Showing 78001 words to 81000 words out of 228147 words

Chapter 27 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10366

kuwa wannan uwa ta d'auko hanyar tarwatsa iyalanta da al'uma mai yawa, dan kuwa mu dukanmu muna samun tarbiya ne daga iyayenmu, daga bakin lokacin da aka samu gurb'attaciyar tarbiya lamarin b'atanci zai yawaita a cikin al'umah."

Sassauta muryarsa yayi yana kallon sarki ya furta" Rud'ani, tashin hankali ya hana min kallonsu a cikin idannuwa, sai dai ya zama dole zamu hau wata shari'ar a yau a wajen nan dan danne wata b'arakar, amar yanda na fad'a cewar a duniya baki d'aya babu mumunan sirrin da fitarsa ke haifar da mugayen sakamako irin sirin masu mulki da kuma manyan malamai da masu iko,
akan d'auki hakan da fuska biyu, masu d'aukarsa da mummunar fuska ta hanyar kwaikwaya sukan yi yawa a cikin duniya baki d'aya, k'alilan ne ke yi masa kyakyawan fahimta har su gane b'atancinsa."

Kuma kausasa muryarsa yayi ya furta" Ba'a kyauta ba, an tafka abinda Allah ya haramta, sannan an shiga hakin baiwar Allahn da bata ji ba bata gani ba." Shiru ya kuma yi kafin ya dubi wajensu.

Muryarsa ya sanyaya sosai kafin ya furta" UMMUKULSUM, shin zaki iya jurewa, ki jajirce, ki d'auki hak'uri ki yafewa bawan Allahn nan duba da irin abubuwan da suka gabata da shaidar wace abin ya faru a sanadiyarta ? Zaki iya yafe masa har cikin zuciyarki? Ki tuna Allah na yafewa bayinsa masu yafiya ya Ummu."

Kanta dake kife a jikin kafad'ar Najeeba tun daya kama k'afarta yana gunsheken kukan nan ta ji wani irin tausayinsa ya tsirga mata haka kawai sannan wani irin tsigar jikinta ta ringa tashi, bata k'arasa jin tausayinsa ba sai da ta ji kalaman mahaifinsa da kukan mahaifinsa da shi kansa.

Gimbiya ce ta k'ara duk'awa tana kallonta muryarta na rawa ta furta" Ki rufa masa asiri, ki rufawa kanki Ummukulsum, kar ki manta kema mace ce, fitar sirin nan tamkar fitar da sirrinki ne, ki rufe shi dan girman Allah."

Cire dubanta ta yi daga kanta, muryarta na rawa ta furta" Na yafe masa."

Sai kuma ta fashe da kukan da ya saka Najeeba wace jikinta ya d'ume da zafi kanta na sarawa ita ma fashewa da kukan tana k'ara rungumeta, Zahrau kuwa ta zama wata mutun mutumi sai juya kai take baki d'aya ta rasa me take ji.

Hamdallah yayi kafin ya maida dubansa wajen sarki a sanyaye sarki ya ringa sakin ajiyar zuciya, muryarsa a sanyaye ya furta" ina neman alfarma, ina neman alfarmar a bar min ita a nan gidan, ta yi istibra'i a d'aura masu aure, domin na rantse shi zai gyara abinda ya lalata."

Daga Gimbiya har matarsa a tsorace suka kalli sarkin da ya watsar da su yana cike da jin haushinsu, sam tamkar basa wajen tun da ya masu tambaya yayi watsi dasu.

Da baya ta kai zaune tana mai d'ora hannayenta saman kanta a b'oye, kishiyarta kuwa bayan tarin tausayin yarima domin yaron yana da mutunci sosai, sai kuma tarin al'ajabin abinda ke shirin faruwa, auren yarima da matarsa aure aka yi na zobe, yar k'awar gimbiya ta k'ud da k'ud wace ak'idarsu d'aya cewar ba za'a yi masu kishiya bace ya aura, hakan yasa Gimbiyar ke taya ta yak'in maganar kishiya sai gashi a yau abu biyu ya faru da su baki d'aya, wato wanzuwar *KISHIYA* a tsarin da basu ajiyeta ba.

