Showing 159001 words to 162000 words out of 228147 words

Chapter 54 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10410

ya zare yan kunnayen ya mayar gabansa ya ci gaba da dan cin abincin

Baki ta turo gaba sosai ta ringa kallonsa, shi kuwa sam baya kallonta, su Ammi kansu sun kula da yannayinsu aman ba wanda ya nuna ya ga wani abin

Nan da nan kowa ya gama cin abincinsa banda Najeeba da ta yi ta cika tana batsewa

Ammi ta kalleta ta ce" Najeeba, ya haka? Ki ci abincin mana na ga baki ci komai ba"

Najeeba ta kara takwakwafe fuskarta sai kawai ta saki dan kukan shagwaba ta ce " Ammi, yan kunnayena ya dauka bayan da tsada sosai na siye su fa "

Shi kansa da mamaki yake kallon fuskarta da lebunnanta da take hadawa tana kukan tabarar da su, haka kawai ya samu kansa da kara tsare fuskarta da ido yana jin wani irin abu tamkar tabarar tata na birge shi

Dan tissu ya ja yana goge bakinsa ya tabe bakin nasa bai ce komai ba

Ammi ta kale shi, ta ce" eyah yayansu bata abinta mana baka ga itace karama, ai ummuna ta bar mata ko?"

Ummu ta turo baki itama ta ce" Ammi, to tace na bata sai na bata aman ta daina yin karyar wai ita ta siya "

Najeeba ta gala mata harara ta ki yin magana tana kara matsar kwalar dole sannan baki daya ta saki jikinta rigar jikinta bata dameta ba tana ta kara tura bakinta da yannayi na rigima take ji

Dan murmushi ya yi a lokacin da ya mike tsaye, tura yan kunnen ya yi a aljihunsa sannan ya kai dubansa wajen su Nusaiba

Hannunsa ya mika mata a hankali ya ce" Nusaiba zo"

Nusaiba dake kallon fuskarsa da yar dariyarta ta yi wajensa ta kama hannunsa ta rike tana ta kara kallon fuskarsa so take ta tina inda ta sanshi

Murmushi ya kuma yi mata ya dauketa baki dayanta sannan ya yi wajen babar kujerar fallon ya zauna yana ajiyeta gefensa kafin ya shiga yi mata wasa

Da yannayin farin ciki iyayen suka karasa wajensa gannin da gaske zama ne zai yi tare da su du sai suka bar yaren nan zaune

Kasa kasa Bilkissu ta ce" auntyna dan girman Allah wannan shine sarki?"

Ummukulsum ta gyada mata kai tana murmushi

Bilkissu ta ce" wauh, walahi haka yake da kyau? Kuma ashe ba tsoho bane auntu Najeeba ke cewa za'a aura mata tsoho, kuma Aunty ya fita kyauma ko?"

Najeeba ta ringa share fuskarta ita a dole fushi take, kuma Ammi bata amso mata yan kunnen ba, ita haka kawai take son yan kunnayen ba wani na zinari ba karfe ne sak aman an masu tsari ne sosai,

Yar dariya Ummu ta yi tana kallonta ta ce" SORRY sis, ba zan kuma ba na bara maki yan kunnayen kin ji kanwata?"

Zahrau da ta gama amsa waya kasa kasa ta kashe tana binsu da kallo a hankali ta ce" ta ina zamu fita ne? "

Ummulkhair ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsu ta ce" gaskiya gwara ya ringa rufe maku kansa, ina wannan da budewa yake ai da rikicin mai yawa ne, lalle Najeeba baki da kunya wannan ne kike cewa ke bakya son fari waye waye? Tap, yanzu dai Aunty Zahrau tashi mu je kawai kar mu yi da sanyi, walahi mu je, kai ni daga yau na daina jin haushin kishin Zinaria a barta ta yi kishin mijinta walahi"

Su dai kannanun karasawa suka yi suka hadu da shi da su Ummu sunna wasan su

Da yake AMMI ta san da fitar salamarta kawai suka yi suka tafi su uku tare da dogaran da zasu dafe masu baya har mutun hudu

