Showing 147001 words to 150000 words out of 228147 words

Chapter 50 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10384

zuwa inda kuke da cikinta a jikinta ta yi ta kulawa da ku, har sai na kasa jurewa dan kaina na dawo na lalabata domin du abuna nakan kasa nutsuwa idan muka yi fadan da ta min fushi har ta kaurace min, zaku ga na dawo ina lalabata mu shirya"

Dan murmushi ya yi ya ce" har zuwa lokacinda yar uwarta wace ta kasance yar mahaifinta ce ta bayanna,
Wannan itace rayuwar da na yi mafi muni a cikin rayuwar da giyar kudi ta kaini ta baro ni"

Kallonsu ya yi da kyau ya ce" a lokacin bata fi wata hudu da cikin Najeeba a jikinta ba, murna farin ciki haka take bugawa mutane tana fada masu ashe tana da yar uwa? Kuma itama yar uwar nata da danginta bangaren mahaifiyarta, wato dai ta samu dangi

Sosai ake shige da fice ana tayata murna, harta da dangin na yar uwar tata sun zo sun taya murna, inda yar uwar tata ta tare a gidanmu suke zaune kalau

A hankali yau da gobe, kadara da haduwa da wata irina wace ta sako duniya a gaba muka shiga fandarew, munna watsewa, munna aikata alfasha a boye a cikin gidanta na aure cikin du dakin da hakan ta kama"

Subahannalah, Ummu ta fada da karfi ta ce" wai wa ya tambayeka?"

Hararanta ya yi ya ce" ko dai bakin ciki kike na huta da nauyin dake kaina ne?"

Ci gaba ya yi da fadin" tun bata sani ba, har Allah ya sanar da ita,
Ta ci kuka, ta yi dana sanni harma ta so bara min gidan sai dai a lokacin da DAYABU ya riki kafarta yana ihun UMMU UMMU, sai kawai ta fashe da kuka ta rungume shi ta bara mana wajen wato gamu ga duniyar"

Kunya ta hanna min zama sai na bara masu gidan na tsayin sati, ashe aikin gama ya gama har ta dauki ciki na tsayin wata uku, UMMU kuwa na dauke da nata wata bakwai

Dole na waiwayo iyalaina, dole na waiwayo matata da y'ayana,
Sai dai kash bayanuwar cikin ya kara hadasa mata tashin hankali

Na takaice maku, ni da kaina sannu a hankali na ringa haifar da dalilan da suka ringa kara nisanta ni da matata ta rufin asiri wace du abubuwan nan da nake mata ko kanwata daya kwal wace ta ragen a duniya kuma aminiyarta bata sanarwa ba, sai dai ta rufe daki ta ci kuka ta fito a yi abinda za'a yi

Akoy ranar da ta tasheni tsakiyar dare ta ce da ni" MUTALAB, na aureka ne domin Allah, ina zaune da kai dan Allah ya saka min kaunar y'ayanka, Mutalab a da ina tunanin ina iya hadiye komai dan yarenka, aman a yanzu na gane harta NAJEEBA dake da shekara uku ina iya bara maka na tafiata idan har baka bar rayuwar nan da kake ba, idan har baka takawa zuwan uwar yarinyar nan da take takenta birki ba zan wanke kafa na je na daki mamanta na daketa na yi kason haka, MUTALAB idan ka kai zuciyata makura zan halaka ka na halaka kaina, dan walahi walahi irin yanda nake maka magiyar ka aureta idan sonta kake ka nuna min yaya zaka kuma iya auro bara gurbi a cikin gidanka to fa ka kiyayi du wata mu'amala da ita, idan ba haka ba MUTALAB zan halakamu baki daya mu shiga uku, na roke ka ka sawake min na yi tafiata"

Sai kawai na fi ta hawa dokin zuciya, na rufe na ringa shiga ina fita ina fadin" Mariama, kin jima baki halakani ba, ki gwada idan kina yiwa Allah ki gani! Ni zaki nunawa zuciya? Kin san ni gaba da baya ko waye, kuma idan takamarki kina da kudi kin san na dame ki na shanye, ki zubar min da y'ayan mana, sai na auro wata ta zo ta kularmin ai kin san ba ke na fara aure ba, kai ni banma yarda da rashin aurena har yanzu ba, na tabata kin asirceni ne malama"

To fa ranta ya bace, muka ringa sakawa muna fidawa wannan karron har gaban sarki da kuma BILKISSU,
Ko a nan kin fadin dalilin fadanmu ta yi, Sarki na mata nasiha sai da aka tambayi musababi ba kunya na fadi dalilin kai tsaye wanda ban taba jin kunyar abinda nake aikatawar ba sai da ya ringa yi min nasiha yana tino min rayuwa da mutuwa, a lokacin na furta walahi walahi walahi sau daya tak ne, yarinyar ce ta cika neman fitina har take nuna kamar wani dinkewa muka yi da ita,

