Showing 45001 words to 48000 words out of 228147 words
Chapter 16 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
ita je ba tare da an san ko meye a motar ba
Najeeba ta lumshe idannuwanta ta furta" *Sarauta* wani sa'in sai ma ga sarauta ta cika izgili
Kun ga cewa a fada aka daura auren nan? Maimakun gidan su budurwar tasa?
Zahrau ta yi murmushi tana kallonta ta ce" baba da karamin kennan
Najeeba ta yatsina fuskarta ta ce" ai shi girma ko wani iri ne hawa yake yana sauka
Akoy wajen da zaki ga girman zai samu yaya wanda dole zai sada
Idan har sarki nada zuciya a cikin kirjinsa.......to tabas zai saurari kidan wace ke motsa masa ita
Ummukulsum dake kallon wajen da suka tsaya ne ta yi murmushi duba da irin wajen da sarki ya dauko mace
Tabas ta yarda a yanzu cewa sarkinsu baya mu'amalantarka dan kana mai kudi ko talaka
Yana mu'amalantar kowa ne bisa tsarin da ya zo masa
Ashe da wata motar a bayansu wace ke dauke da wasu yan matan bayi su su shida
Irin kayan gidan sarautar ne a jikinsu sun yi kwaliya daidai misali
Hannayensu dauke da sako du suka layu a bayan su NAJEEBA
A hankali suka ringa takawa inda Dogarin nan ke ta fama wajen ture yaren dake son taba su Najeeba, wajen kaiwa du wani wanda ya janyo waya dan yi masu hoto ba tare da sun amince da hakan ba
Gannin gidan cike da jama'a ya saka dogarin sada kansa da neman alfarmar su koma mota ya fitar da mutanen ciki
Da sauri Zahrau ta girgiza masa kai a fili ta furta" zamu cudu da su dan bama kyamatarsu
Murmushi Najeeba ta sakar mata da ido ta jinjina mata
Duda hakan sai da ya fara shiga ya shela cewa a bada hanya kannen mai martaba na tafe
Sannan ya dawo da sauri ya koma gefensu da zabgegoyar bulaliyarsa a hannunsa yana kuma sama masu hanya sunna ratsawa a hankali a hankali
Kallo fa ana binsu da shi gaba daya sun mimike sunna faman yi masu sannu
Wani daki aka nufa da su wanda suke tunanin a ciki amaryar take
Zaune take da zumbulelen hijab dinta da kawayenta su hudu
Ba kujeru a dakin sai tabarma su kansu sunna zazaune ne saman wata yar katifa wace take ta kanninta domin dakin kanninta ne
Kanta a sade yake tana jin gabanta na faduwa cike da tsoron dago da kanta dan gannin kannen mijin nata
Har yanzu ta kasa gaskata cewa ita Bintu itace ta zama matar mai damagaram
Zata iya rantsewa cewa bata taba gannin fuskarsa ba ko a hoto, haka kuma idan dai ta hange shi to sun fita kallon hawan sarki ne da yake yi ana gobe sallah wanda ke shaidawa al'umar garin cewa sallah ta kama a washe gari ne
Takan hangi hannunsa daya tak dake rike da igiyar dokinsa dayan kuwa a cikin alkyabarsa
Farin hannun wanda ke dauke da wasu irin jijiyoyin sai idannuwansa dake dauke da kwali wa'inda idan ya juyo yana mai bin jama'ar garinsa da kallo sannan yana dan amsa gaisuwarsu da ihun kiran sarkin da suke sunna biye da tawagar
Wai yau ita Bintu yar gidan malan sulaiman itane Allah ya yi zata tare a gidan sarki?
