Showing 57001 words to 60000 words out of 228147 words

Chapter 20 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10387

ya yi ne ya saka NAJEEBA daga hannayenta duka biyu ta dora saman kanta
Gaba daya ta ga wajen ya masu kadan idan tace zata gudu ta rantse ba inda zata je zai kamata

Ruwan nan masu sanyin gaske sannan babar butali ne ya yi tsaye daga jikin motar

Da hannunsa ya yafito ta

Kafafuwanta ta shiga dokawa a hankali tana jin uwa ta ce na ki, sai dai gannin daga ita sai shi fa sai mai shigar masa taraya sai kawai ta ji kafafuwanta na kaita inda yake tsaye

Daga dan nesa ta ja ta tsaya ta sada kanta

Kansa ya kara gyadawa gannun bata zube ta ringa yi masa fadanci ba
Rabonsa da ya ga mutun ya yi tsaye haka kansa da kansa ba tare da ya bashi izinin hakan ba tun barin garin sarkin agadez , sai Anmy wace take mahaifiyarsa
Ko matarsa takan zube ne kafin ta nemi wani lamarin a wajensa

Yatsarsa baba da ta tsakiya ya hada ya dan bada wani sautin da ya sakata dagowa

Kudaden daje zube a kasa ya nuna mata da idannuwansa

Itama kudaden ta bi da kallo domin wutar motar a kunne take

Da sauri ta karasa ta duka tana tsintsincewa
Sai da ta gama dauke dukan wa'inda take ganni ta harhada su ta karaso kusa da shi wannan karron ta miko masa su

Hannayen nata da kudin duka ya bi da kallo,
Wa shi? Take mikowa kudi haka?

Sai abin ya so bashi daria a kasan zuciyarsa
Idab ya fahimta yarinyar banda rashin kunya harda rashin hankali ke damunta
Yau gashi da rigar sarautarsa a tsaye a gaban yar yarinyar nan marar kunya tana miko masa kudi hannu da hannu a tsaye kikam

Baban goran ruwan nan ya saka hannunsa ya bale cikin dakiya ya mika mata muryarsa a kausashe ya ce" *ki tsaftace najasar dake tare da ke*


Najasa? Ta tambayi kanta, ko fitsarin da na yi? Ta kuma tambayar kanta

Amsar gioran ruwan ta yi ta matsa gefe kadan ta duka ba abinda ya dadata da kasa domin ita ai ganni take dare ne yayama aka yi ya gane fitsari na yi? Take tambayar kanta

Ruwan sanyi ne da shi, gata bata saba anfani da ruwa masu sanyi ba sai dai ita kanta yanda take jin jikinta na yi mata kaikayi dole ta yi anfani da ruwan tana kara matse hikinta ta mike tana ajiyar zuciya

Ruwan ta riko ta juyo sai dai ganshi a tsaye a wajen da yake

Dan bakinta ta tabe a ranta tana ayanna wato bayan cin haram ko dai kwarto ne? Yo wannan saka ido har ina?

Karasowa ta yi kanta a sade a kasa dan nesa da shi kadan

Gannin bata yi abinda ya yi jiyar sai ta yi a yau a waje a bakin titi ba ya saka shi juyawa kusa da tagar amintacensa

Murya a kausashe ya ce" bani biyu

Dauko masa biyun ya yi masu sanyin balaki ya miko masa

Amsa ya yi wannan karron ya ringa takawa cike da kasaita da isa har ya karasa inda take tsayen

Buda goran ruwan ya yi cikin dakiyar fuska ya ce" ki dauri niyar yin wankan janaba a zuciyarki

Da sauri ta dago kanta da wani irin tsoro da mamakin jin abinda ya fada

Sai dai kafin ta gama fahimta tuni ya shiga tsiyaya mata wannan ruwa mai sanyin balaki tun daga saman kanta mai dauke da alkyaba da hijab a kasa ruwan na ratsata har cikin jikinta ga yannayi na sanyi ga kuma tana da cutar huka wato athsma

