Showing 69001 words to 72000 words out of 228147 words

Chapter 24 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10372

san abin mai a jiki irin maikon kilishin kadan sannan ashe abin ice cream din har a rigarsa

Mikewa ya yi ya nufi motarsa
Hannunsa ya mika ya janyo abin goge baki da goran ruwa ya matsa gefe ya ringa goge du inda ya san zai samu abin

Sai da ya gama gogewa tas tas sannan ya mika hannunsa ya amshi kayansa da amintacensa ke miko masa ya koma gefe ya shiga kimtsawa

Yana gyara rawanin kansa ya kuma girgiza kansa a ransa yana ayanna" ita ga salihar mace mai tarbiya? Lale da bakone ni a rayuwarki da hakan ya birge ni, sai dai Zan iya rubuta labarinki a tafin hannunki harda wanda ke baki sani ba! NAJEEBA zaki zamo aya a garina, a kanki zan yi maganin kananun yan tsageran garina!

Ya kasance a wannan dare cikin nishadi da dan sanyi a zuciyarsa wanda ya jima bai ji ba a kala tun rasuwar yaronsa

Tabas wasa da Nusaiba da ya yi ya saka shi jin sanyi a zuciyarsa dan yarinyar sosai ta rukunkumeshi sai da ta saka shi yi mata murmushi mai sauti sannan ya bita da cakulkuli duda sakaryar yayarta ta rabata da shi dan iyayi nata

Adu'a ya yiwa kansa da sauran musulmai baki daya na Allah ya basu masu albarka baki daya

Sai a lokacin ya tuna da cikin jikin Zinaria, cikin na nan ko ta barar da shi? Duda da irin zubde zubden jinnin da ta ringa yi shi kuwa rabonsa da ita an jima, bai san me ke dauke hankalin yarinyar nan ba kamar itace sarkin ba shi ba,
Uzuririkanta sun yi mata yawa, uzururikanta kamar wace keda nauyin talakawa a kanta? Har ya zama uzururikanta sun fi shi mahainmanci
Shi kennan haka zai yi ta rayuwa ne? Sunna kusa da macen da suka fi nisa da junna
Sunna karkashin innuwa daya aman tafiarsu nada tsayi
Bai san me yasa ta dauki wasu lamura da zafi ba
Ya dace ya ringa samun kulawa ta miji da matarsa wace ta amsa sunnanta a cikon dakansa
Takan saka shi jin nauyinta idan tana masa kirarin nan
Wani sa'in har sai ya dubeta da sauri da mamakin shin mata ya aura ko baiwa?
Sam mace bata da lamari irin na tafiar da soyaya yanda ya dace?
Shi dai ba mai kallon film ko sauraron labarun soyaya bane
Yana anfani ne da ilimin da ya karanta na islamiya
Kwarai adininsa ya koyar da yanda zaka gudanar da rayuwar aurenka koda kiwa kai din shugaba ne
Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wa salam , shugaba ne na duniya baki daya, aman irin yanda tsarin tsaftataciyar soyayarsa da matayensa ta kasance dole mutun ya yi sha'awar gudanar da irinta

Idannuwansa ya mayar ya lumshe yana jin wani takaici guda gefe guda dake yawan zo masa
Ko tunani take yanda na iya dane tarin rigingimun talakawana zan iya dane rigimar dake jikina? Ko ni din bana tare da sha'awa ne?

Gannin kamar tunanin ya sako shi gaba ya saka shi mikewa ya shiga nafila, zai fi kyau ya samu ladan nafilar tunda dayan ladan ba zai samu ba, ba zai fita ya je bangarenta ya lalabota ba, idan har ba'a nuna mata mahinmancinsa a islamiyarsu ko a gidansu ba ba damuwa, zai kuma kwatanta wani auren!