Sai da aka shirya mu da *SIRRINA* kafin muka dawo gida

Shekara kamar uku tsakani kamar komai ya wuce, ba wai yan mata na daina yi ba, ba kuma take taken masu kudin zamani na daina ba kaina sama da isata da komai gefena ga hajiata tana kawar da kai ga jiginiyar y'ayana da suke dauke da wata irin tarbiya ta shakuwa da junna da soyayar junnansu bale DAYABU da ya kasance ya iya tafiar da tarbiyarsu daidai gwargwadon iyawarsa,
Wata ranar asabar, wace ta kasance ranar da ta kai bango, ina katon shagona na buga madara suka kawo mata ziyara da yar da aka haifa min da siyaya rigijib dan neman fitina

A lokacin tana da saurin rama mari, dan haka a gabansu ta masu dan karamin hauka, ta nuna masu halaya na mata, suka ringa raba haki har hayaniyar ta kawo inda nake

Kafin na mike sai da wani abokina elhaji Saley ya ce" lale kura ta yi lafia, yo ni mace ta isa ta ringa yi min abinda matar ELHAJ MUTALAB ke yi masa ban lakada mata duka ba na nuna mata ita ke kasa da ni na koya mata hankali ko dan gaba ba?

Da wannan hudubar ta shaci fadi da bacin na isa gidana rai bace jinnina a sama ga oga ya zo ga ogan da zai zartar da hukunci wato mai gida tamkar kububuwa na fada gidan

Ina zuwa ido rufe na tsayar da su,
Rai bace na dubeta, a matsayinta na wace na kilace matata mai daraja, a gaban mutanen da suka ci amanarta, ni kaina wanda na ci amanarta dan rashin kunya irin tawa na murje ido irin ga boss din nan na kai na kawo sunna bina da kallo kowace na jiran ta ji kalaman bakina sai kawai na dubeta ido rufe na daga hannuna na kai mata marin biyar zazafan da ya sakata dafe kumcinta cike da mamaki, da firgicin rashin adalcina na kuma daga yar yatsana na nunata na ce" banza jahila! Da ke kadai zan rayu hala da kike nuna halin mahaukata ne? Ke har kin isa ki tare min budurwara ki daka har ki cira mata riga? To wannan da kike ganni ki saka a ranki sai kun yi zaman kishi da ita domin sai na aureta na kawota gidana kun zauna kin dafa mata ta ci kuma ta je shinfidata a karo na biyu! Yau na ga matar balaki dan kawai na aureki ban isa na dubi wata ba? Ba'a auren ke na aureki ko ni zaki nunawa hauka a nan? Ke ki je inda zaki je na sake ki saki daya domin ni ba sakarai bane da zaki ringa zuba min shirme kin bi kin tatare min gaba da baya na kasa aure to yau dai asirin bokan naki ya karye sai a kara gaba malama!"

Hawayen da bata yi idan muna fada ne ya bale mata,
Tana dafe da kuncinta ta matso kusa da ni sosai,
A hankali ta ce" *sakayar soyayar kennan MUTALAB?, ka yanke min zama da y'ayana? Ka sake ni a karshe dai a kan son zuciyarka bayan ka san iyayena sun rasu ina kake so na je na yi zawarci? Ba asirceka na yi ba, kai ka hanna kanka aure, sai dai kash Mutalab, kash, walahi da ka san koda zaka maido ni ni ba zan dawo ba domin na haramta hauranka, Mutalab na rantse da Allah na kare da y'ayanka da du wani abu da ya fito daga hannunka! Kishi da wannan? Ta nuna matar, kafin ta tsartar da yawu ta kunce goyon Najeeba ta saketa daga tsaye hakan ya saka Najeeba zabura ta wawureta tana kukan MAMA, sai dai ina kuma hankadeta ta yi ban aune ba ta bala min mari ta kuwa ci damara da dan kwalinta ta ja baya ta ce" idan ka isa bismillah, walahi ko a da ban mari fuskarka ba dan kana dauke da igiyar aurena a yanzu da kai da bola du daya, Mutalab bismillah, da kai da dadiron taka sai nai maku jina jina a gidan nan*

Mamaki ya hanna min motsi, ita kuwa karambani ya sakata tunkararta, lalle kuwa sai da ta mata jina jinan ina tsaye tamkar gaula domin marin nan da ta min ya aniya maido min maganar sakin da na mata

Da gudu ta shige dakinta , dan kwali da dukan takardunta da jaka daya tak ta dauka ta fito
DAYABU na kuka yana riketa haka yan uwansa sai kawai ta kubce ta fice da gudu ta fita

