Showing 210001 words to 213000 words out of 228147 words
Chapter 71 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
yake mata tun da ta fito sai yanzun ya kifta idannuwansa, ya je ina? A cikin wannan halin da ya wankawa Najeeba mari har ta yi kuka?
Ammi ta kuma kallonsa tana hade rai sosai kamar wace bata taba yin daria a rayuwarta ba ta ce" ka tashi ka tafi bangarenka lokacin sallah na gabatowa kuka yaren nan dan wake ne zasu yi ka ga har kwabin nasu ya hadu "
Wajen kwabin ya kai dubansa, robar da Najeeba ke tukawa da kwabeben abin da bai san ko meye ciki ba, sai muciyar da ta saki nan kasa sanadiyar shigar zazafan marin da ya sakar mata, sai kwalbar yaji da abin kwai da mayonaise da lemun tsami da magi
Mikewa ya yi dan bin Umarnin mahaifiyarsa, cikin nutsuwa yake takawa har ya idasa ficewa aman ya bar rawanin nasa da babar rigar tasa a nan
UMMU ta girgiza kanta ta ce" Gaskiya kawata kina takurawa Sultan haba, gaskiya ki daina biyewa wancen sangartaciyar yarinyar, meye lagonsa kuka samu ne zaku fara bashi wahala ko me ? "
Yar daria AMMI ta yi, cike da farin cikin da ta fito da shi, da farin cikin gane idanma SHAHEED na cikin halin matsananciyar soyayar Najeeba to fa itama ta kamu da ita , domin abubuwa da dama sun nuna mata haka tun kafin su samu wannan sabanin, idan ka dauka irin yanda ta yi hakuri da maganar fita saloon, ta yi hakuri da fita yawo, Najeeba ce ke yawan murmushi idan ana maganar shaheed maimakun da, abinda ta fi tsana a yi maganarsa, uwa uba yanzun tana shinfideta saman bed ta bata goro ko zata daina jin tashin zuciyar sai ta yatsina fuska ta ce" AMMI, to ai ba sai ya ringa nuna min ya fi son Nadia ba ko? " sun taru sun sakata a farin ciki, AMMI ta ce" wai kin san wani abu nana, anya yarinyata ba tana da wani abu ba? "
Ummu ta yi murmushi tana gyara zamanta ta ce" Ba yarinyarki kadai ta harbu ba, harta Nadia, dan a zaman da muka yi a dakin cen tare na tabata tana da wata kama "
Idannuwa AMMI ta lumshe sakamakon jin wani irin farin ciki na lulube zuciyarta, Alhamdulilah, Alhamdulilah, Alhamdulilah, ta ringa ambata a fili,
Shekaru nawa sunna dakon jiran samun wannan kyauta?, ashe dai bayan Aliyu marigayi yana da rabon samun wani? Ashe dai ba zai biyota ba daga shi dif haihuwa ta dauke ko sama ko kasa? Najeeba na dauke da junna biyu, hakama Nadia? To ita me zata ce da Allah ne da irin ni'imomin da yake lulube ahalinta da su? Zata kara ninka ibadarta ne, zata ringa barin goshinta a kasa ne tana yiwa mai gaya mai duka kirari, zata ringa kai gaisuwa ga fiyayen halita, sannan ta kara rokar Allah kan ya bara mata yan tayin nan, duda hasashensu ne a matsayinsu na datijan da suka ga yau suka ga jiya suka iya bambance abubuwa da dama na rayuwa
Ammi ta mike tana fadin" Mariam, ki zo mu kira docter ya auna min ita Maryam "
Kamo hannunta UMMU ta yi tana girgiza kanta ta ce" ki kyaleta Bilkissu, idan shi din ne da zai bayana kansa, sam bana so ta san da wani abun a yanzu kin fa san shi kansa cikin baya tashi ciwulwutarsa sai an ambace shi, yanzu zo mu jefa masu dan waken nan sun yi gudun tsira "
