Showing 90001 words to 93000 words out of 228147 words

Chapter 31 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10374

*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*

*SADAUKARWA GA*

*SAMIRA HARUN (YA MAMA😉)*
*BILKISU KANAR*
*YAGANA*
*AYSHER*
*JALILA*
*MA NAZIFA*
*RAHIMA*
SADAUKARWA GAREKU BAKI DAYA GRUP MAGE DA FANS MAGE......ina matukar jin dadin kasancewa da ku

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



30


Daga b'angaren mai martaba cikin kamala da datijantaka yake furta" Allah ya taimakeka kana ji na kuwa? Ko dai matsakar network d'in nan ne."

Ya k'arashe yana mai duba wayarsa da yarima dake gurfane gabansa.

A hankali yake sauke wayar daga kunnansa sam baima san yana yin hakan ba.

K'ara k'ura mata ido ya yi da duba irin na son ganin abinda zata aikata, sannan a kasan zuciyarsa kuwa fad'i yake" Acikin gidan nan zata aikata aikin nata? A cikin falona? Tabas idan har haka ya kasance yau ba sai gobe ba sai na zartar da hukunci a kanki a kasata!"

Sai da Najeeba ta kawo kofin kusa da bakinsa , ya sakankance zai damk'a ta janye ta mik'e tana murmushi.

Juyawa ta yi ta bashi baya ta ajiye sannan ta koma ta zauna a wajen zamanta ta d'ora k'afarta d'aya a kan d'aya tana d'an karkad'awa tana kallonsa.

Saukowa yayi da sauri ya nufota yana d'an shagwab'e fuskarsa, sai da ya zauna saman cafet d'in ita kuwa tana saman kujarar ya sakata gaba kafin ya furta" na so ki fara cika aikinki na lada amaryata, ta hanyar shayar da ni da wannan kyakyawan hannun naki mai d'auke da k'unshi ja."

D'an tsura masa ido ta yi kafin ta cire dubanta daga kansa, d'an murmushi ta kuma yi hakan ya saka dimple d'in kumatunta da na kusa da idannuwanta suka lotsa, yar siririyar wushiryar bakinta ta bayyana ga haske da hak'oran ke yi, leb'enta kuwa baya d'auke da komai sai dan man leb'e kad'an da ta goga saman leb'unan hakan ya saka na k'asan mai ruwan pink color k'ara shek'i haka ma mai duhun shima ya k'ara shek'in.

Fuskarta ce ta yiwa kwaliya ta hanyar shafa hodar ruwa daidai da kalar fatarta yar kadan kafin ta caje girarta da kyau ta saka kwali mai kyau mai baki ta ja dan ail liner sannan ta dora gashin idonta mai tsayin da ya girmi na idannuwanta hakan ya saka idannuwan nata kara yin sidik da su abin dai ba'a cewa komai

Dinkin jikinta kuwa wata lafiyayiyar chiganvy ce aka yiwa dinkin sket da riga cif cif da jikinta
Najeeba na dauke da wata irin kira abin birkita lisafin du wani da namiji sannan abin mangarin ga y'aya mata
Ta kasance mai matsakaicin tsayi, domin tsayinta ba cen cen bane,

Najeeba bata da rama sam, tana da dan jikinta mai dan kwabri wanda ke tafe da wasu mama masu dan girma sannan a tsaye suke cirr domin irin masu fadin nan daga kasa ne dauke da yan kawuna bakake sidik masu dan tsini da dan fadi tamkar wace ke cikin sha'awa koda yaushe

yannayinsu kan zama a haka basa shafewa haka halitarsu take shi ya sa bata saka body a waje domin idan ta saka sukan nuna kansu ne koda da rigar mama a ciki,

Cikinta munafukin ciki ne da baya nuna ana cin abinci a cikinsa, ko dan tana gudu tana sport tana abdo a cikin gidansu, hakan ya saka cikinta ke lafe sosai saman wani irin tafkeke, fafadan kugunta mai dauke da wasu irin duwawu da suke da girma sannan suka hade da cinyoyinta suka kara masu fadi ga tudu hakan ya sa take dauke da yannayi na Niki minaj daga kasan

