Showing 225001 words to 228000 words out of 228147 words

Chapter 76 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10402

ya dora yatsunsa ya rubuta mesage kamar haka" Ma ji ma gani, aman mai yaren RR din nan sai ya zamo uban y'ayanki da izinin Allah domin ba inda zan je Sarkin Damagaran uba ne ga kowa, ya kuma bani daki"

Haka suka yi ta raha tsakaninsu har zuwa shiga kwonci kafin kowace ta labe da waya tana dan taba hira da mijinta, ciki kuwa harda Najeeba wace a irgenta bai fi kwana takwas zasu koma bangarensu ba, wato zata fara daukan duty
Hotunnan dinkunnansa da aka kawo ne take ta bi daya bayan daya tana kallo, bakinta ta turo ta danna voice tana shagwabe muryarta ta ce" Ni du kayan nan na rasa wanda kyansa bashi da yawa, Ni gaskiya haka kawai ka saka masu kyau ka fita daurin aure Har ka samo mana wata? "


Murmushi ya yi daga kwoncen da yake yana mai jin dadin irin yanda lokaci zuwa lokaci take nuna kishinsa a fili wanda hakan ke saka shi jinsa wani gingirigin, kafin ya danna ya shiga bata amsa daidai da maganarta

Asubah alkhairi Fari mijin Najeeba

A ranar dake gobe daurin aure sun wuni ne sunna tsaye kan harkar tsare tsaren tarbar baki da irin abincin da za'a girka wanda baki daya girkin larabawa ne za'a yi a wannan taron aure na y'ayan Mutalab

Sai da magariba ta yi suka kile a baban filin dake zagayen wajen AMMI ya su ya su suka shiga gabatar da sister Days, wanda ya dauki larabawan da suka zo da tsuma su Ummu, da su Ammi da Ummu, sai yan matan da su Najeeba

Kwaliya ce suka dauka irin ta larabawa, sun shirya shiri mai tsarin gaske ga turaran wuta sun jojona waje waje sun zuba uban turaren da ya ringa game masarautar ba iya nan ba, a wajen kuwa harda DAYABU wanda yake tare da kannen nasa tun da yama, sallah kawai ke tashinsa
Raguna har uku aka gasa masu,
irin gashin nan mai fita daidaya, aka gabatar masu da komai da komai sunna shan kidan larabawa sunna cin gasashen ragon nan sunna korawa da jusss

Ai kau rawa suke sha abinsu iyayen na shan dariya

Daga inda yake ringeshe da computer a kunne a gabansa da tablettt dinsa yana bin yanda suke gabatar da bikin nasu ya fi kurawa Najeeba ido, wace kugunta ke daure da irin abin nan na larabawa wanda sunna rawa yana bada sautin cas cas cas, hannayenta rike da wata yar igiya fara, gabanta kuwa wani kwanon silba ne karami, sai kafarta da ta dora kafa daya kan daya ita kuwa dauke da sarkar kafa mai walwali, kasancewar wajen da wadatacen haske sai ya zamanto komai yana ganni
Hirarta take hankalinta kwonce, sannan ba abaya bace a jikinta, sket ne budade da wata bak'ar riga wace ta bi lafafen cikinta wanda ko shi da ba dan ya san shine ya yi mata cikin da ta raina a gabansa har ta haife shi ba da shi zai fara karyata cewar ta taba haihuwa a wannan shafafen cikin, sannan ko a zaunen da take duwawunta da cinyoyinta sun kara wani irin bajewa wanda ke nuni da kibar haihuwar a cen ta tare, sai mamanta da suke cike bam ga ruwan nono na shayarwa ga asalin halitarsu

Ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana jin wayarsa na ta tsuwa, kiran nan ya kai na tara a kadan, tun da magariba ake kiransa aman wannan da ya zamanto a kusa kusa sai kawai ya mika hannunsa ya dauko yana mai duba sunnan dake sama

Dan kara kurawa sunnan ido ya yi da dan mamaki, dan gannin Gimbiyar garin agadez ce,
Yana da numberta a wayarsa, ama kira bai taba hada su kai tsaye ba, koda jaje ne ko gaisuwa takan bi ta kan y'arta ne