Gaba daya ta rikice jin saukar ruwan nan hakan ya sakata kwala kara tana furta" ANMY

kafarta ta daga da niyar kwatar kanta sai dai abin ya gagara dan wata damka da ya yiwa hannun nata da hannunsa daya ya kuma bale dayan da hakorinsa shima ya daga tun daga kan nata ya shiga bulbule mata shi

Da karfin gaske ta fincike Alkyabar dake saman kanta da dayan hannunta, ido rufe ta yi cikinsa ta rukunkumeshi gaba daya jikinta na rawa tana jin numfashinta na neman fara bugawa

Bakinta ta buda zata bashi hakuri sai dai ta gaza sakamakon jan shedarta da ta fara har numfashin ya fara wani kara sama sama yana hiiiiiiiiik, hiiiiik tamkar wace ta zo fitar rai

Sarai ya san cutarta kuma ya san ta tashi ne aman bai daina ba sai da ya gama bulbule mata yana son bambareta da jikinsa aman ta mane masa tamkar cingan

Yana gamawa ya saka hannunsa ya dago fuskarta
Muryarsa a kausashe yana yi mata duba irin na tsana ya ce" me ya sa kika zabi zubar da mutuncinki? Idan na iyayenki bai dameki ba naki fa? Ke kin kasance sakarya a cikin mata
Ban taba jin kyamar halita irin yanda nake kyamar halayanki ba, na tsani na ji a cikin kanena akoy ki! Ki sani tsakanina da ke ba alfarma ko tausayawa!
Magana ta karshe da zan maki bayan ta idannuwana da nake maki kan ki kiyayi hada hanya da ni, sarkinki nake ba tsaranki ba! Idan ke takamarki *Mage ce* ni kuwa *kaifin wuka ne NAJEEBA MUTALAB!*

gaba daya ta idasa sikewa ta tafi luuuuu ta fada a jikinsa sumamiya

Baya tare da wani damuwa ko firgicin gannin ta summe masa
Hasalima idasa rikota ya yi ya turata motar sannan ya shiga gidan gaba domin ko suturar jikinsa kyamatarta yake bare zama kusa da ita a karo na biyu bayan ta gama wannan wulakancin

Amintacensa kansa a kasa, magangannun sarki tas a kunnayensa sai dai bai san wanka ne ya mata da kayanta a saman titi ba

A hankali ya tashi motar zai nufi cikin gida, muryarsa a cinkushe ya ce" Degza da allura

Yana gama fada ya maida dubansa bakin titin yana mai bale agogon hannunsa
A nan ya yarda agogon , ya kuma bale botiran rigarsa daga ciki

Da gudu ya shiga pharmacy ya amso maganin da allurar

Yana kawo masa ya duka ya mika masa sannan ya juya ya shiga wajen direban

Ruwan Allurar ya fashe kanta ya tsira tsinnin allurar ya zuki ruwan ya saka kwalbar cikin ledar

Sunna karasawa cikin gida hanyar sirrinsa ya fito da kansa cikin takamarsa ya buda bangaren da take

Hijab din nata ya kama ya cire dan samun wajen da zai mata allurar
Rigar dake kasa ta atamfa ce mai damamen hannu

Jikinsa ya laluba ya ciro wata yar siririyar wuka mai kaifin balaki ya kama rigar ya yaga wajen hannun

Allurar nan ya caka ya tsira mata ba tare da ya bi ka'idar a hankali ba domin zafin tsiya ne da ita

Yana gama tsira mata ya dauki ruwa ya dan warwatsa mata

A zabure ta farka daga summar wahalar da ta yi, idannuwanta ne suka sauka a kan macijin da ya cire masa dafinsa suka zuki abubuwan bukata a jikinsa hakan ya sa ya kasa motsawa sai ya ki mayar da shi cikin kwalbar dan bashi da niyar kashe shi, zai mayar da shi wajensa ne

Gefen fuskarta na gogar jikinsa hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya ta koma duniyar summa daga kwoncen da take