Ko a baiwa bata taba hasaso kanta ba
Hakan ya hadasa mata rawar jiki cike da tsoron kannensama kafin a kai kansa
Tana cike da zulumi da tsoron matarsa da aka yi tataki a jiya aka zo aka baiwa iyayenta labarin wacece Zinaria
Ta san cewa ita tana kasa da ita ne, ita talakarta ce, dan haka zata nemi masalaha da ita tun kafin ta gagari zama a damagram
Daburcewa yan matan suka yi wata na faman bara ta samo kujeru, wara na kallon abin shansu da cinsu da baki daya suka kare saura kadan kadan dan sun yi taro kamar me duda a kure lokacin ya zo ko anko basu samu sun yi ba
Da sauro dayar ta ce" bara na je shagon kalamu na samo jus
Da kallo Najeeba ta bita har ta fita
Kujeru ne dogarin nan ya ja daga kofa ya yi salama yana rike da su
Bashi da hurumin shiga wajen da matar sarki take kai tsaye hakan ya saka shi tsayawa daga kofa da kujerun da ya fita da gudu ya sauke mutane ya dauko
Najeeba ta bi hannunsa da kallo
Kujerun da alama zasu yi nauyi gashi itane karama a cikinsu
Matsalar bata daukan abu mai nauyi gaskiya dan haka ta juya ta koma cikin dakin da du suka bubude windows din dakunnan ta kakabe tabarmar nan ta dube su da murmushi a fuskarta ta furta" bismillah
Ba tare da wani damuwa ba yayun nata suka zazauna baki dayansu
NAJEEBA kuwa ta kai dubanta wajen amaryar
A hankali ta shiga takawa ta karasa kusa da bed din
Baki baki ta zauna cikin nutsuwa ta saka hannunta ta dago habarta wanda hakan ya saka baki dayansu jin gabansu ya fadi
Ita Najeeba gabanta ya fadi ne a kan dalilin da bata sani ba
Ita kuwa gabanta ya fadi ne jin wani irin lalausan hannu ya taba fuskarta wanda zata iya rantsewa hannun nan ya fi fuskarta laushi
Da sauri ta sada kanta, yar karamar muryarta na rawa rawa ta ce" Barkanku da isowa
Subahannalah
Najeeba ta furta a kasan zuciyarta
Bata so haka ba!
Sam bata so haka ba!
Ta yaya za'ayi wannan ta iya kwatar kanta a wajen Zinaria? Yarinyar kamaninta sam basu nuna yannayi na wada ta iya fada ko ta san tsatsaya a rayuwarta ba
Yarinyar gaba dayanta yannayi na wata irin saliha ne a tatare da ita
Haka kawai ta ji ranta na bacewa domin ita ba haka ta so ba,
ta so ace wada ya auran nan ta ci ubam Zinariya a iya iskanci sai su ga ta iskanci
Muryarta a sanyaye ta ce" yaya sunnan ki?
Bintu ta kara sada kanta ta ce" sunna na Bintu
Najeeba ta gyada kanta ta kai dubanta wajen kawayen nata
Su kansu basa yannayi da yan iska
Aman a kan me zai tashi ya wani dauko saliha haka? Wannan ai wulakanci ne salon banzar matarsa ta wulakanta yar mutane?
Cikin nutsuwa Najeeba ta ce" ku dakata daga kofa, lokaci na tafia zamu kimtsa gimbiya
Gaba daya suka yi waje bayan sun risina sun kara gaishe su
Tabatarwar da suka yi cewa ta yi wanka mahaifiyarta na zaune tana kallo Najeeba ta buda akwatinta na kayan mak up
Cikin nutsuwa ta shiga gabatar da aikinta cikin wata irin kwarewa wace a dan kankannin lokaci yar budurwar ta kara wani irin fresh da ita ta kara wani irin kyau hancinta ya fito zuwat sa shi yana wani irin sheki
Gaba daya yarinyar kanta ce mai kyau, wani irin nutsatsen kyau mai birgewa
Turaran wuta suka shiga yi mata ita kanta kafin su dora kayan da suka zo da su suka shiga turare mata su baki daya
Mahaifiyarta na rike da turaren ruwan da suka bata concentrer mai wani irin dadi tana shafa mata lungu lungu na jikinta
Daidai da pant dinta sai da suka turara mata sannan suka bata baya ta saka sabuwar bra din da pant din
Taimaka mata suka yi wajen suturta mata jikinta da suturar da aka zo mata da ita wani farin lesh ne mai wani irin laushi
Dinkin ya karbi Bintu sosai
Nan Najeeba ta kuma zaunawa da agraf dinta tana kashe mata daurin dan kwali tana dantse shi yanda zai zauna
Dole yarnan ta birgeka
Saima da suka rufa mata alkyabarta mai dauke da wani irin ado tamkar dawisu
da ta kalli kanta a madubi sai kawai ta fashe da kuka ta fada jikin mahaifiyarta tana jin gaban kirjinta na dokawa
Ashe zata ga irin wannan daukaka daga Allah kafin ta mutu?
