Showing 9001 words to 12000 words out of 228147 words

Chapter 4 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10401

da nan suka shiga zanen idan ya kama su ya kashe su sun yi, yayansu kuwa ya rafka tagumi yana kallon dan karamin kanensu wanda su biyu ne kawai maza sauran su goma sha biyar baki dayansu mata ne kuma ko daya ba'a yiwa aure ba tukunnan

Ajiyar zuciya kawai ya kuma saukewa ya janyo pizzar ya shiga bubudewa yana raba du gida guda a biyu yana mikawa yaran kannanu
Sai da ya yi sauran manyan ya basu guda guda har NAJEEBAR sannan suka shiga ci sunna dan taba hirarsu

Sai da suka gama yar karamarsu mai sunna lalla wace bata kai shekara shida ba ta je ta langwabe a jikinsa tana hamma, a hankali ta ce" yaya Dayabu, ina Abihna?

Gashin kanta dake dadaure da tsakiya masu shegen kyau wanda NAJEEBA ta mata kitso kananu sosai ta jera mata su ya ringa shafawa a hankali bai bata amsa ba

Kamar minti biyar har ta yi baci hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya kalli ZAHRAU wace ke bi masa ya rage murya ya ce" Zahra yau a dakinki zata kwana dan Allah dan ki kular min da ita, kin ga Abih fa fushi yake da mu baki daya yau ko ita bai nema ba

Kanta ta gyada ta mike da wayarta dake ringin saurayinta ne wanda aka saka masu rana ta duka ta dauke kanwar nata ta nufi dakinta da ita

Tana kaita ta shinfideta ta hade kitson cen sama ta daure shi dan kar ya dameta wajen baci
Ta yi mata adu'ar neman tsari kafin ta tsareta da ido a cikin ranta kuwa fadi take" inama Abih zai maido mahaifiyarki ke, ki tashi da jin dumin uminki a cikin jikin ki, ki rayu irin na kowata yarinya mai shekaru kananu irin naki?
A hankali ta ja abin rufa ta rufe mata daidai kirjinta ta duka ta mana mata kiss a goshinta ta kuma ayanna" ya Allah, kar ka jarabemu da aure aure, wato ka sa dukanmu idan mukai aure ya zama mijinmu shine wanda zai birne mu, Allah kar ka kama mu da halayan mahaifinmu na yawan auri saki, ka sa mu zauna komai rintsi mu rayu da y'ayanmu

Jikinta sanyaye itama sanye da kayan bacinta dogon wando sakake sosai da riga budadiya sosai ta fada saman bed din ta kara rungume kanwar nata kafin ta amsa kiran saurayin nata dake ta maido kiran

Yana nan zaune sai da kowace ta shiga dakinta domin dare ya tsala sosai har sha biyu kafin ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya fita ya ja kofar bangarensu ya nufi nasu shi da kanninsa

Tana shiga dakinta ta cire rigar jikinta

Shafafen cikinta da ta gama cin pizza aman sam bai tasa ba ta kala tana shafawa ta ce" Alhamdulilah na koshi

Mika ta yi ta shige bayi
Wani wankan ta sake daurowa da alwallah sannan ta kuskure bakinta

Tana fitowa eigar sallarta ta saka ta yi shafa'i da wutiri ta yi adu'a ta shafa

Cire kayan ta yi ya rage mata daga ita sai pant, ta dauko bras kadai ta saka domin a rayuwarta sam bata iya baci da kaya masu nauyi, ta fefeshe jikinta da turare ta shafa humura

Madarar da ta kwaba da tumatur din danye ta shashafa a fuskarta kafin ta haye saman lafiyayan bed dinta mai sasaukan shinfida

Sama take kallo kanta saman matashin kan dake ajiye dan kar ta goge abin domin bai bushe ba
Gefe daya kuwa wayarta ne ta shiga shating da tarin samarinta wa'inda ita kanta ba zata iya irgasu ba

Dakinsa daya da kanninsa dan sam bai raba daki da shi ba, gadonsu ne dai daban daban

Sai da ya shinfide shi domin ya yi baci

Sannan shima ya shiga bayi ya yi dukan uzurinsa ya fito
Baki daya yayan MUTALAB sunna da wata irin tsafta da kuma rikon adini, shima sai da ya yi raka'a biyu domin ya yi nafilarsa kafin ya kishingida da wayarsa a hannunsa

