Showing 150001 words to 153000 words out of 228147 words
Chapter 51 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
a kan har uwarta
A hankali Zahrau dake ta harhada yanda zata bilo mata ta ce" tsoho ne?"
Najeeba da sarai ta san wa take nufi aman sai ta kasa bata amsa
Zahrau ta yi murmushi ta ce" matsalarsa dai farinsa da kuma sarautarsa ko?"
Najeeba ta sauke ajiyar zuciya, a hankali kamaninsa suke dawo mata , da sauri ta saki ajiyar zuciyar da ta kwace sakamakon irin yanda kamaninsa suka kawatu a idannuwanta
Wani murmushin Zahrau ta yi, domin a rubuce sai dai ta rubuta labarin kanwar tata ta baiwa wani tsabar yanda ko da ido ta yi magana take gane gaskiyar ciki da kuma wanda ta fada dai ne
A sanyahe ta furta" sai kike ce min na yawaita shiru a kan yawan magana, nan kika nuna min daga mijin da na aura har matansa kar na zake wajen buda bakina ina magangannun da ni kaina zasu gundureni domin kuwa a irin haka ina iya bada kofar da za'a gane raunina, tashin hankalina, sakarcina, jin tsorona"
Najeeba ta ci gaba da kitse gashin Zahrau, itama Zahraun sai ta yi shirun tana sauraronta dan kuwa ta san kitson nan ba na karewar yanzu yanzu bane
Sai cen kamar bata wajen, kamar ba zata tanka ba ta ce" Ban taba shiga halin firgici da tashin hankalin da na shiga ba,
Dan jan iska ta yi ta ci gaba da fadin" just ki kwatanta abin a gabanki, mutumen da tun bana biyewa maganarsa har ta kai min buga wasa daga ni sai shi,
Lebenta na kasa ta cije da hakoranta na sama kafin ta ci gaba da fadin" ya yawaita yi min tambaya a kan gidan nan, sai na nuna masa ni ban san gidan ba, ban san kowa ba, karshe na furta masa ni fa bai min ba"
Tsagawa ta yi da dan karfi har Zahrau na fadin" Aush"
Najeeba ta furta" Du a kan me ya min basaja yake hira da ni? A kan me ya ringa yi min tsmbayoyin da suka shafe shi? A kan me ya ringa hakuri da fadana? A kan me ya ci gaba da janyoni jikinsa ina fadin maganar da ta raya min a kansa?"
Sai da ta ja numfashi ta sauke , irin abu ya dake kan nan ta ce" sai kawai na ganshi a lokacin da ya shirya wulakanta ni shi ne a gabana da kamaninsa da komai sai dai fuskarsa na dauke sa kallon tsanar nan da ya zamo ayar tambaya a wajena!"
"Kun ban amsar hasashenku, sai dai zan kuma yi maki wata tambaya Aunty Zahrau, kasancewarsa baban mutumen dake mu'amala da mutane kala daban daban, har ya kasance ya iya basaja ya shiga gari ya yi lamuransa, shin bai taba sannin menene halayar yan matan zamani hade da samarin zamani ba ko kuwa yana nufin du yan matan yanzun ba soyaya ce suke yi da samarinsu ba aa zubar da mutuncinsu ne suke?, kina so ki ce min Aunty ya taba kamani da namiji turmi da tabarya ne ya saka shi wareni daban a cikin yan uwana ya sako lamarin tsana a tsakanina da shi? Ko tsabar rashin yancin kai ne zai saka matarsa marar tarbiya du haduwata da ita ko yan uwana da ita tun bana kulawa har ya kai kimarta da shakunta suka zube a idannuwa sakamakon mamakin kalar fatata da ta yan uwana da jifanmu da kalmar y'ayan talakawa ya saka har ta kaini da daga hannuna na fara jin dadin sauke iskancina a kan fuskarta shikenan mu ba zamu iya ramawa ba dan bamu da yanci? Shi mutun idan ba sarki bane shikenan sai ya zama talaka? Anya kuwa ta san menene talaka? Ba narar arziki bane talaka, mai mataciyar zuciya shine talaka! Aunty kina son ce min dan muna samun matsala da sakarya nunar ranar matarsa ce ya tsane ni ko me na tare masa ne ni? Na ga dai gidan nan wajen kawo kara ne, na tabata ban kasance wace aka fi kawo karana ko na rako gabansa dan shara'a ba a cikin garin DAMAGARAM! Ko shima so kike ki ce min shine dalili?, Aunty kadara cewar wai na bata rayuwar tawa, na zama fitinaniyar na gagari kowa a kasarnan, ina ruwansa da rayuwata da zai sakota gaba?"
