Showing 171001 words to 174000 words out of 228147 words

Chapter 58 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10368

sha'awa nema kwata kwata shima tana masa fatan shiriya

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" to in bama gagawa irin ta dan adam ba, MUTALAB fa goma sha shida ya kyankyashe mata, ciki kuma biyu kawai ya kilace a dakin miji, suka san ko na tausayawa wahalar yan tsofafin mazajensu na mika masu wata jinnin MUTALAB din? Kun san abinda ya yi yaya shi ya yi kanwa"

Daya daga cikin kawayen Mardiya, wace ta bata wannan rana takanas tare da fada mata sirrin nan, bama kawarta bace kawar kanwarta ce wace ta turota takanas dan a kunna masu , rikakiyar yar bariki ce kana ganninta ka ga wace ta auri duniya auren zobe ta yi kas kas kas da cingan ta ce" kwarai kuwa hajiyata, ai MUTALAB ya iya haihuwa, aman ba ku goma sha shida babe matan, ku goma sha Bakwai ne ko kin manta wace aka samu *KYAUTA?* (irin sararsu ne, zaka ji an cewa yaron da Allah ya yi aka same shi haka KYAUTA)

Sai da Zahrau ta kusan faduwa daga tsayen da take, a tsorace ta kai dubanta wsjen wace ta yi maganar hakama su UMMUKULSUM ,
Najeeba kanta sai da ta rintse ido, aman kuma dama walahi ta shiryawa irin ranar nan, ta san da a irin yanda ta tarawa kanta neman magana sai an binciko sirikan rayuwarta dan a nemi tozartata, tama yi mamakin sirrin gidansu da ya jima haka ba tare da an jima da bankado shi ba, shi yasa ko ba komai take gannin ba laifi Mardiya fa ta yi hakuri, domin tsayin lokacin nan bata fada ba sai yanzu ai kuwa ta yi kokari

Kannanun magangannu ne suka shiga girmama, harma wasun na neman karin haske da maganar KYAUTA

Najeeba ta girgiza kanta ta ce" kai dan duniya, dan duniya bai yi ba, wato shi ko yaya ka yi da shi hakan take gareshi, kwarai kuwa mu goma sha shida ne kamar yanda na fada hakan ne, domin duniya ta san MUTALAB ya haihi y'aya goma sha bakwai ne, maza biyu, mata goma sha biyar, a yanzu da na gano munada yar uwa sai nake fadin sha shida, abin farin cikin alfahari nake da Ubana da bai zubar da yar kanwata ba, ya haifo abinsa santala sannan ta samu kilacewa wace zata yi min wuf da mijin daya a wajen nan alkawari ne........ta karashe tana mai sakin murmushi ta kai dubanta wajen Aida ta ce" ina take?"
Da sauri Aida ta shiga dakin hutun NAJEEBA ta fito da wata budurwa kyakyawa mai tsayi irin na yan uwanta, kamarsu daya sai dai ita din fara ce, sannan hijab ne jikinta yannayinta ya nuna tana da dan tsoro domin sai rarabewa take

Su kansu yayunta sun sha mamaki, a hoto suka san yarinyar yaushe Najeeba ta santa har ta kawota?

Da sauri Najeeba ta fincike hannunta da take jijimkewa ta ce" Jinnin Mutalab Allah kawai yake tsoro, jinnin Mutalab dokokin Allah yake karewa, haduwa da shi kawai yake tunani, idan ba dan haka ba da ya yanka dan mutun sai dai uwarsa ta haifo wani ba shi ba! Sakar min hannunki ki kalli du wace ta bi ki da kallo daidai misalin wanda ta yi maki, idan yar mutunci ce ki yi mutunci da ita, idan ba yar mutunci bace kika daga mata kafa walahi sai na tsinka maki mari, kema ganninki kika yi, suma wa'inda suka same ki daga ke basu kara wata ba hakan na nufin kadara ce ta afka masu wace ba yar shegiyar da ta fi karfinta, ina alfahari da ke, ZAHRAU na Alfahari da ke, Ummulkhair na alfahari da ke, Ummukulsum na alfahari da ke, mu kam muna alfahari da ke a ahalinmu"

