Showing 141001 words to 144000 words out of 228147 words
Chapter 48 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
karon a kasan zuciyarta ta ayanna" Allah ya isana mugu, ai nima me zan ci da farin mutun? Nan da nan ka wani koma ja uwa k'osai, daga an yo abu fuska ta zame maka ja, ko rana ka shiga sai ta dafe maka fata, Allah na tuba na ci me a farin mutun banda mugunta me ka iya, ka ci nasara ta biyu a kaina aman ba zaka kuma gannina bama bale har ka wulakanta ni! Kuma na fada mai cinye kudin talaka, yo in ba cin haram ba ji bayin da ake wanka ko na Anmy albarka, sai na yi girki a wajen nan na ci, to na godewa Allah nima ba mabaraciya bace, da sana'ata bale har kaka naka yi ta kawo ni neman taimako."
Wankan take da ruwan masu zafi tana ta fadace fadacenta a kasan zuciyarta har ta gama ta dauki sabon tawul ta lulubama jikinta tana jin kirjinta na mata nauyi domin bata saba wanka tsakiyar dare haka ba gata da ciwon huka.
A hankali take takawa, du irin ruwan da ya ringa sakata ji take uwa ana tsikarinta da allura, haka kuma wani fayau take jinta uwa an wawushi wani nama mai yawa a kasanta.
A hankali ta idasa fitowa daga bayin tana sando, so ta yi ta ficewarta komai ahirun fadar da abubuwan tsoro yau a wajen Anmy zata idasa wayewa.
Sai dai tana fitowa ta ji an kama tawul din nata an shiga gogoge mata ruwan dake jikinta.
A tsorace take binsa da kallo har ya gama ya karb'e ya yi gaba da shi.
Da sauri ta nufi wajen da take gannin abin rufa dan rufe jikinta sai kuma ta rage tana furta" aushhhhhhhh!"
A k'asan mak'oshinta
D'akin ya d'auki dumi mai dad'in gaske sakamakon abin dumama daki da ya kunna ya kashe AC din domin ya san tana da ciwon Athsma ga garin ba laifi garine wanda daukan zafi du kiwa da irin manyan duwatsunsu
Lulubawa ta yi ta yi zaune a bakin gadon tana binsa da kallo dan gannin karshen gudun ruwansa
Shima saman kujerar dake facing din bed din, inda take zaunen ya hau ya zauna, sai da ya dan gyara zamansa irin na sarakai sannan ya kura mata ido irin yanda take kallonsa
Furtawa take" mugu, azalumi, mai kwacen abinda ba nasa ba, sai Allah ya saka min irin hararan nan da kake min, kuma na rantse daya bayan daya sai na tarda matanka na daki banza har dakinsu idan ya so ka kule ni a dakin kaji!
Shi kuwa fuskarta kawai ya kurawa ido, yana furta" inama ace baki da taurin kai? Da na kwatanta mayar da ke yanda nake son ki kasance, idan dare ya yi ki kawata min lokacina ta hanyar wankeni da bakon yannayin da kika sakani, shin me kike tunani? Yanda zaki yi da ni ko? To nan gani nan bari, kuma ba dai saki ba? Ba zan sake kin ba, tunda na ci wake a lambun nan, ba wanda zai ci irinsa, MAGE KAWAI MAI KWONCIYAR DAUKAN RAI!
...........ma ji, ma gani, ma gane waye Magen tsakanin mutanen nan biyu........baci dai ya iya sata........kuma baya yafe bashi.
Talatainin daren nan ya faru cikin wani lamari mai wuyar fasara
Mutun biyu ne tsaye a cikin duhu, sunna magana wace bata fi a irga ba aman yannayin taba hannayensu ya fi yawa
A shafe nake, tun shekarar da aka so shafe shi ta same ni, gashi ya ajiye har uku yana bin daya bayan daya bayan ni nawa iyalan sun barni
Dayan ne ya furta" kai naka iyalan ai ka tara, ni ban tara ba, ba kuma zan tara ba har sai na rama!
Abubuwan hannayensu suka cenza kowane ya dauki hanyarsa suka shige ciki
.........................................