Sai da ta gama zamanta saman table din sannan ta mike bayan ta yiwa yaya DAYABU mesage cewar tana son ya shigo mata da babar waya da layi

Niyarta ta ratsa ta yi shigewarta daki domin yayunta fu sun fice, kannen nata kuwa kowane ya shiga wasansa kafin malamin makarantarsu ta islamiya ya zo

A tausashe, yana sauraran hirar iyayensa da suke bashi labaru kala daban daban ya bi bayanta da kallo kasa kasa har ta bacewa ganninsa

Ajiyar zuciya ya sauke ya dago dubansa ya dora saman AMMI, a sanyaye ya ce" *SHIN LAFIA UMANI AKA RIKEN MATA YAU KWANA HUDU BATA ZO INDA NAKE BA?*

Ammi ta kale shi da sauri tana kara jin dirara magangannunsa a kunnayenta, UMMU kuwa sai ta kaida kanta a kasan zuciyarta tana murmushi, AMMI na kallonsa da kulawa ta ce"








*SAKON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI ZUWA GAREKU A DUK INDA KUKE, NA SAN KUN SAN DALILIN SHIRUNMU BAKI DAYA YAN NIGER, ALHAMDULILAH MAY BE KOMAI YA DAIDAITA, SOSAI NA TARAR DA SAKWANI MASU MATUKAR YAWA YAN UWA DA AMINAN ARZIKI, DA YAWA NA NUNA TASHIN HANKALIN RASHIN JI NA, DA YAWA NA NUNA KULAWARSU DA SAKON GAISUWA, NA GODE ALLAH YA BIYA ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKHAIRI YA BAR KAUNA, HAKAMA WA'INDA SUKA RINGA SAKWONNINSU NA KYAUTATAWAR DA SUKA YI NIYAR YI MIN DAN JIN DADIN WANNAN NOVEL NAWA SAKWANNINSU SUN SHIGO KUMA AN SHAIDA MIN ALLAH YA KARA ARZIKI YA BIYA, MASOYA, A DUK INDA KUKE SAKON GAISUWATA ZUWA GAREKU, ALHAMDULILAH GRUP MAGE BANI DA TAMKARKU, ALLAH YA BIYA YA KARA DANKON ZUMUNCI, GASU FA, KADAN NE....AMAN IN SHA ALLAHU MUN DAWO BAKIN AIKI😅😅😅😅, daga taku ce SAJIDA*
[31/03 à 21:56] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



50


Cike da basarwa AMMI ta ce" eh ta dan yi rashin lafia ne"

Idannuwansa masu girma da ladaftar da mutun ya zubawa mahaifiyarsa yana kallonta, bai ce komai ba aman a yannayin kallon da ya kurawa fuskarta ya fasara irin tarin tambayoyi ko nace tarin son karin hasken da yake,

Cire kanta ta yi daga dubansa ta maida wajen tanfatsetsiyar tV din dake jikin bango wace ke kashe tana dan girgiza kafarta daya ta dora da fadin" idan kuwa ita dinma gaba za'a yi da ita a hanna min ganninta sai na ji karin bayani "

Dan murmushi ya yi yana sauraron Nusaiba na tambayar ya saka mata Game a wayarsa bayan shi ko kwaya babu a cikin wayar, ya maida dubansa wajen UMMU,
Cikin yannayin wadatacen murmushin fuskarsa ya ce" UMANI, me ke damun kawarki ne daga farin ciki sai na ga kamar kawarki zata bata ranta fa ko menene?"

