Showing 63001 words to 66000 words out of 228147 words

Chapter 22 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10413

da kai

Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa, bai ce komai ba

Sai da lokacin ya yi du suka nufi bangaren harda kananen

Ta lungun da zai sada su da dakin karatun suka bi suka karasa dakin karatun

A dakin nabar kujera daya tak ce sai shinfidun cafet na alfarma
Sai manyan kur'anai, da alo manya
Maka makan tableau ne dauke da sunnanyen Allah da ayatul kursiyu, da sunnan Muhammad (sallalahu alaihi wa salam), su Alhamdu

Ac hudu ne a dakin sai manyan panka tafka tafka dake kunne suma sunna aikinsu

Tun kafin su Zauna muryar Abih ta shigo da salama

Ba shi daya bane tare yake da matarsa hakan ya sa Anmy kallonsa da kallo irin na me ya sa zai zo da ita?

Kawar da kansa ya yi ya nemi waje ya zauna

Yanda aka yi zaman Abih ya zauna ne tare da Dayabu da Najeeb a bangare guda
Gefen daya kuwa Anmy ce tare da yan matanta kananun du sun dadane mata jiki da yan kananun alkuabarsu sun yi tsaf kamar ka sace su ka gudu

Manyan kuwa kowace na gefe gefenta , su kam yanzun basa sanye da Alkyaba sai zumbula zumbulan hijabai har kasa irin mai habar nan

Mardiya kuwa na zaune gefe guda itama ita daya, ga yarinyarta sai tsala ihun kuka take tana so ta saketa aman ta ki sakin nata
Ta sha wani rantsatsen lesh sai kyalkyali yake yarinyartama ta shiryata cikin wata riga doguwa mai shegen kyau, kyanta zai shaida maka kudinta

Sai ihu take tana kallon Najeeba, dan kaf a cikin yayun nata babu wanda ta shaku da shi irin najeeba dan goyata take ta yi ta mata doki , sannan du idan zata shigo sai ta shigo mata da tsarabar sweet

Wani uban tsaki ta ja ta dangwarar da yarinyar saman cinyarta ta dale keyarta ta ce" zan ci ubanki Nusaiba ki zauna min yau ga jaraba ba inda zaki je

Da sauro Najeeba ya kama bakinsa yana kallon yayansa, a fili ya ce" yaya Mardiya na zagin kanwata bayan ka hanamu zagi walahi
Duban Mardiyar ya yi ya ce" walahi ki bar zagar min kanwa

Mardiya da a cike take irin yanda Abih ya tasota ya tiso keyarta ya kawota a zaunar da su kan laifin da bata san me ta yi ta harareshi ta ce" sai ka hanani zagin nata shege mai katon kai

Da sauri ummulkhair ta dubeta ta ce" aman me yasa kika cika son neman fitina ne ke?

Anmy ta yi mata wani kakausan kallon da ya sakata sada kanta aman kasan zuciyarta a bace yake

Ai kuwa Bilkissu da ba kallon Anmy take ba ta ce" to fa, an tabota

Ranta ya kara baci ta ce" ke bilkisu an taboni ni ga mahaukaciya ko? Yan iska kawai da iyayenku kuke kuma du irin rashin hankalina na fi su domin ni na fi uwar kowa cikinku jimawa da ubanku

Da sauri Anmy ta dago kanta a karo na biyu ta sauke dubanta a kanta

Zahrau ta sada kanta tana jin hawaye na son zubo mata

Ummukulsum ta ce" me yasa idan kin tashi masifarki kike sako iyayenmu? A kan me zaki ringa koya mana muguwar tabi'a ne? Kin dai san uwa ba fin uwa ta yi ba ko? Kuma yai da gobe sai Allah kin san watarana zaki ji kunya? Kar ki manta a damagaram muke idan wannan bai san sirrinki ba wani ya sani balema a tafin hannuna sirrin naki yake

Rufe min baki shashasha, siriin nawa da kika sani meye? A ciki akoy cikin shege ne? Ko akoy yawon ta zubar ne?