Tun fil'azal Najeeba tafiarta ta kasance irin tafiar nan ta tsokalo rigima, haka halitarta take ba da gangan take yi ba aman da yawa kan kokarin kwaikwaya dan a ganninsu tana sane take yi kuma gannin abin ya karbeta sai su yi kokarin kwaikwaya aman ba hali domin tafiar kasaita tamkar wata sarauniya a jinninta yake tana yi kuma jikinta na motsi daidai misali, shi yasa idan halin ta yi rawa ya kama take anfani da kugunta wajen saka mata sakin baki sunna kallonta bale maza tsabar yanda ta iya juya shi da gadara

Tana dauke da dan dogon wuya sai fuskarta mai dauke da saje sakamakon tarin gashin da Allah ya basu na mahaifinsu da ya kasance shuwa arab
Gashin kanta baki ne sidik har gaban goshinta hakan yake haska copy choko color din fatarta mai santsi da kyalkyali,

Gashin girarta tamkar ta SHAHEED take sai dai ita tana daidaita tata tana gyarata koda yaushe daidai da tsarin da take so a fuskarta

Tana dauke da dara daran idannuwa masu tsaga tamkar na damisa, sunna dauke da gashin ido masu yawa da tsayi wa'inda ko a haka wasu na tambayarta idan ta yi kari ne?
Hancinta kuwa dan daidai mitsali ne, bata da karan hanci mai tsayin nan aman kuma ba a duke hancin yake ba, dan karami ne daidai da fuskarta
Lebunanta sun kasance na kasan ya fi na saman girma da kadan, sannan na kasan tamkar wanda akai masa yannayi na heart domin daga tsakiya ya fitar da yannayin nan gashi idan ta yi niyar shagwaba sai ta kara nitsar da shi sai kawai ka ji ka afka a shaukinsa da son cinye shi
Lebunanta sunna da dan duhu kadan, na kasan ne yake da dan hasken pink sakamakon irin yanda take bashi kulawa ta hanyar saka brosh dinta tana dan gurza shi a hankali a hankali har sai ya fara zafi zafi sannan ta wanke ta kawo hadin zuma da lemun tsami da man haba dinta da take hadawa ta dan shafa kadan sai ta kwonta,
sai ta wanke da asusuba sannan ta kawo maganin bushewar lebe da saka lebe ya yi wacila wacila wato *Sabarob* ta shafa kadan kafin take tafia wajen aikinta ta wanke hakan ya saka yannayin lebenta ya zama wani unik saman ya dan fi na kasan duhu na kasan ya zama mai ruwan pink shi ba orange ba, sannan suke da wani irin laushi da santsi wanda ko da ido idan ka kala zai tafi da kai ne
Daga kasan lebenta gefen hagu kadan, wani dan kurji ne dan karami mai haske irin wanda ake cewa na masasara ne ya fitowa mutun, to ita dai ya fito mata tun tana karamarta kuma bai bace ba, wannan dan kurjin sai ya zama wani cikon sirrin kyan fuskarta, dan tamkar ta yi yar huda ne ta saka abu mai kyalkyali a wajen, har akan tambayeta yanda ta yi ta fitar da shi a kusan lebenta domin idan ta tashi sangartarta takan yi rawa rawa da lebenta sannan ta dan cije wajen kurjin nan idan ta sake shi sai ya kara haske da walwali kafin ta yi wani irin farrrr da idannuwanta

Dafe daidai zuciyarsa ya yi da hannunsa na dama yana kallonta a sanyaye ya ce" me kike so na malaka maki? Me kike so na baki? Ki kama daga kaina har dukiyata duka naki ne Najeeba, ki bani kulawar da nake bukata na roke ki

Najeeba ta dan yamutsa goshinta kadan kafin ta dan fitar da harshenta ta dan lashi lebenta na kasa as usual, a hankali ta ce" me ya sa kake tunanin dan ka malaka min wani abin zan iya yarda da soyayarka? Ka zo da shirin baje min haja ne Elhaj?

Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce" da haja, da ni mai hajar, baki daya nake son baje maki ki taka ki yi abinda kike so da su Najeeba, ni dai burina ki wanke ni son ranki aman ki aureni kwana kusa dan ina mai tabatar maki a matse nake da ke

Idannuwanta ta dan rintse dan jin kunyar wai a matse yake din da ya fada, kafin kuma ta bude tana dan kaucewa kallonsa

Hannunta ta saka daga sama wajen rigarta ta janyo chek din da ya bata a saloon shi kuwa yana kallonta, ba kalacin shi ba, harta wanda ke jiran su fara ya samu huja a kusa na kallonsu ta miko masa gefen damtsen hannunsa

A hankali ta dan ragewa idannuwanta girma ta ce" shi ya sa ka fara marina da yayan banki?

Kafin ya bata amsa ta kara rage tsayinta,
Kanta ta waiwaya cikin dabara ta kurawa wajen dake dauke da abin camerar dake nuna cewar ta nan ake iya ganninta

Shima idannuwansa ya kura a kan nata tamkar sunna kallon junna da mugun kallo,

Cire kanta ta yi a wajen ta ja tsaki a ranta tana furta, wani irin hira ne zan yi da mutun bayan mai yiwuwa matarsa marar mutunci na kallon mu?
Ko kuwa cikin barorinsa?
Ko kuwa kawayenta yan iska da suke jirana su gane min miji ko me?
Gaskiya da sake

Haka kawai sai ta sauko itama ya kasance sunna zaune ne a saman cafet din zama irin na kusa da kusa kadan kafin ta rage muryarta sosai ta ce" ban san yaya aka yi ba daga nan da kwana uku lamarin wankar maza ya fara fice min a rai
Ka san wani abu?

Kansa ya girgiza yana kallonta, ta ci gaba da fadin" na fi kwarewa wajen wankar aljihunnan mazan da suka ajiye mataye a gida suka zo suke bin mu, sukan bude bakin aljihunsu su kashe mana kudaden da a shekara ba zasu iya anfanar iyalansu da su ba,
Ina matukar jin dadin karbar kudin wanda matarsa ta tarbe ni ta zageni
Shin ka san cewar sunana bashi da kyau a waje?
Dan bakinta ta yatsina ta ce" kama sani ne domin wa'inda ke zagin nawa da irin haka da yawansu matan da na zame masu tashin hankali ne, sai samarin da na raina shekarunsu irinka
Ban san yaya aka yi na raina mai kananun shekaru ba
Ni din ce mai rigima
Ina famma da fitina da yawa hakan ya sa nake tunanin anya kuwa namiji mai kananun shekaru zai'iya hakurin halayana?

Matsota ya yi sosai yana dubanta ya ce" kannanun shekarunna ba su zasu hanna na kasa hakuri da halayanki ba Najeeba
Baki san cewa babar kadara ita ke saka biyaya dole ba?

Najeeba....

Ya fada a sanyaye yana mai kara dora mata takardar nan tare da wata takardar itama ta bankin ce sannan ya hade hannayensa ya ce" ba rokona kika yi ba, ban kuma nuna zan iya da dawainiyarki dan kin kasance mai son kudi ko wani abin ba
Abinda na sani *MACE* yar gyara ce, dole a gyara mace, dole a kashe mata kudi idan ana so a ganta tsaf tsaf tsaf da ita, ba wai abinda ya fi karfina na tarka ba, kowani mutun kan yi daidai karfinsa ne
Najeeba, da kwaliyarki, da kyan tsarinki na ganki, a yanzu da nake son kasancewa da ke ina so ki zauna da ni daya kwal, hakan ya sa nake jin zan iya maye maki gurbin sauran samarinki ta kowani fani, zan iya da kowace lalura taki ta yau da kulun, ki yarda da ni ki amincewa motsina hakan zai saka na kara gyara tsayuwana na faranta maki