Tsaki ya ja a cikin zuciyarsa gannin summan fa ta kuma yi

Dubansa ya kai wajen amintacensa
Ba zai iya tura shi ya kaita bangaren Anmy a irin wannan lokacin ba, idan kuwa shine zai kaita dole ya bi ta hanyar da zata sada shi da fallon Zinariya sannan ya bi ta fallonsa ya bi ta doguwar hanyar da zata kaishi bangaren Anmy din ba tare da ya bi ta hanyar da kowa kan iya ganninsa

Hannunsa daya ya mika ya daukota
Dauka irin na yara ya yi mata a hannayensa bai rufe motar ba bai masa magana ba ya juya ya nufi bangaren Zinariyar

A daidai lokacin tana zaune a fallo ita da yayarta sunna cin abincin da ta saka aka masu wato gasashen naman rago ya ji kayan hadi sai turiri yake sunna ci sunna hirarsu hankali kwonce

Kasancewar hanyar ta sirri ce, ba'ai masa iso ko ta saka ran zai iya zuwa a irin wannan lokacin

Jin karar bude wajen ya sakasu waigawa a tare

Da yake kofar mai dauke da dan haske ne sai suka ga yannayin tsayi da fadinsa hakan ya sa da sauri suka mike yayar nata ta warci hijab dinta ta saka haka itama

Kofar ya turo da kafarsa
Kasancewar tafiar nan tamkar ta giwa a jinninsa ne ko yanzu ba sauri yake ba a hankali yake tafia da uta a hannunsa

Gaba dayansu suka zube kansu a kasa har sunna hada baki wajen furta" barka da war haka mai martaba

Bai iya amsawa ba, da kansa kawai ya dan gyada kai,
Jin kamar zai wuce da kyakyawan takalminsa ne ya saka Zinariya dago kanta a hankali

Gabanta ne ya kwonci kwonci ya yi faduwar da ita kanta ta kusa zubewa daga duken da take

Ya shige ciki hakan ya sa ta kara zabura ta mike

Da sauri yayar tata ta riko hannunta ta ce" ina zaki je?

Warve hannun nata ta yi ta ce" baki ga waye a hannunsa ba? Yarinyar nan da nake fada maki nace da ita yar talakawa ta mari fuskana itace a hannun mijina mai daraja me ya kawota bangarenmu? Me ya hadata da shi? Me ya sa ya dauketa da hannayensa masu matukar daraja da kima a duniya baki daya?

Aman idan kika je me kike son yi bayan kin san sarkinki ne shi kuma kanwarsa ce? Ta fada tana son tareta

Hannayenta ta kuma warcewa tana kallonta ido cikin ido ta ce" shi ya sa kika kasa gagarar kishiya! Koda kare jinni biri jinni ni Zinariya sai na kafa tarihin zama daga ni sai mijina
Babu shegiyar da ta isa ta hau hannunsa haka ya bi ta falona na barta da hankalinta da ranta koda kuwa zan yi yawo tsirara ne!

Tana gama fada ta juya da sauri tana bin bayansa, yayar tata kuwa ta yi gagawar daykar waya dan kiran mamansu

Tun da ya shigo Anky dake zaune da su Zahrau suka zabura sunna kallonsa

Da sauri Anmy ta karasa dan itace kawai zata iya tarbansa

Har hade maganarta take wajen fadin" sususubahannalah, Shaheed me ke damunta kar dai ciwon zuciyar ya yi tsanani

Irin yanda ta rikice yake kallo, da ta san shagalinta ta je ba asibiti ba zata rikice haka?

Anmy ta ce" likitan ya yi kurana yake ce min da sauki aman zata koma ya kara bincikata, wai summa ta yi ne Shaheed?