Rage sautin kidan ya yi ya dan gyara kishingidarsa da wayar a hannunsa da kuma tablettt din yana kallo ya amsa kiran ta hanyar salama cikin nutsatsiyar muryarsa mai kamala

Mamaki ne ya dirar masa jin tana gaishe shi, bai idasa mamakin ba ta dora da kara neman afuwarsa sannan ta fara magana a sanyaye kamar haka" yara sun zo Damagaran wajen auren, aman mai martaba ya hanna masu sauka a fada cewar su sauka a gidan kanwata da safe zasu zo baki dayansu harda Zinaria , dan Allah a kara nema mana afuwarsa ko zai sasauta mana fushinsa"

Shaheed ya dan kara buda idannuwansa a kan yan matan AMMI da suka fara tashi sunna yin rawa yana dan girgiza kai yana murmushi a hankali ya bata amsa da fadin " In Sha Allah "

Gimbiya du sai ta kara dirircewa tama rasa ta inda zata bi dan fada masa abinda matar Yarima ke shirin yi, aman shi kadai ke iya tsawatarwa a masarautarsa dan haka fada masan ya zama wajibi

A sanyaye ta dora da fadin" sai yarinyar nan ta wajen Yarima, wato matar tasa, itane ta tafi ashe itama, kuma da niyar rigima ta tafi dan haka ina neman alfarmar a katse hanzarinta "

Shaheed ya kara buda idannuwansa da kyau, rigima? Zata zo wajen auren? Uhum

Karshe dai haka suka yi salama bata samu wata gamsashiyar fuskar da zata kawo masa dayar maganar dole haka ta yi hakuri da kudurin cewa idan da rabo zata koma dakinta

Shi kuwa ido ya zubawa Najeeba da ta dauki dan kwanon nan ta dora shi saman kanta bayan ta cire dan kwalin
Ido ya kara zarowa yana kallonta a lokacin da ta mikar da hannayenta ta shiga kada kugunta su kuwa larabawan nan me zasu yi banda yi mata ruwan turare da buda sama sama

Da sauri ya lalubo wayarsa yana cije lebensa na kasa yana mai furta" ya isa haka neman maganar, a watse tun muna shaida junna!"

😁😁😁😁ni ban ga laifin rawa ba wollah haka kawai a dai ringa jin tsoron Allah.....ah tom😊😊😊😊😊😁😁😁😁😁😁

___________________________


An daura aure lafia, duban jama'a sun shaida bisa wakilcin Sarkin sarakuna Mai damagaran, da sirikinsa, amininsa, babansa sarkin garin agadez, da manya manyan sarakunnan da suka halarta bisa gayata da suka samu domin kuwa shi din mai zuwa taro ne hakan ya sa idan yana taro ake zuwar masa ta ko'ina ba iya Niger kawai ba

An wuni cikin shagulgula, shagalin da ya dauki salo kala daban daban
Matansa du sun halara, kwaliya da shiga ke ware yayar wane ko uwar wane😊

Zinaria ta halarta tare da yayunta ko ba komai auren dan uwansu ake suma sannan masautar biyu sun zama yan uwa hakan ya sa suka shiga mutane duda irin tarin mamakin da ake na ganninta irin yanda ta rame sosai ta kara wani fari fat kamar wace bata da jinni a jiki tsabar saka damuwa a ranta, sai dai ta ji dadi da iyayen mijinta basu nuna mata komai ba, kai harta da yarinyar da ta sako gaba da zagin cin mutuncin bata wani nuna mata wani abin ba saima gaisuwar mutunci da suka yi a tsakaninsu

Bayan magariba du an fitar da tarin jama'ar nan sai na jiki sosai ke shigowa falon, su kuwa sun yayada zango, Zinaria na rike da Abdallah tana dan jijiga shi cike da begen yaron a kasan zuciyarta Najeeba na gefe guda lulube da wani jibgegen hijab mai nauyon tsiya wanda fitowarta kennan daga wanka ta hau kan yar kujerar tsugunon nan da jimkin abubuwanta da ta harhada ta ringa zubawa a hankali yana bin jikinta hankali kwonce tana hangen Zinaria daga zaunen da take, dan bakinta ta dan tabe, ita fa ba za'a hanna mata jin kishin mijinta ba, domin ya isa ne