Daria AMMI ta yi itama ta shiga tatara kayan tana fadin" Allah ya shiryi Shaheed, ka zo waje maimakun a ringa ihun murnar zuwanka aa, kowa fashewa yake abinsa, kuma ba wata magana yake masu ba da ido ne zai ringa bin su uwa ya samu sabuwar hakita "
Itama UMMU dariar take, nan suka shiga shapter abinda ke faruwa idan yana waje da yaren sunna shan daria
A wannan rana sallah kawai ke tashin Najeeba daga nanauyan bacin da ta ringa yi, sai dan waken nan da ta wuni ci, domin baki daya kwadayinta ya taru ya tare a kan dan wajen
Cen dare wajen karfe biyu ta ga message da numbersa, abinda aka rubuta a ciki shi ne *NA KASA BACI* , ta karanta ya kai sau hudu kafin ta tabe bakinta ta kashe wayar ta ajiye ta juya ta ci gaba da bacinta hankali kwonce
Da asuba ta makara domin har an gama sallar asuba sannan ta iya mikewa jiki du a mace ta shiga wanka
A lokacin yan uwanta du sun fara aiyukan gidan da ya zame masu jiki, kowace ta kama aikinta, da farko tana jin hayaniyarsu dan sun share dakin sun cenza abin shinfidar, sai dai daga baya sai ta ji diffffffff a lokacin kuwa Ummulkhair na kakaba daria muryarta sama sama
Idasa broshing din bakinta ta yo, dama ta yo wankanta ta daura alwallarta ta juyo a hankali ta fito daga bayin ta juya tana rufewa ta idasa shiga cikin dakin
Turuss ta yi sakamakon ganninsa zaune bakin gadon, cikin doguwar bakar riga irin ta sallah, rigar ta kara haska shi ya yi wani freshh da shi, sajen nan nasa lufluf sai dara daran idannuwansa dake kabta kikam yana mai binta da kallo
Cire kanta ta yi a sanyaye ta furta " Morning "
Bai iya amsata ba, duda mamakin jin ta gaishe shi da ya yi bayan tana fushi da shi, yana kallonta ta karasa wajen kayansu ta buda ta ciro rigar sallah da pant da bras
Bata saka pant da bra din ba rigar sallar ta fara sakawa sannan ta dauki turare ta shashafa du wani sasa na jikinta kafin ta shinfida darduma ta shiga gabatar da sallar asubahi
Sai da ta gama salarta cikin nutsuwa sannan ta mike ta dauki pant dinta
Juyawa ta yi ta duka ta saka wanda hakan ya saka shi kara yi mata kuriii yana kallonta
Sai da ta gama sakawar kafin ta ciro doguwar riga ta atampa, rigar kuwa ba'ai mata gidan mama ba dan haka take son saka bras
Rigar sallar nan ta dan sasauta ta kaita daidai kugunta sannan ta juya masa baya hakan ya sa dogon bayanta shafafe wanda baya dauke da lungu lungu ya tsatsare shi sai dan fadin mamanta kadan da yake hangowa har ta saka bra dinta sannan ta sabule rigar baki daya
Dukawa ta yi irin dukawat rakumi kansa kasa jikinsa sama ta dauki rigar wanda hakan ya saka shi sakin ajiyar zuciya yana kara gyara zama yana mai binta da kallo
Rigar ta saka ta juya tana jan zif dinta sannan ta dauko dan kwalin rigar ta daura saman kanta ta kashe irin daurin nan na ture ka ga tsiya
Rigar bacinta da ta cire ta dayke ta ninke ta mayar da ita wajenta sannan ta koma wajen dardumar itama ta nade ta kaudata ta karasa gaban madubi ta ja ta tsaya tana bin kayan kwaliyar su Ummu da kallo
Murmushin mugunta da neman fada ta yi kafin ta shiga uda turarukansu