Da sauri Dayabu ya dubeta, da yake mahaifiyar Ummukulsum bata zama waje dayan nan ba kennan gori ne ta mata na hakan

NAJEEBA ta kara sada kanta tana jin zuciyarta na yi mata tukuki, sam bata so ta furta ko A a wajen nan domin ba a ko'ina take son raba hali ba

Ummukulsum ta ce" Alhamdulilah, haka ne, na sani na kuma yarda uwata haka take, ke fa ubanki kafin ya zama malami meye bai yi? Ta fada muryarta a dan dage

Fuskarta da Anmy ta tsinke da mari ne ya saka du suka firgice sunna kallonta

Sai a lokacin Anmy ta buda bakinta a hankali ba a tashe ba ta ce" ashe lalacewar tarbiyar naku har ta kai ina zaune a waje kuna tozarta kanku ta hanyar sakarwa harshenku linzami?
Kun san ikon harshe a tare da mutun kuwa? Harshe kan saka bawa ya zama sakarai a cikin al'uma,
Idan baka iya rike harshenka ba zai fada maka maganar da zata saka ka da na sani a cikin duniya baki daya!
Ku shikenan a wajen da ya dace a ji muryarku da wajen da bai dace bama sai ku saki baki ku furta kalma daya?
Ummu a gabana kike rashin kunyar nan? Ummu ni zaki tozartawa iyali? Wuyanki ya yi kwarin da ya isa yankan da zai jazawa mahaifiyarki zagi daga bakin mai nemanki da fitina?

Abih da kansa ke sade yana cike da mamakin rayuwa irin yanda yau shine mace, matarsa take budar baki tana zagin y'ayansa a gabansa aman ya kasa furta mata komai

Sunnayen Allah ya ringa kira ido rufe domin baya so rashin kunyar Mardiya ya kaishi wajen da zai kuma aikata kaifin rabuwa da mace, irin yanda ya rabu da matansa ya yiwa kansa alkawarin ita wannan ta birne shi ko ya birneta, sai dai kash ya yo hakan a lokacin da yake aure da matar da bata san darajar kanta ba, ya yi zama da mata kala daban daban, har yar bariki da ustaziya, bai tashi daukan wannan niyar ba sai a kan wace zata tarwatsa masa nutsuwar zuciya

Tun da Anmy ta fara magana sauranma suka kara sada kansu
Ummukulsum kuwa sai ta fashe da kukan nadamar sakin bakinta da ta yi har haka ta faru
Kanta ta dora a gefen kafadar Najeeba tana kukan inda Najeeba ta rintse idannuwanta tana jin kukan yar uwar tata har cikin zuciyarta
Bata taba jin tsanar matar abih irin na yau ba, tabas bata zo wajen nan dan furta kalma daya ba aman ta rantse a yau b sai gobae ba sai ta tardata du gidan ubanda ta shiga ta ci uwarta!

Sanarwar shigowarsa ya saka Anmy sada kanta tana jin kamar ta fashe da kukan itama, kai ina, dole ne ya bara mata yaren nan dan walahi ba zata yarda ya kara tafia da su ba ya kaisu tarbiyarsu na kara shiga hatsari! A haka zaa aurar da mace a kaita gidan miji a kai me? Ta tabata irin yanda ummu ta kasa dane bacin ranta ta nuna shirme ko miji ya fada zata fada ne!

Ya kai minti ashirin kafin yake karasa shigowa cikin shigarsa ta kamala

Da hannayensa ya dakatar da amintacensa kan ya tsaya a kofa domin shara'ar ta cikin gidansu ce

Direct wajen kujerar ya karasa yana tsaye yana bin kowa da kallo

Yarinyar dake sheka kuka kamar zata sike ya bi da kallo, mahaifiyarta da ta riketa gam ya kuma bi da kallo kafin ya maida dubansa inda yarinyar ke nunawa tana son a saketa ta karasa wajen Najeeba aman an hana