Zahrau ta matso kusa da su su hudun, tana kallonsu ta lumshe idannuwanta ta ji wani dadi a kasan zuciyarta, burinta dama itama ta dawo cikinsu ashe yar rigimarsu har ta kawota gidan nan? Hannunta ta kama a hankali ta dan murza sannan ta sakar mata murmushi wanda ya sakata fashewa da kuka ta shiga rungumarsu cike da wani irin farin ciki, ashe zasu karbeta? Ta sha labewa ta kalle su tana son su a ranta aman kuma tarin tsoron ta kusance su ya saka kulun take kara hangensu daga nesa, tunaninta kar ta kusance su, su fatataketa dan ta kasance ba da aure aka haifeta ba, ko a message din da suke da NAJEEBA walahi gani take wasa ne, ashe dai da gaske ne? Ita kam ina zata saka ranta dan murna da farin ciki?

Habu ne ya ringa kikifta ido yana gannin yanda wajen yake kara daukan haramar rikicewa a fili ya ce" toh fa"

Zahrau ta dan zunguri keyar NAJEEBA a hankali ta ce" itace surprise din da kika ce min kin adana mana?"

Najeeba na satar kallon budurwar nan tana kokarin fita ta gyada kanta da wani irin sauri ta saki hannun yan uwanta ta finciko hannun budurwar da ta kasance karya uwar fada, domin dai ita sanadiyar fada du an yayage mata fuskarta da reza an yi mata dinkunna hakama a wuyanta tafka tafkan dinkunna ne na ciwo ga kuma wajen girarta

Ai kuwa a shirye take, ita ta fara kokarin kaima NAJEEBA bugu, cikin ikon Allah wajen ya nemi harfitsewa domin kuwa da kyau NAJEEBA ta ware take rama rigimar da bata yi ba na satitika dan kuwa har ta tsigewa budurwar nan kitson kanta jinni ya fara zuba hakan ya sa itama cike da bacin rai ta ciro rezarta ta nemi yanke mata jiki, daidai polisan nan sun shigo da gudu dan Zahrau ta kirasu tana ihun su taimaka, Najeeba kuwa ta saka hannunta ta tare rezar sai aka yanketa a hannunta yanka mai girman da jinni ya bale mata

Yanda suka ringa hankado du wani mai rigimar waje ne ya saka shi kara tsaida abin a kansu yana kallo
Su kansu sai a nan suka ankara da Habu, shima sukai waje da shi

Kokowa ce ake tsakanin NAJEEBA da yayunta, ihu take su saketa sun tatare sun riketa sai tirjiya take ja hakan ke sakawa suke kara matsowa waje ga hannunta da Ummulkhair ke ta kokarin daurewa sunna mata ihun ta tsaya ta tsaya aman firrr ta ki idonta ya rufe ji take baki faya zuciyarta ke son tsayawa idan har bata janyo makoloton yarinyar cen ba

Police din ne ya umarci su saketa, dan kuwa su sunna wajen nan dan su hanna du wata fitina da shigar du wani fitinane ko namiji, sai gashi yau ranar farko an fara a haka? Sunna tunanin hutu ne ya same su ashe dai zasu motsi motsi na arziki?

Zahrau ta ce" ba zaka gane ba, ka bamu hanya mu koma gida da ita idan muka saketa mu muka san wa muka saki"

Irin jarumin nan, sannan yana so su gane shi ko zuwa gaba dan idan ana son tsaro su nemi sunnansa a masarautar ya ce" Gimbiya ki yi hakuri ku saketa , mun san aikinmu zamu iya da komai"