Idannuwansa ya bude wa'inda sukai masa jajajir, ya ce" kun ji abinda ya faru tsakanina da NANA MARIAMA, tabas wani sa'in Allah kan baiwa mutun mace ta mutunci sai dai irin rikon da zai mata ke hadasa cenzawar lamarinta

UMMU dake dafe da kanta dake sara mata ta kalle shi ta kuma kalli yarwn sai kuka suke

Dubanta ya yi wannan karron maganar tata ce, sai da ya sanyaya muryarsa ya ce" bayanta na auri mata, daya bayan daya ina kara saki domin ido rufe uwar y'ayana nake nema wace zata kuma daukan dawainiyar gidana da y'ayana tamkar ita ta haifa

Tun ina saki da karfina har na dawo ina saki da hawayena

A hankali na ringa dana sani, har na je na zauna gaban kanwata na zayane mata gabli da ba'adin zamantakewar da na yi da matata,
Sai dai kash, a lokacin ta so ta maido min da farin cikina sai Nana mariama ta gindaya rantsuwar cewa" ai kuma ita da mutalab sai a lahira

Kuma sada kansa ya yi ya ce" walahi na sha wahala, ina cikin shan wahala
Ina ta kame kame ido rufe
Yarana na ta gararamba zuciyata na ciwo
Du irin tarbiyar da suke samu ba ta mace tsayayiya gashi na kasa bada su wajen kanwata kwata kwata domin idan na shigo gidana burina na ga layin motocinsu, na tsinkayi kwaramniyarsu na zauna mu yi hira mu yi goyo goyo da kannanuwan, manyan na daukanmu a hoto
Sai nake kwatanta irin macen da nake so, sai na fadawa Allah
Sai da na dangana da auren wace nake zaune da ita a yanzu, sai malan liman na baba ya ce da ni" *kar ka saketa, koma meye halayanta, ka jure, idan ka kuma sakinta wace iri zaka kuma daukowa y'ayanka? Kar ka manta y'aya mata masu barin gaban iyayensu da wuri ne, kai kuwa goma sha biyar gareka mata masu rai da lafia a ciki baka aurar da ko daya ba, shin wai baka tsoron sake saken nan a sako maka naka? Bana so ka ji ciwon sakin y'aya a zuciyarka, domin ba uban dake so ya budi idannuwansa ya ga yarinyarsa a gabansa na zawarci*"

A hankali ya kuma maimaita" *NA SHA FAMA, INA CIKE DA TSORON RANTSUWAR MARYAMA*

Da sauri UMMU ta kuma kallonsa, zuciyarta na kara dokawa,

Mikewa ta yi tsaye tana jin zata fashe da kuka
Kafarta ta daga zata gudu ABIH ya kuma furta" *Marayu ne mu, daga ni har y'ayana, walahi ba zan kuma rayuwar dadiro ba ba zan yarda na hada SIRRINA da dadiro ba*

Da gudu ta tafi wannan karron tana mai barin kukanta fitowa

Abih ya mike tsaye da sauri , sai dai riko hannunsa da ya ji an yi ya saka shi juyowa

A hankali NAJEEBA ta furta" *ABIH*"

idannuwansa ya lumshe wasu hawayen suka ci gaba da zuba a idannuwansa

Da sauri ya koma ya zauna kansa kasa
Dagowa ya yi ya ga irin kukan da suke
A sanyaye ya ce" da na san rayuwa haka take da daci, da na roki takaituwarta a kaina daga bakin lokacin da na rasa matar kwarai, Mariam ta kasance mai hakuri, da juriya da kawar da kai, ni sai na bazantar na ringa tunkudata har na kaita wajen da ta fashe ta kasa da ni, ni da kaina na yiwa kaina mugunta waye ba zan yiwa ba? DAYABU, UMMULKHAIR, UMMUKULSUM, ZAHRAU, NAJEEBA, *SHIN ZATA DAWO GARENI?*

Tabas tsakanin da da iyaye sai Allah, tausayin iyayen nasu ya saka su hawaye sosai da sosai kafin su aniyar kwontar masa da hankali
NAJEEBA jikinta a mace yake tana kallon Abinta
Gaskiya Abih ya aikata ayyuka kala daban daban sai hamdallah

Bata iya cewa komai ba har suka wawatse aka barta da zahrau

Zahrau ta ringa kwontar mata da hankali tana kara nuna mata cewar UMMU bata da laifi

Cike da hawaye ta ce" Auntu Zahrau, ashe shima ya tsani bak'ar mace aka aura masa ni?"

Da mamaki ta ce" wata irin magana ce haka, SULTAN din ne ya tsani bak'ar mace? Me aka yi? Me ya sa ya fadi haka? Wani abu kika ce masa?"

