Showing 6001 words to 9000 words out of 228147 words
Chapter 3 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
tana matso kwalar da ta yi mata tawaye ta ki zuwa a irin wannan lokacin
Tana zuwa tsayawa ta yi tana kallonsu, idan ta kalli wannan sai kuma ta kalli wancen
Muryarta ta buda, kamar wace idan ta fito zaka ji wani tashin hankali da kururuwa, aa sai muryar ta fito da wani irin sanyi sannan tana kalkaltu irin na larabawa ta ce" Ya salam, yayarki kika mara?
NAJEEBA ta ringa matso kwallah aman ina kukan ya ki zuwa dan ta san tana yin kuka yanzu zata manta fadan ta dawo rarashinta domin ita kanta ta san uwar tasu na matukar son ta
A hankali lebenta na rawa ta ce" *ANMY* (wato mama), ta taba martabar iyayena ne
Gimbiya ta kalli Zulaihat dake tsaye dafe da kuncinta, a hankali ta ce" rama
Sarki dake jin dukan abinda ke faruwa ya kara dan muzkutawa yana sauraronsu
Kamar jira take ba wani kauce kauce itama ta daga hannunta ta dauke NAJEEBA da mari
Karar marin nan shi ya saka kanwar NAJEEBA mai bi mata wato Khairat zabura tana ruko idannuwanta da niyar tashi
Da sauri DAYABU ya saka hannunsa ya mayar da ita ya ringa yiwa kannen nasa gargadin kar wanda ya tashi, ya kara sada kansa kasa
Tun da ta mareta ido kawai ta rintse tana jin yanda jijiyar kanta ke harbawa
Da mamaki ta buda idannuwan nata ta sauke a kan hannun Zulaihat, gata dai farar mace, kana kallonta ka ga laushi sai dai hannunta wani irin tauri ne da shi kamar dutse wanda ba komai ya janyo haka ba sai mayukan bleating din da take shafawa fatarta dan karin haske a kan nata kamar yanda wasu buzayen ke yi ya hadasa mata taurin tafin hannu kamar mai kwaba suminti da hannun nata
Da sauri kuma ta maida dubanta wajen Gimbiya wace itama karan marin ya sakata saurin rintse ido da jin wani irin ciwo da daci a ranta, sannan mamakin rashin kunyar Zulaihat ya darsu a cikin zuciyarta, haka kawai take ayanna Zulaihat ba kara? Ba zaki yafe ba ko dan ni?
Juyawa ta yi bata kuma kallon fuskar NAJEEBA ba dan ta san zuciyarta zata karye ne
NAJEEBA kuwa kallon tsana ta bi Zulaihat da shi wace ke binta itama da kallon tsana harda na kyankyami kafin ta motsa labanta ta ce" kin mari *SHAHID* kuma sai na rama a kan *ALI*!
ido ta ruruko tana kallonta sai dai ba damar kuma tofawa da sauri ta juya ta fita tana jin zuciyarta kamar zata bale , ta yi rantsuwa ta maya ba'a yi yar talakawan da zata zagar mata miji da kuma yarima ba! Sai ta ga bayan wannan tsinaniyar bakar yarinyar mai bakar zuciya!
Kusa da yayanta ta je ta zauna wanda ke bin kuncinta da kallo zuciyarsa na karyewa, walahi baya son abinda zai taba masa kannensa, ko dan ya kasance baba a cikin gidansu, ko dan du yawancinsu iyayensu na fita sunna kannanu ne su bar masa yar jarirai ya raina? Du cikinsu ba wanda uwarsa ta rufa shekara hudu da shi, da wuri take tafiarta inda za'a bar masa shi kuwa ya raina domin mahaifinsu mai tafiye tafiye ne, sunna da masu raino aman baya iya motsawa yana tare da su hakan ya sa yake masu soyaya daya tak tamkar mahaifinsu, gani yake yama fi mahaifin nasu son su domin baya tunanin da shine wata mace ta isa ta shiga tsakaninsa da su ba!