Tana gamawa ta shige ciki dan kwontawa, ta gaji, gajiyartama ta gaji, sai dai maimakun ta samu bacin sai kiran da mijinta ya yi mata na vidio call ya sakata kura masa ido tana kallonsa ta saman screnn din

Bakinsa da yake dan dantsewa ta di baiwa hankali, kafin ta saki murmushin jin abinda ya ce , cewar ta zo gareshi

A hankali ta ce" Na ki "

Ido ya zaro yana kallonta ya dan nuno karamar yatsarsa ya ce" Beebah, satinki nawa rabonki da ni? Ke tunda cikinki ya tsufa kika ysane ni, a yanzun da kika haihu har kika fara sallah shikenan ba zaki zo gareni ba? Nine fa? "

Murmushi ta kara yi a sanyaye ta ce" Kwana nawa ya rage mu hadu ne SHAHEED?"

Idannuwansa ya kausasa jin ta kama sunnansa, kit ya kashe kiran yana kumburi, hakan ya sakata tashi ta zauna da sauri ta shiga doka masa kiran tana kallon wayar, ama fir ya ki ya daga hasalima kamar baya nan haka ya mata shiru bayan yana kallo

A hankali ta koma ta kwonta ta shiga yi masa message sansanya mai sanyaya zuciya, ta dora da fadin" Fushinka na iya hanna min baci khalb, na tuba abin kaunana "

Murmushi ya yi yana mai bin kalaman da shauki a cikin zuciyarsa, a hankali ya sake kiranta,
Tana dagawa ya kura mata ido na dan lokaci har sai da ta kashe masa ido daya sannan ya yi murmushi, shi kadai yake ayana irin abinda zai mata, wato har sati take tunanin zata kara shi kuwa yana nan uwa wani sakarai ko? Zata gane bata da wayo, ta dai yi gigin zuwa bangarensa

A washe gari tun karfe tara suka tashi da hayaniya, ba ta komai bace sai ta matar Yarima wace a yau ta shigo da sunnan ita din matar yariman ce harma ta samu sadawa da bangaren Ammi

Kuka take cikin harshenta da baya fita da kyau tana mai nuni da Ummukulsum zata shigar mata gida ne dan ta rabata da mijinta kamar yanda yayarta ta raba sarakuwarta da mijinta hakama kanwarta ta raba Zinaria da mijinta

Ba wani nan sulhu ba take, fada ne take wanda ya baiwa Najeeba daria tsayen da take cikin shiga ta wani danyen lesh mai kalar orang da ratsin fari ta dora farar alkyabarta har kasa sai baza kamshi take fuskarta dauke da nitsatsiyar kwaliya , hakama yan uwanta da du sun riga da sun dauki kwaliya sun shirya dan bikin da ake a cikin gidan du sunna kallon ikon Allah, sai hakurin da ake bata na ta zauna a yi magana , gefe AMMI na tsaye itama sai UMMU da ta tabe bakinta ita kuwa ba alkyaba bace a jikinta bubu ce ta babar atampa ta kashe dauri ita kanta fuskarta da mak'up simple, uwa uba Amaryar tsarin kwaliyarta ba'a cewa komai du sunna kallonta

Karar buda bangaren shigowarsa ya sakata saurin kai dubanta wajen, haka kuma du wani mahalukin dake falon sai kake jin tsitttttttttt ya yo, yan matan har sun kai kasa dan girmama mai girma, wa'inda basu rigaya sun zube ba AMMI ce da Ummu da Najeeba, da matar Yarima,
Ita Najeeba ta ki dukawar ne dan bata so ya bayana a cikin tsarin da ba rawani, a yau tana jin kishin du wata mace ta gane mata shi ba rawani ciki kuwa harda matar Yariman!