Itama dubansa ta yi, ta yi dan murmushin zata bashi amsa Mardiya ta fito daga dakinta,
Karar rufe kofar da dan karfi ya saka UMMU yin shiru bata ce komai ba

Niyar Mardiya ta fice ta karasa diner, ta gaishe da Ammi kawai, sai dai hango wani mutun mai girman jiki, kyakyawan gaske, uwa uba tarin tarin kwarjinin dake fita daga jikinsa, tarin haske da lamari mai girman dake hanna tunkararsa kai tsaye, irin tarin hasken Azhkar da salar asuba, da tarin nafilfillu dake dakushe du wani karamin tsagera, sai ko wadinnan idannuwa nasa masu zabgawa tsagera mari da suka hadu suka sakata rage saurin da ta kwaso da niyar shigewa

Da dan mamaki ya yi mata kallo daya ya cire idannuwansa a kanta, domin kuwa ya ganeta matar Abih ce, sai dai abinda ya bashi mamaki irin shigar dake jikinta da kuma ganninta kamar wace ke zaune daram dakam haka a gidan?

Tana karasowa ta dan rage tsayinta ta gaishe da Ammi

Ammi ta amsata da kulawa ta ce" Mardiya, mijin NAJEEBA ne ai ku gaisa"

Da wani irin firgici da mamaki ta dago dubanta ta yi niyar kara kallon fuskarsa, duda ba ita yake kallo ba sai ta kasa yin hakan ta tsinci kanta da saurin sada kanta idannuwanta na kara zazarowa tamkar zasu balo su fito waje, what? Mijin wa? Idan bata manta ba SULTAN SHAHEED ne ya auri Najeeba, Sultan din da take tunanin wani margayaye ne bayan rawanin nan dake kansa koda taushe, da yawa a cikin gari na tunanin wai ko dai wata kama ce da fuskarsa dake sakashi kin son bude fuskarsa ko ya ringa yin sasaukan rawani irin na sarakan zamani komai zafi? Bata taba jin du abinda take aikin banza bane irin na yau, ashe haka yake? Tana gannin ta samu galaba a kanta tunda ta aurar mata uba hakan na nufin ta rama rabata da saurayinta da ta yi, sai kuma a yau ta ga wannan bawan Allah da bata san da wani sunna zata sufanta shi ba ace shine SULTAN?

Muryarta na rawa rawa ciki ciki ta kai gaisuwarta kafin ta mike ta juya da sauri ta nufi ciki , wato ta koma tama fasa zuwa table din, sam bata da karfin iya cin wani abu, kwata kwata bata da karfin hakan, a yanzun jin zuciyarta take tamkar zata fashe, ji take tamkar zata hadiyi zuciya ta mutu, bata taba kawowa kanta Najeeba zata samu irin wannan mijin ba, bata taba tunanin zata kasance a irin wannan ranar ba, itafa bata da makiyiya sai Najeeba da uwarta, wayarta ta warto tana sintiri tana tunanin me ya dace ta yi? Wa ya kamata ta yi kira? Ko dai shawarar bin bokayen take dauka ta fara ne? Domin kuwa a da ta yiwa kanta alkawarin ba ita ba harkar boka ba dan komai ba sai dan ta kawo rantsuwa ta gita kamar yanda Najeeba ta ce da ita ba boka ba malan zata yo andani da lamarinta na mace ta zartar da hukunci ta hanyar haramta mata soyaya da saurayinta, itama ta kawo rantsuwar ba boka ba malan ita kuwa sai ta auro ubanta kuma sai ta hanna mata kwonciyar hankali karshe sai ta yi sanadiyar da ubanta ya kore ta! ,
Sai dai kash, a yau sai ta fara tunani cikin daya biyu.......anya kuwa zata iya ci gaba da gogaya da Najeeba da Uwarta ba tare da ta bi ta kasan kasa ba?

Wayarsa ce ta dauki kuka a hannun Nusaiba

Amsa ya yi ya kara a kunnensa, a tausashe ya amsa gaisuwarsa

Abih dake tsaye kofar dakin ya ce" Allah ya taimakeka, na shigo ne tanzun zamu gaisa da su Bilkissu, shine nace yau ko zaka fita fada ne? Zancen aminin nan nawa dake kwonce wanda nake maka bayanin matarsa ta tashi hankalinta bisa maganar da ta ji makocinsu na yi a waya tsakiyar dare wanda ya saka mata tsantsamta da saka hannunsa kan rashin lafiar mijinta, shine na ce ina so da kanka ka yi shara'ar nan, walahi ciwo gaba yake ya ki ci yaki cinyewa gashi asibiti basu ga komai ba, ana ta na hausa wannan ya ce matabiya ce, wancen ya ce jifa ne, kai dai ka san lamuran kwashe kwashen mutanenmu, shine nace dan Allah a shigar mana lamarin nan"