Sai da ta saisaita nutsuwarta daga tsayen da take kafin ta karasa gabansu ta aniya neman zama a kasa saman kafet din
Da wani irin sauri SARKI wato mai martaba ya zabura daga zaune a saman kujerar falon ta alfarmar da yake ya tashi tsaye, da wani irin sauri ya karasa ya saka hannunsa ya tare ta
A tare suka tarota da sauran y'ayan
Sai a lokacin kukan ya zo mata ta fashe da kula tana rike da hannun Gimbiya ta ce" ANMY a kasa kuma?
Irin yanda zuciyarsa ke bugawa gannin majaifiyarsa zata zauna kasa bayan shi yana sama ya saka shi lumshe idannuwansa
DAYABU dake rike da ita shiga ta gabanta ya ce"ANMY ki rufa mana asiri kar ki zauna a kasa
Itama fuskar ta kwabe, wanda sai a nan na gano kwabewar fuskar nan ta NAJEEBA tata ce,
A hankali ta ja shashekar kuka ta ce" ku barni mana, ku barni na zauna kasa nima ya zo ya saka min layar, ku barni ya zo ya mana tsakanin nima kar a je na cuce ku a zamantakewar yau da kulun
Kanta take girgizawa da sauri ta shige jikin Gimbiyar ta rukukumeta ta cusa kanta a kirjinta tana ta juya kanta tana nufin aa, aa
Gimbiya ta kara riketa da kyau a jikinta, ga hannunta na dama dake cikin na SARKI ga kuma DAYABU da ya koma gefen hagu shima ya riketa da kyau, ga sauran yaran du sun zagayeta kowane ya kama kunnensa ya rike
Idannuwanta lumshe ta ce" so kuke ku kashe min shi shima ya kasance bani da kowa? Ai gwara ku hade mu ku kashe sa8 ku huta ya ku y'ayana
Du kansu suke jujuyawa cike da dana sani
Gimbiya ta ce" yaya zaku kawo karar mahaifinku a cikin bainar jama'a? Koma me kuke tsoro shin baku yarda da Allah zai kare ku bane ko kun fi yarda da tozarcin? Yaya ina tashin tsakiyar dare ina rokan Allah ya raba ku da bakin duniya irin yanda kuka sha jinnin rigima aman kunna kara janyowa kunna hada kanku da su? Kai kuwa da na yi hannin ku tozarta mu sai ka nunan ai adalci aka nema ka je ka yi gaban kanka ka zaunar da yayana a gabanka ka bashi laya?
Da sauri NAJEEBA ta kara riketa ta ce" Anmy, Layar fa ba a cike take ba, ya zare abubuwa a cikinta
Da sauri ya kai dubansa keyarta da dan kwalinta ya zame ya fadi sai gashin kanta dake waje wanda yake daure da dan ribom a sama sama ya zubo sosai
Mamaki ne ya kama shi na yanda aka yi ta gane Alkur.anin ba a cike yake ba, ko wani ne ya fada mata?
Kai ina da wuya a cikin mutanensa wani ya fitar da sirrin, hasalima liman baba ne ya cire abinda ya cire a ciki daga baya kuma ya mayar da shi yanda yake , wanda sun yi haka ne daga shi sai shi sai Allahn dake kallonsu
Idannuwansa ya lumshe yana jin mamansa na tambayarsa wai gaske ba cikaken bane?
A hankali, a karon fari kennan da ya budi bakinsa tun farko cikin wata irin murya mai dadin sauraro da nitsar da firgitace ya ce" Na'am
Wata ajiyar zuciya ta saki a hankali ta janyo shi ta hade shi da NAJEEBA dake jikinta ta gefenta ta kuma janyo DAYABU ta dayan gefen ta hade su ta rungume su tsam a jikinta wanda hakan ya sa kwabrin hannunsa na gogan wajen wuyan NAJEEBA
Ajiyar zuciya ta ringa saukewa na samun nutsuwa kafin ta sake su
Juyawa ta yi da NAJEEBA rike a hannunta du ta yiwa sauran nuni da wajen zama
Baki dayansu a kasa suka zauna, Banda Sarki da ya koma kujerarsa ya lume ciki ya lumshe idannuwansa
A hankali ta ce" yaya zaku biye mata koma me take maku ku fitar da sirrin cikin gidanku waje? Yaya kuke so hankalinmu ya kwonta a yanzu da tsufa ke riskarmu na zamu iya tafia kowani lokaci mu barku bari na har abada bayan kuna kokarin lalata kanku?
