Showing 165001 words to 168000 words out of 228147 words
Chapter 56 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
kin nunan cewa yawanci magungunnan nan na zamani su ke haifar da cutar sanyi, sannan wasun sunna hadasa ila a mahaifa, gashi kuma lamarin nan fa yanzu na shigo aman na gama gane cewa idan ba gyara akoy matsala, dole sai da gyara, me kike iya gabatar min dan na ringa anfani da shi? Idanma ke ke siyarwa muna so"
Balaraba ta gyara zamanta tana kallonta ta ce" Gimbiya Zahrau, ba duka magungunnan gyara suke da matsala ba, sai dai ganewar da mutane suka yi cewar mata mun haukace idannuwanmu sun rufe kan wannan lamari sai kowa ya tashi kai da fata shi mai magani ne, ina iya rantse maki wata mai maganin ita ke saidawa aman bata taba anfani da shi ba domin ita kanta bata san me ya kunsa ba bata yarda da shi ba,
A ganina a yanzu da kuke yaran mata me zai hanna bayan irin taimako da na tabata Gimbiya zata tsaya maku kansu irin na su kankana da ake yi da yusufa da sauransu, da su daguwar kaza da tantambaru, sai ku rike sasaken baure da karanfani da mazarkwaila, walahi Zahrau zan fada maki du girman nan nawa haihuwata uku ko? Bani da wani siri da ya dara wannan, domin ina jina sakayau, marata bata daurewa, ni'ima daidai misali alhamdulilah, sai ko ruwan dumi da karanfani idan na ji ina bukatar na dan kara matsewa ne nake saka karanfanin da gishiri kadan idan bana bukatar hakan iya ruwan dumin nan shine nake yi du asubar Allah na zuba a baban flask dina na rufe, da shi nake wuni ina sirkawa ina anfanina, ban ce maki idan na hadu da wani sirrin da na yarda da shi bana aiwatarwa kaina ba, domin kuwa mace dai yar gyara ce ko wacece dan kuwa ko satin da ya shige sai da na yi tataki har garin maradi wajen Hajia SAMIRA HARUNA ta yi min tukunyar nan da ta taba yi min, na maganin zafin da garin dahuwar, na zauna na cinye tas kafin na juyo idan kin kula na cenza mota, to a washe garin ne oga ya min kyautar nan"
Murmushi bayanane Zahrau ta yi, domin kuwa Tukunyar nan yau kwana biyu kennan da UMMU ta yi masu ita sai da suka cinye tas tas, gaske ta ringa haduwa da yannayi na jika haka kawai
Kudade ne masu yawa suka cakewa Balaraba kafin suke mikewa zasu tafi
Har sun zo bakin mota dogarai sun bubude masu da sauri sai Balaraba ta ce" Gimbiya Zahrau "
Dakatawa Zahrau ta yi ta dawo tana kallonta, Balaraba ta kamo hannunta na dama ta ce" Dan Allah kar ki fadawa Najeeba na ji tsoron bada wasu daga cikin sirikana, bana so ta ji haushina a kan hakan domin ita din ita ta koya min kitso da kunshi"
Murmushi Zahrau ta yi ta ce" ba zan fada ba "
Bangaren UMMUi kuwa cike da mamaki take kallon Bilkissu da suka gama sauraron Najeeba na fadin wai bata son auren mahaifinsu, hakan ya saka Bilkissun kama hannunta tana kallonta ta ce" MAMA, me ya ba zaki auri ABIH ba? "
Rasa mai zata ce da yarinyar ta yi, sai kawai ta shiga kikifta ido, NAJEEBA ta koma ta yi kwonce saman bed din tana kallon sauran sam basu wani damu ba kasancewarsu yara sosai, ita kanta Bilkissun dan shekarunta sun kai goma sha uku haka shi yasa ta fahimci abinda ake nufi harma ta ji kwata kwata ba dadi a ranta, dan tsaki ta yi ta cire kanta, haka kawai take jin haushin mutumen, wai haka kawai ya kwace mata yan kunnayenta?