Zahrau gannin Yaya Dayabu yana tahowa da wani irin sauri sai ta saki Najeeba, domin kuwa ta tabata a irin yanda yake jefa kafar nan tasa idan ya iso su kansu sai sun sha mari dan haka ta shirya karbar nata, ita dai kam ta shiga uku, dama Najeeba sai da ta fada mata yau ta tabata sai an yi rigima domin haka ne idan ta jima bata fito ba takan tarar da an shiryawa fitowarta, shine harda fadin ita kuwa ba zata kula kowa ba

Sunna sasauta mata rikon da wani irin karfi ta yi ciki da police din nan, wanda hakan ya saka SUKTAN kara rintse idannuwansa yana jin bugun zuciyarsa ya karu kashi casa'in, numfashinsa ne ya ringa doka masa da karfi yana fita da sauri, idannuwansa suka kara yin ja a lokacin da ya ga ta daki police din nan da hannayenta uwa uba ciki ta yi da shi wanda hakan ya zo masa a ba zata ya nemi riketa ta damki damtsen hannunta da karfi dan ya samu ya hanna mata ficewa,
Dan daudun nan na nesa kadan yana ta dira yana ihun a saketa ya tare mata matsiyaciyar nan shegiya busashiyar karuwa

Juwa ke daukan NAJEEBA dan da gaske jinni take zubarwa mai mugun yawa aman zuciyar ta shuwa ta tashi, idannuwanta sun gama rufewa sai ta cire makwogwaron karuwar cen

Baki dayansa ya mike tsaye, jikinsa har rawa yake tablette din a hannunsa ya saketa sakamakon gannin da gaske Police din nan so yake ya rungume masa mata ta baya dan ya ci karfinta ya hannata zuwa wajen fadan ita kuwa tana son fin karfinsa, gashi dayan kuwa du yana ta fitar da kutane yana fadin kar wanda ya dawo sai da katin gidan sarautar da za'a buga a rarabawa du wani client dinta

DAU kake jin karar wani mahaukacin marin da ya saka NAJEEBA dauke wuta lokaci daya , domin gaba daya hayaniyar nan ce ta dauke mata ta daina jin maganar kowa, sai kuma fatar idannuwanta sukai mata nauyin tsiya a saman lebenta take son furta kalmar nan kwaya hudu wato *yaya ka mare ni?*
Aman fir maganar ta ki fitowa a lokacin da ya warci hannunta dake cikin na Police din nan ya yi mata wani irin ja ya karasa kusan yayunta da du suka aniya kare fuskokinsu sai dai cikin ikon ALLAH da hannun nasa na hagu ya shiga sauke masu tankadeta mareta ciki kuwa harda bakuwar yau tau, wace yau yau ta fara irin haduwar nan da su haka, hakan ya sa ta kwala wata kara idannuwanta waje ta dafe kuncin nata tana zazaro ido cike da mamaki da tsoro da tashin hankali harma ta ringa jin zata saki fitsari

Luuu take yi daga bayan DAYABU wanda bai cika hannunta ba ya aniya zazaga masifa, sai dai lokaci daya ya yi tsittt sakamakon irin yanda jibga jibgan dogaran Fadar suka shiga cika wajen da wani irin bulaloli a hannayensu sunna dakatar da du wanda bai rigaya ya baiwa kafarsa mai ya kara gaba ba, sunna gurfanar da su

Lokaci daya Amintace ya ware babar muryarsa fuskar nan tasa a hade ya furta" ku zube a kasa, ga MAI DAMAGARAM zai karaso, kowa ya kai gwuiwarsa kasa ya sanda dubansa ko kuwa na rantse da wanda raina ke hannunsa zan saka babarbara na yanke kafafuwan mutun sannan na kwakwale idannuwan shege domin ga MAI WUKAR YANKA NAN TAFE