Murmushi ta yi har cikin ranta, itafa ta mayar masa ne dama dan ta ga iya gudun ruwansa sannan ta nuna masa kudinsa basa gabanta, aman ina ita ina nuna bata son kudi? Ta fada ta kara tana son kudi yanzu tana son su gobe
Ba wanda bai fito nema ba
Ba wanda idan aka mika masa baya karba ba
Halal take ci ba haramun ba
Domin bata je ta baza haja an kwasa an biyata ba
Da dabararta take samun kudi a wajen du wanda ya saki bakin aljihunsa
Da wayonta suke wanyewa lafia da mutun
Bata taba zina ba
Bata taba kusanta kanta da zina ba
Ko rayuwar shan minti ba'a yi da ita
Takan saka kaya wanda ranta ya so aman idan ka yi gigin tab'a jikinta zaku samu matsala kai da ita koma waye kai
aljihun gara kuwa zata wanka har zuwa lokacin da zata shige daga daka.

D'an murmushi ta masa sannan ta k'ara gabatar masa da abubuwan da aka kawo masa dan tarbarsa aman ina shi ya shagala bin motsinta yake da kallo yayama za'a yi ya shigo da wasa ne shi?
Tabas bai shigo da wasa ba, kuma sai ya daki wannan sha'ani da zafi zafi.

A hankali ya saka hannunsa yana shafa wajen hancinsa, ji yake har kamar wani hucin zafin balaki na cin k'owata gab'a ta jikinsa har zuwa cikin k'wak'waluwarsa, shin ina kunya da kawaici irin na y'a mace? Ina girman daraja da mutunci irin na y'a mace? Ita bata da su tun haihuwarta ko daga baya ta saka k'afa ta shure? Wani dalili ya sakata shurewar saboda kud'i ko dan wata buk'ata da ta kasa hakuri? Shi ya sa a rayuwarsa yana addu'ar idan Allah ya bashi y'aya mata zai aurar da su tun sunna k'ananun shekaru ba dan komai ba sai dan kar su zama gandama gandaman yan matan da ko sun je da budurcin to fa ya samu rauni.

Sai yake jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa na lamarin, yana jin abin har cikin k'ok'on ransa, me ya sa a cikin yan uwanta ta kasance wace ta fi sauran irin wannan halayya?
Tabbas suma Dayabu ya shaida masa suna da samari, sai dai shi idanuwansa basu tab'a kama masa su da wani lamarin da zai zargesu ba, me yasa take irin shigar nan sannan take sakin jikinta da kowani k'ato ta yi hira ba damuwa ba wani d'ar? Me ya sa ta b'ata rayuwarta da yarintarta take harkar maza ido rufe? Me ya sa kika yi abinda kika yi har ya kasance na mayar da ke abinda nake harin na kama tsamo tsamo da laifi?

A bayyane sannan a sanyaye ya sada kansa muryarsa da rauni ya furta" Haba *NAJEEBAT*, me ya sa kika saka min madaukakiyar tsanarki ta hanyar zubar da mutuncinki a wajena kasancewata yayanki sannan sarkin ki?
Meye ribar da zaki ci a nan gaba cikin gidan duniya? Waye zai iya aurenki ya rik'e ki da amana bayan ya san wacece ke? Kaico da zamanin da zina ta zamo ado ga al'umma, kaico da wannan zamanin da mutane kan iya dukan k'irjinsu su taka da tink'ahon su d'in yan iska ne.