Murmushi ya yi a kasan zuciyarsa domin nan take ya gama fahimtar matsalarsu baki daya sai dai kamar yanda ya kasance sai ya saurara to fa zai sauraran ne dole


A hankali murya a tausashe ya ce" *KI SAKE TA TA JE WAJEN YAN UWANTA*

A hankali ya yi maganar, sai dai kasancewarsa mai cike da kwarjini da bulaliyar dukan magana ya sakata tunkudo yarinyar a biye wanda ita a boye ta yi aman du an gani

Yarinyar kuwa da gudu ta karasa jikin Najeeba
Tana zuwa ta ringa dora kanta a jikinta tana rukunkumeta, sai dai Najeebar bata riketa a jikinta ba itama
Zuciyarta na mata tsale, so take ta riketa ta rungumeta aman ba hali a hankali ta saci kallon yayansu wanda komai a kan idannuwan sarki, shima duban nasa ya kai wajen DAYABU sai ya ga idannuwansa a rintse suke, ya gama hawa stage din da ba zai iya furta kalma daya ba tare da ya yi maganin matar nan ba!

Murmushi ya yi ya idasa gani kan matsalar kafin a hankali ya kai zaune

Sai da ya zauna ya gyara zamansa sannan ya yi sakama a hankali

Baki daya suka dago kawunnansu daga sadawar da suka yi,

Dubansa ya kara kaiwa wajen yarinyar dake ta wawuwar Najeeba dan bata yi shirun ba so take ta kulata ta yi mata wasa ta rarasheta aman ta ki yi mata hakan

A tausashe ya ce" Abu hauraira Allah ya yarda da shi yana cewa" ka so masoyinka daidai gwargwado domin zai iya zamowa makiyinka, haka kuma ka ki makiyinka daidai gwargwado domin zai iya zama masoyinka wata rana

Numfasawa ya yi ya shiga binsu da kallo tun daga kan Abih har zuwa mahaifiyarsa

A hankali ya kuma furta" *ME KE DAMUN AHALINA NE? ME KE DAMUN SHUGABAN CIKIN GIDAN BIYU NE?* *YAYA AKA YI YA YARDA KIYAYA TA YI ZAFI HAKA A CIKIN GIDANSA BAYAN YANA DA IKON KATSETA KODA KUWA TA HANYAR KAWAR DA MAI HADASATA NE A WAJE?*
[31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



23



Baki daya wajen ne ya dauki shiru , kawunnansu du a sade a kasa haka kuma NUSAIBA bata daina kukan da take ba

Sarki ya kuma buda bakinsa ya ce" mazon Allah tsira da amincin Allah su tabata a gareshi yana son yin alfahari da mu a gobe kiyama
Aman ta yaya?

Shirun dai ne ya kara tabata a wajen hakan ya saka ya dago yar yatsarsa ya yi nuni da Zahrau a tausashen dai ya furta" Bismillah

Zahrau ta kara sada kanta a hankali ta ce" Allah ya kara girma, ya umarcemu da mu hayayafa dan gobe ya yi alfahari da mu

Kansa ya gyada a hankali kasa kasa ya furta" barakalahu fihk,

Kansa tsaye ya nuna Najeeba dake dan janye Nusaiba daga jikinta ya furta" meye ilar gaba a musulunci?

Dungurar da Anmy ta yi mata ya sakata dagowa domin ta so ta yi kamar bata gane da it ake ba , sai dai ba hali domin a irin yanda Anmy kanta ta nutsu a gabansa abin sai wanda ya gani,
A sanyaye ta furta" *Allah yana yiwa mutane afuwa, aman banda masu gaba da junna*

Dubansa ya maida wajen DAYABU da kansa ke kasa shima kafin ya ce" shin me ya dace shugaba ya koyar tsakanin hakuri da rashinsa?