Cikin ikon ALLAH tun daga kan polisan, har zuwa su yaya DAYABU da sauran mutanen dake wajen du suka zube kan gwuiwoyinsu, a nan ne NAJEEBA ta tafi luuuuu ta kusan faduwa kasa, sai dai Yaya Dayabu bai bari ba ya saka hannunsa ya tarota jikinsa yana kallon fuskarta gabansa ya fadi, a hankali ya dora kansa saman goshinta hawayen da yake ta rikewa dan marin kannen nasa da ya yi suka samu damar fitowa, Zahrau kuwa hannunta na rawa kasa kasa ta kara tauke kullin hannun NAJEEBA kafin ta saci kallon dogaran nan da baki dayansu suka yi wani irin gurfanawa hannayensu a jijimke sunna masu kawo gaisuwa sai dai ba magana, wajen kuwa ya yi wani irin dif ba magana sai ajiyar zuciya kala daban daban dake tashi, sai kuma takun tafiyar dake shaida koma waye ke yinta yana yinta ne da fushi, da kuma karfi


Zuciyoyi ne suka shiga tsintsinkewa a lokacin da Amintacen sarki ya kai gwuiwarsa guda kasa dayar a tankwashe ya dago jimkaken hannunsa kansa a kasa muryarsa sama sama ya ce""""""





Hello mutanen yaya ne😊, sorry walahi yarinya ne ba lafia, godia nake da sauki yanzun Alhamdulilah
[31/03 Γ  21:57] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



53

Sai da ya ware murya, wanda hakan zai iya tsoratar da wanda bai saba ji ba, ya nutsar da wanda ya saba ji, jikin mutun ya kwashi tsuma ba tare da shi aka koda ba amintacen sarki ya ce" Gagara badau kake dan sarki jikan sarki, takawarka lafia jarumi hamshaki barde, kai ne namu kai ne nasu kai din na kowa ne, tafiyarka ke shaida sahunka Mai wukar yanka, kai ne usulin Babarbara ba itace usulinka ba, daga kasa kake dagowa sai ka nuna sama ka saki, baka fito ba sai da ka shirya *SULTAN SHAHEED ABDUL MALIK ALI BUZU* Takawarka lafia miji a wajen *ZINARIA, NADIA DA NAJEEBA,*

Idannuwansa da suka cenza launi ya daga a hankali ya sauke dubansa a kanta, gashin kanta da ta daure ribom din ya kunce gaba daya gashin ya sauko sosai yana walagigi
Hannayenta a fili, dama dama rigar bata yaye ba sannan da safa a kafafuwanta

Dan gyaran murya ya yi a sanyaye hakan ya sa amintacensa mikewa da sauri tsaye

Da idannuwansa ya kai dubansa kan Habu dake ta rawar jiki ya dan dantse gefen lebensa sannan ya kuma duban police din nan

Ba magana ya yi ba, aman irin kwatancen ya yi ya saka amintacensa fahimta
Nan da nan aka shiga salamar mutanen banda su biyun nan
Du kawunnansu a sasade suke ba wanda ya dago har aka fitar da mutanen nan baki daya sannan ya sauke dubansa kan bakuwar fuskar dake cikinsu

Bai ce komai ba sai takawa da ya ringa yi har ya karasa wajen da suke tsugune

Hannayensa ya saka ya dan rage tsayinsa
Hannunsa dake talabe da ita ya cire sannan ya dauketa da hannayensa
Muryarsa ciki ciki ya ce" ka kai Bilkissu aeroport yanzu

Daga haka ya juya da NAJEEBA a hannunsa ba tare da ya kuma bi ta kan kowa ba har ya bacewa ganninsu

Sai da Amintace ya basu damar dago kansu sannan du suka dadago a tsorace, dogaran nan ne suka kara korar kowa suka rurufe sannan suka dora gadi a wajen

Kuka Zahrau ke yi bilhaki, domin ko gidan fir an hanna mata komawa , DAYABU ya dubeta yana tuki zasu karasa aeroport murya da fada fada ya ce" Zahrau, ko ki min shiru ko kuwa na baki mamaki a nan, aman kin ban mamaki, kin bani mamaki Zahrau, kina tsaye kina kallo? Da darajarku da komai ku zubar da wannan rashin mutuncin? Zahrau kin san waye SHAHEED a kan NAJEEBA? Lalle ina mai adu'ar Allah ya sanyaya fushinsa, ina rokon Allah ya sasauta masa damuwarsa, Zahrau SHAHEED ne ya fito da kansa a irin wannan lokacin ya dauki NAJEEBA da hannayensa a gaban dogaransa, Zahrau kun bani kunya"

Wani kukan ta saka tana yarfe hannayenta ta ce" yaya dan Allah ka yi hakuri, ni kaina sai da na ga abin ya idasa rikicewa, yaya ban gane ban san SHAHEED a kan NAJEEBA ba?"