Ai kam wani irin wanka ta shiga yiwa jikinta da turarukan nan tana harhadawa har suka fara hawan mata kai dan tsabar barna ama bata daina ba sai da ta ji ta jika da turare sannan ta ajiye
Juyowar da take kanta ya kusa gwaruwa da kirjinsa hakan ya saka kirjinta bugawa ta ja baya kadan ta dora hannunta kan abin madubin nan da ba kwari gareshi ba, gannin hakan ya saka da sauri ya sa hannunsa ya taro kugunta ya rikota jikinsa har sunna jin numfashin junna na garwaya waje guda
Muryarsa a shake ya ce" Ni zaki nuna tamkar bana waje BEEBAH? "
NAJEEBA ta hadiye busashen yawun makwogwaronta, so take ta masa rashin kunya ta mumurguda masa baki, sai dai walahi tsoron marin nan nasa na jiya ya mata katutu a rai, ama idan ya san wata ai bai san wata ba
Fuskarta ta yatsine a hankali sai kuma ta saki wata irin shagwababiyar murya ta ce" Haba SHAHEED, me kake so? Ko na kara fada maka sirrin abinda nake sha dan samun ni'ima ka kaiwa kawata? To SHAHEEED abunuwan ne da yawa walahi, da ka je wajen su Ammi su suke bani sai su harhada maka ka kai mata ta ringa sha may be a dace "
Bakinta ya kurawa ido da mamaki, furucinta yake aunawa bisa mizani, a hankali ya yi niyar yin magana sai dai bugawar da zuciyarsa ke yi ya saka shi lumshe idannuwa yana ayanna yau ya ga tashin hankali, ya yi gwa da gwa da maza masu abin tsoro basa kayar masa da gaba sai wannan ficiciyar yar?
Najeeba ta dora hannunta saman nasa ta shiga kokarin kwace rikon da ya yi mata idannuwanta saman fuskarsa tana tsinewa zuciyarta da dukan wasu burikanta, yaya zuciya da buri zasu yi mata haka? Dama su din masu cenza ra'ayinsu ne suka sakata hawa kan turba yanzun suke son sakinta a tsakiyar filin daga? Wannan wani irin tashin hankali ne da bata shiryawa haka ba? Rayuwarta da shi ta dauri niyar ko a yaya ta zo mata hamdan, idan da dadi idan babu oho, sai gashi banzar zuciya da banzayen burika na k8n fari mai mata sunna neman tarwatsa mata shiri? A hankali ta kuma kallon kyakyawar fuskarsa wace ke wartar du wani tunaninta da nazarinta, murya a shake ta kama hannun da dan karfin da take tunanin tana da shi ta ce" KA CIKA NI NA KARA GABA! "
buda idannuwansa ya yi da wani kallo mai tafe da sako, sakon ya kunshi magangannun ban hakuri, da rarashi, da roko irin na ki ji kaina ki tausaya min,
Bakinta dake mutsu mutsu tana rike shi dan kar ta yi abinda zai kurumtata ta kuma budawa ta ce"
Barka da juma'a jama'atul musulmi
A gaskiya ba zan iya kwatanta maku irin farin ciki da nishadin da kuke sakani yan gidan Mage Grup, walahi na wuni ina shan dariar chafterku, harda masu rrrrrrrrrrr na ce ku yi hakuri kar ku yi amai😌😌😌😌😌
[31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
65
*SAKO ZUWA GARE KU JAMA'AR CIKIN GIDAN MAGE, JINJINA, GAISUWA, FATAN ALKHAIRI, ADU'AR GAMAWA DA DUNIA LAFIA, HAKIKA ADU'O'INKU SUKAN SAKANI NA RINGA JINA CIKIN MATSANANCI FARIN CIKI, UWA UBA IRIN KOKARIN DA KUKA RINGA YI A KAINA, SAKWANI SUN SHIGA WAYA KUMA AN GODE, TABAS ALLAH SHI KE HADA BAWA DA MUTANEN KIRKI, SANADIYAR RUBUTU NA HADU DA MUTANEN KIRKI WA'INDA NAKE FATAN KODA NA DAINA RUBUTU ZAMU CI GABA DA KUTUNCI TARE DA JUNNA, ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI YAN UWANA MA SAMIRA DA BILKISSU, SHAWARWARINKU GARENI KO A WANI LOKACI ZAN DAUKA DOMIN KU DIN AMINAI NE KUMA YAN UWA NE*