UMMU ta kara kama hannun Bilkissu tana kallonta a sanyaye ta ce" Biki, ki yi hakuri kin ji? Ba kin mahaifinku nake ba aman ina bukatar ku min adu'a idan alkhairi ne Allah ya tabatar"
Kai ta gyada a hankali ta shiga jikin UMMU ta dora kanta, hakan ya sa NAJEEBA lumshe idannuwanta sannan ta mike a sanyaye ta fita ta koma dakinsu
Wata kwonciyar ta yi ta kuma lumshe idannuwanta tana ta tunanin rayuwa, a haka har yayunta suka dawo bayan sun gama nunawa AMMI abinda suka siyo da UMMU suka sameta a dakin tana kokarin yin baci
To dai bacin da bai samu ba kennan domin kuwa sai da aka saka jigidar nan tsaf aka tare nan ana ta training din tafia da ita a jiki sunna daria abinsu
Bayan salar isha'i UMMU ta kalli AMMI da kulawa ta ce" AMMI, ban ga yarinyar nan ta shirya dan zuwa wajensa ba"
AMMI ta yi murmushi kadan ta ce" kin san meye UMMU, sam ban ji dadin ranar nan da bai biyo bayanta ba, na san da kamar wahala na samu abinda nake so kai tsaye da SHAHEED, aman fa koda a kwatance ne ina so ya ringa kokartawa......u see ko waya bai bugo ya yi wani bayani ba, kamar wanda ya baro wata uwar mata aka kawo min ita nan, sarai na gane ta samu lafia , abinda ke faruwa nima ina son samun bambanci , a gaskiya ina son ya fara gane lamarin nan kala daban daban ne, sannan ina so koda kuwa cenza namijin da ka samu bisa tarbiyar da matarsa ta dora sa nada wahalar gaske cenza shi......aman ina son kwatantawa. Believe me na san a kan me nake magana, nd trust me sai na ga kul uwar daka!"
Dan murmushi kawai ta yi ta kada kanta ta ci gaba da jan carbinta
Cen kusan karfe tara UMMU ta yada zango a daki ta zauna kusa da yan matanta da suka fara kitson Zahrau
Kasancewar kannanu ne sosai, gashi kuma Dayabu ya ce a jibi jibi zata koma dakinta shan nonon ya isa haka ta dan dubi yanda Najeeba keda saurin kitso ta yi murmushi tana amsa sannun da suke mata inda Ummulkhair ta mirgino daga kwoncen da take ta dora kanta saman cinyar UMMUN ita kuwa Ummukulsum sai fama take da ruwan albasa da kumb a hannunta
UMMU ta kuma yin murmushi, ba karamin dadi take ji a rayuwarta idan ta ga yanda kan yaren nan ke hade ba, takan godewa Allah harma ta ji wani hawayen farin ciki na son silalo mata a lokacin da bata shirya ba tsabar jin dadi
Dubanta ta maida wajen sif ,cen sama ta ringa hangen sauran jigidar da suka rage kafin ta maido dubanta tana dan shafa gashin kan Ummulkhair a sanyaye ta ce" ina son magana da ku "
Su dukansu sai suka maido hankulansu kanta harma Zahrau ta mike itama sunna sauraronta, UMMU ta ce" ina so ne mu yi magana a kan rayuwa, duda ku biyu baku je dakin auren ba tukunnan aman du ba mai bacewa bace dan koda Allah ya yi bana nan kuka je dakin aurenku ina so ku rike wannan"
NAJEEBA ta kalleta da kyau, bata nan? Ina zata je kuma?
