Showing 81001 words to 84000 words out of 228147 words

Chapter 28 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10392

fuskarsa ta yi, tabas Huzaifa namiji ne mai kyau bakar fata ne shi mai tsafta,
Yana da fara'a sosai gashi mai tsayi daidai misali, yana da kakauran jiki sannan yana da dan tumbi na jin dadin rayuwa

Murmushi ta yi tana cire idannuwanta daga kansa,
Wayarta ne ta dauki kuka da wakar su akon wace yake fadin For ever i love for ever........ da yake ta kuma ajiye wayar a saman kujera ya saka du suka kai dubansu

*LIKITAN ZUCIYATA* , shine ke haskowa a saman sunnan mai kiran

Bata damu ba ta mika hannu ta dauko sannan ta daga

Salama ya yi mata kafin ya furta" ina cike da begen ranar da zan ganki, shin kina Niger kuwa?

Sai da ta dan saci kallon Nadia ta ga kamar zata dauketa da mari sannan ta dan yi murmushi tana satar kallonsa sai ta ga fuskarsa ta dan cenza daga yannayin fara'a zuwa sad

A hankali ta ce da shi" zan taboka Likitana

Shima murmushi ya yi ya kashe yana fatan ta tabo shin

Idan kana da time, ranar Wednesday ka zo fada

Farin ciki ne kuma ya mamaye zuciyarsa harma ya kasa boyewa da yatsunsa ya irga cewar....nan da kwana uku ko?

Kanta ta daga hakan ya sa ya mike, chek din da ya rubuto makudan kudi ya ajiye kusa da wayarta sannan ya juya yana murmushi ya masu salama

Da sauri Nadia ta dauki Chek din tana dubawa sai da ta yi dan ihu kafin ta ce" ke, wai kin san nawa ne?

Najeebama tana ta daria tana kallon chek din ta ce" da alama dan uwanki banar harka ne

Nadia ta ce" Najeeba ina fada maki ko waye shi kennan baki yarda ba? Babar harka ne,

Najeeba ta ce" na san waye shi, abinda ya sa na bashi matsayin babar harka nawa suke da kudi aman basa iya cirewa su yi kyauta da su? Sai ki ga sun tatare budurwa ita ba ga wani ba sai su kadai aman dan iskanci kudin zuwa saloon sunna bakin cikin bata? Gaskiya irin mazan nan basu da Mutunci!

Nadia ta ninke ta soke mata ita cikin jakarta tana fadin" bana tunanin zai kasance irin mazan nan, domin ni kaina dominki kwana biyun nan hajia ce bale ke

Ita dai Najeeba litafin da ake rubuta wa'inda suka nemi mak'up ta dauka tana ta dubawa dan gannin wanda zasu samu

Sai d yama ta yi sosai wajen ya kuma fara saukan mutane masu fitar dare

Ita dai zuwa lokacin sai ta kilace kanta sunna hira da yar uwarta wace ke magana kasa kasa bata jin dadin jikinta domin a jiya dai sarki sai da ya karbi sadakinsa

NAJEEBA ta zaro ido tana ganni uwar sarkar da ya baiwa Zahrau da makulin mota da hoton motar da kyautar wasu kuyangin amana kafin ta ce" Zahra wai kyautar meye wannan?

Zahrau ta yi murmushi kawai ta ce" zaki san ko ta meye, ba yanzu ba

Itama murmushin ta yi tana kallon uban badon da ta markada ta zabga masa madara da karanfani fiye da adadin da aka bukata ta kafa kai ta shanye
Zahrau da suke vido call ta zaro ido ta ce" Najeeba, ba zaki daina shan kayayakin gayran jikin nan ba ko? Gashi wa'inda kike dura min sai da na raina kaina , Najeeba sai da na ringa maki Allah ya isa

Najeeba ta yi murmushi tana gyara kayan gefe guda sannan ta rufe frij dinta ta koma ta zauna ta ce" aunty, ko gobe na ji abu naturel wanda zai sharen fage ya gyaran jiki zan yi na sha abina dan a gaskiya ba zama zan yi sai an tashi yi min aure a shiryani ba

Zahrau ta girgiza kai ta ce" anya ba babar mai jaraba bace ke kuwa? To yanzu idan kika auri mijin da hakan bai dame shi ba?