Ko da gaskiyarka a lokacin da aka saka maka shi sai jijiyoyin jikinka arba'in sun tsinke
Shine kai da girmanka ka tashi ka yi ja gabar kannenka da ka san cewa ko me za'a yi idan dai fada ya tashi sai sun yi ka zo ka tsugunna aka saka masu layar fada? Wato baki dayanku ku mace ko ku lalace shikennan ko?
Kansa ya kara sadawa ya ce" Allah ya huci zuciyarki
Hannunta ta buga gefen kujerar ta ce" ba wannan na tambayeka malan ka bani bayanin uban me take maku da ya karfina ni ka fada min na magance maku shi?
Rintse ido sarki ya yi a ramsa kuwa fadi yake" subahannalah, itama zata fitan kennan?
DAYABU ya kara sada kansa ya ce" Anmy, tana zargin ko mu ke hada mata fitinar da take yawan samun matsala da Abih, tana tunanin ko zamu hadewa yarta kai ne mu cuce ta, yajin nan da ta yi ta dawo ne da abubuwan nan wa'inda suka birkita mana lisafi
Yan uwanta sun zo har gida da laya za'a saka mana iya mu aman banda ita, mune kawai za'aiwa shingen nan kuma ABIH na kallo bai hanna ba saima fadi da ya yi cewa a core duka, a cire fada, a saka mana iya na magani kar mu yi mata magani domin ya yarda da tarbiyar y'ayansa, bama bin boka bare malan
Anmy to idan itafa ta mana?
Sasauta muryarsa ya yi ya dago yana kallonta da idannuwansa da suka cika da kwallah ya ce" idan ta lalata rayuwar kanena fa?
Idannuwanta ta rintse tana jin har wata zufar bacin rai na keto mata, a saka masu alkur'ani kuma yayanta ya yarda? Ta yayama za'ayi yo shi ya yarda bayan shima ya girma ga kuma soyayar kannensa da yake?
Gyaran muryar da SHAHEED ya yi ne ya saka kowa yin shiru harma suka kara sasada kansu, inda NAJEEBA ta lafe jikin Gimbiya ta dora kanta , a zuciyarta kuwa fadi take mai tsamin bakin ya samu da kyar zai yi maganar ko?
Sai da ya sha fama da mulkin dake cikin jinnin jikinsa kafin ya ce" samu gaskiya ne, haka kuma neman tsari ta hanyar adu'o'i da kiyaye sabon Allah da kadaice kai wa ibada gaskiya ne,
Sai da ya kusan minti biyar bayan wannan maganar yana sauke numfashi kafin ya dora da fadin" ba abinda ke samun nagartacen bawa face kadarar da Allah ya hukunta zai same shi, sannan na yi imanin zai zo masa da sauki a kan wanda bai rike adini ya yi imani ba
Dubansa ya maida wajen yaran baki daya ya ce" baku tafasa bama bale ku kone
Wani kakausan harara ya saukewa NAJEEBA wace ta yi gagawar lumshe idannuwanta daga kallon kyawawan idannuwansa dake bayane tun da ya fara maganar take binsa da kallo, a hankali ya ce" rashin jin magana kuma baya haifar da abin alkhairi
Dubansa ya kara maidawa wajen DAYABU ya ce" haba yaya, kai ka san menene girman hukucin alkur'ani kuma har ka yarda a saka a cikin gidanku?
Ajiyar zuciya ya sauke ta girgiza kansa ya ce" ba zan iya sakawa ba, ba dan na yi zabunta ba, sai dan Abu ne mai hatsari wanda bana garajen sakawa wanda bai malaki hankalin kansa ba
Numfashi ya yi ta saukewa yana hutawa doguwar maganar da ya yi sai ya kuma kallonsu ya ce" hukuncin bulala zata tabata ga du wanda ya fitar da maganar cewa ba cikake bane aka saka
Lale hukunci zai tabata ga duk wanda ya kara kokarin fitar da sirrin cikin gidanmu waje!