Mahaifiyarta na mata murmushi ta rasa inda zara ajiyeta domin sai ta ga katifar nan ba zata zaunu da alkyabar nan ba
Zahrau ta kamata tana murmushi itama ta zaunar da ita suka sakata tsakiya suka kashe hoto nan suka fito reras da su tamkar ka sace su ka gudu
Sakwanin aka ringa ajiyewa kala daban daban kafin su yi masu salama a lokacin har an shiga salar magariba suka fito
Tuni kuma motoci sun fara layuwa dan daukan amaryar mota hudu ce kawai dan ba'a so a ga shigarta ta kofar baya idan ya so daga baya sai a kawo mutane
Su dai daukansu ya yi ya maida su fada
Sunna fita Najeeba ta tserewarta dan tana son zuwa ta shaki iskar duniya ta ji sanyi na ratsa mata jikinta
Motar yaya Dayabu ta shiga ta tayar abinta ta tafi siyan ice cream
Zuwa lokacin da ta nufi wajen hutunta wanda rabonta da wajen yau kwana hudu kennan tuni an kira isha
Da piyawatanta a mota da kuma abin sallah
Tana sauka daga motar ta dauki piyawatan
Gefe ta koma ta daura alwalarta sannan ta dawo cikin motar ta dauko salayarsa ta dauko alkyabarta
A nan ta shinfida cikin nutsuwa ta tayar da sallarta
Sai da ta gama baki daya sannan ta mike ta mayar cikin motar ta cire alkyabar ta dauko ledar ice cream dinta da wayarta
Tun da ta tinkaro wajen ta dan ja ta tsaya sakamakon gannin mutumen nan zaune kansa sade
Yau kuma irin shigarsa sai ta sakata kara kallonsa da kyau
Dan waigawa ta yi ko zata ga motar da ta kawo shi? Sai dai hata ga mota ba
Adu'ar neman tsari ta ringa yi da miyagu
Kasancewar ya saka shada marron sai gaba daya hasken fatarsa ta kara fitowa
Daga sajensa zaka gane mai summa ne sosai sannan baka ce sidik summar
Kwalin idannuwansa dake nuna kansu ko a cikin dare ne sun kuwa nuna kan nasu da taimakon fitilun dake kukune
Karasawa ta yi ta zauna a wajen da take zama hakan ya sa suke facing din junna
Shima bai yi tunaninta a wajen nan a irin wannan lokacin ba kasancewar ya san cewa ita din kirjin biki ce du inda ta ji da maganar biki ko ba na gidansu ba zuwa take bale yau nasu?
Kura mata ido ya yi gannin ta kasa bude abinda ke ledar sai dan jujuya cokalin hannunta take
Shin dama tana da kunyar cin abu a gaban bakon ido ko cikin salon yaudararta ne da neman janyo hankalin namiji a kanta?
Basarwa ya yi ya ki yi mata magana a yau din ya daga kansa sama yana gannin yanda farin wata ke kara haske
Kasancewar ta rasa nutsuwar hutawar ya sakata kallon wajensa
Sai da ta yatsina bakinta a hankali ta ce" hi
Dagowa ya yi daga kallon saman ya sauke a saman kanta
Da sauri ya cire idannuwansa domin dinkin lesh din nata daga gaban kirjinta an yi kata wani heart ne an cire wajen an zagaye shi da kyalkyali aman kuma an baiwa mararabar kirjinta damar bayannuwa sosai
Kai kam ina ne gidanku kake zama a nan koda yaushe? Ko a saman bishiya ne?
Ta fada tana nuna masa bishiyar dake wajen
Shima bishiyar ya kalla, sai ya ji murmushi na zo masa, wato da alama a tsoracema take da shi ko?