Kansa ya kuma sadawa yarima ya k'ara duk'awa shima yana rok'an hakan.

Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya furta" zamu juya gida a jirgin safe in sha Allahu, zan yi kira na sanar da abinda ake ciki."

A haka dole aka tashi, sarki na zaune saida kowa ya tashi sannan ya bi bayan Zahrau dake son shiga d'akin jikinta a mace.

Hannunta ya kamo ya maidota baya
A hankali ya sakata cikin jikinsa ya rungumeta yana buga bayanta kad'an kad'an kafin ya jata suka koma saman kujerar
Sai a lokacin ta samu kuka ya kubce mata cike da tsoro take nuna masa ba zata iya zama ba yan uwanta a wannan gidan da ya gama tsoratata ba.

Sosai yayi anfani da hikima ya ringa rarashinta har ta dawo nutsuwarta ta ringa sauke ajiyar zuciya da kansa ya mata alk'awarin zai nemi alfarmar malan ya bashi y'aya biyu k'annenta su tare da ita su tayata zama kafin a kawo mata Ummu.

Da wannan ya samu ta kwontar da hankalinta kafin ya rakata har d'akin suka ci gaba da gabatar da sallah baki d'ayansu suna godewa Allah da irin wannan ranar.

....................................

Zabura ya yi tsaye sai kuma ya yanke jiki ya fad'i zaune saman kafet d'in hannayensa aje saman kansa muryarsa na rawa ya furta" innalilahi wa'inna ilaihi raj.une, hasbunnalahu wani'imal wakim
aya ta tabbata a kaina ni MUTALAB gashi, abinda na aikata ya kamo ni da wuri haka a kan yarinyata."

Sai ya fashe da kuka yana kallon yanda D'AYABU ya tsurawa sarki ido kamar wanda ya suma a zaune.

Da sauri Anmy dake kukan itama ta kaleshi a firgice jin zai tona asirin da suke lullub'ewa kansu da k'afarsu, zai tonawa kansa asiri a cikin irin rud'anin nan da suke ciki zai k'ara masu wani.

Duban da Ummu ke masa ne ya saka shi k'ara sada kansa yana hawaye
Ummulkhair ta kalli Najeeba wace ita ma ita take kallo kafin Najeeba ta bud'a bakinta a hankalì tana kallon Ummulkhair tana dan yatsine fuskarta tace" eyah, eyah, yau kin yarda da ayar tambayar da na d'ora a kan maganar da Abih kan fad'a wani sa'in?"

Maida dubanta tayi wajen Abih a sanyaye ta furta" *ABIH, WACE AYA CE TA TABBATA A KANKA?*

komawa sarki yayi ya jinginar da bayansa jikin kujera yana lumshe idannuwansa, ta faru kuma ta k'are, rikicin cikin gidansu zai k'ara kunnuwa a yanzu, ya tabbata wani tashin hankalin ne zai k'ara kunno kansa hakan ya saka ya idasa had'e fuskarsa da dukan wani abu wai shi annuri ya lumshe idanuwansa a lokacin da Anmy a firgice ta kallesu tace "...






Happy juma'at
[31/03 Γ  21:39] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



28



Bata motsa daga yanda take ba tana dai kitson tana kallon yanda yake iya yinsa dan gannin sun barshi ya shigo wajen

Kasancewar saloon dinta, sun kwana da sannin maza kan shiga ya saka ba wace ta wani damu dan sun hangi namiji na son shigowa domin akoy mazan dake zuwa takanas a yi masu manyan kitson nan na irin samarin nan na zamani
Wasun kuwa sukan rako yan matansu ne wasu kuwa su kawo matayensu

Nadia ta mike tana daukan dan kwalinta ta ce" a gaskiya wannan sabon tsari na tare mutun a waje ba zai haifa mana d'a da ido ba, ni banma san a kan wani dalili zaki yarda da irin lamarin nan ke da bakya so