Yaya DAYABU ya dago yana dubansa kafin ya furta" Hakuri, Hakuri shine ya dace da kowani bawa, mai hakuri zai ci riba

Sarki ya gyada kansa ya furta" Mai hakuri zai kai ga ci

Dubansa ya maida kan iyayensa daga Abih har Anmy
A sanyaye ya furta" shugaba, ya dace ya kasance mai matsanancin hakuri, ya ringa shanye abinda da yawa ba zasu iya shanyewa ba
Shugaba koda na wasan yara ne, ya dace ya zama mai yanke hukunci cikin aminci, da kawar da kai

Dubansa ya maida wajen Mardiya, sunna hada ido ta yi gagawar sada kanta, a hankali ya furta" ka karfafa zumunci, ka yada zumunci, kar ka zamo wanda zai yi silar yanke zumunci

Shiru ya kuma yi kafin ya furta" mai magana bismillah

Anmy ta sauke ajiyar zuciya tana dubansa kafin ta maida dubanta wajen yayanta, a hankali itama ta furta" burina, bai fi zumunci ya dore ba Allah ya ja da ran sarkin damagaram

Shaheed ya lumshe idannuwansa ya maida dubansa wajen Abih

Abih ya buda idannuwansa da sukai masa jajajir , a hankali ya furta" Allah ke bada girma, koda kuwa yaranmu sun zamo shuwagabaninmu mu masu biyaya ne, Allah ya kara datako Mai damagaram

Kuma lumshe idannuwansa ya yi sannan ya maida dubansa wajen DAYABU

Kansa ya sada , a hankali ya furta" na yi kuskure, baki daya ni na ja ragamar wanzuwar wannan fitina,Allah ya ja da rai daga yanzu daga kan DAYABU MUTALAB, har zuwa NUSAIBA MUTALAB bamu da wariya, Allah ya huci zuciyar sarkin garina

Da sauri Najeeba ta kankame NUSAIBA a hankali a jikinta sannan ta sakar mata dan murmushi tana shafa kitson kanta wanda tun wanda ta mata ne ba'a tsefe shi ba kusan sati uku a kan ko wankin kirki ba'a masa ba hakan ya sa ya tsufa duba da sunna da izgar gashi nan da nan gashi ke tohowa a kansu shi ya da du sati sauran ke yawan kunce kansu domin kitso ko saloon a gida ba wani wahala shi ya sa kawunnan nasu ke kara albarka

Murmushi ya yi wanda iya zuciyarsa ne sam bai bayanna a fili ba

A hankali ya kuma furta" Allah ya yi mana jagora

Baki dayansu suka amsa amen banda Najeeba dake kara buda bakin Nusaiba tana kallon hakoranta da suka yi dan duhu hakan na shaida mata bata wanke mata baki har gashi ya kama hakoran yar yarinyar

Shirun da ya dauki wajen ne ya sakata dago kanta dan gannin har ya gama maganar ne?
Idannuwansu ne suka sarke da na junna a lokacin da ya kusan karasowa inda take zaune , da sauri ta mayar da kanta kasa ta sada sakamakon faduwar da gabanta ya yi da kuma irin kallon tsanar da ta ga ya yi mata
A ranta kuwa fadi take" azalumi, ashe harfa fuska biyu ne da kai? Gaka yanzu ka gama maganar wa'azi da masalaha ni kuwa ka tsane ni? Ba damuwa, zaka gane ne dan yanda ka tsane ni ni naka fi ka tsanarka!

Sai da ya fice a fallon da kamar minti goma sannan du suka mike

Irin yanda ta karaso ta warci yarta ta juya buguzum buguzum ya saka baki daya suka zaro idannuwansu

Da sauri Abih ya daga kafarsa zai bita sai dai maganar da Anmih ta yi cewar" idan ka bita yaya zaka rarasheta ne ta maido y'ar?
Ya saka shi dawowa da sauri inda take tsaye da yarensa

Muryarsa har tana hadewa da junna ya ce" yanzu domin Allah Bilkissu ba zaki yi min adalci ba kema? Kema a yanzun ganni kike ni ke daure mata tana haka? Ko so kike na yanke igiyoyin da sukai saura a tsakaninmu ne na jara dauko wata? Ita watar idan na daukota kin san meye halayanta? Wani sabon zama ne za'a kara dorawa da y'ayana shin da me zata shigo?