Ta fada tana rungumota jikinta a lokacin da ya ajiyeta saman kujera

Tsayawa ya yi yana kallonta, yayaunta kuwa du suka duduka kansu sunna faman yi masa barka da warhaka

Bai baiwa Anmy amsa ba ya juya a hankali zai tafi

Har ya kusan fita ya juyo, muryarsa a hade ya ce" ZAHRAU, ki shirya aurenki karshen watan nan idan Allah ya aminta

Yana gama fada ya juya ya fice a dakin

Kicibis dukai da ZINARIYA wace ta labe dan jin abinda ya hada shi da ita har ya rungumota haka, sam bata ji takun fitowarsa ba

Bai kulata ba ya fice ya barta kai sade tana fadin" a huta lafia mai damagaram

Yana fita suka rikice, kan mai dankarawa da gudu ya daukowa Anmy ruwa, sai mai kara rungumarta

Da gudu Anmy ta yi ciki dan kiran likitansu ,
Tana shiga Najeeba ta ja dogon numfashi

Idannuwanta a rintse tana jikin Zagrau bata bude ba ta furta" *BAN TABA TSANAR HALITA IRIN YANDA NA TSANEKA BA! NA RANTSE SAI NA RAMA A KANKA KO A KAN ALADEN MATARKA!*

a tsorace suke kallonta, Zahrau ta dora hannunta gefen fuskarta a hankali ta buda bakinta zata yi magana sai ga Anmy ta fito da wayar a kunnenta tana fadin"




...............😓







[31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



2 1



A sume ne take docter ki zo yanzun

Da sauri ummulkhair ta ce" Anmy ta farfado

Anmy ta ajiye wayar tana karasowa itama ta duka ta kamo Najeeba ta rungumeta a jikinta tana fadin" Najeena, meye? Jikin ne ya saka kika suma? Likitan ya nuna min da sauki kar na damu kuma yayanku ya shigo da ke a summe meye ne?

Najeeba kam irin yanda zuciyarta ke kunna bata da bukatar komai sai na kadaicewa

Ga jikinta du a jike yake gashi zuciyarta na yi mata zafi tamkar ta ciji babu

Anky, zan kwanta

Tsurawa fuskarta ido Anmy ta yi na dan lokaci kafin ta shiga taba jikar jikinta da cirar hannun rigarta sannan ba alkyaba a tare da ita ba hijab dinta

Tana kallonta ta ce" me ya fari da ke kika dawo min ba a yanda kika fita ba?

Najeeba ta ja numfashinta da kyar ta ce" Anmy, athsmana ne ya tashi,

Anmy ta kara jin tausayin yarinyar fiye da sauran yan uwanta
Kamata suka yi suka nufi dakinsu da ita

Saman bed din suka shinfideta Anmy na ta shafa kanta tana kallonta

A hankali ta ce" Allah ya baki lafia bara na je na fadawa yaya cewar da sauki

Mikewa ta yi ta juya ta fita

Tana fita da sauri Zahrau ta riko hannayenta ta ce" me ya faru da ke? Me ya maki? Waye kika tsana? Me aka yi?

Gaba dayansu hankalinsu a tashe yake su duka

Najeeba ta cije lebenta na kasa tana jin wani irin kunci a zuciyarta

Muryarta a kausashe ta ce" SHAHEED NE, Shaheed ne ya min wankan janaba

Da karfi suka kusan fadi a tare kan me cewa" quoi? (What?), sai me cewa Me?

Idannuwansu a zazare a waje cike da tsoron abinda ta fada din

A hankali ta ja hancinta ta tashi ta dan jingina tana kallonsu, sai da ta kuma lumshe idannuwanta ta bude , a hankali ta kabarta masu abinda ya faru

Kwarai sun ji tausayinta sai dai Zahrau na budar bakinta sai ta ce" Najeeba, rashin jin maganarki ke jaza maki fitina
Ke da ya sauke ki ya ce ki je ku hadu a lokaci me ya hana ki zuwa ki yi jiransa?

Ummulkhair ta ce" bama wannan ba, tsakani da Allah ciwon zuciyar nan dama karya ne Najeeba? Ke kam bakya jin magana ban san me ke kwakwaluwarki ba

Ummukulsum ta ce" NAJEEBA, kudin da ya baki kika watsar? Sannan kika yi fitsari a gabansa a gaban yaronsa? Me kike so ya dauke ki? Najeeba ko bai yi tunanin baki da kamun kai ba ai kema kin san baki da shi ko?