Ita dai bata ce komai ba sai dan sauran gashin da ya yi saura take son idasa kitsewa

Fita ta yi ta shiga kokarin gannin an barshi ya shigo, sai dai dogarin nan na buda baki ya ce da ita" MAI MARTABA YA FADA MANA CEWAR BA WAJEN SHIGAR MAZA BANE DAN HAKA BA ZAI SHIGA NAN BA

Da mamaki ta koma ba tare da ta yi gardama ba jin ashe mai martaba ne ya saka dokar hakan a kan kannensa?

Najeeba bata ce da ita komai ba bayan ta shaida mata, sai da ta gama kitson nan sannan matar na murnar an gama mata ta cire jika ashirin ta mikawa Najeebar tana ta godiya kudin kunshi ne da kitso da gyaran faratuna da gashin ido tamkar wace aka yiwa kyauta

Itama Najeebar cike da fara'a sukai salama matar ta tafi

Gurin da take wanke hannaye ta je ta wanke hannayenta tas tas tana murmushin jin darun wata budurwa dake fadin ita gaskiya ita zata yi mata gyaran gashinta idan ya bushe yarenta kuwa sunna fadin ba kananun aiki take yi ba, zasu iya yi mata ko wani kala take so domin ta koya masu kuma sun kware sosai
Sai dai ta kiya ta ce ko nawa ne zata biya ita dai NAjeebar take so ta yi mata

Hijab dinta mai ruwan ash color ta saka mai hannaye sannan ta kara fesa turare ta juya ta fita daga shagon kafarta sanye da takalmi mai ruwan hijab din aman kafa ciki ne mai dan tsini a kasansa

Tana fitowa suka shiga bun bayanta hakan ya sa da mamaki ta dakata ta juyo tana kallon su
Du kawunansu a kasa a lokacin da ta juyo sannan sunna fadin" Allah ya ja da ranki, Allah ya huci zuciyarki

Bata iya basu amsa ba sai karasawa da ta inda ya kafeta da ido kamar ya dauketa da idannuwansa yana kallonta fuskarsa dauke da wani irin murmushi mai girman gaske

Tana isawa ta dan harde hannayenta tana kallonsa
A sanyaye ta ce" menene?

Murmushi ya yi yana shafa kansa daga gaba zuwa baya, a hankali shima ya furta" kauna ce, dan Allah ki bani dama

Motar da ya zo da ita ta kalla, motar nan zata yi kudin hudun tata gata baka sidik mai shegen kyan tsiya

Bakinta ta dan tabe kafin ta ce da shi" mu je

Tare suka juyi suka nufi cikin saloon din

Da sauri baban dogarin ya ce" Allah ya taimake ki, an hanna maza shiga ciki

Dakatawa ta yi ta juyo tana jin uwa ta ce da shi da ubanwa suka yi tarayar siyan wajen da har zai ringa shiga sabgar da ba tasa ba? Sai dai kasancewar kwakwaran gargadin da ta samu daga wajen Anmy a lokacin da ta nuna ba wanda zai bita ya saka ta cire dubanta daga kansa ta furta" harda mijin da zan aura?

Da sauri ya girgiza kai yana bashi hanya, shi kuwa wani mahaukacin dadi ya saka shi saurin cin mata suka jera suka shige saloon din tare

Sunna shiga sanyin Ac din dake busa saloon din ya dake shi, kanshin turaran wuta fa kuma tarin turarukansu na siyarwa dake cikin wani katon waje mai dauke da madubai ya hade ya saka shagon zama cikin wani kamshi unik da sansanyan sanyi

Juyowa ta yi tana kallonsa a hankali ta ce" ina fatan baka dauki maganar da na fada da mahinmanci ba domin dan ka samu shigowa na fadeta

Matsota ya yi yana kallonta kafin ya furta" zan tabatar da ita ne, domin ba wanda ya cencenci amsa kiran sunnan mijin princss sai ni