Message ya tura kamar haka" Allah ya huci zuciyar kanina


Har ya cire rai da zai bashi amsa domin lokacin karfe kusan daya na dare ne, sai dai cen ya ga amsarsa kamar haka" wata biyu ne ka bani DAYABU

Murmushi ya yi dan ya san dama baya so ya kire shi da kanninsa,

Wani message din ya dora kamar haka" na san ba zaka kulaceni da yawa ba idan ka yi duba baki daya kanena tamkar y'ayan cikina na dauke su, ina kokarin basu kariya da dukan karfina....ka gafarce mu

Nanma ya jima sosai kafin ya bashi amsar cewa" Allah ya shirye mu

Da sauri DAYABU ya dora" amen ya Allah
Sai kuma a kasa ya dora" ka yafe mata, yarinta ce, na mata fada ba zata kuma kai hannunta jikin Zinaria ba

Ya buda message din, ya karanta sarai, aman sai ya ki bashi amsa
Hakan ya sa hankalin DAYABU ya kasa kwonciya, yana rike da wayar a hannunsa ya kasa samun baci, yana tsoron yaki yafe mata ya rama ta wani wajen, yana matukar tsoron shirun Sarkin nasu wanda ake kasa gane inda ya dosa

Shi kuwa sarki dama ba sauka yake ba domin sam baya kashe data , wayar ya ajiye gefen abin bed ya koma a hankali ya kwontar da kansa ya lumshe idannuwansa yana tunnani

Murmushi ya yi yana girgiza kai da takaicin yarinyar cinkushe a kasan zuciyarsa
Kwarai ya ga karfin halinta, ya kuma yarda cewa bata da kunya
Ya kara yarda da shawarar da ya yiwa kansa cewa sai ya koya mata hankali a duniyarta

Zinaria dake falo yana jiyo shashekar kukanta, domin yana zuwa zai kwonta ta zo ta tsaya tana kukan a gabansa aka mareta aman ya kasa datse hannun wanda ya maretan?
Hannunsa kawai ya daga mata ya yi mata nuni da ta tafi, domin sam baya iya hakurin jiyo koke koken nan

Wani murmushin ya yi a kasan zuciyarsa ya ayanna" bayan batawa zuri.armu sunna da take faman yi a cikin garina, yana jaza mani zagi dan kawai mahaifiyata na kanwar mahaifinta ana kiranta da kanwata na zuba mata ido tana tabara, irin yanda wasu ke tunanin samun dagin kafa dan sunna soyaya ko watsewa da ita, shine yau zata nuna gwarjinina baya kaiwa gareta? Shine yau zata nunan ita jinnin shuwa arab ce ta hanyar daga hannunta ta mari matana a gabana?

Kansa aya girgiza yaumshe idannuwansa yana tunanin tafiar da zai yi ya kai yaronsa waje, Aliyu bashi da lafia yana fama da rashin lafia mai tsanani mai tashi lokaci zuwa lokaci
Yaron kan fita a hayacinsa ya mimike ya ringa wani irin zabura wani sa'in harma ya sume
Yaron na fama sosai yana jin jiki wanda hakan ke matukar dagwa mahaifin nasa hankali da kuma mahaifiyarsa wace ta dora dukan so da isarta a kansa cewa yarima ne mai jiran gado.....................

DAYABU kam sai da ya gaji da zaman jiran amsa ya fara gyangyadi ya ajiye wayar bayan ya kasheta ya kwonta a hannunsa na dama da tunanin da izinin Allah gobe daga wajen aiki zai koma cikin baban gidan ya same shi ya bashi hakuri

Tun da asuba kiran sallar fari mahaifinsu ya ringa bi daki daki yana dokawa da karfin gaske
Baya tsayawa su bude yake yin gaba domin yana cikin fushi da su, da da ne sai ya shiga ya ga tashinsu sun dauro alwallah yake barin wajen

Haka kowace ta dauro alwallah suka fito falonsu suka tayar da sallah

Bayan sun gama sun yi adu'o'insu du suka mike suka yi bangaren mahaifinsu zuwa lokacin har karfe bakwai ta yi

Du zama suka yi kamar yanda suka tarar da yayansu kansa sade

A hankali suka shiga gaishe shi, sai dai sam baya amsa masu yana ta danna carbinsa ya kure waje daya da ido

DAYABU ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" ABIH fushi zaka yi ta yi da mu ne? Ba zaka yafe mana ba bayan ka san bamu da inda zamu nufa mu ji sanyi?