*NA GODE*
Ta kuma furta" ka sake ni Shaheed "
SHAHEED ya dan girgiza mata kansa bai iya bata amsa ba yana kallonta
Takaicin shirun nan nasa nukurkusarta yake har cikin hanjinta
A rikice ta ce" Ka sake ni dan girman Allah ka bani lafia na huta da fitintunun nan, zuciyata ba zata iya dauka ba SHAHEED, me kake jira da ni ne? Wani wulakancin kuma kake shirya min ne? SHAHEED tun ban san yarenka a kaina ba ka yi min wanka a bakin titi da ruwa masu sanyi, athmata ta tashi tun ina jan numfashi har na sume ka dana min allura ka kawo ni ka watsar, Shaheed ka tashi ka hada ni aure da aminiyata zaman kishi?, Shaheed ka saka aka kawo ni bangarenka na zauna a daren da yake nawa kunnayena suka jiyo min du wani irin abinda ke faruwa tsakaninka da NADIA, Shaheed Nadia
Wasu hawayen wahalar ne suka ziraro mata masu zafo ta dora da fadin" du bai isheka ba ka dauke ni ka kaini saman datin da ta zubar ka dora ni
Shin ni ba mutun bace?, Shaheed kana nuna min ido da ido matanka, ai ba cewa na yi ba matanka bane ba ko?
Sannan Shaheed du bai isheka ba ka tambaye ni abinda nake sha? An fada maka ina shan wani abin ne? Ba abinda nake sha, bai isheka ba sai da ka mare ni dan na ki fada maka abinda zaka kaiwa yar gwal?,
A hankali ta shiga rera sansanyan kukanta kafin ta dora da fadin" Nima ba son naka nake yi ba ai kau ......... " ta idasa fashewa da kuka mai ciwo
Shaheed ya ringa girgiza kai a hankali yana jin wani irin ciwo da zafi da tashin hankali a kasan zuciyarsa, a hankali ya ringa sasauta irin rikon da ya yi mata muryarsa cen kasan makoshi ya ce" Dan Allah, ki daina cewa bakya *So na*, ki daina BEEBAH "
Yana fada ne yana idasa sakinta, har ya saketa baki daya ya dafe goshinsa da wata irin juwa dake son maka shi da kasa ya juya mata baya kansa na sara masa, a hankali ya shiga cira kafarsa yana neman hanyar da zai fita a dakin, baki daya jikinsa kuma rawa yake masa
Bata dakatar da shi ba sai hannayenta da ta harde a kirjinta tana mai binsa da kallo har sai da ya bacewa ganninta sannan ta saki dan murmushi tana share hawayen da ta yi forcing ta fitar a gabansa ta karasa gaban madubin nan ta zauna
A hankali take tsara kwaliya a fuskarta a kasan zuciyarta kuwa fadi take 'Zan zame maka mace wace ta fi kowace mace rauni da zubar da hawaye a gabanka, SHAHEED ba zan yarda ka cin min ina zaune ba'
Da kallo Ummulkhair dake zaune goye da NUSAIBA a bayanta wace ke rigima ta bi shi da kallo domin ita daya ce a falon, itama an sakata zama ne dan ta duba Mardiya da aka gama shaidawa cewar gatanan zata zo domin abih ya yi kiran Ammi ya fada mata cewar Mardiya ta yi rantsuwar daga gidan cen zata zo wajenta
Kanta ta sada da sauri sakamakon ido hudun da suka yi tana dan kara jijiga yarinyar, sam basa jin nauyin goyanta su kam, kansa ya cire ya fice a falon
Tana shirin mikewa ta shige ciki wajen Najeeba ta ji an banko kofar an shigo falon
Mikewa ta yi a tsorace tana kallon wace ta shigo a haka din