Najeeba ta yi murmushi ta ce" aunty ai shikenan, kin manta ban saba ba bale hakan ya wahalar da ni? In sha Allahu ko wani kalar miji na samu shi zai horani ta yada yake so na zame masa

Zahrau ta yi murmushi ta ce" wa kika tsayar? Dayabu ya fada min komai, dazu mai martaba ya turon sakon na tura number Ummu yarima na tambaya zai kirata , ke da Ummulkhair ku na sako gaba yanzun

Najeeba ta koma ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" ni kaina ban sani ba, abinda nake son yi zan tsaida kwara biyi, a cikinsu sai na kaiwa Allah kukana kan ya zaba min daidai da ni

Zahrau ta gyada kanta daga ringeshen da take, tana mai adu'ar Allah ya basu mazaje na gari, kwari ta yi mamakin irin yanda Najeeba ta yarda zata fitar da miji haka cikin sauki, sannan a yanzu ta kara jin nutsuwa ta shigeta jin cewar Najeebar da kanta ta kara jadada mata har Najeeba ce zata fitar da miji? Lale ta yarda kanwar tata ta fara zama mutun mai nutsuwa

Sun sha hira kafin suke katsewa ta barta cike da tunanin abinda ta fada cewar su janyo yar uwarsu jikinsu
To ita ta ina zata fara wannan lamari bayan Abih bai san cewa sun san da maganar ba? Yarinyar kanta menene halayenta shin tana da ra'ayin kasancewa da su a matsayin yan uwanta?

Bayan salar magariba ta shirya cikin wando da rigarta na spot ta saka takalmanta tun a nan kafin ta dora hijab dinta dogo har kasa ruwan ja mai duhu

Salama ta yiwa yaren shagonta ta harhada kudadenta cas sannan ta fito daga ciki

Bude mata daya ya yi da gudu sannan dayan ya zagaya ya shiga wajen direba ita kuwa ta shiga baya ta zauna daya ya zauna gidan gaba suka dauki hanya

A hankali ta masu bayanin inda zasu fara zuwa

Sunna zuwa ta ciro jaka goma ta mikawa na zaunen ta umarce shi da ya yo nama leda biyu a saka tukunya a dayar mai zafin gaske

Fita ya yi ya siyo naman ya dawo yana kokarin ajiye mata

Mai dauke da tukunyar ta ware ta mika masu dayar ledar, dan murmushi ta yi ta ce" na san baku ci komai ba ko? Ku ci abinci mana kuma ina dalili wai wannan kamewar? Kun ga dai ni kanwarku ce ba ruwana ba abinda zan maku ku ci abincinku mu je stade bangaren basket ball a cen zan buga ball yau
Kasancewar ta yi bayanin sport dinta harma Anmy ta amince sai dai ta fada mta cewar lokacin da aka yanke mata kar ta saki ta wuce shi a waje ya saka basu yi gardama ba, sannan alkhairin da ta masu ya saka suka ji dadi dan walahi yinwa suke ji an basu kudin abinci fa kawai ba damar su motsa ne yau suka fara aikin nan dole haka suka wuni da yinwarsu

Sunna karasawa ta cire hijab dinta daga cikin motar take hangen wajen

Terrain din bashi da dati ko daya, shi terrain din ne bai cika samun mutane a ciki da dare ba, da yama aka fi basket a samansa idan dare ya yi sai ya zamana yan gayun yan kata da samarinsu ke zuwa su yi zancensu a nan
Daidaiya zaka ganni a saman wajen sun zo buga basket