Dinkuna masu rai da lafia ke shigowa daga wajen telan Anmy na yaran baki daya
Sai dinkunnan da aka ware tela biyu aka kilace suke zuba aiki na gimbiya Zahrau

Aure har ya zama saura kwana daya tak wanda tun fitar nan ta su Najeeba Anmy bata kuma barinsu fita ba baki dayansu

Abincinsu su ke shiga kicin bisa jagorancinta su girka,
Hirarsu sunna dakanta daidai da masu yi mata hidima ta dakatar, su kuwa basu sako komai a ransu ba domin takan yi haka dama idan y'ayan nata suka zo yi mata yan kwanaki

Bakin da suka zo gidan a daren yau ne suka dan fara daukan hankulan mutane
Sai dai ba wanda ya kawo wannan lamari a ransa

Wayewar garin safiyar juma'a, tun da sasafe ana ta karatu da sadaka a baban masalacin juma'a na gidan sarki
Sosai ake kara gyare gyaren masalacin da zagayensa an saka turaren wuta mai wani irin dadin kamshi ya zagaye ko'ina har cikin anguwanin kusa da gidan sarki

Lokacin sallar juma'a na yi wajen ya gama daukan musulmai

Ko'ina ka duba sune cikin shiga mai tsafta tarin musulman garin damagaram ne sun fito ba yara ba manya ba tsofafi, kowa ya fito cikin tsafta da turare a jikinsa ya zo da karfin gwuiwarsa da tarin son kasancewarsa a wannan waje mai albarka wajen da zai gabatar da sallar juma'a

Dawakai biyu dake tafe da ado irin na sarakuna ya shaida cewa yau zunna da baki bayan sarkin garinsu harda wani sarkin

Sosai aka ringa bada hanya ana miko gaisuwa har suka idasa shiga ciki sannan fogaren dake kakare da dawakansu suka rike dawakan aka rurufe saukarsu

Sallah aka gabatar cike da nutsuwa, kafin a ja doguwar Adu'a sai kuma sanarwar a dakata za'a daura auren SARKIN GARIN AGADEZ

Da yake akan yi daure dauren aure wasu har sun fara tashi sai dai jin daurin auren ya saka su komawa suka zauna

Abih ya saki murmushi a lokacin da yake bayar da auren Zahrau, sai kuma wata nutsuwa da farin ciki ya shiga cikin zuciyarsa a lokacin da ya amshi sadakinta a hannayensa

Daurin aure ya tafi cikin tsarin islama, ya amshi adu'o'in manyan malamai

Lasifikar dake ajiye ce ke sanarwar daurin auren da ya saka zuciyoyi da dama neman tarwatsewa

Daga kwoncen da dake a saman doguwar kujerar falonta daga kasa bayi ne ke yi mata hidima wasu na yi mata tausa wasu na hada mata abin bukatarta ta wuntsilo ta fado daga saman kujerar sannan ta ruruko idannuwanta tana kara kasa kunnayenta dan jin abinda ke fitowa daga spiker masalacin gidan mijinta

Alhamdulilah, Alhamdulilah muryar liman ta furta a lokaci daya ya kuma maimaita kalmar" An daura auren SARKIN GARIN AGADEZ TARE DA GIMBIYA ZAHRAU BISA SADAKIN JAKA HAMSIN TARE DA DOKI MAI KWALIYAR ZINARI WANDA YA ZAMA HALALIYAR GIMBIYA ZAHRAU

wani irin ihu ta saki daga tsayen da take

Bata tsaya ta dauki alkyabarta ba ta juya da gudu ta nufi bangaren Anmy ta biyayiyar hanyarsu

Hanya ce dake boye, wace ba kowa ya san da ita ba aman a yau ta tashi tonata bata tsaya wata wata ba ta bude kofar ta fada falon Anky dake dauke da Anmy da zuga zugan yan matanta da suka fito a gimbiyoyi reras a jere abin ba'a cewa komai

Tana shiga hannayenta saman kanta ta furta" Anmy, me nake ji? An daura auren mahaifina da Zahrau wacece zahrau? A kan me sarki zai yarda a zo garin nan a yiwa mahaifiyata kishiya? Anmy kin san irin yanda Aya ta tsani maganar kishiya shine zai jaza min bakin jinni a wajen mahaifiyata? Walahi ba zai yiwu ba Anmy, Anmy wannan wani irin abu ne bai jima da tozartani ya min kishiya ya bara min abin fade a duniya baki daya ba shine yanzu zai jagoranci tozarcin uwata??