Kowa da irin shiryawar da ya fi ganewa da ita
Kamar yanda magaifiyarta ta fantsama neme nemen malaka, abubuwan da zata kasance ta malake shi sai yanda ta yi da shi, tana zuba tsabar dukiya tana amso yan kuli bisa yarda da ta yi cewar wanda ya bata kulin ya isa ya zartar da hukuncin abinda take so ita da yarinyarta ta dawo ta kuma dukufa ta ci gaba da dadaure Zinaria da kalamai irin na....ki turara, ki tsuguna, ki yi wanka, ki kurba, mu binne inda aka ce a binne, ina mai tabatar maki na lungu baya karya
Cike da kalaman nan har hankalinta ya fara dawowa jikinta, hakan ce ta kasance a yau tsakiyar dare suka fito suka yo bine binen, kafin ta bude mata abubuwan turaren ta saka mata
A lokacin da ta fara turaren ne ihun NAJEEBA ya karade wajen, wanda in dai ka kusanci bangaren tabas zaka jiyo sai dai ka yi kamar baka jiyo din ba
Wannan ihun ya kusan summar da ita harma ta shiga kuftayar son zuwa dan ta ga ko menene
Janta uwar ta yi, a lokacin suka hade da munafukin nan
Murya a kausashe Gimbiya ta furta" ko da rai, ko ba rai, ko da hankali, ko babu, ko da yarda ko da karfi sai sun bara maki fillin mulkin ki! Tana maganar tana idasa janta cikin bangarenta ne hankalinta du a tashe domin kuftaya Zinariyar ke yi kan lale lale sai ta je bangaren Sultan dake zazagaye da dogarai
Niyarta daya ta idasa shigewa falon da ita tana kara rike abinda ta amsa a hannun mutumen kafin ta shiga kai kawo yayun Zinariar na tambayar abinda ke faruwa
Rai bace ta ce " wani irin rashin mutunci ne za'a ringa jin ihun mace a bangarensa? Ba zai iya hannata ihun ba sai ya buda an san abinda ke faruwa da ita ko sallon iskanci ne tsagera ce itama wace yake taren da ita? Wacece? Me ta zo da shi? Tabas zan nemi mu je Agadez da Zinaria, dole zan kai y'ata na shiryata a wajen da zan yi abinda na ga dama ba tare da an dakatar da ni ba, dole zan nemi layin Sarki na fada masa rashin lafiyarta sai mun zo gida!
Su dai yayun nata sunna son danarta ne, aman sun san da kamar wuya mahaifinsu ya yarda da a zo da ita gida,
Zinariya kuwa bata taba jin tsana mai tsanani irin ta yau ba, bata san da wace yake tare ba aman abu daya da ta sani koma wacece sai ta ga bayanta, har ya kai ga zuwarma wata?
Gujin kuka take ido rufe hannayensa a daidai kirjinta
Hasko irin tsarin mijinta, sansanyan kamshin jikinsa, ni'imatacen laushin fatar jikinsa, takamarsa mai kara sakata macewa a kansa, kamshin bakinsa mai sanyi da saka nutsuwa, du ya anfanarwa wata? Sam bata son kawowa ranta cewar zai iya kusantar Najeeba, qbu daya take son tabatarwa cewar Nadia ce, idan kuwa ita din ce ta rantse sa hannunta zata kwakule mata du wani abin anfanuwa na jikinta! Ta tanata a irin yanda ta lura sam Najeeba bata cikin wa'inda zasu iya samun alfarmarsa, hakan ya sa ta yarda da maganar mahaifiyarta cewa ta sada kanta, ta yaki lamarin a hankali ta kasan kasa,
....................................
