Showing 18001 words to 21000 words out of 228147 words
Chapter 7 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
batsewa ya zaunar da ita tsakiyarsu suka hadu sunna cin abincin sunna hira sunna wasa da daria tamkar ba sune suka shiga hali na matsananciyar damuwa yanzun ba
......................................
Da wani irin karfi ya diro daga saman bed din da yake kwonce a mike idannuwansa lumshe ya kai dubansa kan yaronsa da mamansa ta shigo da shi tana kuka tamkar ranta zai fita ta ajiye masa shi saman bed din hannayenta saman kanta sai jujuya kai take
Irin yanda zuciyarsa ta buga gannin yanda yaron ya mimike sannan jijiyoyin kansa sun yi rado rado sun yi tsanwa sharr idannuwansa na kallon sama sam baya motsi ba allamun motsi a tatare da shi
Hannunsa ya kai wanda ke wata irin rawa a hankali ya juyo yaron
Zinariya ta kara fashewa da kuka hankali tashe ta ce" ya mutu ko? Ya mutu?
Shaheed ya kalleta da sauri haka kuma zuciyarsa ta kara bugawa da karfi ya kara riko yaron ya ce"......
[31/03 Γ 21:37] Sadjida: π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*Na*
*SAJIDA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
8
Da wani irin karfi ya juyo shi yana kuma kallon fuskarsa
Idannuwansa ya lumshe cike da tausayin kansa da kansa kafin ya rage tsayinsa ya shiga dodora hannayensa dan tabatar da abinda yake ganni a gabansa
Tsintsiyar hannunsa ya kama ya saurara da zuciyarsa dan kara tabatarwa kansa
Jikinsa a mace ya juyo wajenta inda ta yi tsaye tana jiran jin amsa
Wani ihu ta so saki, sai dai ta sake shi a cikin zuciyarta sakamakon rufe mata baki da ya yi da hannunsa na dama sanann ya talabeta da hannunsa na hagu
A hankali ya jata ya nufi falo baba da ita inda ta saki jikinta tamkar sumamiya tana gunjin kuka
Sunna fitowa falon a kujera ya zaunar da ita still bai saki bakinta ba
Yana dubanta har sai da ya rage tsayinsa ya kasance sun daidaita da junna a hankali ya ce" ihu zaki yi masa?
Gunjin kukan da take har jijiyoyin wuyanta da kanta sun fito rado rado ya saka shi janyota ya bata kyakyawar runguma
Hakan ya sakata kara sakin kukanta tana mai tambayarsa" shikenan ya tafi ya bar ni?
Idannuwansa ya lumshe yana shafa bayanta, baki daya ta yi jajajir ta rikice
Ta kuma fashewa da kuka ta ce" sai da na hana shi yin wankan nan na dare, ina shafa mai ya shige bayi har yanai min gwalo ya shiga kasan shower ya sakarwa kansa ruwa a kansa
Sai da ya ga raina zai baci ya fito ya bude min
Sai dai tuni jikinsa na rawa hancinsa na zubar da jinni
Fashewa ta kuma yi da kuka tana rike hannunsa da ya tsurawa fuskarta ido yana sauraronta ta ce" shikennan sai ya fara karkarwa sosai da sosai har hakoransa na hadewa waje guda sunna bada sauti hakan ya tsoratani na yi gagawar rufa shi da bargo na je dakinsa na shiga binciko magungunnansa tare da wasu kayan darin dan na saka masa
Ta rushe da kuka tana nunawa ta ce" ina dawowa da na daga shi na ganshi a haka, baya min murmushin, baya cewa" ki yi hakuri Anna
Baya barin jikin shine nace ko summar ce ya kuma yi?