Du kawunansu suke gyadawa , sai da ya gamsu da hakan kafin ya maida dubansa wajen mahaifiyarsa ya sada kansa sosai ya ce" ALLAH ya huci zuciyar ANMY,
Su duka suka shiga maimaitawa a hankali sunna fadin" ALLAH ya huci zuciyar ANMY
Ajiyar zuciya ta sauke tana mai jin dadin yanda suke da biyaya a gare su du kuwa da irin yanda suka kasamce masu fada da taurin kai da taurin hali
Da daidaya suka ringa tafia, inda Dayabu ya fara tserewa da yan kannensa uku domin baya son a barshi daga shi sai kanninsa kuma warinsa sannan sarkin garinsa a wajen nan, dan ya tabata yanzu zai titsiye shi ya karasa sauke masa laifukan da ya aikata
Kanta ta kara shafawa ta ce" daga nan ina zaki je ne NAJEEBA?
NAJEEBA ta kara kwontar da kanta a jikinta a hankali cike da kasala ta ce" ANMY, zan je gida ne kawai
Murmushi ta yi ta dago habarta, hakan ya sa ta dago manyan idannuwanta masu dauke da kwali da kuma karin girar ido, dan bakinta kuwa dauke da jan baki kalar lebenta da dan man lebe daidai da ita yana sheki
Hannunta ta saka ta kara goge mata dan hawayen da ta zubar saman kyakyawar fuskarta da bata da digon hodo ko daya a jiki
Cike da kulawa da kauna ta ce" ki rike mutuncin kanki kin ji? Darajar mace mutuncinta yarinyata
Shi kuwa a kasan zuciyarsa ya furta " wani mutuncin kuma? Ko dama akoy matan dake da mutunci sama da daya ne?
Kanta ta daga a hankali tana jin kaunar maman nasu,
Gimbiya ta shafa wajen da ZULAIHAT ta mareta ta lumshe idannuwanta a hankali ta mana mata kiss a goshinta ta ce" Allah ya tashe mu lafia
Mikewa ta yi ta dauki jakarta, bata dauki dan kwalinta ba ta juya abinta da niyar tafiarta hakannan ba abinda ya shafeta
Gimbiya ta dan daga muryarta ta ce" mayafinki fa?
Juyowa ta yi ta dawo kusa da shi, domin mayafin nata ya take shi da kafarsa mai sanye da safa fara kar
Dukawa ta yi bata ce masa ya daga ba ta janye abinda harda dan kadewa ta yafa a kanta ta yi gaba tana juyinta yanda take so
Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai ya kalli Mahaifiyarsa a hankali ya ce" kin shagwabata, zata sha wuya kafin ta samu mai daukan haukanta, sannan marin matana fa da ta yi?
Murmushi Gimbiya ta yi ta ce" ku kai kararmu, sai mu fada cewa ai itama ta mare mu
Kansa ya girgiza yan murmushi kafin ya mike tsaye ya kara sada kansa ya ce" ALLAH YA HUTA GAJIYA GIMBIYA
Tana murmushi ta ce"
[31/03 à 21:33] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
4
Tana murmushi tana kallon yanda sarauta ta karbi yaron nata, yanda sarauta ke kara masa wani irin nutsuwa da kamala a hankali ta ce" Allah ya tsare gabanka, Allah ya tsare bayanka, ya tsare makwoncinka, ya tasheka da kansa
Allah ya yi maka albarka
Idannuwansa ya lumshe sakamakon jin dadin adu'ar da mahaidiyarsa ke yi masa har sai da ta dasa Aya sannan ya juyo ya kara dukar da kansa ya furta" amen Anmy
Cike da tafiar kasaita ya fito daga bangaren mahaifiyarsa
Bai zame ko'ina ba sai baban dakin karatun da suke raba dare sunna karatu da kuma ayukan sirri shi da mutanensa na sirri ciki kuwa harda yayan mahaifiyarsa da baban liman din fadar baki daya
Sai da ta tsaya a baban wajen saida abinci ta sayi pizza wajen gida goma inda ta bayar da jaka hamsin cif aka zuba mata a cikin motarta
Tana tayarwa ta karasa gidansu,
Mai gadi ne ya bude mata kofar ta idasa shiga da motarta
Yabi daya daga cikin masu aikinsu ta saka kwaso mata pizzar tana kai mata bangarensu da kannenta mata
Sai da ta gama kwashewa ta rufe motarta da dan kwalin nan a hannunta tana dan wasa da shi ta shige cikin falon nasu
Ja ta yi ta tsaya sakamakon gannin yayanta na bangarensu sannan kannen nata da kuma yayunta har sun yi wanka sun sasaka kayan baci
Wani dan malalacin murmushi ta saki tana idasa shiga ta ce" aa, me kuke a zaune?