Ta karashe maganar tana huci sosai ranta a matukar bace
Murmushi Zahrau ta kuma yi a hankali ta ce" NAJEEBA kitsa min sannu sannu dan Allah zafi fa"
Bata bata amsa ba, dan kuwa ta gama shaka mata ba dadi a ranta
Aunty Zahrau ta ce" Tambayata Najeeba a kanki shine: shin ke zaki tsara rayuwarki ne ba Allah ba?"
Najeeba ta ce" Me hakan ke nufi Zahrau, na isa na tsara rayuwata ne?"
Zahrau ta yi murmushi ta ce" Good, kin san da wannan shine kike haushi dan Allah ya wanzar da ikonsa a kanki? Daga ni har ke har Ummukulsum shin mun san rayuwa zata kasance haka a kanmu? Kin taba tunanowa cewar ni Zahrau zan auri sarki, sarkinma mahaifin ZINARIA kuma dansa namiji kwalin kwal ya tafka aikin da zai shigo zanen kadarar ahalina?, wa ya taba kawowa kansa cikinmu wace ta fi mu tsoron harkar maza take gudunsu tun karfinta hakan ne zai risketa? Me ta yi? *HAKURI* ta yi, tana kallon ikon Allah a lokacin da ta gane bata isa ta zana zanen rayuwarta ba"
Dan dago kanta ta yi tana kallon NAKEEBA ta ce" Kina nufin kina son nuna min cewar ke din daban kike a cikin halitun Allah da har kika kai matakin da zaki samu aure mai daraja mai mutunci dan kawai ya kasance mutumen da kike naki zato yana nasa kuma ya zama fari sannan yana da mata ciki harda wace haka kawai kuka tsani junna shikenan kin isa ki nuna ba'a maki adalci ba, Najeeba har ta kai da ke da bakinki musulma kike kina kallonsa dan kin rikice ki ce masa ya sake ki ko auri HUZAIFA?"
Najeeba dake kallon yannayin yanda Zahrau ke magana a sanyaye ta ce" Aman"
Zahrau ta ce" Aman me? Idan bamu isa ba, iyayenmu baasu isa ba, kina son ki nunan bakya tsoron Allah?"
"Aunty wani irin baku isa ba?" NAJEEBA ta fada tana dan nuno hannunta fuskarta na nuna yannayi na tashin hankali
Zahrau ta yi dan murmushi tana dan girgiza kanta ta ce" bamu isa ba NAJEEBA, meye bamu gwada ba? Meye bamu nuna maki ba? Ciki harda mamansa wace ta haife shi ta roke ki, ba wai dan kin fi sauran matansa daraja ko wani abin ba a wajen Allah, aa, sai dan tana yi maki so daya tak fisabililahi sannan ta rayu da son samun iri daga tsatson kawarta aminiyarta? Du kika watsa wannan, yanzun ta kai har kina kallon mutun mai daraja, da mutunci, mai nagarta, mutun wanda Allah ya daukaka, ke dan kin samu dama kike furta masa ka sake ni? Idan har da gaske kike ba zaki iya rayuwa da SHAHEED ba, gwara a yau mu samu Ammi a san yanda za'a yi, ki tashi kawai ki je ki sameta, ki fada mata gaskiyar cewa ke fa ba zaki iya zama da shi ba dan haka a sawake maki, kin san aure Najeeba idan ba so, ba yarda akoy matsala, idan har mace ta tsani namijin komai na iya faruwa, tunda har shi ya amince zai zauna da ke a gaban mahaifinki da yayanki da kuma mahaifiyarsa ke kuwa kin kasa hakura da hakan sai a dauki mataki, ya sake kin ki koma wajen Huzaifanki, mai yiwuwa shine abokin rayuwar taki aman sai kin bi ta kan Sultan kafin ki karasa hannunsa"
NAJEEBA kawai galala ta yi tana kallonta, 'ita? Ta tashi ta je ta samu Ammi da maganar nan? Sannan ita ta rabu da shi ta komawa Huzaifa? Ita kanta tana wannan furuci a kan Huzaifa ne a kan dalilin da bata sani ba, aman yau ko dan dan abinda take taka iya shegenta dan ta kwana da sannin a kilace yake da ya kwace me kuma ya mata saura?'