Irin yanda ya yi maganar ya sakata dan juya idannuwanta sannan ta idasa shiga tana mai cire hijab dinta dan itafa idan tana ciki tana aiki gaskiya bata saka komai a kanta

Waje ya samu ya zauna kusa da Nadia saman kayataciyar kujerar zaman mutun hudu kafin ya shiga binta da kallo

Budurwar nan ce ta hau saman kujera Nan NAJEEBA ta karasa ta shiga ciro atash din da za'a saka mata a boye cikin gashin kanta ya zama tamkar gashinta
Sak sak irin gashinta ta ciro maroon mai duhu sosai, sannan yannayin santsintama ya zama irin na gashin matar
Col (gam, wannan abin dai mai danne atach din )
Ta fitar sabo ta ajiye

Sai da ta kara busar da gashin sosai sannan ta shiga fitar da wadatacen da zai boye atach din baki daya zagayen kan budurwar

Cikin nutsuwa ta warware atach din nan ta wari daidai misali ta tsaga wanda zata hadewa ta hade sauran ta soke da yar wukar kitson sannan ta shiga shafa col din nan a jikin atach din
Sai da ta shafa ta dan hura da bakinta ya dan sha iska sannan ta daidaita ta dora shi gaba kadan da tsagar sannan daidai tsiron gashin kafin ta hade da gashin cen kasa ya kasance ya zauna das da shi ta kuma tsaga wani
Nan da nan ta idasa sakawa shi kuwa ya wani irin kura mata ido tamkar zai cinyeta yar uwarsa tun tana masa magana har ta yi shiru ta rafka tagumi ta zubawa sarautar Allah ido

Wanda ta ware din nan ta kunce ta hade su , mai ta lakato ta shafa sama sama dan col din baya son mai sannan ta saka abin cajewa ta ringa caje gashin har ya hade da atack din ya hade sosai da sosai kafin ta dago daga bayan matar hakan ya kasance ta baiwa su Nadia baya kennan

Da sauri ya koma saman kujerar yana daga hannayensa ya dora saman kansa ya kara zubawa kugunta ido kafin ya cire dubansa da sauri a fili ya furta" takwarankwatsa sonta nake kuma sai na aureta

Du yawancin yan matan wajen shi suke kallo, babar yarinyar Najeeba ta kawar da dubanta daga kansa ko jus din da aka ajiye masa bai taba ba, Najeeba kuwa tana jinsa ta yi kamar bata san me yake fada ba sai da ta tsaga gaban kadan ta saka wata yar na'ura mai saka gashi ya bi umarni ta ringa bi a hankali tana kara kwontar da shi ya yi lumbuk a gefe guda ya kwontar da hankalinsa waje daya sannan tsagar ta fito sosai
Dan gel ta bude ta ringa lakata da broch cike da kwarewa ta ringa dan kwonto da kananun da suke gaban goshin hakan ya sa nan da nan budurwar ta kara wani shegen kyau tamkar gashinta ya yi mugun hadewa da gashin nata domin kalar daya ne sannan yannayin santsinsama daya ne

Dan ribom sabo ta siya a nan aka daure mata shi a tsakiya sai murna take kamar me kafin a saka mata gashin ido a gyara mata girarta
Itama ta ci kusan jaka goma sha talwas da rabi sannan ta roki idan zata samu mak'up gobe domin auren yar uwarta ne ake

Sai da Najeeba ta duba time din da take so ta amshi numberta tana mai sheda mata zata duba ta gani zuwa safe zata bata amsa idan har zata samu i.a

Kudin da ta bata ya mike ya dauko ya zauna yana kallo, budurwar ya bi da kallo har ta fita kafin ua maido dubansa wajen NAJEEBA da ta dawo ta zauna tana dan matsa yatsutsanta

Nadia ya kalla ya ce" Nadia, yanzu duka wannan tsayuwar da matata ta yi tana faman aikin nan sun tashi a wadinnan yan kudaden? Duba fa ki ga yanda ta kayar da wancen budurwar kamar gashin kanta ji yanda ta zama wata mai kyan gaske wannan tana fita ta fara wankar maza aman kuma sai kudin aikin matata ya zama ko jika ashirin bai rufe ba?