Idannuwansa ya rintse yana jin wani irin yanda yake jin kansa ba karfi ba dabara
A yau ya samu kansa cikin wani tashin hankali mai gigitawa a tarihin rayuwarsa
A mutanen dake makale a cen cikin zuciyarsa yau ya shafe mutun na biyu kennan, bayan shafe idannuwan mahaifinsa da ya yi da kannanun shekarunsa
Hasbunnalahu wani.imal wakim
Sosai ya barta a kirjinsa ta samu kukan ita wanda hakan ya saka ta dan ji saukin zuciyarta
Sai da ta ci kukan har ya so zarce misali kafin ya dago habarta yana kallon fuskarta
A hankali ya kai bakinsa daudai nata, idannuwansa ya rintse kafin ya damki lebunnanta ya shiga tsotsa yana jin zuciyarsa ta yi masa nauyi
Bashi da kalaman da zai nuna mata ta yi shiru
Baya so gawa kwonce ta ringa irin wannan kukan
Sai da ya san ya kashe bakin kukan sannan ya dubeta ido cikin ido cikin yannayin tausasawa domin ita uwa ce, ba wanda zai kaita jin ciwon rabuwa da yaron nan shi ya tabata da hakan, shi yasa yake jin bashi da kalmar da zai iya rarashinta sai dai ya tunatar da ita cewa itama yau ko gobe, ko watarana sunnanta gawa, wannan kira na mahalici ba wanda ya isa a manta da shi ko a yafe masa, an halice mu ba tare da mun roka ba, zamu mutu ba tare da mun shirya ba
Tabas shi daya suka malaka a duniya sai bari biyu da ta yi bayansa, aman kuma wanda ya halice shi ya fita son sa
Dan haka cikin tausasa kalamai da iya yinsa dan gannin shi ya jure ya bata kwarin gwuiwa ya ce" ki daina kuka haka zinaria
Ki yi masa adu'a irin ta bakin uwa na tabata mala'ikun rahama zasu yi rige rigen zuwa amsarsa
Ki yafe masa har cikin zuciyarki tun daga daukan cikinsa, naludarsa, shayar da shi da kika yi, da hakurin tarbiyantar da shi, ki yi kokari daga yanzu idan kin buda bakinki dan ki yi salatin annabi ne sai ko ki yi ta yi masa shinfidar kabari har a kai shi
Wannan ita ce kaunar da zaki iya nuna masa a matsayinki na uwa
Wannan itace babar kaunar da zaki nuna masa zinaria
Kar ki manta *dukan mai rai mamaci ne*
(Allah jikanka babynaππ)
Gani take du da ya samu bakin yi mata magangannun nan dan ba shi bane ita
Gani take sam bai san irin zafin ciwon da take ji a kasan zuciyarta ba
Yaya zai hanata kuka da daga murya?
Yaya zai hanata ihu da birgima?
Yaya yake so yarensa na shiru ya kasance a kanta a irin wannan bakar rana a gareta?
Bai san zafin da take iya ji ba, bata tunanin zai iya sanin karfin zafin da zuciyarta ke mata ba dan ba zai haihu ba kasancewarsa namiji
Wannan lamaru kuwa shi zai sa har ya mutu ba zai ji jrin yanda baki daya zuciyarta ke tsartuwar jinni ba
Zaunar da ita ya kuma yi sannan ya juya cikin irin tafiar nan tasa ta kasaitacen bujimin sarki
Sam bai iya sauri ba , wannan shine saurin nasa domin har yana kokarin kauce sawunsa na kafar gaba
Dakin ya koma,
A hankali ya karasa wajen bed dinsa
Cike da jin lamarin a kasan zuciyarsa ya langwabe kansa yana kallon gawar yaron
Ko jiya har kusan karfe goma yana zaune gefensa, abinda ya fi tsaya masa a rai irin yanda yaron ya nace sai ya ga fuskarsa sai ya cire masa rawaninsa a wajen karatu
Bai barshi ba har sai da ya ga ya fara gyadi gyadi ya dauko shi ya taho da shi nan bangarensa ya shaidawa mahaifiyarsa ta zo ta dauke shi yana jin baci
A lokacin ne kuma ya dauke rawaninsa wanda hakan ya saka yaron yin murmushi yana shafa gefwn fuskar mahaifin nasa sai kuma baci ya dauke shi
Ashe farkawa ya yi har mai afkuwa ta afku da shi?