Baki dayansu idannuwansu a kanta suke
Shigar jikinta riga ce diguwa irin ta shan iskar nan domin bata da kauri ko kadan sai malalalen gashin kanta dake daure da dan ribom
Ga cikinta nan ya tasa sosai dan kamar ba cikin watani shida ba sosai ya fito dama alkyaba ke boye shi

Anmy ta cire kanta daga dubanta a hankali ta furta" subahanallah
Zulaihat, auren ne tozarci? Dama auren da mai martaba ya yi tozarci ne a wajenki ke a matsayinki na uwar gidansa? Sannan a yanzu kin ga halin da kike ciki kika fito a haka kina irin magangannun nan muryarki a sama sama tamkar ba ZINARIYAR Sarkin Danagaram ba? Dama haka kuke ko a yau ne abin ya sameki ?

Kallonta Najeeba ta yi ta kuma kalli Anmy ta ga Anmy ta kawar da dubanta wato ita kunyar kallonta take ji a haka ita kuwa ta tsaya kikam sai surfa tambayoyi take da sakin zance haka

Dubanta ne ta kai har wajen cikinta sannan ne ta ga shatin pant din dake cikin jikinta
Itama da sauri ta cire kanta tana kallon Zahrau,
Gani ta yi Zahra'un ta hade hannayenta ta rike da dan karfi
Bata hannata ba, bata kuma yi gigin rarashinta ba, dan bata so tun yanzu ya zamanto ta ringa shiga wani hali bayan bata ga komai ba

Juyawa ta yi ta shige ta bugo kofar da ya saka Anmy dago kanta da sauri ta kai dubanta wajen kofar

Idannuwanta ta lumshe, a hankali take tambayar kanta....shin itane Zulaihat ta bugawa kofa a yau? Lale idan kana raye ba abinda ba zaka gani ba
Yau itane aka bugowa kofa haka
Idannuwanta ta kara rintsewa tana mai taune lebenta na kasa
Aure? Abinda ta kwana da sannin cewa sai an mata shi ita dake auren sarki? Shine zata yi ikirarin an tozartata?
ZULAIHAT kar ki saka ni zarginki mana?
Zaihat kar ki saka zuciyata kin aminta da ke mana bayan hakan bai dace ba zato zunubi ne
Zulaihat a kan auren ne kike aikata haka?
Idannuwanta ta lumshe ta ji zuciyarta na furta mata" *MAI DAMAGARAM ZAI YI AURE, ZAI SAKE WANI AUREN KWANA KUSA KUWA ZULAHAT DOMIN NA IN DAI YARON YA GAJI MAHAIFINSA TO BA ZAI IYA ZAMA DA KWAYA DAYA TAK BA*



Gaba daya hargitsewa gidan ya yi da hayaniya da gude gude da murna domin sai da aka daura auren ne aka shiga shigowa da abubuwan yanka ana yin waje da su dan za'a yi sadaka ne da su

Ba'a jima ba gidan ya kwashi shiru sakamakon dogaren da suka fitar da kowa aka saki hanya aka kara gyara hanya

Cike da nutsuwa da kasauta suke takowa har suka idasa shiga bangaren Anmy

Tunda suka shigo gaba daya yan matan suka zube kasa kawunansu a kasa cike da girmamawa

Waje suka samu suka zazauna kafin suke amsa gaisuwar Anmy

Sai da wajen ya dan dauki shiru kafin cike da muryarsa mai nagarta ya buda bakinsa cikin nutsuwa ya koro adu'a
Ya yi fatan alkhairi kafin ya dora da wata zazafar nasiha wace ta kare a aure bauta ne, zaman raya sunna ta je,
Ya karashe da kausasa muryarsa yana fadin" kar na ji, kar na ga abinda zai saka ni taka kasar garin agadez ba da sunnan zumunci ba ya Zahrau