Najeeba ta lumshe idannuwanta a hankali ta ce" eyah, me zai hanna ku taru ku min dukan tsiya dan na taba dan gwal?
Dagowa ta yi ta firfito da idannuwanta ta dauki hannunta ta nuna kanta ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa bashi da mutunci, kuma bai sani bane irin yanda ya yi ikirarin ya tsane ni na fi shi tsanarsa, zan nunna masa a aikace, ba dai ni Najeeba ba? Nice ya kwontar jikin maciji?

Kallon Ummukulsum ta yi ta ce" ji wani kililin kasau da ita kamar ta Allah ke nan kyankyaso ne ya shiga rigarki kika cire rigar da wasu kannanun nonuwanki kina ihu a gaban kannenki,

Ummukulsum ta ce" ai dai ni ban yi fitsari a gaban mazan da ba maharamaina ba

Ta buda baki zata rama Zahrau ta ce" kun ga ku saurara mu ji da abinda ya sha mana kai mana haba da Allah, ku kawai baku da aiki sai fitina? Maganar zaki rama bata taso ba! Ki rama me? Ta yaya? Ki bari ki mutu maza su kaiki ba mata ba dan walahi da zaki ji tarihin bawan Allahn nan sai jinninki ya hau, baki yi mamakin yanda aka yi yake damkar maciji da hannunsa katon maciji ba wani jariri ba? Ke ki kiyayi maza walahi bana son fitinar da zata saka ransa ya bace ya batar da ke Najeeba! Ke kin san albarkar anmy kike ci, kin san albarkar su Abih kike ci, aman kina da izgili a abinda ya shafe shi, ke idan ba rigima ba ina ke ina tsayawa kafada da kafada da shi? Ai ko ba sarautar dake yawo a jinnin jikinsa ba shi din yayanki ne, yaya aka yi kike girmama yaya DAYABU ne? Bale ko a cikin mutane akan yi wani halayensa daban!
Najeeba mutumen nan adali ne, aman kuma inaai tabatar maki ya fi macijin nan da ya sumar da ke balaki idan kika tankwalo hakan zaki samu domin mu yan uwanki ba abinfa zamu iya yi maki NAJEEBA!

NAJEEBA dake kallonta ta yi murmushi tana dan girgiza kanta, a hankali ta dan yi atishawa tana dafe daidai kirjinta ta ce" tabas shi din wani ne na yarda, shi din ya girme ni kuma na yarda
Dubansu ta yi ta yi murmushi ta ce" sai dai ni din kamar yanda ya ce ne *MAGE ce ni mai kwonciyar d'aukan rai* zan dauki ransa a lokacin da bai ji ba bai gani ba bai san da zuwan lamarin ba
Tunda ya yi saken na kasance mace......zan nuna masa irin girman karfina a kansa! Shi da takobi take suka, ni kuwa da kalamai nake suka idan na tashi harbi da tawa kibiyar nakan harbi wajen da baya jin magani!

Ummulkhair da ta bude victago ta lakuto ta nufi wajen kirjinta tana shafa mata a hankali ta ce" ki dai bi a hankali, kar kibiyar ta kasance mai zuwa ta dawo ce

Ummukulsum wace itane ta fi su tsoro ta ce" ni dai dan Allah ki yi hakuri, a bar maganar wata ramuwa dan ba wajen bane, ko dan Anmy ai ya isa ya taka ki ki sada kanki, kinafa ji NAJEEBA yanzu yace auren aunty Zahrau karshen watan nan, ke kin ga Anmy kanta sai da ta zabura ta kale shi hakan na nufin ita kanta bata san da maganar ba bale Abih kuma ya zama wajibi su masa biyaya, ke kina kasa zaki wani ce ke aa?


Da yake ta fi rainata dama yan watani ne ta bata ba shekara ba sai ta ce" Ummukulsum ni abin ya fi maki ciwo dan nace zan rama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login