Cikin nutsuwa ya shiga shirya shi
Yana yi masa wanka ne hawaye ya shiga zarya a saman fuskarsa
Shikenan mutun din kennan, shikenan an kare kana kwonce sai yanda aka juyaka
A hankali ya ringa llaba shi dan raunin fitar rai
A hankali ya gama tsaftace shi ya kimtsa shi
Ruwa ya watsa a jikinsa ya saka farar jalabiya irin ta saudiya sannan ya fito
Hannunsa ya mika ya dauke shi a hannayensa ya rungume shi ya karasa saman bes dinsa da shi ya dora shi
Alkur'ani ya dauko ya zauna ya buda ya shiga karanta masa murya a bude a bayanne
Irin yanda yake karatun zaka gane zuciyarsa a cikin wani yannayi mai rauni da tashin hankali take
Cikin nutsuwa ya samu ya yiwa yaronsa dukan abinda ya dace kowace gawa mai sa'a ta samu, ya samu adu'o'i kamar me
Kiran sallar fari akai a baban masalacin gidan sarki wanda yake cikin gidan
Shiru bai fito ba, a na biyu ne har hankalin liman ya fara tashi sai gashi ya fito
Sallah aka gabatar, ana gamawa ya fadawa liman cewa idan an jima a samu a leko rakiyar yarima, Allah ya yi masa rasuwa
Da mugun mamaki liman ke kallonsa irin yanda ya sanar da rasuwar cike da nutsuwa wada a irin ahekarinsa da yawa zaka same su da rashin nutsuwa har haka
Tabas ya yarda abin sarauta ya gama ratsa sarkin nasu sai fatan Allah ya tsare
Nan da nan ya sanar, wanda rasuwar ta matukar fifita mutane harma aka yi ta kokarin son ganninsa dan gabatar masa da gaisuwa sai dai ya shige da sauri ta kofar da yake shigowa
Direct bangaren mahaifiyarsa ya je
A hankali ya cire takalmansa ya karasa shiga ciki
Tana lazumi zaune saman salayarta, sanye da wata bakar riga mai hade da hijab har kasa rigar kuma budadiya ce sosai wace take sallah ne da ita
Yana karasawa gabanta ya je ya zauna wanda hakan ya sakata saurin dago kanta tana dubansa
Rawanin kansa ya shiga warwarewa a hankali da sauri ta maida dubanta sosai a kansa
Yana gama warwarewa ya kamo tafin hannunta ya dora a gefen fuskar nasa sannan ya lumshe idannuwansa
Da sauri ta kai karshe tana kallonsa , zuciyarta kuwa ta shiga tsintsinkewa
Muryarta na nuna tashin hankali ta ce" me, me ke damunka? Me ya faru a masarauta?
Sai da ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa da kyar kafin ya sauke ajiyar zuciya cikin nutsuwa ya ce" ALIYU, ya amsa kiran mahalincinsa
Da wani irin sauri ta zabura tana furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Yaushe? Ciwon ne ya tashi? Ina yake? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Sai ga hawaye a kan fuskarta
Cikin matsanancin tausayinsa take kallonsa tana nin mutuwar dan jikan nata, sai kuma lokaci daya ta ce" ina mahaifiyarsa? Ina zinariyar take ne?