Kanta ta dukar muryarta a raunane ta ce" Aunty, shi din da ba so na yake ba fa?, ki duba ki ga wai ni ya cewa baya son bak'a, kuma ya auri Nadia Aunty NADIA fa?"
Zahrau ta yi murmushi ta dukar da kanta ta bata damara tsagawa sannan ta kuma daukan wani kitson
A sanyaye ta furta" me kika ji a zuciyarki a lokacin da kika ga wata fuskar a matsayin matarsa bale Nadiarki? Yaya kika ji da ya furta maki baya son bak'a?"
A hankali saurin kitsonta ya ringa ragewa sakamakon irin zafin da ta ji ya ringa dawo mata sannu a hankali,
Tabas ta ji wani irin zafi mai girman gaske, faduwar gaba, da jin an gama wulakantata
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin irin yanda idannuwanta suka cika da kwallah, a hankali ta furta " *RAINA YA BACI SOSAI*
wani murmushin Zahrau ta yi a bayane ta kuma aiko mata da wata tambayar da ta sakata tsayar da kitson harma ta kurawa wajen da ta tsaga da tsirarun gashin kan na Zahrau ido,
ZAHRAU ta dago kanta tana kallonta ta ce" Tall me an mata, zaki iya beman sakin ki ne a hannun Ammi, ki fito ki yi zawarcinki, ki samu bakin mutumen da kike hasashe ya aureki a matsayinki na bazawara ku je ku samu irin rayuwar da kike tsarawa kanki ki barawa NADIA da ZINARIYA mijinsu?"
*MIJIN SU?*
Abinda ya fi tsaye mata a kasan zuciyarta, 'aman a kan me Aunty zata ringa yi mata irin wannan? Dan ta tayar mata da hankali ne ta sakata kuka ko dan ta birkita mata lisafi ne? Mijinsu? Ita har ya saketan ne da aunty zata kirayi namijin da ya gama karbar du wani tanadinta ya kare amshe du wani guzurinta sannan ya shiryata kafin ya sakata a jikinsa ya bata rungumar da ya kusan minti biyar a tsaye da ita a hakan ya furta mata kalmomi kamar haka :Ki kula da kanki, ki tsaftace harshen ki, Allah ya sa ki wuni lafia....: ya karashe yana mai kara matseta a jikinsa wanda tuna hakan da ta yi sai da ta ji wani irin yarrrrt a jikinta na ba gaira babu sabar
Du tunanin nan da take, sam bata san har Zahrau ta janye kanta tana kallonta ba
Kwalar da ta cika mata ido ce ta samu damar zubowa a hankali saman fuskarta
Zama ta yi kusa da ita hakan ya ankarar da ita
Dumin da ta ji a fuskarta ta laluba cike da mamaki tana kallon lema lemar da ta lalubo
Zahrau ta harde hannayenta ta ce " zan fada maki gaskiya, kin taki sa'ar samun miji haka mai tsada bayan kina zaune a waje daya, a gaskiyar magana a irin wannan zamani koda kuwa da gasken baya son bak'ar fatar ba zan ga laifinsa ba, domin kuwa yanzu zamani ya zo da wani irin kida wanda ya saka mata hawa suka cenza salon takun kidan
Ba komai bane sai irin yanda yawancin maza suka fi son farar fata kan bak'a,
Zaki ji namiji ya furta shi fa farar ko maya ce, ko mahaukaciya ce yana so, koda bata da nasaba!, hakan ya bada gudunmuwa sosai wajen shafe shafen yan matan zamani, Najeeba, ke shaida ce irin yanda kawarki burinta ta taba magana da shi, sai kawai Allah ya malaka mata shi,
Wa'inda basu kaishi bama daraja sun samu ana wawarsu bale shi? Ki cire masa rawanin ki ajiye shi ba ko sisi na tabata jinnin Ammi da mai martaba zai kawatu a idannuwan da zasu furta: ko bashida ko sisi sunna so!"