Kafadunsa ya dan daga a hankali ya ce" daga wajen auren sarkin garinnan nake, na gaji shine na zo nan na huta
Bakinta ta dan tabe ta daga kafadunta
Muryarsa mai sanyi ta kuma jin ya ce" daga ina kike haka? Me kike zuwa yi nan? Ko kema daga wajen auren sarkin kike ne?
Dago idannuwanta ta yi ta sauke saman kansa a hankali ta ce" ban san shi bama ni sarkin nan, sannan wajen nan wajena ne ban san dalilin da zaka tambayen me na zo yi ba
Wajenta ne? To ka ji ya fada a ransa
Mikewa ya yi cike da isa ya dawo kusa da ita ya zauna inda take binsa da kallo har zamansa
A hankali ya ce" freind?
Hannun nasa dai ya miko mata yauma, shi kam ko a inda ya fito haka yake gaishe gaishe da mata? Duda yanzu abin ya zama ruwan dare dan gaisawa da mace ba wani abu bane da namijin da ba muharaminta ba bayan ba kyau
Murmushi ta yi tana hararan hannun nasa a hankali itama ta ce" zan yi tunani
Haka yauma ta bara masa hannun sakaye yana binta da kallo har ta shige motarta sannan yauma bata dauke abin cikin ledar nata ba nan ta bara masa su ta yi tafiarta
Kansa ya gyada yana ayanna" du salonki, sai na ga ainahin wacece ke! Du iya tsare tsarenki na kwana da sannin ke din *MAGE CE MAI KWONCIYAR D'AUKAN RAI*
da wani irin sauri amintacen dogarinsa ya karaso wajen da yake zaune ya zube kasa kansa kasa jikinsa na rawa ya ce" Allah ya ja da kwananka, Allah ya taimaki mai damagaram kiran gagawa ya samu daga wajen Gimbiya Allah ja da rai
Da sauri ya kalle shi ya waiwaya baya ya ga har ta tafi
Kira daga wajen gimbiya da gagawa?
N
Mikewa ya yi yana takawa ya nufi motar
Bai shiga ba sai da ya mayar da rawanin kansa ya dora alkyabarsa ya cenza takalminsa ya rige sandar girmansa sannan ya shige baya ya lafe
Jan motar yake gabansa na faduwa duba da irin abinda aka fara fada masa
A haka suka samu shiga ta baya suka shige suka karasa wajen da Gimbiya ta umarci a kawo shi
Du mutannen wajen dukawa suka yi a lokacin da aka shiga shelar shine
Cikin taku irin na kasaita ya ringa daga kafarsa daya na korar daya har ya karasa wajen da GIMBIYA ke tsaye tare da y'ayan yan matanta
Yannayin tashin hankalin da yake karanta a fuskarta shi ya saka shi kara rage hanzarin tafiarsa
Motar da ya bada dan kawo amaryar nasa ce ya ganni a bubude
Wasu mata ne ya ganni a duke nesa kadan aman kuma kuka suke
A hankali ya kai dubansa wajen motar
Idannuwansa ne suka sauka kan wasu fararan kafafuwa da aka fitar
Irin yanda kafafuwan suke ajiye ne zai shaida maka mai su idan dai ba barci yake ba to yana cikin halin rashin lafiar da baya iya motsa su
Da alama kuma mutumen dake ciki ahi daya ne
Haka kawai ya ji zuciyarsa ta doka da wani irin duka mai tsanani
A hankali ya karasa gaban mahaifiyarsa
Kansa ya dula sosai ya ce" Allah ya ja da ran Anmy
Anmy ta dago tana dubansa cike da fargabar abinda zata fada masa da tausayin yarinyar dama shi kansa da iyayen yarinyar
Me zata ce masa ne?
Ce masa zata yi su kansu yan rakiyar yarinyar basu san cewa ta rasu a cikin kotar ba har sai da aka zo aka kamo hannunta dan fitar da ita a sadar da ita da dakin mijinta? Ko kawai ta ce da shi SHAHEED ALLAH YA YIWA YARINYAR DA KA AURA YAU RASUWA?