Ya salam, wani rudun ta shiga sakamakon tunawa da ta yi irin yanda zinariya ke takama da yaron nan
Takan daki kirji cike da gadara ta furta wata rana itace gimbiyar masarautar nan domin ta rigaya ta haifi magaji
Koda jikin yaron ya motsa takan tirsasa shi fita ya zauna kusa da mahaifinsa wai dan ya koyi yanda ake tafiar da sharia
Akoy ranar da ta yi wata magana a gaban amarya cewa" ya dace a ringa kiran yarima da mai martaba, dan ko a yanzu ba'a iya cire rai da hawansa kujera, bale idan mahaifinsa ya yi kaira da wuri
Wannan magana ta matukar girgiza amarya harma ta kasa riketa take sanarwa Gimbiya
Hannayensa ya saka ya maidota ya zaunar da ita yana dubanta a hankali ya ce" tun wajen karfe biyu da rabi ya rasu Anmy, tana bangarenta ta yi salama da shi na yi mata kiran likita ne ta dubata domin ta fara zubar da jinni sakamakon tashin hankalin da koke koken da ta ringa yi gashi cikin bai yi kwari sosai ba
Sosai mutuwar nan ta daki Gimbiya, ta kara tsoron Allah sannan ta tausayawa mahaifiyar Aliyu da mahaifinsa
Mahaifiyarsa ya kasance tana ta kuka a fili, mahaifinsa kuwa ba wanda ya ga kukansa sai dai ya sada kai sannan ya sauke ajiyar zuciya
Nan da nan masarautar ta cika makil da jama'a, yan uwa da aminan arziki kowa da kararsa
Da wuri wuri aka kaishi makwoncinsa sannan aka shinfida tabarmi dan amsar gaisuwa inda wajen ya cika makil ana ta amsar gaisuwa
Baki daya ahalin gidan Mutalab sunna wajen rasuwar tun da sasafe
Gaba daya matan sunna bangaren Gimbiya, nan du aka taru da yake falon ba karami bane harta Zinariyar nan take da yayarta sunna zaune sai kuka take har bayan magariba sam ta ki ta kwontar da hankalinta ta bi yaron da adu.a, idannuwanta sun kasa gane mata irin suturar da Allah ya yiwa yaron nata irin yanda aka taru ana amsar gaisuwa
Lakada lakadan kafet uku ne shinfide, daya GIMBIYA ce zaune da tarin y'ayanta wato su NAJEEBA
Daya Zinaria ce da yar uwarta da abokanansu dake ta shigi da fici
Dayan kuwa idan baki sun shigo nan suke zama a amshi gaisuwa
Bangare bangaren gidajen kowa ya tara jama'arsa yana amsar gaisuwa
Sai yanke yanke ake ana sadaka, rasuwar dai taro na mamaki tamkar wani tsohon magidanci ne ya rasu
Babu wace ta koma gida, a nan bangaren suke kwana wajen Anmynsu wace ke shiga tsakaninsu su layu du su lalafe mata domin baki daya wayoyinsu ta karbe ta kashe dan ta lura wayar NAJEEBA bata daina kuka gashi ita kuwa ta jima tana son ta kasance da y'ayan nata haka
Iyayen daidaiku sun zo har masarauta sun yi gaisuwa, mahaifiyar NAJEEBA dake saudiya ta yi vidio call sai dai sam NAJEEBA ta ki amsarta, sai da Anmy suka gaisa
Yau akaiwa yarima adu'ar uku
Yau ne jama'a ta ringa ragewa tun bayan adu'ar
Kafin ake cewa azahar ta shigo kai ya kasance du sai na kusa wato na kud da kud
A yaune kuma jirgin mai martaba sarkin agadez ya sauka da abokannan tafiyarsa suka yi tataki da kansu dan zuwa gabatar da gaisuwa wa sirikinsa da kuma yarsa na rashin dansu daya cilo da sukai
An masu tarba irin ta bajinta
An sauke su a bangaren Mai martaba Sarki SHAHEED, ya sauke su tare da mutanensa na arziki su ABIH, su DAYABU, su liman Baba,
Dogarai kuwa sun cika ko'ina sai kai kawo suke sun tatare ko'ina
Cike da kamala ta mike ta kai dubanta wajen ZAHRAU, da UMMULKHAIR da UMMUKULSUM, da NAJEEBA
Cikin nutsuwa ta ce" ku tashi ku min rakiya mu gaishe da mahaifin ZINARIA
Mimikewa sukai yan matan reras , baki dayansu sanye suke da bakaken abayayoyi yan saudiya masu shegen kyau da tsari ga tsada
Wani sirrin kyau ne da y'ayan nan tamkar idan kana kallonsu kar ka daina
Bakin fatarsu irinsa ne ke wartar farar fats harma ta yi mangarin idan ta samu kalar nan ai sai yi
Ga najeeba dake anfani da roger cavalais, sannan sabululukanta na anfani tana hada kayanta ne da kanta ciki kuwa harda su kurkum da sabulun victago da zuma da su kankana da dai sauransu hakan ya saka fatarta ita kadaima sheki take tana haskawa, sai haskenta ya fi na sauran ya kasance bakin nata irin na American din nan ne mai kyan gaske
Ko yanzu da take zaman makokin bakinta baya rabo da dan jan bakin nan, hakama idannuwanta bata cire abin nan ba, gata da kallon kasa kasa sai ta lumshe idannuwan nata
Anmynsu ce gaba
Su kuwa sai sukai biyu a bayanta, biyu a bayan biyun wato sun jeru sunna wata irin tafia mai cike da kasaita idan ta ajiye kafafuwanta sai ta dauke su zahrau dake bayanta ke ajiye nasu, sannan su Najeeba su ajiye nasu
Jakadiya na tafe tana shelar fitowarsu hakan ya sa du wani bawa ko wanda Anmy ta girma ya ja ya tsaya ya sada kansa dan girmamawa ga uwar gidan marigayi sannan uwar mai martaba
Fuskarta sake take daga kanta a hankali sannan da dan murmushi tana amsa irin gaisuwar da ake ta jefo mata, da yawa cikin manyan samarin gidan sukan bi y'ayan dake bayanta da kallo, da yawa sun dauri niyar isar da sakonsu dan a kara kulla zumunci, wasun kuwa na masu kallon sha'awa da tsoro domin su din dai ba dai kyau ba sai dai masifa!