DAYABU ya yatsina bakinsa yana girgiza kansa, lale ta samu damar da take tunanin har zata iya taka sawun kafarta ta fita da y'ar da sarki ya gama nasiha a kanta

Fitarta kawai suka ganni, hakan ya saka Zahrau kallon Anmy, sanyaya muryarta ta yi ta ce" Eyah, Anmy Najeeba ta fice da sauri Anmy

Anmy ta kallota da sauri, sai kuma ta kalli Ummulkhair ta ce" maza ku bita

Sai da suka fita ta kuma kallon DAYABU ta ce" wai Ummulkhair na tura ta bita, ko ta je ta tayata ba, bi min su ka maido min su ka ji?

Irin yanda take sauri ya yi daidai da Mardiya ta buda gaban motar Abih ta shiga kennan zata rufe ita kuwa ta karaso da wani irin mahaukacin sauri ta tare marfin kofar ta hannata rufewa

Hannunta daya ta saka ta finciko yarinyar ta direta kasa cen gefe sannan ta maida hannayenta ta finciko uwar waje

Da ihu ihu uwar ke fadin" ke baki da hankali ne? Ke wata irin karamar yar iska ce?

Dauke fuskarta ta yi da mari, ta maimaita mata wani sannan ta saka hannayenta ta hankadata jikin motar nan ta rike mata wuya
A masifance ta ce" ke wawuya ce Mardiya, kin so ki ci darajar uwa koda kuwa shekarunmu daya da ke, sai kika bata rawarki da tsale!
Tanas gaskiya kika fada babu wace ta zauna ta yi hakurin zama da shi har zuwa wannan lokacin kamar ke gashi yarki har zata ryfe shekara hudu nan da sati uku da kwana biyu,
Kin san me? Dalilin wannan ni kaina na so na ga mutuncinki, domin a duniya du macen da ta iya jure zaman waje domin y'ayanta nakan bata wani waje mai daraja a cikin mata wanda ba kowa nake ba shi ba
Sai dai ke din kin kasance wawuya a lokacin da kike anfani da kadarar wani ko dama da kika samu na zama matar MUTALAB kina taka mu son ranki!

Warto hijab dinta da Dayabu ya yi da murya a dan dage yana fadin" Najeeba me kike haka? Sakar mata hijab kin san da labari na iya iske sarki har yanzu a cikin gidansa kike fa kin manta a wajen ajiye mitoci kike

Fuzge hijab dinta ta yi, Ummulkhair kuwa na gefe rike da yar ta juyar da ita gefe guda tana dan jijigata har ta yi shiru daga kukan da take na rabota da su ta kwonta a kirjin Ummulkhair duda ita Najeeba take so ta dauketa aman ko a Ummulkhair din aka tsaya da dama domin mamanta ta cika duka da fada da zagi abu ga yaro inda ta fi jin dadi nan ta fi zuwa

Gannin sai kakari Mardiya take ya saka wannan karron ya fardota baki dayanta daga jikin Mardiyar da ta yiwa shakar mutuwa

Yana rike da ita tana tirjewa sai da ya matsar da ita gefe ya riketa a hannunsa da karfi karfi ya ce" zaki dawo hayacinki ko ba zaki dawo ba?

Wata tirjewar ta so yi ta hanyar kuma ridar Mardiya dake tsugune tana rike da wuyanta sai dai bai bata dama ba ta hanyar dauke fuskarta da marin da ya sakata saurin ja ta tsaya tana mai dafe kuncin nata da hannayenta bibiyu dan walahi bata son mari, kai ina dalili za'a maren mata fuska? Ita bata son mari ko kadan

Randa bace ya ce" ke baki isa na tankwasa ki bane ko ke idan ranki ya baci mahaukaciya kike zama?
Na fada maki ki daina, na maido ki da laluma , na nuna maki hanya sai tirje min kike kinai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login