Dubanta sukai gaba dayansu, gannin sai wayancewa take ya saka yayarta mai sunna Umakhulsum girgiza kanta ta ce" ai dole ki ce haka, dole ki ce haka Najeeba bayan ke kin iya tankwalo masifa tana baci!
Da sauri NAJEEBA ta ce" toh fa
Dayar mai sunna Zahrau wace itace mai sanyinsu ta ce" yanzu Najeeba kennan nima kina iya daga hannu ki wanke ni da mari? Kuma kin sani sarai da ba barinki zai yi haka ba koda kuwa Anmy ta yi dabarar sakawa ta rama sai ya maki wata muguwar muguntar marin masa matarsa ko?
Da Sauri DAYABU na dan dago hannayensa ya dunkule guda ya ce" fisabililahi idan ba jarababiyar y'a ba bilahilazi da ta wanka mata marin nan sai na shiga neman na tashi ni ba fifike ba, NAJEEBA a gaban sarki ki mari matarsa dan kina yar yayan mamansa?
Gaban goshinta ta dafe tana karasa shigowa
Sai da ta zauna tana kallonsu ta ce" meye hukuncina? Cin uwani zaku yi yanzun ko yaya?
Tasowa yayansu ya yi da sauri ransa bace ya nufota
Da sauri ta rufe fuskarta domin wajen da bata so a kuma taba mata a yau kennan ,
Sai da ya karaso ya daga hannunsa ya yi ya yi ya bambarw hannayen nata aman sai kara shigewa cikin jikinsa take, nan fa tumurtu ya tashi gannin zata wahalar da shi a banza ya saka shi sakinta yana maida numfashi ya zauna ya ce" shegiya mai ilimin kokowa, kin ci sa'a fuskarki a boye da yau na fitar da sahun hannuna a jikinta
Kanwar NAJEEBA dake dariya ne ta ce" wai ku ji fa, kamar wanda yaya zai mata wani duka mai karfi abinda nan zaka ringa zanen idan ka kamata ka fara kwalo da ita, tana zuwa gabanka sai ka bige da yi mata nasiha
Da sauri ya kaleta yana zaro ido ya ce" kin ga wannan mai sunnan Gimbiyar sam bata da kirki, idan ta tashi magana sai ta ringa yiwa mutun shari ba gashi ba na jijigata kuma ki bari ki ga ta kuma marin matar sarki zara ga abinda zan mata
Su dai du murmushi suke ita kuwa NAJEEBA ta hade fuska sai kara turo baki take wai sun hade mata kai sunna mata fada
Sai da suka gama yi mata kashedin ta kiyayi yiwa sarki hayen nan ta sada kanta ta ce" kennan sai na kyaleta ko? Kun san me tace ne? Cewa fa ta yi *ke kauce yar talakawa*
Ido Umulkhair ta zaro ba shiri ta ce" kan ubancen, shi yasa na so zuwa na ji a kan me zata maida maki mari yaya ya rikeni ashe iyayenmu ta zaga?
Yayansu ya yi shiru shima ransa na kunna
Zahra ta ce" kin min daidai dan ubanta ya kashe mu!
Su masu yi mata kashedin kar ta kuma sai gasu sunna fadin ai ko sunne sai sun rama, nan