Hannun Najeeba ta kamo ta rike a nata ta ce" zaki iya zama da shi?"
Najeeba ta kasa budar bakinta, du kuwa da irin yanda take son yin magana, sai ya mata nauyi na gaske
Zahrau ta ce" zaki amshi abinki cikin ruwan sanyi! Bakya son sa? Ai kin fahimci an wuce wajen so ko? Baya son ki? Zamu jaraba mu ganni......, matansa? Zasu yi yaki ne dominsa, kema kuma zaki yaki abinki .......kowa salonsa ya fishe shi"
Najeeba ta kifta idonta a sanyaye ta furta" bana son hada bawa da wata, ban taba tunanin kasancewata a gareshi ba, lalle Allah shi ke da byro da takardar bawansa"
"Hakkun, kuma a yi masa biyaya koda ba'a so a hakan za'a samu rabauta" Zahrau ta karasa fada
Da sauri Najeeba ta kamo hannunta tana kallonta, a sanyaye ta furta" ta ina zan fara? Ta ina zan iya wannan yakin? Aminiyata da kuma ZINARIA, wa ya fi so cikinsu? ta yaya zai dubi bak'ar fata bayan ga farare nan a gabansa?"
Zahrau ta yi yar daria tana jin sanyi a ranta, sannan a lokacin ta ga tsantsar yarintar NAJEEBA, wai ita nan ta yarda da kalamansa cewar ya tsani bak'ar fata? Sai ta tsinci kanta da kuma yin yar daria, tun a yau zata fara gwadawa, ita kanta ta fi so mijinta ya dawo da kansa su koma dan kawai ta maidawa Gimbiya maganar da ta yi cewar ya halarci auren nan dan zumuncin dake tsakaninsu na sarauta ba wai dan zai kara aure ba, bayan auren kuma ta furta mata lalle bakake kun fara kasuwa fa, aman ki koma mu gani.....tana son ya zo da kansa su koma sai ta tabatar cewa lalle bakaken sun yi kasuwa
A hankali ta ce" kan abinda kika fi kwarewa, ina so ki buga wasan da kike bugawa a kan kowa, idanma yana tunanin karantarki ya yi ya san ko wacece ke to zamu yi anfani da sannin nasa mu gwada masa bai san komai ba!
Najeeba kallonta dai take,
Zahrau ta mike tsaye tana mai kokarin kwontar da ita ta ce" abinda nake son ki kula wanda da alama idan kina tare da shi yake bale kansa shi ne *Harshen ki*, ki kiyaye furucinki, ki tsadanta muryarki da kalamanki
Kallon yayar tata take cike da wata kaunarta, tabas ita kanta da ta irga irin abubuwan da ta ringa furtawa sai ta ji wani iri, kamar wata wace aka kunna?
Abin rufa ta ja ta rufa mata har wajen wuyanta kafin ta yi murmushin tsokanarta ta ce" zaki iya jure kwana shida baki je turaka ba?"
Ido Najeeba ta zaro a dan rikice ta ce" Aunty fa"
Zahrau ta yi daria ta ce" yeah, zan rikita iyayenmu, da yan uwanmu dan fara gannin zargin da nake yi idan har gaskiya ne? Ko kuwa hasashena ne
Najeeba kam bata iya cewa komai ba sai rakata da kallo da ta yi kafin ta maido dubanta waje guda, wani irin dukan jikinta ke kwasa du idan ta hango shi a kasan idannuwanta, gaba daya jikinta sai ta ji wani irin yar yar yar take iya bude idannuwanta da sauri
.......................