a haka har suka karasa wajen shigar
Dogaran kofar dake tsaitsaye da jakadiyoyin ne suka kwashi summa nasu kirarin da kawo mata gaisuwar da adu'ar Allah ya jikan yarima karami da fatan Allah ya jawo masu zama
Babar jakadiya, tsohuwa ce ta shiga ta duka ta sanar da isowarsu
Tana fitowa anmy ta shiga da bismillah sannan kanta a sade dan girmama sarkin garin agadez duda tana kyautata zaton ta girme shi domin shima ba wani tsoho bane
Saman kujera ta zauna kafin ta ja alkyabarta ta gyara
Baki dayansu kasa suka zazauna kusa da kafafuwan Anmy,
Tun da suka shigo ta lumshe idannuwanta sakamakon kanshin turaran nan dake matukar kasheta a duniya
Sunnan turaran *MUSKI-JAH* sakamakon jinsa da take a wajen wannan bawan Allah ya sakata nemansa a lokacin da suka fita waje a paris
A ranar baki daya tanadinta ta saka ta siyo turaran nan, tana bude shi ta ga wata yar karamar kwalba sannan ba'a cike ba dan ko rabin kwalbar bata kai ba aman kuma yakeda muguwar tsada mai rikitarwa
Daga ranar ta nemi waje ta ajiye maganar turaransa, yanzu abinda ta fi sakowa a gaba irin yanda yake saka tufafinsa
Tana son ta ji wai du suturarsa daya zata kai nawa? Ba dan komai take son gane wasu al'amura nasa ba sai dan ta gane shin gayunsa da sarautarsa na bagidaji ne ko ya waye? (Ji fa rigima)
A hankali ta dago da idannuwanta a lokacin da dogarin nan ke ta fadin" saraki sun amsa gaisuwarku jinnin MUTALAB, saraki sun ji dadin kulawarku .....
Bakinta ta tabe tana ayanna ko a ina mukai magana?
Idannuwanta ta sauke a fuskar mahaifinta wanda akaiwa sasaukan rawani
Irin yanda yake dan murza goshinsa ya sakata sakar masa murmushi domin kwarai ta fanr ya takura da rawanin nan ne
Dubanta ta maida wajen DAYABU, hararar da ya sakar mata ta sakata yi masa murmushi har hakoranta suka bayana domin ta san hararar baya wuce numbersa da wasu daga cikin samarinta zasu dama dan ta tabata zai sha kira domin akoy masu numbersa a cikinsu idan sun sha mata kai ta hada su da yayanta takan basu ba abinda ya shafeta
Kalle kallenta ya kai fuskar sarkin Gadez , a hankali ta bi wajen da ya kurawa ido
Zahrau ce ke kallon Dogarin dake ta zuba ta san tausaya masa take a cikin ranta, sai dai irin kuretan da ya yi da ido ya saka NAJEEBA sakin murmushi har tana dan dantse lebenta na kasa
Idannuwanta masu kale kale suka kaita wajen fuskarsa
Irin yanda sukai ido hudu ya sakata da saurin gaske ta sada kanta sakamakon kallon nan na tsana da ya wurga mata wanda ke sakata jin faduwar gaba da tambayar kanta shin me