Ummu ta ci gaba da fadin" Tabas aure ya ginu ne da rayuwar Sex, sai dai baban abinda nake so ku gane kyakyawar mu'amala tsakaninka da mijinka shi ke sakawa a fi jin dadin komai, ina so ku yi kokarin jajircewa dan gannin kun wanzar da kyakyawar mu'amala irin ta shakuwa da fahimtar junna tsakaninku da mazajenku, ba wai dan kuj auri masu mata ba wanda ke kanki Ummukulsum zaki tare da mai matar ne halayansu ya saka ku hau kuma ku bi, ko kuwa ku ce da karfi da yaji zaku cenza su......aa, ita rayuwar baki dayanta yar dabara ce, yar siyasa ce, hakuri, da kuma fadawa Allah. Ba ina nufin kowani namiji ya saba da gim gim gim da matarsa ba aa, wani namijin matar tasa da ka zo ka tarda mace ce da ta san kanta, ta gane cewar idan har ya ci gaba da irin halayan nan na komai ba ruwansa ba ita kadai zai shafa ba harta da y'ayan da zasu haifa yana iya shafar su sai ta jajirce har Allah ya sa suka kasance aminan junnama ba tsorata zaki yi ba, zaki shige ne kema, zaki damki damar nan sannan ki dan kara naki salon da zuciya daya ba dan ki cutar da ita ko y'ayan mijinki ba. Idan kuwa namijin nan kin tarar da shi da halaya tamkar fan dambe kamar yanda na fada maku dole sai kin bi a hankali sannan kin bi da zafi zafi, kuma sai kin jure kin saka hakuri a zuciyarki a hankali har ki samu sasauci.....sannu sannu har ki fi karfin wulakanci a wajensa, irinsa ne sai ki ji ana cewa wane ai ya dauko ruwan dafa kansa, zafin nan du babu, mutumen nan idan yana gidan amarya hum zaka ga ya shige ne da wuri fitiwa ta gagara, zai je ya lafe abinsa ko me suke yi a gidan? Lolz abubuwa dai ire iren haka............."
Dan nisawa ta yi tana kallonsu ta ce" komai tsufan namiji, komai yarintarsa idan har ya hadu da mace zata iya daidaita abinta irin yanda take son rayuwarsu ta kasance, aman fa ban ce da ku wai zai zama mijin kan tace ba, kai ni kaina bana son namijin da lokaci zuwa lokaci ba zai botsarewa maganana ba domin hakan na bambanta min ni ba mamansa bace sannan a karkashin ikonsa nake, tunda muka samu kyakyawar fahimtar junna koda kuwa mun samu sabani shiryawarmu abu ne mai matukar sauki, mai yiwuwa daga idannuwanmu sun sarke da junna komai zai wuce, ko idan na zo wucewa yana iya riken tafin hannuna shikenan na huce, ko ya yi anfani da wani sunnan dake sakani nishadi, idanma nice na bata masan da nawa salon da ina yi zai sauko komai hawan da ya yi, abinda dai nake so shi ne *KAR KU KASANCE KU KOMAI FUSHI, KAR YA ZAMANTA IDAN HALIN NUNA FUSHIN NAKU YA KAMA A RINGA ROKAR KU ANA LALASHIN KU KU KI SAUKA HAR KU GUNDURE SHI YA YI BANZA DA KU, SANNAN KAR KU KASANCE KU BAKWA FUSHI EHE*"
Wasa wasa a nan UMMU ta tare da y'ayanta, tun sunna jin kunyar wasu magangannun har ya zamanto sun fara yi mata tambayar ta yaya hakan zai kasance? Har ya dawo sai su yi murmushi su kalli junna, a haka har Ummukulsum ta samu kwarin gwuiwar duba wayarta, irin tarin sakwanin da Yarima ke turo mata ta ringa karantawa Ummu da yan uwanta a hankali cike da nutsuwa har ta kai karshe wanda sakwannin tun sunna nuna tsagwaron ban hakuri da neman yafiyarta, har suka dawo kamar da wasa yakan dan sirka kalmomi kamar haka" kin tsaya min a zuciyata, na kasa cire wannan rana " , har ya dawo dora harafi a cicire kamar haka "i lv u", karshe dai baro baro ya doro shi a hade cewar "walahi i love you", har da irin yan yayan wayan nan dake nuna idan mutun na cikin halin sad da dai sauransu