Kanshinsa ne ya fara rufe kofofin hancinsu, kafin sandar girmansa ta fara shigowa baka mai lankwasa da adon zeba sai farin hannunsa mai dauke da zoben azurfa da agogon azurfa sannan jijiyoyin sun mimike rado rado ana ganni a jikin

A hankali yake kara bayana lokaci daya ta ji wani irin abu na mata yawo a jiki da kwakwaluwarta da zuciyarta,
Bayanuwarsa cikin shiga mai duhun haske ya sakata sada dubanta kafin itama ta zame ta kai kasa ta dukar da kanta cike da jin shayinsa da matsananciyar kaunarsa

A SARKINSA YAKE, SARAKI NE, MANYANMU NE, MASU MULKINMU NE, UBA GA ABDALLAH DA MUHAMAD, BABA A WAJEN YAKUB MIJI A WAJEN NAJEEBA DA NADIA, cike da kasaita ya dan juyo da kansa bangaren mahaifiyarsa wace ta kai zaune itama cike da sada kanta domin kuwa ita ta kawo shi duniya aman ko ita takan bambance lokutan da take iya kama kunnensa ta ja, da kuma lokutan da take sada dubanta a kan nasa dan kuwa daukaka ce daraja ce da Allah ya bashi,
Kansa ya mayar wajen UMMU, itama kan nata a sade yake a kasa
Matar Yarima na idasa gane komai itama ta zube a kas wajen da su Ummu suke duke, AMMI kuwa a kan kujera ne take, Ummuma a kasan take kanta kasa

Duban kowa yake daya bayan daya har idannuwansa suka sauka a kanta,
Yana kallon nata kallo na kurullah, kallo na soyaya, kallo na bege,

Salamar Yaya DAYABU da ya kwana a gidan amarya ne ya saka shi kai dubansa inda yake shigowa, yana karasa shigowa ya duka shima nan kasa da sauri yana mai kawo gaisuwarsa

Shiru bai amsa ba, hakan ya sa ya kara sada kansa kasa

A haka mutun uku suka shigo da salama, wato ABIH, YARIMA, DA AMININ YARIMA

Bayanuwar yannayin wajen ya saka su zubewa suma sunna mai gaishe da MAI DAMAGARAM MAI WUKAR YANKA GURNANIN ZAKI

Da sauri ya cire dubansa daga kansu bayan ya gama gannin bakin Yarima harda shi a wajen da matarsa take, ta dauki wannan kwaliyar da ta tsintsinke masa zuciya, tana baza kanshin nan da yake matukar kishi, sai kawai bakinsa ya kara yin nauyi ya kasa amsa gaisuwar sirikinsa da yariman da abokinsa

A hankali ya kuma cirw dubansa ya dora shi kyam a saman kanta

A hankali ta ringa dane idannuwanta dake son dagowa dan dubansa, har matse hannunta ta yi du dan ta hannawa kanta kallonsa sai dai ina, abinda ya zame mata jiki, ya rigaya ya zame mata sabo bata tunanin akoy wani hargagin da zai hanna mata dago da kan nan nata da take jin yanai mata balin bal

A hankali ta idasa dago da dubanta ta zuba idannuwanta cikin nasa

Irin TSADADEN kallon nan da ya saba yi mata wanda a da take dauka da na tsana, kallon nan mai yi mata nuni da tsantsar kaunarta da matsanancin kishinta da madaukakin bukatarta, kallon nan mai tsuma zuciyarta ya sakata lumshe idannuwa koda bata shirya ba ne ya kafeta da shi ko kyaftawa baya yi

A hankali ta ringa jin zuciya da gangar jikinta na mikar da uta tsaye daga zaunen da ta yi

Tana gama mikewa ta ringa takawa da kafafuwanta dake dauke da farar safa kal kal da alkyabarta har ta karasa gabansa
Sakamakon ya darata a tsaye sai ta dago dubanta tana kallon idannuwan nasa
Gannin a yau yan sarautar aka tashi da su, ga shara'a ta samu a irin wannan lokacin sai ta saka hannayenta a hankaki ta dan ja rawanin nasa kasa kadan ya kasance lebunansa a waje sannan da girarta ta yi masa tambayar menene?

Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya dora hannunta na dama daifai kahon zuciyarsa sannan saman labansa ya furta" *KISHINKI NAKE, SON KI NAKE, ND I NEED U A SAMAN GADONA* "

Murmushi ta sakar masa mai tsada kafin ta dube shi da kyau itama a kan lebenta ta ce" *BURINA NA DAWAMA A CIKIN JIKIN KA, ZAN JE NA YI JURANKA HAR ALLAH YA KAWO MIN KAI....* hannunsa ta ja ta dora a wajen mararta ta dan shafa ta kara tsura masa ido ta ce" *Marata a shirye take da daukan ajiyarka ko da kuwa mace na iya dauka sau billion a rayuwa.......zan amshi ruwa daga mai dauke da ruwa, zan baka hardar karatun da kake koya min fila fila KHALB* "

Har ga Allah sai kawai ya ji jikinsa ya fara bari bari, yana kallonta kamar wani wawa har ta shige ta kofar da ya biyo

Ji ya yi tsayuwa na neman gagararsa, da duba ya ringa bin jama'ar dake wajen du kawunnansu a kasa

Wani yawu mai santsi ya hadiye ya ja ya mayar da rawanin har wajen bakinsa

Muryarsa na crakin ya kai dubansa wajen Yarima ya dan limshe idannuwansa a kasam zuciyarsa kuwa fadi yake 'Ina, koda na ce zan gabatar da shara'ar nan ba zai yiwu ba, ta lalata komai ta tsatar da komai sannan ta tafi da komai', sai kawai ya dan kara gyara tsayuwarsa ya ce" *YARIMAH ABDUL JABAR, KA GABATAR DA SHARA'A WA AHALIN GIDAN SHAHEED ALIYU DA MUTALAB NA BAKA WUKA NA BAKA NAMA*


Yana gama fada ya juya da dan hanzari ya shige ta hanyar nan,

Ai kau ta dan dage alkyabar dake jikinta ta juya da niyar kwasawa da gudu tana daria dama ta dan tsaya ne dan ta ga shin zai zo ko sai ta yi jiran nasa?

Shima dariar ce ta kubce masa ya shiga warware rawanin kansa ya kara hanzari dan cin mata domin kuwa shi Suktan Shaheed ya jima da gane cewa ifan yana daka shi din sunnansa Shaheed khalb din BEEBAH, sarauta na hannun *NAJEEBA MUTALAB*





ALHAMDULILAH


ALHAMDULILAH


ALHAMDULILAH


Allah yaa nuna min kamalawar wannan labari nawa mai sunna MAGE, Mage kirkiraren labari ne, idan har ya yi shige da rayuwarki/ka an ci sa'a ne, dan haka a gafartawa yar mutan Niger

Ya Allah ina rokonka da sunnayenka tsakaka ka yafe min kuraran dake cikin wannan labari da wa'inda na yi a baya da wa'inda nake tunanin yi idan har da raina, ya Allah ka bani ikon rubuta alkhairi da yan yatsunna ka hane ni lalata tarbiyata ,
Ya Allah ka jikan iyayenmu ka sa mu cika da kyau da imani


Sakon gaisuwa


*Zuwa gare ku daukacin al'umar da sukan nunan kulawa, soyaya, a aikace da aljihunsu a kan wannan sako more specially Mage grup fans, ku din nawa ne, nima taku ce, ina mai baku albishirin cewa in sha Allahu zan dawo da sababi har kwaya uku, da ba dan daukan sunna ba da na furta maku sunnayensu, sai dai ina mai rokon ku da ku kasance tare da ni bayan azumi idan Allah ya nufemu da gannin lokacin, ku ci gaba da bani kwarin gwuiwa da hadin kai dan kuwa na fada da karfin murya cewa ni dai ina rubutu ne domin ku, idan ba ku ba ni, Allah ya yi maku albarka, ya kara lafia, ya kara imani, ya kara arziki mai anfani, ya sa a gama da duniya lafia*



Jinjinar ban girma


*JINJINAR BAN GIRMA ZUWA GARE KU YAN UWANA, TAURARI WRITER MA YAR UWATA SAMIRA HARUN, MA Y'ATA RAHIMA, MA KANWATA NAZIFA, MA KAWATA HALISA WATO LISSA AND MA NUSEE, ALLAH YA BARMU TARE, YA KARA DANKON

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login