Ajiye tablette d'in ya yi ya mik'e daga wajen, domin ya had'u da b'acin ran da yake gudu, tabbas yana jin zafin irin abubuwan da take yi ba dan komai ba sai dan ta kasance yar uwarsa, y'a a wajen auntynsa aminiyar anmynsa wace take matuk'ar k'aunarsa,
taa d'in k'anwar DAYABU ce d'an uwa kuma amininsa wanda suke hirar sirri da junna harma ya haye masa, ita din y'a ce a wajen Abih d'insa, daga ita har yan uwanta yanai masu soyayya ta yan uwantaka, shi d'aya amynsa ta mallaka, yana da yan uwa yan mata wajen sauran matan mahaifinsa sai dai babu wata shak'uwa sosai a tsakaninsu ko dan sunna nesa ne?
Yana jin zafin du abinda za'a ce su suka aikata domin yana masu kallon y'ayan da Anmy ta haifa.

Hira suka sha har bayan magariba ita da aka ce ta salame shi kafin sallah magariba.

A daidai lokacin da ta zo shiga b'angarensu ta ringa jin hayaniya da kuka sama sama hakan ya saka gabanta ya yanke ya fad'i ta afka da gudu dan gannin abinda ke faruwa.

Mai martaba ne zaune a kujerar da idan ya hau kowa kan zauna a k'asa.

Yau ma Abih ne zaune, matarsa gefe tana rusa kuka da Anmy cen gefe tana jan carbi, sai yan uwanta dake zazzaune kawunansu du a k'asa kusan su dukansu.

Tunda ta afko d'akin a tsorace sai da ta bi kowa da kallo, hakan ya saka sukai ido hud'u da shi.

Gabanta ne ya kwanci kwanci ya fad'i sakamakon irin yanda idanuwansa suka kad'e sukai jajajir ya kuma b'alla mata kakausan hararan da ya sakata jin tana jin fitsari.

Da sauri ta kai k'asa a wajen da take tsaye kanta a k'asa tana jin har jikinta ya d'an fara rawa rawa dan irin fad'uwar da gabanta yayi sakamakon tsagwaron b'acin ran data gani a tattare da shi sai ta shiga taitayinta ta sadda kanta baki d'aya ta had'e hannayenta a saman cinyarta bata kuma d'agowa ba.

"Allah ya k'ara maka lafia wani irin zama ne wannan? Wace irin rayuwa ce wannan? Daga na fad'i gaskiya shikenan ya tsintsinka min mari, ya hankad'a ni na fad'i gaban goshina ya tsage bayan ya d'auki kusan kwana goma yana min gabar da ban san abinda na masa ba nice ya dace na masa gaba dan a gabansa NAJEEBA ta shak'e min wuya ta marar min fuska yar uwarta na rik'e da y'ata da na haifa, yayansu na kallo aman bai d'auki wani mataki a kansu ba bayan a ranar da ka mana shara'ar nan ne. Daga na tambaye shi inda Zahrau ta je wai da gaske ta auri sarkin agadez shine yake ce min eh Allah ya yi, ai ta Allah ba tawa ba?"

Sasautawa ta yi tana k'ara sada kanta domin ba ido da ido take maganar ba ba zata iya kallon idanuwansa tayi bayanin nan ba, cikin kuryar kukan da son lalle sai ta fasa k'won daya tsaya mata a wuya ta ce" Allah ya taimake ka, shine yau MUTALLAB zai bud'i baki ya ce min na daina sheganta masa y'aya dan ba shegu bane sai dai na nemi shege wa wajen ubana?"

D'agowa tayi tana kallon yaren daya bayan daya ta ce"
*Allah ya ja da ranka shi ya manta tasa shegiyar ne?"*

A firgice du suka dago sunna dubanta banda wa'inda ta yi hakan dan su ji sai yan uwansu da ko a ka basu damu ba , tun daga DAYABU, DA UMMU, DA UMMULKHAIR, DA NAJEEBA wa'inda suka rigaya suka mallaki hankalin kansu wa'inda ta d'aukaka rigimarsu ne dama dan tana so sai ta fasa sirrin da ya fad'a mata ya rok'eta kan ta b'oyewa y'ayansa dan yana jin matsananciyar kunyarsu, yana jin kunyar ranar da zasu ji irin abin nan su kale shi da shi, ya boyewa duniya da y'ayansa yarinyar nan ba dan komai ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login