Kanta dake kasa tana ta hawaye ta kara sadawa tana dan gyadawa

Anmy ta yi musmushi da dan guntun hawaye a gurbin idannuwanta

Najeeba ta kara rike hannunta dan zuwa lokacin hannunta daya a cikin na Najeeba dayan kuwa a cikin na Ummu

Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya furta" ANMY, zan kaita da kaina ne

Anmy ta gyada kanta ta sanyaya muryarta ta furta" zan so a je da yan uwanta su yi mata kwana biyu Allah ya ja da kwanakinka

Kai tsaye ya furta" zamu je da UMMULKHAIR da UMMUKULSUM

ANMY ta tsare shi da kallo da mamakin jin abinda ya fada, Abihma dake cen gefe yana amsa waya kasa kasa hankalinsa na kan yaren nasa, sai ya kebance da su sun zanta tare da yayansu, Dayabu kuwa yana zaune dan nesa da su shima a kasa ya tankwashe kafafuwansa

ANMY ta ce" ai su uku ne, akoy NAJEEBA

dubansa ya kara kaiwa wajen Anmy, da duba irin na kar ki min haka, kafin ya zafafa dubansa zuwa ga Najeeba wace tun da ya nuna banda ita ta dago da mamaki tana kallonsa itama cike da jin haushin kalamansa

Irin duban da yake mata na tsananin tsana da wanda ta masa wanda tsaf duba me mai hade da harara kafin ta sada kanta tsaf a idannuwan Anmy

Da mamaki ta kara dubansa ta kuma kalli Najeeba

Murmushi ne ya kubuce mata kafin itama ta maida kanta ta sada tana jin wani tunani na son ta yi shi yanzu yanzu

Muryar sakin Agadez cike da kamala ya furta" Allah ya ja da ran mai Damagaram, zan so a je da kanwata domin na tabata zata debewa Gimbiya kewa

Yana fada ne yana nuna Najeeba hakan kuwa sai ya baiwa kowa mamaki ciki harda ita kanta Najeebar

Yaya aka yi kike da farin jinni a wajen manyan mutane bayan ke din baki dace da samun hakan ba *MAGE?*
Ya ayanna a ransa kafin yake cire dubansa daga kanta ya maida wajen Abih dake dawowa yana dan murmushi, shifa yau wani fayau yake jinsa, yau wani farin ciki yake ji mai girman gaske, yau ya aurar da daya
Tun dazu yake samun kiran mahaifiyarta da kuma Mardiya wace ya ajiyeta gefe ya yi watsi da ita

Yana karasowa shima kansa ya sada a gabansu, domin koda kuwa yana uba a wajen SHAHEED sannan siriki a wajen sarkin Agadez to fa shi din yana kasa da su ne daga indalah, Allah ya umarceshi da ya yi masu biyaya a matsayinsu na shuwagabanin kasarsa



A hankali ya buda bakinsa yana kallon Abih ya ce"""""
[31/03 à 21:38] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



25




Cenxa harshensa ya yi zuwa harshen larabci, ya tausasa muryarsa ya kara sada kansa yana kallon yayan mahaifiyar tasa wanda ke zaune kusa da y'ayan nasa mata shima zuwa lokacin yannayin rashin son rabuwa da su ya bayana a tatare da shi

A hankali ya furta" Allah ya saka da alkhairi Abih, Allah ya biya da dukan bukatu na alkhairi ya kara girma ya kara rufa asiri
Yanda ka bani ragamar komai Allah ya fitar da ni da kai da kowa kunya a lamarin

Kuma dagowa ta yi da mamakin jin irin yanda larabcinsa ke son yi mata wahalar fahimta bayan larabcin yarenta ne, kasancewar larabci ya shiga cikin junna sai ya yi anfani da baban mai wahalar wanda shi Abih din shi ya koya masa shi ya yi magana, a ciki abu kalilan ne ta fahimta

Abih ya yi murmushi shima ya dauki yaren wanda ya tabata ko Anmy bata iya shi ba, shima kasancewar a saudiya ya yi karatu tun yana karami ya kasance yaren larabci kala biyu yake ji, da na wajen mahaifiyarsa da kuma wanda ya zame masa na makaranta ya bashi amsa kamar haka" nagartarka ta shaida kanta, bayan kasancewarka sarki sai kuma kyawawan halayenka suka sayan maka biyaya daga wajenmu iyayenka, Allah ya yi maka albarka, ya baka zuri'a dayiba