Abinda ya fi birge Ummu bai taba tsalaken rana ba, hakan ya sa ita kanta a yau ta ji tana iya yafe masa harma ta dubi Ummukulsum ta umarceta da tana iya rubuta masa amsa dan gannin idan har ta fara daukan darusan da take masu a yau
Cike da nutsuwa ta dora kalamai kamar haka" *Asalam Alaikum, fatan an wuni lafia? Dan na kawo gaisuwata ne da fatan a yi baci lafia*
Bayan ta gama ta karantawa Ummu , ta yi murmushi domin kuwa kwarai hakan shine daidai, sam bata so ta nuna zumudinta ta hanyar bashi amsa ta farko ko ta nuna masa kamar shi take jira, sannan rashin ambaton sunnansama nada nasa wajen, tana turawa ta sakata kashe wayar dan ta tabata idan ya gani yana iya beman kiranta ita kuwa ta hane su amsa wayar saurayinsu mai mata a irin lokacin nan, dan kuwa ba dadi idan ka yiwa wata kaima za'ai maka!
Murmushi kawai NAJEEBA take har tana dan rage girman idannuwanta irin tana dan kausasa kallonta tana hangen abubuwa da dama, ta tsinci kanta da jin zata kwatanta abubuwan nan, tabas zata kwatanta abubuwan nan.
........................................
Baki daya a falo ya yada zangon aikinsa a yau, ba komai ne yake hadawa a computernsa ba sai binciken da ya saka wani kwararan police abokinsa ya yi masa a kan rayuwar mutanen nan uku komai da komai da ya shafe su
A hankali ya ringa nazartar irin abubuwan da aka kawo masa har ya tsaya kan Amintacensa
Ya maimaita wani waje ya kai sau uku, wanda abinda ya samo da gaskiyar lamarin ba haka bane
Kan soyayarsa ne da ita, an nuna ya so ya yi soyaya da ita sai dai mahaifinta ya dakatar da kamarin bayan ba haka abin ya kasance ba, soyaya sak suka yi mai zurfin gaske daga baya suka rabu a lokacin da mahaifiyarta ta fito karara ta nuna masa shi din ba dan wani bane, ba jinnin sarauta bane kwarai zai yi rashin kunya idan ya nuna yana son yar sarki, dan haka ya kiyaye takunsa ya bar matar manya wa manya
Hakan ya hanna masa zaman garinsa ya dawo DANAGARAM, karshe ya ajiye aikinsa harma ya samu kusanci da sarki ya samu karbuwa, wannan shi ne gaskiyar lamarin abinda ya kawo shi garin DAMAGARAM har ya zama gagara badau a cikin masarautar ta hanyar samun kusanci mai karfi da SULTAN
A hankali ya ji ya kasa cire ayar tambaya a kansa, *WACECE* a cikin y'ayan sarkin?
Sai a kan Liman baba, wanda shima ya samu wasu karin bayanai kan wa'inda yake da su a kansa
Sai kuma mai bulala, wato baban dogarin zabga, wanda shi ke tsaye da babar bulala a fada......labarin *Dandatsa* da akai masa tun a shekarun mahaifinsa, ya kasance ya afkawa mata har shida hakan ya sa akai masa hukuncin dandatsa aka jefa shi a gidan yari na dan lokaci
A lokacin da ya fito sai ya samu matansa biyu sun barshi, y'ayansa kuwa ba maganar su yi masa biyaya, dan haja sai ya koma wajen sarki Allah ya jikan rai da koke koke da komai da alkawarurukan ya shiryu,
Sarki sai ya amince, ya janyo shi jikinsa dan ya kara shiryuwar, ya nuna masa kyakyawar hanya da komai karshe har ya samu mukamin nan, sai dai har yanzu shi da mace sai dai kallo, shi a yanzu matan nema sam basa bashi sha'awa sai dai ya kalla ya cire kansa.