SHAHEED ya dan gyada kansa, a hankali ya ce" ABIH yau ba zan fita fada ba, ama ka saka a fada masu gobe in sha Allah mu yi zaman karfe tara a cikin gida "

Godiya Abih ke ta yi har ya sanyo kansa falon, sai kuma ya dan yi turus da mamakin Gannin wai da gaske SHAHEED din ne yake ganni a zaune tsakanin UMMU da BILKISSU ba RAWANI??

Murmushi ne ya fadada a fuskarsa kafin ya karaso shima yana kara kallonsa da kallo mai nuni da yannayin farin cikin da ya tsinci kansa a ciki ya mika masa hannu suka gaisa kafin ya samu waje ya zauna yaran du suka shiga dane shi sunna gaishe shi da murna da ihun fadin ABIH ne ABIH ne

Wannan abin shi ya saka Mardiya zabura ta ajiye wayar da suke da kanwarta fitinaniya wace a yanzu haka ta kai wajen da bama a gida take ba ta tafiarta Maradi wajen wani Alhajinta da ya kama mata gida, sam bata ji yarinyar ko a lokacin da mahaifinsu nada rai, da adu'a kawai yake binta , a yanzu da kasa ta birni idannuwansa sai da ta yi bikin bayana cewar ta zama rikakiyar yar bariki sannan ta faso gari da lasisinta take fantamawarta hankali kwonce

Da sauro ta warto hijab dinta maroon ta saka ta bude kofar ta fito

Daidai ta kusa karasowa UMMU ta ajiye masa ruwan da ta zuba masa a cikin copin glass mai dan tsayi mai sanyi ta koma wajenta ta zauna duda tunda ya zo ba wani magana da ta hada su daga gaisuwa sai ruwan da ta dauko masa ta ajiye masa

Du irin yanda Sultan ya cika wajen bai hanna Mardiya karasawa ta dauke kofin ruwan ta je saman table ta ajiye a ranta kuwa fadi take 'karya ne walahi , ba zaki zauna kina gwada min bariki a wajen da mijina yake ba '

Tana dawowa ba ko dar sai ta samu waje dan kusa da Abih kadan ta zauna, ita bata gaishe shi ba, ita bata bar wajen ba, sai binsa take da kallo , sai kawai take ga kamar wanda ya cencara kwaliya domin ya sha sabuwar shada ne ya hade abin dai ba'a cewa komai, hakan ya sa ko dan datijantakar tasa ke son boyewa sai yan tsirakun furfurar dake jikin gemunsa dake iya shaidawa da ya dan kwana biyu da kuma fuska irin ta baba daban take da ta yaro

Sai da ya ajiye wayarsa ya dan matso da zamansa ya hade hannayensa biyu ya dora gwuiwoyin hannayen nasa saman rigar shadarsa da ya dan ja baya kadan yanna kallon Abih, muryarsa a dake kadan tamkar ba sirikinsa ba, ya dauko muryarsa da yake magana da ita a kausashe a wajen shara'a ya ce" *Meye anfanin zaman iyalinka a gidan nan bayan ba wata sabga ake ba ABIH?*

ABIH ya kale shi, sai ya maida dubansa kan Mardiya da sai da ajiyar zuciya ta kwace mata jin abinda SHAHEED ya fada, dama hanya take nema ido rufe dan haka ta samu nauyin da zuciyarta ta yi mata ta fara ragewa

Abih ya maida dubansa kan SHAHEED, a hankali ya ce" gata ai SHAHEED ka tambayeta"