A hankali wani baci mai nauyi ke fuzgarta , ga ciwon da jikinta ke mata , a zaunen nan da take ita kadai ta san irin azabar da take ji a kasanta , ta luluba sosai har kuma zafi ya fara damunta aman ta ki sararawa jikinta sonin tsoronta Allah gudunta ta kuma rufe ido wa'innan idannuwan nasa masu dauke da kwali da wani irin launi da ya tsaida tar a kanta na sakata cikin yannayi na shaku da taka tsantsan
Daga inda yake zaune, bai taba kasancewa a nishadi irin na yau ba, dadin kallonta yake ji a kasan zuciyarsa, murmushi yake a boye wanda sam ba'a gani
Sarai ya san tana jin wahalar zaman nan, aman yana kallonta dan ya ga irin jarumtarta, ai ko da yar yatsa aka kaiwa wajen nan zihara za'a ji jiki bale uwar yatsa
Muzgutawa ta yi , baci na rinjayarta, kanta na kara nauyi ga ciwon da yake mata ta kwonta a karkace tana hangensa
Tun tana ganninsa har ya kasance kamar ta sume, ta daina fahimtar komai ta daina gannin komai, ta shige wani irin baci mai tsananin nauyi
Ajiyar zuciya ya sauke ya kai dubansa wajen agogon dakin
Gannin karfe biyar ce ke shirin yi ya saka shi mikewa a hankali ya nufi wajenta.
Hannunsa ya saka ya gyara mata kwonciyar da ta yi ya kuma zubawa fuskarta ido na dan lokaci
" *Who are u NAJEEBA?"*
Karasawa ya yi bayi ya kuma dauro alwallah ya fito.
Kad'aice kansa ya yi ya shiga bautar ubangijinsa cike da nutsuwa mai girman gaske.
A inda yake zaune sai da haske ya fara nuna kansa kafin ya d'ago kansa daga dukufar da ya yi yana jan carbi.
Adu'a ya yi ya shafa sannan ya mik'e ya koma d'akin.
Tun kwoncinta ne dai bata juya ba, da ka ga kwonciyar ka san a takure take, a gajiye take.
Ya saba komai gajiya a irin lokacin nan yake shiryawa, du irin bacin da yake ji kuwa ba zai iya zama bacin ba.
Wanka ya tsalo ya dawo ya shirya kansa cikin shiga ta alfarma kafin ya fita ya yi zaune saman kujerar dake facing d'in wace komai ya wakana tsakaninsa da ita a tsakiyar daren nan.
Idanuwansa ya lumshe yana girmama lamarinta a cikin zuciyarsa.
*"SHAHEED, BANA SON KA, MUGU, BANA SON FARIN MUTUM, SAI KA SAKE NI, HUZAIFA."*
Kalaman nan ya yi wani waje mai girman gaske ya ajiye su,
zai iya rantsewa ko Anmy sai ta kakare take fad'in sunansa kai tsaye.
Ko da ranta a b'ace yake zata sanyaya muryarta cike da rarashi ta kwatanta masa.
A fannin mace kuwa, bai tab'a had'uwa da macen da ta kalleshi shi SULTAN SHAHEED ta kama sunansa gatsai haka ba, sannan a irin damk'ar da ya mata ta kuma duban idanuwansa ba.
Murmushi kawai ya yi, idan har bai zurfafa a sanin wacece ita ba , akoy damuwa.
.....................................
Hannunta da ta tokare gefen kumatunta UMMU ta kama ta cire tana kallonta ta ce" yaya wai meye wannan dan Allah?"
Anmy ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubanta wajen agogo ta ce" MARIAM, karfe goma ta gota bai yi kira a je a rako min yarinya ba, Maryam ko dai zuwa zan yi?"
Idanuwanta ta zaro cike da mamaki ta ce" Anmy, ki je ina? Sai ki je ki ce me ya tsayar maki da yarinya? Kin ga fa su Zahrau du sun yi wani iri yau na ga ikon Allah, ita Zahrau tun dazu jake fama ta tashi ga mai kitso da kunshi a shiga yi mata domin gobe walahi zata juya gidanta aman ta ki tashi da waya a hannu wai ko zai kirayeta? To cinyeta zai yi ni NANA MARYAMA? kun ga Bayan kun san yau DAYABU ke kawo yarinyar da yake nema kuma du sai ku wani baje a nan? Dan Allah ku tashi hakanan."
Jakadiya ce ta shigo ta duk'a ta shiga kwasar gaisuwa.