Kansa ya dago ya kuma kallon hanyar da ta nan ya dace a ce ta shigo tun dazun, sai dai yanzunma ba alamunta
Dan murmushi ya yi a bayane yana dan girgiza kansa, wato dai AMMI ta shirya? Bakinsa ya tabe irn bai dame shi ba, sannan ya mike da computern nan ya yi ciki
Sai da ya daura alwallah kafin yake hawa Bed sinsa bayan ya yi wanka
Idannuwansa ya lumshe a hankali ya cije lebansa na kasa
Baki daya jikinsa ne ya amsa masa a lokacin da ya hango kogin nan, tabas wannan shine kogin zuma
A hankali ya buda idannuwansa da har suka fara amsar sakon nan ya sauke dubansa kan AC din dake kusurwar dakin, a fili saman lebensa ya furta "Bacin zaki hana min yauma?"
Sai kuma ya lumshe idannuwansa yana hasashen irin haduwarsu ta gaba, zata amshi tukwuicin tsagerancinta ne a hannayenta! Wato dai yar fitsarariyar AMMI ba zata shiryu da neman magana ba?
Jikinsa ya ringa hadewa ko zai samu dan sasauci cike da wani takaici dake taso masa, wai yana da mace uku aman yau kwanansa hudu rabonsa da Mace dan kawai yana tare da amarya? Hum! Ai kwanakin amarcin saura gobe kawai zasu zo ne a yita ta kare walahi shi ba waliyi bane!
Wani tsakin ya kuma yi a hankali sannan ya mike ya shiga cire rigar bacin da ya saka ya koma bayi
Sosai ya ringa zubawa kansa ruwa sannan ya fito ya zauna saman kujera da karamar wayarsa a hannunsa, shi kadai ya ringa tunani shin kiran AMMI din ne zai yi ko me? Mtsssssss han hm,
A hankali ya ringa jin ransa ya fara bacewa sakamakon wani tunani da kalamanta da suka fado masa a ransa
Na tsane ka! Bana son ka! Ka sake ni na auri masoyina! Ni bana son farin mutun Huzaifana nake so!
Idannuwansa ya rintse da dan karfi a lokacin da ya ji wani abu mai karfi ya soke shi a kahon zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin abin ba dadi a ransa harma ya tsinci kansa da fadin" *Yanzu fisabililahi me ya yi zafi a maganar nan da har zan ringa tunota ina jin tamkar wani mai ciwon athsma zuciyata na tafarfasa bayan na san gaskiya ne tana da saurayinta aka raba su ai kau?, kuma shine hankalina zai ringa tuno min shirmen nan? Idanma bata so na ai inada masu so na! Nima kuma ai ba son nata nake ba!*
Lebensa na kasa ya kuma dan cijewa, da gaske zafin maganar yake ji kamar a yanzu ta fada masa
Sunnan Huzaifa ya yi masa katutu a zuka yana jin wani irin daci a kan sunnan da wani tunani daban
Gannin zai cutu ta hanyar tinane tinanen nan sai kawai ya nemi kusanta kansa da Allah ta hanyar dora nafila, domin kuwa ba zai yarda yana ji yana gani kamar wani yaro karami ya tinga tino maganar yarinyar nan da bata jin magana mai fadan tsiya gabansa na faduwa haka kawai!
Morning peopleπ, ga breakfastπ
[31/03 Γ 21:57] Sadjida: π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*Na*
*SAJIDA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
52
Tun karfe bakwai su Najeeba suka gama kitson nan, kitson da akai masa wani irin kannanun tsinta har sai da Zahrau ta ce yanzu Najeeba haka kikai min kannanun kitson nan wa zai tsefe min?
Sai kawai Najeebar ta yi murmushi abinta ta janyo sabuwar wayarta IPhone da yaya DAYABU ya