DAYABU ya girgiza kansa kawai ya yi mata shiru, har sai da suka karasa gidan jirgin sunna zaune dan bai saura minti ashirin su daga ba a hankali ya ce" Harda dan daudu, ga maza nan sunna son rungumota a jikinsu, shin sake na yi da tarbiyarku har haka ko menene?"
Sai kawai wasu hawaye masu zafi suka shiga bin gefen kumatunsa, hakan ya mugu mugun kara daga hankalin Zahrau dan haka ta ririke hannayensa tana ta girgiza masa kai hankali tashe muryarta a rikice take fadin" Dan Allah kar ka yi mana kuka, ka dakemu, ka yi mana komai dan Allah kar ka tuhumi irin tarbiyar da ka bamu domin kuwa mu mun san kai din ubanmu ne"

Kansa ya girgiza a hankali ya ce" Zahrau, Allah ya yi rayuwarmu wata iri, tabas na san ba wanda zai iya raba NAJEEBA da fada, aman ban yi tunanin a yanzu da take amsa kiran matar SHAHEED zata cike mayafinta ta nemi dakuwa da wata matar da bata kama darajarta ba, ZAHRAU kema dake dauke da taki darajar kika tsaya a matsayinki da kasancewarki yayarta kuke danbatuwa, to bara ki ji, wace aka turo din AMMI ta kama wayarta dazu kafin mu iso tana fadin ta tabata idan har aka tsokani NAJEEBA sai ta rama, idan kuwa ta zubar da hauka a cikin masarauta ga kishiyoyi ga mijinta mai zafi ana iya kilaceta a dakin horo, daga nan ko uban me take takama da shi an karya saura uwarta, Zahrau wato maradinku ba zai ji kunya ba? Me zai faru, me zai yi mata, Allah masani, aman kun cutar da zuciyata"

Kanta ta dora gefen hannunsa tana hawaye, ita kanta zuciyar tata ta mugun raunana, shin Najeeba wace irin zuciya ne da ita mai karfi fada haka? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une idanfa aka sakata dakin horon? Idan labari ya kaiwa zinaria fa?"
Motar shiru ta dauka a haka har lokacin tafia ya yi, nasiha ya kuma yi mata mai ratsa zuciya kafin su rabu tana ta hawaye, sai da ta shiga ta ga GIMBIYA hakimce a wajen VIP din, dama nan suke zama hakan ya bata mamaki matuka, ta gaisheta da mutuntawa aman ita sai ta cire kai kamar bata santa ba.

Zaune yake ya cire rawanin, kansa sade kasa ya dafe kan nasa da hannayensa biyu biyu yana kallon kasa

Da wani irin sauri AMMI ta nufi wajen NAJEEBA dake shinfide saman doguwar kujera, UMMU kuwa ta yi wajensa hankali tashe ta saka hannunta ta cire nasa tana kallon fuskarsa har sai da gabanta ya yanke ya fadi

Idannuwanta ta lumshe tana jin wani irin daci a zuciyarta, tabas AMMI ta fada mata komai dangane da wayar Mardiya, ita ta hanna a shaida masu dan tana son gannin yaya zasu tafiyar da abin, sai gashi cikin sauki sun tafka rashin hankalin da abu daya take jira shine gannin farkawarta ta nadi jikinta tamkar an aikota

A hankali ta ce da SULTAN" ka yi hakuri "

Idannuwansa ya lumshe, ya kuma budewa a kan UMMU, ya kama hannun nata na dama ya rike a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login