Shi daya kwal ta gani da wata irin ball a hannunsa
Irin yanda yake juyawa ya daka tsale ya jefa ball din cikin raga ya sakata shagala da kallonsa

*Freind* ta furta a hankali
Ashe kana basket? Ta kuma tambayar kanta

Sai ta ringa jin wasan na kara shiga ranta irin yanda yake bugawar sai kace wani jordan

A hankali take karasa takawa har ta isa

Bata yi masa magana ba sai gudun da ta fara shi kuwa tun da ta tinkaro amintacensa ke sheda masa ga wata na matsowa idan kar a barta ta karaso a tare ta,

Yana fahimtar itane ya furta" barta

Gudu ta ringa yi cikin nutsuwa da earpiece a kunnenta tana sauraron kidanta mai tashi a cikin sanyo ba kwaramniya

Sai da ta hada zufa jinna sannan ta shiga cirewa ta ajiye saman abin zama

A hankali ta ringa karasawa inda yake buga ball din shima ya hada zufar kamar me aman ya kasa bari dan ba yanzu yake bari ba sai ya gama bugawar yake zuwa wajen hutunsa ya dan huta kafin ya tafiarsa

Yi ya yi kamar a lokacin ya ganta ya juyo yana dan doka ball din tana dawowa hannunsa yana kallonta

Shamatarta ya yi ya cilo mata, da sauro ta cafe ball din itama ta shiga dan dokawa tana tunakararsa

Fahimtar da ya yi cewar tana son ta tsineshi ne ta je ta saka ya saka shi kokarin karewa yana tarewa ita kuwa tana neman hanyar bu tun karfinta

Sai da ya bari ta sha wahaka sannan cikin sauki ya karbe ball din ya juya ya yi wani tsalen da ya sakata zaro ido cike da mamakinsa daga inda yake ya cila ball din ta shige zuruf wato 3 point

Abin ya kayatar da ita, hakan ya saka ta shiga tafawa tana yar dariya cike da mamakinsa

Ai kuwa nan wasa ya bale suka ringa yi sunna kasawa da gudu sunna kilkila dariyar da su kansu basu san ta yi nisa har haka ba su dai dariyarsu suke sha idan ya amshe ball din

Ball din na hannunta ya dagata sama da hannunsa daya yana mata daria kadan kadan

Irin yanda take daka tsale tana fadin ya tsaya dai ya ga ikon Allah sai ta kamo ya shagaltar da shi harma ya kasance idan ta daka tsalen kanta na dukan kirjinsa sannan da hannayenta ta saka ta daki kirjin nasa tana fadin" in ba tsoro ba baki korere mana

Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa ya sakar mata ball din

Warta ta yi da gudun tsiya ta nufi ragar
Sai da ta karasa ta wurga ball din
Ai kuwa ta shige ciki hakan ya sakata sakin dan ihu na murnar ta saka sannan ta juyo ta shiga kwaso shoki tana watsa masa

Daga inda yake bai motsa ba sai hannayensa da ya harde yana kallonta
Murmushi ne ya subuce masa a lokacin da take kwasar shokin nan kafin ya dan girgiza kansa ya cire kansa daga dubanta yana gannin yanda mutanen dake zaune sunna zamcensu suka dauki hankalinsu harma suke kyakyata dariyar lamarin da masu yi mata tafin ta saka daya kwal bayan tun dazu yake ta sakawa ta kasa sakawa

Kansa ya dan girgiza ya juya ya nufi wata lafiyayiyar kujerar da aka ajiye masa da ruwan gora da abin goge zufa fari kart sai kamshin fitinanen turaran nan nasa yake ya yi ya karasa ya zauna

Ba din ta dauko ta kara jefawa sannan ta kuma daukowa tana kallonta ta gane ba karamar ball bace irin wa'inda ake kawowa daga americar nan ne masu tsadar gaske da karko

Wajensa ta karaso tana jin mugun kishi dan kana gannin fuskarta zaka gane ta sha wahala sai shasheka take sosai

Goron ruwan da ya bude ya kafa kansa ya dan sha kadan take kallo
Gannin ya sha sai ta cire kanta a wajen tana gannin yanda yake dan goge zufar jikinsa har wajen wuyansa
Ball din hannunta ta nuna masa ta ce" ball din nan ta kanpani Kapto ce? Ko copy ce?