SULTAN
Yana cikin aiki da computersa bayan ya gama da taron mutanen da ya gama da rigimarsu yan kasuwa ne sannanu da suka kawo karar junna kan a masu tsakani da junnansu bayan sun kasance makota ne sosai, wannan shara'a sai da ta saka aka kirawo manya manyan malaman da suka zo suka ringa kawo manyan ayoyi bisa hakan, dayan ne ya kasance mai neman fitina ko rufe ido ne? Sun hada makotaka da junna, layi daya aman sana'a ta zamo tak tak iri daya, kuma abin kamar da gangan yake yi domin baya tashi siyan abu sai ya ga dayan ya siyo ya zuba shima sai ya kawo da yawa ya zuba sannan da neman fitina ya rege kudinsa sosai ta yanda zai kwacewa wancen mutanensa sai daidaiku, yana yi masa haka sosai da sosai har asara yake saka sho tafkawa wanda karshe ya gane da wata a kasa, domin shima ba wani uban kudi yake sakawa kayansa ba, yar ribar da zai bi shi sai ya ki dorawa ya bada kayan a yanda ya sara, hakan ya matukar saka masa tashin hankali duba da shi din yanzu ya fara tashi yana ta kokari ne dan ya ciyar da iyalansa ya fi karfin yan matsalolin rayuwa, shi kuwa dayan shagonsa cike yake makil sannan zai kai ukun na dayan kuma sana'arsa wace aka fi saninsa fa ita saifa kayan abinci ne, aman tsabar neman fitina a yanzu ba abinda baya saidawa domin daga makocin nasa ya saro wani abin shima sai ya saro ya kima karya, sam baya so ya ga yana samun na rufin asiri shi kuwa abin ya kaishi bango ya maka shi a gidan sarki
Lamarin ya so ya ja daga sosai sakamakon mutumen da aka baiwa damar magana ya nuna Niger din shin ba kasa ce ta republic ba?, yana da yancin yin sana'ar da yake so da zarra ba satar kudin ya yi ba, ya dora da fadin ya san yancin kansa ba zai kawo shi kara kan wannan ba
Wannan lamari ya saka sai da ya yi kira ga manyan malaman fada da na garin baki daya, suka amsa kira kafin a fara gabatar masa da nasiha mai ratsa jiki, da manyan hujoji da ayoyin da suka zo da maganar haka, kafin ya samu ya gabatar da shara'ar
Hakan ya saka kansa ya dauki zafi sosai ga harkar kasuwancinsa da yake son zama ya hada kan irin abubuwan dake shigowa da irin abubuwan da aka fi muradi wa'inda yaronsa baba zai je shaina da kansa ya yi oder su
A hankali ya mika hannunsa ya dauki cofin glass mai dauke da jus din ananas ya kai bakinsa ya dan sha kadan kafin ya ajiye ya ci gaba da dane danensa
Yar karamar wayarsa wace yawanci ahalinsa ke nemansa ta layin ce ta dan motsa alamar vibration
Dauka ya yi ya duba
Sakon Zinaria ne, rabonsa da ita yau zai kai kwana hudu, sako ne tana son zuwa bangarensa idan ya gama hutawa
Amsa ya tura mata da ok kawai kafin ya ci gaba da aikinsa
Yana nan zaune a falon nasa kamar da minti talatin, har ya gama dane danen ya rufe ya daga kansa sama ya lumshe idannuwansa ya tsinkayo tafia daga corridor din dake kawota bangarensa
Bai daga kansa ba, har ta shigo ta karaso dan kusa da shi kadan
Kamar yanda ta saba ta zube kasa kanta a kasa ta jimke hannunta guda ta sanyaya muryarta ta budi bakinta ta fara magana kamar haka"
......................
[31/03 à 21:56] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