Sultan ya maida idannuwansa dake dauke da yannayin kausasa ya ce" Mardiya, me kike a nan zaune tamkar wace bata da aure?"
Mardiya ta hadiyi wani yawu jin wai a tambayetan da Abih ya ce, kafin muryarta na rawa rawa karshe ta fashe da kuka ta ce" wai yaya kake na yi ne MUTAKAB, yaya kake so na yi? Bayan kana min gabar da ban san a kan me ba dan kawai na fadi gaskiyana shikenan?, ni bani da damar nuna fushina shine zaka nunan na tafi gidanmu? Da zaka ce a tambaye ni a kan me nake zaune a nan so kake na yashi na kara komawa gidan namu ka hadu da wannan kunna cin amanata?

Wannan din da ta ce da wada ta nuna ya saka da SHAHEED, da AMMI, da ABIH baki daya suka kai dubansu wajen UMMU dake zaune
Ga mamakin SHAHEED wanda ya yi jiran jin irin hukuncin da UMMU zata dauka ta hanyar ramawa sanninta da ya yo cewar bata da hakuri da daukan raini, sai ya ga ko nunawa bata yi cewar ta san zancen da ake ba, hasalima abin yanke farce ta dauna ta duka tana dan karkare karamin farcenta na yatsarta karama,

Juyowa ya yi da yannayin mamaki, lalle dunia ta yi sanyi, sannan ya yarda idan ba auren ba babu abinda zai saka ka kalli mutun da girmansa da komai ka farfada masa magangannun da sukai maka dadi dan kawai ya taba auren mijinka bayan ya girme maka nesa ba kusa ba

"Haba Mardiya, me yasa kike da saurin daukan fushi a kan lamarin duniya harma ki rufe ido ki ringa magana na neman magana ne? Me ya hada zamanta da mijinki ne? Me yasa kike ta shigota da gudu bayan tana iya yinta tana kauce maki da dukan karfinta ne?" AMMI ta karasa tana mai kallon Mardiya

Mardiya ta ce" Haba maman Sultan, tsakani da Allah karya na yi ne? Meye hadinta da mijina da zata ringa dauko masa ruwa daga ya zo? Meye zai sa ta zo nan ta tare bayan na san ba danginku bace?"

Da wani mamakin Ammi ta budi baki zata yi magana , Abih ya rigayeta yana dan murmushi ya ce" in ba Mardiya ba macen da ka haihu da ita a yi maganar meye hadinka da ita?"

Da sauri ta tare shi tana dan fido masa manyan idannuwanta ta ce" kana nufin du iyayen y'ayanka sunna iya zuwa nan su tare dan kawai aun haihu da kai?"

Mutalab ya dago idannuwansa da sukai masa ja ya kalleta, ya dauke dubansa ya kai kan UMMU, sai da ya lumshe idannuwansa kafin ya cire ya dora kan SULATAN dake bin du wanda ya dauki magana da ido yana jira su gama, dan murmushi ya yi ya dan cije lebensa ya ce" ka ga ilar rashin zama waje daya ko? , Shaheed a da ce mata na yi ta je gidansu, aman a yanzu ina so ta koma dakinta sai dai da sharadi, dan Allah Shaheed ka rokar min Nana ashuwa ta koma dakinta, ina mai roko da kokon barana uwar y'ayana ta koma dakinta"

Shaheed ya kurawa Abih ido, lokaci daya Mardiya ta zabura , baki daya jikinta ya kwashi rawa, tana mai kukan nan sama sama ta ce" walahi ba dai da ni zan yi kishi da macen da ta girmeni ba, matar da ta haifeni ne za'a hadani kishi da ita? Me yasa ake son kai a wajennan? Kowa idan ya budi baki sai dai ya goya mata baya ni kuwa a kwaye min? To walahi ba zan hada kishi da ita ba sai dai ka sake ni MUTALAB,"

UMMU ta dago daga gyaran farcenta da take ta kai dubanta kan Mardiya a karo na farko kennan, sai da ta rintse idannuwanta ta saki bakinta da ta cije da karfi tana kallonta ta nunata da abin yanke farcen nan ta ce" sannin cewar ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login