Sansanyan ruwan da daya daga cikin masu gyaran wajen ta bude ta zuba a tsaftatacen kofin gilas ta miko mata ta amsa ta sha ba mai yawa ba ta mika mata ta dora kafarta daya kan daya kafin ta kai dubansa wajensu Nadia sai kwatanta masa take cewar ai haka aikin yake kuma ina laifi kana samun haka ko a wuni ne baki daya bale kafin a tashi za'a samu kudade na mamaki domin saloon dinta ya zama saloon din da sai manyan mata ko yan mata masu ajin gaske ke zuwa domin akoy kashe kudi sosai sai dai aikinta daban ne ko a waje

Dubansa ya maido kanta ya ga su take kallo
Kudin ya ajiye yana dubanta ya ce" me yasa ba za'a bani dama ba? Bana tunanin zan iya bari ki ci gaba da zuwa wajen nan, zan sama maki aikin ofice ki kasance a kilace Najeeba, idan wata ya mutu ki dafe manya manya dan na san takardunki, Nadia ta fada min irin takardun da kike dasu

Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" waye ya ce maka aikin office ke birge ni? Ka ga aikin nan, shi na tashi da shi a cikin abubuwan da nake son yi a rayuwana shi yasa ka ga na ware nan
Da kake maganar aikin office, kidaya min zan iya samun nawa a wata?

Huzaifa da gagawa ya ce" zaki iya samun jaka dari hudu, ke har akoy na dari biyar din da zan iya zuwa na samu abokin mahaifina ya sama maki gurbi a wajensu domin idan ya ji matata ce zai samo mana da guduma

Murmushi ta masa ta ce" a ranakun da ban yi kwaliya ba, nakan tashi da jaka dari da arba'in, ko dari da hamsin, idan ba'a samu isasun mutane ba nakan tashi da jaka saba'in ko tamanin

Idan na samu yan kwaliya, amare nakan yi masu kwaliya a jaka hamsin, kawayen amarya kiwa jaka ashirin masu zuwa wajen biki jaka goma
Akoy ranakun da nake tashi daga shago da zunzurufun kudade kusan jaka dari hudu ko sama domin idan aka ce maka juma'a ce, asabar da lahadi wajen nan cika yake da mata da yan mata, amaren ne da uwayen gida,

Wayarta ta janyo iPhone tana kallonsa ta ce" irga min, ka dauka a jaka dari dari kulun zan iya tashi da nawa a wata?

Nadia ta ce" million uku

Najeeba ta yi murmushi ta ce" ba ruwa nake biya ba, ba ni ke biyan wuta ba sai idan na yi ra'ayi, Abih ke biyan duka
Idan kayana sukai kasa Anmy ke min oder ta cika min shago

Idannuwanta ta kara kura masa ta ce" shine zan je office na yi me karkashin ikon wani?
Murmushi ya ringa yi , a ransa kuwa ya yarda cewar ashe dai kasamcewarta babar yarinyar ba iya iya kwaliya da kyaun tsari ta tsaya ba, aljihunta nauyi ne da shi, rikakiyar boyayiyar mai kudi ce , to aman yaya aka yi ta zama lashe money? Shi fa ko gara ce ita wace take iya karar da dukiyarsa ya ji ya gani yana sonta

Rage muryarsa ya yi ya ce" ina son ki NAJEEBA

Sai da ta ji wani dan ras, tabas zuwansa kai tsaye da kalamansa na sakata kallonsa da duba na daban

Cire dubanta ta yi daga fuskarsa hakan ya saka ya kara matsota sosai yana kallonta ya ce" ina son na aureki Najeeba, dan Allah ki yarje min mana?

Kuma duban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login