Du Anmy ta yi tsai tana jiran ta ji labarin NAJEEBA ne sai kawai ta ji wai MARDIYA ke neman iso
Da sauri ta kai dubanta wajen Ummu, ta kai bayan UMMU tana goye da NUSAIBA ne wace ke dan zazabi tana dan rigimar zazabin
Mardiya? Ta tabata yarinyar a yanda bata da kunya zata iya yin wani abin na rashin kunya, du abinda ke faruwa ita dai tana kiyaye abinda za'ace an yi da ita, du tsakaninta da yara suke fadace fadacensu
Aman tana tsoron idan har UMMU zata iya hadiye wani iya shege duda yanzun UMMUN ba irin ta da bace aman duda haka tana shakun UMMU.
A hankali Anmy ta ce" ita da waye?"
Jakadiya ta k'ara sada kanta sosai ta ce" Ita da wata mata ce wace zasu yi sa'anni, inaga ana yawan zuwa shara'a da matar wannan wace ake kira da wudiliya."
ANMY ta kuma kallon UMMU sai ta ga ta koma wajen Zahrau ta karb'e wayar hannunta ta nunata da yatsa a kausashe ta ce" ZARA MUTALAB , ko ki mik'e ki cire hijab d'inki a maki kitson nan ko na jibgeki na rantse a wajen nan!"
Da sauri Zahrau ta mik'e tana cire hijab d'in, muryarta a raunane ta ce" Ai da wuri yake kira a d'auko wace ta fara kwana b'angarensa, ai da wuri yake kira tun da duhu duhu, *ina NAJEEBANA? LAFIA HAR YANZU BA'A NEMI A ZO A RAKOTA BA KAR DAI A JE ABIN YA MASA YAWA NE UMMU?"*
Ummu ta saki baki gannin zata tona masu asiri dan kawai ta firgice.
Anmy ta kalli jakadiya ta shiga tunanin me zata ce mata? Baki daya y'ayan na nan, Dayabu na hanya uwa uba UMMU, NAJEEBA na iya shigowa yanzu ko idan an jima,
Shin zata yarda ta shigo bayan ta santa da neman fitina ta tada mata rigima a irin wannan lokacin ko zata hannata shigowa ne?
A sanyaye Anmy ta kuma kallon jakadiya dake jiran amsa kafin ta bud'i bakinta ta ce"...
[31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
45
A sanyaye Ammi ta ce "Ki shigo da ita"
Har ta mike za ta fita Ammi ta kuma faɗin "Ki kai gaisuwata ɓangaren Sultan"
Kuma ɗukawa ta yi cike da ladabi da biyayya ta amsa kafin ta tafi.
Ba'a ɗauki lokaci ba suka shigo.
Wata irin kwalliya ce jikin Mardiyya, ta sha wani rantsatsen lesh an yarfa mata mak'up
Tunda suka shigo hankalinta ya tafi wajen yaran,
Bayan wacve ke goye da Nusaiba kawai take iya hangowa, Ummu kuwa na tsaye ne tana nuna irin kitson da za'a yi wa Zahrau.
Zama suka yi saman kujera sannan suka shiga gaishe da Ammi
Ammi ta amsa masu cike da kulawa tana ɗan satar kallon yaran , sam ba wadda ta yi yunƙurin gaishe da Mardiyya, ko damuwa basu yi da ita ba
Kwarai bata ji daɗin hakan ba duk da mutum shi ke janyowa kansa mutumci ko akasin hakan, amman ai tarbiyyarsu fa?
Sai da ta sadda kanta a hankali ta ce "Allah ya taimake ki, dama kan maganar Abban Nusaiba ne na zo, kwata kwata ya zubar da ni, ya yi block din numbobina ba gabaɗaya da nake samunsa, hatta Mama sai da ta saka a neme shi amma ya ki zuwa, gashi ni ba sakina ya yi ba"
Dan saurarawa ta yi ta dan dago dan gannin shin tana sauraronta?