Sai da ta kara shahsekar kukanta sosai sannan ta ce" *Da karfi ya kwace min abinda nake tanadarwa waninsa Bayan wannan, ya ringa min hararan nan na tsana Na zata ya tafi ni kuwa kaina a sade nake fadin ai ba son farin mutun nake ba, mugu azalumi mai cin kudin talakawa*

Sai da ta zaro ido kafin ta zauna da sauro tana kallonta ta ce" ya ji? Kina nufin ya ji?"

Najeeba ta gyada kanta tana kallonta itama ta ce" ya ji, shine abinda ya saka shi fada min shima ai ba son bak'ar fata yake ba"

Cike da madaukakin mamaki, da ayar tambaya Zahrau ta furta" lalle akoy wani lamari a tare da shi wanda yake da girman gaske
Ke yanzu, kece kika fadi haka a gabansa sannan gaki a zaune daram da ranki? Lalle na tabatar da du wayonki wani sa'in baki da wayo, ko kuwa rashin hankali ne? ALLAH masani"

Zama ta yi gabanta tana kallonta ta ce" na zata zaki iya tafia ke daya ba tare da shawarana ba? Sai dai na kula a kan matsalar wani kika iya samo mafita a kan karan kanki kina zama wawa Najeebana"

Kuma kallonta ta yi gannin itama ita din kawai take kallo ta ce" abinda ya saka ya kasa tataka ki ko ya karya maki kafa sakamakon maganar da kika fada a gabansa ya shanye shi zamu dauka mu yi anfani da shi ta hanyar buga wasan nan"

Kumatun NAJEEBA ta dan riko ta ce" baya son bak'a? Zamu gani idan har furucinsa shine gaskiyarsa, idan har idanniyarsa ba zata karyata sakonsa ba, idan har gangar jikinsa ba zata rikita lisafinsa ba!"

Mikewa ta yi ta kama Najeeba ta ce" zo mu je ki kuma shiga ruwan da AMMI ta hada, domin babu ne kawai bata tanadarwa wannan ranar ba

Abih na fitowa ya karasa Fallon, nan ya kuma tarar da Mardiya zaune ta kumbura kamar zata fashe sai karkada kaffafuwanta take cike da balaki

Yana son ficewa ta mike da yannayi na raini ta ce" ji mana? Meye ka shiga dakin cen ka zauna tun dazu ana cin amanata ne ko meye? Hala ji kake ban san wacece wancen matar da ta wani ja su ciki ba? Malan na gaji da irin abubuwan nan gaskiya amanata za'a ci ido na gani?"







Good morning all
[31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



47

Alhamdulilah na dawo😁


Cike da kulawa, da yannayin da kwata kwata baya nuna mamakinsa a irin halayarta a yanzun, domin ta shayar da shi lamarin da lamarinsa ya fasa bashi mamaki ya dubeta duba na tsanaki ya ce" da gaske kuwa kin san wacece?"

Karasawa ta yi sosai kusa da shi tana dan jijiga jikinta, irin ga mata an batawa mata rai ta ce" eh mana, ba uwar NAJEEBA bace? A kan me zata zo.nan ta tare ko yar uwar BILKISSU ce? Ko kuwa dan kai take zaune?"

Idannuwa baki daya UMMU ta zaro daga wajen diner da suke zaune ita da Ammi , domin tun fitowarta Ammi ke zaune da ita tana tausarta, baki daya hankulansu ne ya dawo, irin rashin kunyar da matarsa ke tatawa ta saka UMMU zaro idannuwanta cike da mamaki

Abih ya ce" dama haka ne, dama ace zaman da take a nan nawa ne? Ke da na fi kowa farin cikin hakan, da ace zata kuma dubana bayan rashin adalci irin nawa da na yi farin cikin hakan na godewa Allah"

Yana gama fada gaba ya yi ya barta nan tsaye, maimakun ya nemi wajen su UMMUN sai ya bar gidan baki daya
Kwata kwata hankalinsa a tashe zuciyarsa bata da nutsuwa

Tunda ta fito daga wankan nan wanda ta ji dadinsa fiye da na dazu ta zauna ta saka pizzar da Zahrau ta kawo mata mai zafin gaske wace aka sarafata da naman kaza

Sai da ta koshi sannan ta kuma mikewa ta koma bakin gadon da Zahrau ke zaune tana kunce kitson da ala fara yi mata sannan ta mika mata abin kitson ta sauaka kasa ita kuwa ta fara kunce mata a hankali,

Basu yiwa junna magana ba har sai da ta gama mata ta caje kan sosai sannan ta raba shi gida uku cen saman ta fitar da kadan na tsakiya sai ma karshe ta dadaure kafin ta fara tsagawa a hankali ta kuma yiwa na gaban gida gida sannan ta fara daukan wani irin kananen kitso masu kwana kwana da shiga cikin junna sannan har karshe take kitse kitson duda irin yanda bata jin karfi sosai a jikinta aman ta ci burin sauke kitson

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login