raini kai tsaye tsakaninku? Kin ga sarai dai yaya ya girme shi aman yake masa biyaya, kin ga Anmy mahaifiyarsa ce aman kasancewarsa sarki idan tana gabansa a lokacin da yake saman mulkinsa takan sanyaya kalamanta sannan ta tafiar da lokacin cikin sada kai
NAJEEBA kina ji kowa na rokar afuwa ke ba zaki yi ba ko?

Ummulkhair ta ce" kin ga, ni kaina dan Anmy ta min wani mintsini ne ya saka ni magana, haba dan Allah matar nan ta Mai martaba bata da mutunta mutane, kunna fa ji ranar nan yanda ta zagi Najeebar

ZAHRAU ta ce" ku dai ku daina irin haka, ina anfanin masifa wai?

NAJEEBA ta ce" ku dakata ni du ba wannan ba so nake ki auri ubanta

Zahrau ta zabura, dan har ga Allah gabanta ne ya fadi jin abinda NAJEEBA ta fada

Ummulkhair dake tare mata ta girgiza kai ta ce" zuwa yanzu na yarda baki da hankali NAJEEBA

Gaba suka fara yi hakan ya sakata itama daga kafarta tana biye da su bayan ta turo bakinta

Sai da suka shige uwar dakan ANMY NAJEEBA ta fada saman bed da baya tana murmushi

Juyawa ta yi tana kallon ZAHRAU ta ce" aunty, yaushe rabonki da ki ga fuskarsa?

Zahrau ta waigota ta ce" wa fa?

Najeeba ta ce" shi SHAHEED din

Da sauri ZAHRAU ta zaro ido, Bilkissu kuwa ta tura kofar da sauri ta rufe wace shigowarta kennan itama da mamaji ta ce" aunty NAJEEBA sunnansa ne kika kama kai tsaye haka?

NAJEEBA ta dubeta ta tabe baki bata bata amsa ba

UMMUKULSUM dake cire mayafinta ta dubi Bilkissu ta ce" ke fice mana a nan muna tataunawa yara sai shiga maganar manya

UMMULKHAIR kuwa itama bakin gadon ta karasa ta zauna tana fadin" walahi aunty ko, nima inaga a yanzu ba zan iya nuna kalarsa ba dan rabona da shi fuskarsa a waje tun kafin a nada shi sarauta

NAJEEBA ta ce" sai dai a yi masa hoto a boye a fitar da shi bayan mun san hotuna yanzu ana iya kara masa haske ko a kara masa girma bayan yaro ne karami

Da sauri Zahrau ta kai hannunta ta buge bakinta ta ce" ke dai neman fitinarki zai saka watarana a yanka maki bakin nan naki gutsi gutsi, ni ba zan manta lokacin da suke hawa dawakai da yaya ba, a lokacinma ya girmi yaya a girman jiki sosai har yaya na nemansa da rigima yana ce masa an hura shi shi din kyankyasar inji ne, shi kuwa yakan ce da yaya shi kuwa dan tamowa ne
Sannanma ina ruwanmu ne muna cikin gidansu muna irin magangannun nan idan ya ji kun san da zai iya sakawa a dauke mu ya halaka mu shikenan ko?

NAJEEBA ta koma ta kwonta tana kada kafarta ta ce" ina tausayawa talakawansa ne, kin ga ya ci ya cinye ya tayar da kai
Turaran nan da yake anfani da shi sai da ya cinye min tanadina na shekara biyu a paris bayan kun san nima mai kudi ce
Ta karashe tana kanne ido daya ta ci gaba da fadin" ku duba ku ga irin yanda fallonsa yake, Ac ban san adadin ko nawa bane, labulayen da karafunnan labulayen dakin nan sai ka rantse ba a africa bane,
Cafet din falon, da kujerun falon kadai ya isa ya haukata wanda bai taba fita ba
Duba ki ga irin dankara dankaran TV da windows da maficin nan dake kyali wanda aka ce da ruwan zinari ake wanke shi
Kausasa dubanta ta yi ta ce" ku kun san me nake nufi da ruwan zinari dan irin tsadar da wankin sarka yake a kasar nan!

Zobunnan hannunsa, da agogon hannunsa da takalmin kafarsa da shadar jikinsa da zubin da ake yiwa suturunsa kan sakani tunanin anya y'ayan mutane dake bata ba mafiya mai garin garin yake ba?


Zuwa lokacin Ummulkhair mayafinta ta dauka ta ce" kun ga, ba'ai min aure ba bale na haihu na haifi mai min adu'a, haka kawai na zauna a je wani tsanwan kuda ya kai labarin nan kunnayen fadawansama ba shi ba walahi sai sun ci ubanmu ko kannensa muke ba cousins dinsa ba

Tsakaninki da Allah NAJEEBA mutumen da ake yiwa maganar adalci wanda mutane suka shaida ake yabonsa ke jarababiya har kika iya kurewa rayuwarsa kallo kina neman masa shari?