Gannin Ammi na kallonta da kyau ya saka ta ci gaba da faɗin "Idan laifi na masa tsakanina da shi ai ya ci ace ya yafe, idan kuwa fadana da yara ne ba ruwansa ya fita a ciki domin tsakanina da su ne"
Da mamaki Ammi ke kallonta a kasan zuciyarta kuwa faɗi take
'Ikon Allah, wai ita a gidansu ba'a fada mata ka so mutun ka so d'ansa ba?'
Dubanta ta kuma kai wa wajen Ummu dake dan jijjiga Nusaiba, ko nauyinta bata ji haka take jibgata a baya ta yi ta jijjigawa, a yan kwanakin da ta yi da yarinyar ta matukar sabawa da ita domin yanzun Mama sak take kiran Ummu da shi kamar yanda sauran yaran ke faɗa.
Mikewa ta yi ta nufi wajen
Muryarta a dan dake ta ce "Sannu fa?"
Dakatawa Ummu ta yi ta juyo daga wajen yaran dake ta mata surutu
Ido cikin ido suka kalli juna, ita dai bata santa ba, sam bata taɓa haɗuwa da ita ba, ko hotonta bata sani balle ta shaida ta.
Ba wata shigar firgita mutum ce a jikin Ummu ba, domin riga doguwa ce sakakkiya baka a jikinta
Sai dai yannayin tarin kamalar da fuskarta mai cike da yalwataccen gashi da ɗan murmushi ya saka Mardiyya jin shakkun yi mata magana a gatsai gatsai
Dan haka sai ta dan kakari murmushi ta ce "bani ita na rarrasheta ko zata yi shiru?
Kallon da Ummu ke mata dan ta fahimci ko wacece ita, sarai ta san matar ta hoto amma ko ita bata taba haɗuwa da ita gata gata ba
A hankali ta ringa kunce goyon kafin ta juyo da Nusaiba ta mika mata ita
Da farko idon yar a rufe yake, hakan ya sa ta yo lufff a jikin Mardiyya, sai da Mardiyya ta ce "A'a, bata da lafiya ne? Jikinta zafi haka me yake damunta?"
Jin muryar ya sakata buda idannuwanta
Kallonta take kafin ta fara rigimar sai ta koma wajen Ummu (idan baku manta na Nusaiba yarinya ce karama, ko a haka Mardiyya ta kasance mai yawan zaginta hantararta da yawan faɗa, a rayuwar yanzu ko ɗan naka ya mallaki hankalin kansa sai da addu'a da kawar da kai, bare yar yarinyar da ta samu mai rarrashinta da nuna mata soyayya hakan na iya haifar da son nisantar mahaifiyarta da ta haifeta, karamin abu ne hakan)
Da mamaki ta kalli Ummu, da yanayin shashanci ta ce "ke ko har kin canza uwa ne haka zaki ringa kuka a hannuna?"
Ummu kam wajen ta bari ta koma saman kujera ta zauna tana mai bin Wudiliya da kallo wace ke zaune tana bin kowa da kallo itama
Wani murmushin ta yi ta kuma maida dubanta wajen yaran
Da idannuwanta take gallawa duk wanda sukai ido hudu harara, sai dai a yanayin yanda ta lura sun rigaya sun hade kan nasu na iya shege wato kar wanda ya gaishe da Mardiyya?
Sallamar Dayyabu ne ta saka su duban wajen
Shine ya fara shigowa cike da yalwatacciyar fara'a a fuskarsa
Bayansa wata yar budurwa ce kyakyawa fara tas , ta saka abaya baka har kasa ta yane kanta da mayafinta
Du sai yaran suka shiga murnar zuwansu
Zahrau ta mike tana yafa dan kwalinta cike da nuna kulawa suke yiwa budurwar yayan nasu barka da zuwa
Kasa ta zauna kanta kasa tana murmushi tana dan murza yan yatsunta, shi kuwa yana zaune kusa da Ummu yana mata magana kasa-kasa, haka kuma kannansa duk sun zagaye shi ban da Zahrau da ta shiga hidimtawa bakuwar cike da fara'a
Hannun Bilkisu ya dan doke ya ce" Mairama ki barni da tsegumi