Shima kallo ya yi kafin ya yi dan murmushi, wai copy wato ba zai iya siyanta ba take son sani ko?

Sai ya dan daga kafadunsa ya ce" ita ce, yayana ya siyan min

Bakinta ta dan tabe tana son ajiye masa ya miko mata ruwan dake hannunsa yana dan lumshe idannuwansa ya shafa shafefen cikinsa wanda ke dauke da wani irin gida gida masu tauri irin na masu sport din nan yana fadin" yinwa nake ji, gashi daga nan zance zan je

Ruwan ta tsurawa ido, ta dan makale kafadarta ta ce" ka kafa bakinka fa, kuma sai kawai nima na kafa?

Da mamaki ya kalli ruwan ya kuma kallonta

Murmushi ya yi ya ce" da zan fito fa sai da na yi broch kuma kin ga ban ci komai ba, sannan bakina baya wari

Itama murmushin ta yi tana kara makale kafadarta ta ki amsa

Juyawa ta yi ta daga hannunta

Su dama ita suke jura sun ci sun yi hani'an

Ledar ya fito da ita ya karaso ya kawo mata sannan ya koma ya zauna sunna jiran ta gama su tafi dan su kansu an masu gargadin daga bakin inda lokacin zuwanta gida ya yi koda a sume ne su maidota gida

Yannayin mamaki ya nuna a lokacin da take miko masa naman ya ce" aman, kika ce min baki san sarkin garinnan ba kuma na ga dogari guda ya kawo maki abu ko dai ke din y'arsa ce?

Da sauro ta kale shi, sai kuma ta yatsina fuska ta ce" ni kuam zai haifa? Yaro ne fa! Bayan wannan ai ba lale na sanshi ba, ni ban taba ganninsa ba kuma ko na ganshi ban sanshi ba tunda baya cikin tsarin mutanen da nake son mu san junna
Dan Anmy dina ne!

Tun da take maganar ya tsura mata ido da mamakinta, kai, shine yaron? Innalilahi sai kawai ya ringa jin me zai hana ya wanka mata marin da zata fita hayacinta har ta buda wannan muryar tata mai kwari ta fasa ihun nan kamar an kasheta?
Yau shine wannan ficiciyar yarinyar ke ce masa yaro?

Amshi mana,

Ta fada tana kara mika masa naman

Shima kafadarsa ya makale kafin ya ce" nima bana ci, na san ko kin saka a bakinki?

Da mamaki ta wangale baki tana kallonsa,

Sai da ya dan hade fuska ya ce" aman me yasa kika raina sarkin garin nan bayan na ji irin yanda ake tsoronsa?

Kafadunta ta daga ta ce" nima raina ni ya yi ai

Ido ya kara zarowa yana jin har kamar kirjinsa ya fara zafi yana kallonta , tabas ya tabata dole ya shaketa ya kara summar da ita a karo na uku a wajen nan

Bai idasa jin lale dole ya hukuntata ba sai a lokacin da ta kara dan gyara tsayuwarta tana duba agogon dake cikin wandonta dan tafia zata yi ta ce"
[31/03 à 21:39] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



27


A firgice, a rikice, a tsawace Anmy ta ce" yaya muna cikin wannan tashin hankalin zaki yi mana wata tambaya kina mai kokarin tirke mun tamkar kece uwarmu mu kuwa y'ayanki?