SAI TA RASA KALMAR DA ZATA IYA HADAWA DAN SAMUN WANNAN BAYANI
BAKINTA NE YA SHIGA RAWA A LOKACIN DA TA BUDA TA CE"
YAU NA YI DA YAWA😓
[31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
17
A hankali yan matan suka marmatsa bayan sunna dan dukawa sunna nan afuwa suka barshi tsaye gaban Anmy
A hankali ya jinginar da sandar hannunsa ya saka hannayensa biyu ya dago fuskar mahaifiyarsa
Irin yanda kwayar idannuwanta ke cikowa da kwallah ne idan wani abu mai rikitar da zuciya ya faru ya ganni
Kwonce kwalar take a kurmin idannuwanta hakan ya sa fuskarta yin wani iri
Sauran matan tsohon sarki biyun ne suka karaso suma da yannayin juyayi a fuskokinsu
Fulani ce ta dora hannunta saman na sarkin dake gefen fuskar mahaifiyarsa
A hankali ta girgiza masa kai wanda hakan ya saka shi saurin rintse idannuwansa domin wannan lamari shi ya faru a lokacin da ya rasa mahaifinsa
Sun ringa dafa hannunsa ne sunna girgiza masa kai
Da sauri ya maida dubansa wajen motar nan
Kafarsa ya daga zuwa wajen motar nan bai ko dauki sandar ba ya karasa kusa da kafafuwan dake sanye cikin wani fari kar din silifas irin shirin da ake yiwa amare dai
hakan ya saka Gimbiya saurin rike hannun Fulani ta lumshe idannuwanta tana tunanin irin abinda yaron nata zai iya ji, dan ta tabata yarinyar nan yana sonta duba da har aka ji kamshin turaranta a tufafinsa kuma bai musa ba har aka bashi damar aurenta ya amsa da murna ta zama matarsa a dan kankannin lokaci ashe ba zasu raya zaman auren tare ba?
Fararan hannayensa ya saka da suke dake ya dora saman fararan kafafuwan nata
A hankali ya idasa saka hannunsa ya saka kansa cikin motar baki dayansa
Daidai lokacin da kunnayensa ke jiyo masa kukan tsofafin da suka rakota dakinta kamar haka" ashe ba zaki ga dakinki ba Bintu, Allah ya jikanki da rahama Binta, Allah ya haskaka makwoncinki salihar yarinya mai hakuro da nagarta
Zuciyarsa ce ta doka da sauri ya saka hannun nasa ya yaye rufar da akaiwa fuskarta
Fuskar nata ya tsurawa ido
Fara ce sal, sannan fuskar nata ya amshi mahaukaciyar makup mai iya doka zuciya ta saka a ji an kamu da son mai dauke da ita
Irin gashin idon nan natural ta saka mata shi ya yi mata wani irin gazar gazar duda idannuwanta a rufe suke ruf domin Anmy ta rigaya da ta shafe mata ido
Dagowa ya yi a karo na farko ya bi mutanen sake wajen baki daya da kallo
Muryarsa a saukake ya ce" ku je
Daga ku je din bai dora komai ba, sai dogarai dake faman aikinsu
Ya rage daga Anmy sai y'ayanta sai manyan datijan dake wajen
Kansa a kasa ya furta" iyayenta sun ji?
Anmy ta gyada kanta ta ce" yaya ya tafi wajen mahaifinta dan na jima ina kiran layinka bana samu, sai daga baya na kirayi amintacenka
Kansa ya gyada a hankali ya kuma fadin" zan kimtsata da kaina, zamu kwana yi mata adu'a, Anmy in sha Allahu zata samu sutura nagartaciya zata yi makotaka da Abih da kuma Aliyu, ina fatan da kuma adu'ar ta kasance a fadar ma'aiki
Salalahu alaihi wa salam suka amsa a hankali
Anmy ta ce" a ina zaku yiwa gawar karatun? A ina zaka kimtsata?
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa mai zafin gaske ya ce" a bangarenta
Hannunsa ya kara mikawa ya kamo na mahaifiyarsa