NAJEEBA ta mike zaune tana kallon Ummulkhair ta ce" Ummu, wata uku fa kika bani a duniya kin ga yaya baya nan idan kika kuma zagina Allah sai na mare ki! Kuma ai ba shari na masa ba gaskiya na fada da yake hararena yana min kallon tsana me na masa yo ni bayan shi da kudaden talakawa yake takama? Ni kuwa neman na kaina nake walahi!


Zahrau ta girgiza kai ta ce" Allah ya shirye ki NAJEEBA, aman shi yaya SHAHEED din ne zaki ce ya dogara da kudin masarauta? Mutumen da shi ke zuba dukiyarsa dan gyaran gidan nan da kuma talafin gajiyayu da talakawansa?
Najeeba kin kuwa san meye aikinsa? Kin kuwa san shagon kasuwanci nawa ya malaka wanda idan aka siyar da daya zai isheki rayuwar duniya? Kuma ma wannan falon ai ba ainahin falonsa na dayan bangaren da yake hutawa bane
Baki san a wancen bangaren yaya yace harda su picsine, da wajen hutawa rikake? Da jardin da komai, shi ke fada min Sarki Shaheed sarki ne mai adakci wanda idan zai kwonta yake cike da damuwar shin yaya talakawansa zasu kwonta baci? Ke ba kyau tone tonen alkahairain mutun idan har yana yi domin Allah aman mutumen nan ya yi nisan da ba zaki iya fita cikin garinsa ki zage shi baki samu wani ya dauke numfashinki ba dan sunna kishinsa
A gidan redio kin ji me ake fada kuwa? An jima ba'a yi sarkin da talakawa ke kishinsa suke kishin komai nasa suke kare komai nasa irin sarki SHAHEED, ke ina alfaharin kasancewata yar uwar bawan Allahn nan dan kasaitarsa ba ara ya yi a jinninsa take!

Bakinta ta tabe ta koma ta kwonta saman bed din ta yi lamo

A hankali ta ce" kun san shan koko bukatar rai, abin dauka dauka ne

Sai da ta ja numfashi kamar zata yi baci ta buda idannuwanta ta ce" *ni sam bai min bane, sai nake jin na tsane shi sosai!*

Itama Zahraun mikewa ta yi a kusa fa ita tana juya kanta ta lunshe idannuwanta inda Ummulkhair ta fita ta shiga zaga gidan ita kuwa Ummukulsum ta he ta harhada sauran baki dayansu sukai cikin falon cin abinci ta shiga zuzuba masu dan su ci abinci

Aba ne biye da Anmy sai yaya DAYABU a bayansu suka shigo falon

Mutanen Falon suka ringa gaishe su sunna fita dan sun ga yannayin na Anmy da alamun magana zasu yi da dan uwan nata da kuma y'Ayansa

Zama suka yi ita kuwa ta shige ciki wajen yaran dan ta san sunna ciki

Karar bude kofar ya saka su tashi da sauri

NAJEEBA ta saki murmushi ta ce" Anmy ki rufa min asiri ki bani wayata na bude na ji yaya shagona da jama'ata kin ji?

Anmy ta zabga mata harara ta ce" ku fito

Tana fada ta juya ta fita suka kalli junna Zahrau ta ce" Allah dai ya sa ba laifi kika yi ba NAJEEBA

NAJEEBA ta tabe baki tana sauko da kafarta ta fara fita

Du an tataro sauran sun layi kamar yanda suke yi idan sun san sun yi laifi ko sun ga iyayen nasu a hargitse

Anmy ranta bace ta ce" NAJEEBA shine wani dan iska ya dake ki a ciki ba'a fada min ba? Cikin mace fa nan ne yaro ke kwonciya, idan ya jiwa yarinyar nan ciwo walahi Yaya sai na daure ubansa!

Najeeba ta shiga sakin murmushi tana gyada kanta tana kallon Anmyn nasu, sai a lokacin ta tuna da ciwonta ta sada kai gannin Aba na hararanta

Ta kai dubanta wajen ZAHRAU ta ce" ke kau an yi wata irin y'a, shine kika tsaya yana zaginki baki dauke min fuskar shege da mari ba?


Aba ya sauke ajiyar zuciya ya ce" ya ilahi BILKISSU ke da zaki hane su fada ke ke fadan sun ki duka? Yanzu zaki gindaya sharudan abinda ya kawo mu ko sai kin sa sun kara raina mutane?

Bakinta ta dan zumburo tana kallonsa ta ce" aman ai kaima kana da wani laifi ko yaya? Ina matarka ne da bata zo gidannan ta zauna da mu ba ko kyankyaminmu take?

Ummulkhair ta yi carab ta ce" Anmy, uhum nan kuwa da kanwarta ta haihu har aka yi sunna tana gidansu aman da yake ta raina mu mu.......

Shiru ta yi sakamakon juyowa da Anmy ta yi ta ce" na koya maki? Tambayarki na yi? Ni na kiya maki tsegumi? Yi min shiru a nan my daughter!

Kansu suka sada su duka jin ta fara hawa da gasken

Tsayawa ta yi kansu tana dubansu murya a kausashe ta ce" *MUTALAB ND BILKISSU FAMILLY*!

su duka suka shiga dago kansu a hankali sunna kallonsa,
Sai da ta dago dan yatsarta manuniya ta nuna su ta ce"
[31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login