A kasan zuciyarsa ya amsa da amen amen amen

Kasa kasa ya yiwa Anmy bayanin ta inda zasu fito su shiga motar da zata sada su da aeroport nan da minti talatin

Mikewa suka yi suka fita ta hanyar da suka shigo

Anmy kuwa ta mike da sauri ta shiga hada hadar harhada mata dukan abubuwan bukata

A lokacin ne Abih ya samu damar kadaicewa da su baki daya

Kansa ya sada kafin ya dago yana dubansu
Sun yi masa wani irin kyau mai birgewa sannan sun yi masa girman da sai yau ya yarda y'ayan nasa masha Allah sun fa girma
Su dukansu sunna cikin wani danyen lesh ne, wanda ya tabata da kudinsa zai tambaya sai ya kalli Anmynsu a firgice hakan ya saka shi kin tambayar kudin domin abinda ya saka ya gansu da shi ya tabata ya kece kudin shada!
Tun daga yan kunnayensu kuwa har zuwa sarkar wuyansu zinari ne da abin hannayensu, ta zahrau ce kawai ta banbanta ta kasance baba sosai da wani irin kira mai ban tsoro domin ba karama bace a girma da tsayi da fadi da kuma kyan fasali

Alkyabobin dake jikinsu kadai abin kallo ne, ta Najeeba ce ta kasance shara shara mai shegen kyau

A hankali ya ce" ban san da wace kalma zan yi anfani dan nuna maku irin tsananin farin cikin da nake ciki gannin Allah ya fitarwa da daya cikin miji nagartace mai daraja a doron kasa a lokacin da na fara shiga rudanin anya irin rikon da na yiwa iyayenku Allah ba zai jarabceni ta fannin zamanku a gabana haka ba?, sai na ringa kai kukana wajensa ina fada masa cewar kar ya kunyatamin ku, kar ya jarabeku da laifukana, ya dora min jarabawar a kaina komai girmanta ya sanyaya maku domin ku din baku ji ba baku gani ba hasalima halayana sun kasance masu saka ku fita a hayacinku lokuta da dama

Murmushi ya saki ya dora da fadin" ina fatan yanda na ga naki, na ga na sauran har zuwa kan Nusaiba
Ina adu'ar gidan aurenki ya kasance gidan da idan kin shiga in sha Allahu ba za'a fitar da ke ba har sai dai idan gawarki ce zata fito

Da sauri Ummulkhair ta kalle shi da mamakinsa, sai kuma ta mayar da kanta ta sada
Murmushi hakan ya bashi har ya kasance ya furta" ummu, dole na so kaina, ban san haka iyayen matan da na ringa yankawa tikiten zawarci suke ringa ji ba sai da na ji an shafa fatiyar daurin auren y'ata, sai abu biyu suka diro min lokaci daya tarin girmamen farin ciki da matsanancin faduwar gaban idanfa aka maido min ita? Sai na samu kaina da kebancewa na kai sujada na godewa Allah sannan na roke shi aa, ni kam kar na ga haka a ahalina
Ya kara tausasa muryarsa ya ci gaba da fadin" Zahrau, kina da saukin hali da biyaya, ki kara jajircewa dan gannin kin kai ga ci a gidan mijinki, ki rike adininki, kar ki yi wasa da ibadarki in sha Allahu komai zai zo da sauki
Kar ki yarda ki yi sake da su azkhar dinki duda na san dama ba mai wasan bace aman ki kara a kan na da, ke kin san rayuwar gidan sarauta daban take da rayuwar da ba ta gidan sarauta ba, yau ko dan zaki kebance a wajen da ba yan uwanki ba ni ba anmy dinku dole abin ya zo maki da wahala
Aman idan kika kwontar da hankalinki haka ne aure ya gaji haka ba inda baya kai mutun

Kanta ta ringa gyadawa kafin ya miko masu hannayensa

Baki daya suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login