MARDIYA da kanta ke hayaki sakamakon labarin da aka kawo mata cewar Abih ya gyarawa UMMU gidansa dake Jeune cadre ya zuba mata kayan alatu tamkar gidan zai tsage dan kaya, ga wani irin fita daban da ya yi a anguwar, bata yarda ba sai da ta je ta ganewa idannuwanta duda mai gadi ya hanna mata shiga aman daga inda take ta ga abinda ta gani shine ta koma masa ta same shi gadan gadan da tashin balagar rashin kunya, ya mata banza shine ta ce zata zo ta sammu Ummun su yita ta kare, ba zata amshe mata miji ba bata isa ba tsohuwar banza kawai
Gadan gadan ta idasa gaban Ummulkhair ta ce" Ke ina tsohhuwar guzumar uwarki take? "
Ido Ummulkhair ta zarro tana kallonta, ita dai bata da fada irin nasu, bata iya hayaniya sosai din nan ba, Ummukulsum ta fi ta iya maida martanin rigima, har solofiyo suke ce mata ita da Zahrau, hakan ya sa ta dan rike kafar NUSAIBA dake daidai cinyarta tana kallonta ta ce" Wace haka kuma Mardiya? "
Mardiya ta matso da wani irin balaki ta hankadata, bata shiryawa gannin hakan ba hakan ya sa ta je baya gaba dayanta ta fadi da bayanta saman Nusaiba jikin karfen kujerar falon
Wani irin tartsatsin ihu Nusaiba ta saki kafin ta dauke dif
Da gudu suke firfitowa daga kofa daban daban
A guje suke nufo yar uwarsu dake yashe a kasa tana ta kokowar son kwonto Nusaiba da ta kara nauyi a bayanta sannan gwuiwar hannunta na zubar da jinni
Da wani irin gudu AMMI ta idasa wajen ta shiga son kama su hankalinta tashe bakinta ya kasa furta komai
Da wani irin sauri UMMU ta ture NAJEEBA dake son karasawa itama aman sam bata iya gudu ko sauri ba hakan ya sa take wata tafia tingil tingil hankalinta tashe
Mardiya dake tsaye idannuwanta rufe ta ce" Baki dayanku bakinku a hafe ko? Bayan auren cin amanar da son zuciya kuma shine za'a kaita sabon gida tana tsohuwa ni a barni a gidan da yara suka tashi suka lalata? Walahi ban ga yar iskar da ta isa ta shigar min gidan miji ba! "
Tas , fuskarta ta amshi wani irin fitinane, mahaukaci, zazafan marin da ya sakata kwala ihu ta juyo tana kallon kantamin hannun da ya sauke mata biyar
Bai wata wata ba ya kara dauke fuskarta da wani tsadaden, wulakantace, fitinanen marin da ya sakata yin luuuuu cike da mahaukacin mamaki da al'ajabi ta kwala ihu ta ce" Kan uban cen kaya sa, ni ka mara? Ashe kuwa zaka iya marin Mutalab da MARIAM? zaka iya marin uwarka mahaifiya? "
Da wani irin hauka hauka ya shiga kunce belt din dake daure a kugunsa , gannin haka Najeeba, da Ummukulsum suka rigaye shi afka mata, kan kace meye wannan kanwarsu bakuwarsu da yake itama jinnin shuwan ne ke yawo a jijiyoyinta ta afka masu, yaren suka ringa neman wajen kai mata duka
Ummu ce ta daka masu wata irin tsawa mai hade da gunjin kuka, AMMI ta dago da NUSAIBA a hannunta wace hannayenta ke yin lagai lagai muryarta cike da kuka ta ce" Ta kashe ta, ta kashe yarinyarta ta cikinta, ta kashe Nusaiba! "
Gaba dayansu ne suka idasa juyowa wajen iyayen nasu a tare, cikinsu mutun uku ne suka zube a summe sakamakon gannin irin jinnin dake zuba daga keyar NUSAIBA,
Abih da shigowarsa kennan a hankali ya silale a wajen zaune dabas ya dora hannayensa bibiyu
Yaya Dayabu ya daga kafarsa ta