Baki daya yan matan sai abin ya basu mamaki, yannayin Anmy din ya saka jikinsu ya yi sanyi harma du suka zuba mata ido da wani irin duba na mamaki

Anmy ta kawar da kanta tana jan hancinta tana kara rintse idannuwanta da sukai mata luhu luhu ranta hade ta ce" ku tashi ku je dakin ku

Jiki sanyaye du suka mimike, Najeeba ta kara waigowa ta kalli mahaifinta ta ga kansa a kasa sannan hannayensa sai rawa suke, ta kai dubanta wajen yayansu ta ga shima kan nasa a sade shi kuwa kuka ne yake a hankali ta saci kallon mai martaba ta ga ya yi wata kwonciya a jikin kujerar ya daga kansa sama idannuwansa lumshe rawanin dake kansa ya kara fadi sakamakon yannayin kwonciyar nasa, shigar alkyaba ne a jikinsa mai ruwan duhu wace ke da igiya wajen wuyanta, fari kal din hannunsa daya ne a waje yana rike da sandar girmansa dake ajiye a kusa da kafarsa, sai dayan dake dafe da gefen zuciyarsa

Da sauri ta cire dubanta a kansa ta juya da wani irin sauri ta bi bayan yan uwanta

Sunna shiga da sauri Ummulkhair ta zube a kasa tana mai dora hannunta saman kanta tana dubansu a rikice ta ce" shin kun fahimci abinda na fahimta? Kun gane cewar akoy wani gagarumin sirin dake damun mahaifinmu wanda da alama mahaifinmu ya shafa wanda nake kyautata zaton idan har ya fito fili mun kade?

Najeeba ta jefar da iPhone dinta saman kujerar dake ajiye ta cire alkyabar jikinta ta jefar ta zauna a kusa da Ummukulsum ta shiga cakuda gashin kanta

Dagowa ta yi da wani irin yannayi ta ce" aya ta kasance a kansa da wuri? Bai fadi haka ba sai da ya ji cewar wannan tsautsayi ya afku da Ummu? Me ke faruwa da mahaifinmu? Wace aya ce wannan ta kasance a kan ubanmu?

Ummukulsum dake share hawaye itama ta budi bakinta a hankali ta ce" sai jake jin tsoron abinda zuciyata ke fada min, sai nake jin tsoron abinda nake tunani

Ummulkhair ta ce" me kike tunani ummu?

Ummu itama ta dora hannunta a kanta ta ce" sai zuciyata ke ce min bayan mahaifiyata mai amsar kudin zina ce mahaifinama ya taba fadawa wata

Da sauri Najeeba ta matso kusanta tana daga hannunta da ihu ihu ta ce" ke ke, yi min shiru, walahi zan tsinka maki mari idan kika fadi cewar Abih ya taba yiwa wata fyade

Ummulkhair ta shiga yarfe hannayenta tana fashewa da kuka ta ce" Najeeba ai ba haka ta fada ba, abinda kike tunani ne kika fada kuma nima abinda nake tunanin kennan innalilahi wa'ina ilaihi raj'une me ke faruwa da mu?

Itama Najeebar baki daya kafafuwanta ne suka gaza daukanta

Tana kokarin zubewa kasa Dayabu ya shigo
Da wani irin sauri ya karaso ya tareta a jikinsa suka kai kasan tare
Da rarafe sauran suka karasa wajensa suka rungume shi sunna kuka baki dayansu

Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, yake maimaitawa hankalinsa a tashe ya shiga fadin" tabas kadara, mumunar kadara ta faru da kanwata, sai nake jin ba wanda ya kaini jin ciwo duda irin yanda aka fada min lamarin cewar ba da son ransa ba, duda na san Allah ya kadarto hakan, sannan har an yanke hukunci zai zama mijinki aman zuciyata ta kasa daina hawaye
Tsoro nake ji , walahi tsoro nake ji
Idan ita ummu ta faru da ita a wajen mutunci wajen da aka isa a tankwasa karfe komai taurinsa ku fa?
Shin wace irin kadara ce ta afkawa mahaifinmu ya aikata mana haka?

Da sauri Najeeba ta dago kanta tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login