Da haushi haushi ya dago ya kale shi ya ce" makaryaci! Makaryaci kawai, karya ne , ni zan matse maku waje ku kai karana a saka min laya? Ba ruwana da ku ba ruwana ku je ku tafiarku

Yar karamar cikinsu ce ta mike da dan karamin hijab dinta cikus cikus tana takawa ta je jikin mahaifin nata ta dora kanta a jikinsa ta yi luff tana sauke ajiyar zuciya

Shima hannunsa ya sa a hankali yana dan talabeta sannan yana bin y'ayan nasa da harara wa'inda suka sasada kawunansu kowane bai ce komai ba

Cen matarsa ta shigo ta dauki kwaliyar safe hannunta dauke da wani irin plat mai yannayin kifi marar nauyi mai kyan gaske da natsakaicin girma

Cikinsa gasashen kifi ne da soyayan dankalin turawa ta rufe shi da farar leda irin yanda ake nadewar nan

Cike da kissa ta duka ta ajiye gaban Abih
Ta koma wajen frij ta dauko ruwa ta dawo ta kuma ajiye masa tana ta takama irin ga matar ubansun nan ta zauna tana kokarin bude masa

Da kallo du suke binta ciki kuwa harda shi da kallon mamaki yake binta
Tsarin gidansa a irin wannan lokacin da y'ayansa ke zuwa gaishe shi a lokacin ake gabatar da kayan karin kumalon da ma'aikatan gidan ke girkawa tun da asuba
Nan suke haduwa su karya kafin du su watse kowane ya je ya shiga shirin tafia wajen aikinsa ko karatunsa

A hankali ya ce" ama yaya haka na ga iya wannan?

Sai da ta juya idannuwanta masu girma da kyau sannan ta ce" iya shi na basu umarnin dafawa

Da wani mamakin ya ce" aman ina abincin *Y'AYANA?*

Itama da wani irin mamaki ta kale shi kafin ta budi bakinta ta ce" y'ayanka fa Habiby? Y'ayan naka da suka kaika suka baka laya a gaban jama.a suka tozarta ka suka wulakanta ka? Y'ayan naka da basa tsoronka basa yi mani biyaya a matsayina na matar ubansu wato uwarsu? Na gaji da wahalar zuwa kicin ina ta faman fadin kowane irin abinda yake kari da shi, na gaji da jido masu kayan kari na kawo masu tun daga kicin su karya kulun, na gaji da rashin kunyar y'ayanka Habiby!


Da mamaki yake kallonta, ransa ne ya shiga tsale yana kunna, y'ayansa ne ta yi tsaye tana wulakantawa dan kawai an samu wannan yar matsalar? Ba ita zata dafa ba, ba kuma ita zata kawo din ba domin daga bakin bangarensa suke kawo mata ita sai ta idaso da shi ciki dan ba yar aikin dake shiga bangarensa
A hankali ya rintse idannuwansa yana kokarin control din haushin da ya kama zuciyarsa domin so yake ya nunawa y'ayan nasa fushinsa a fili dan ko gaba su kiyaye irin abin tozarcin nan da suka yiwa kansu da kansu wanda idan duniya ta ji su za'a zaga bale su matan da suka fi yawa harma suka kawo mizalin aure

Sai da ya samu ya sauke ajiyar zuciya ya kai sau hudu kafin a hankali ya budi bakinsa ya ce"






πŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ₯ΊπŸ₯Ί
[31/03 Γ  21:33] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


5




A hankali ya ce" Mardiya, aman ai y'ayanki ne ina kike so su je su ciyo abinci?

Gannin kamar ta samu dama ya sakata kara juyar da kai gefe ta ce" su je waje mana

Murmushin karfin hali ya yi yana gannin yanda idannuwan NAJEEBA tamkar zasu fado kasa yanda take zaro su tana son gaskata shin Abih dinsa ba zai wanketa sa mari ba? Wai mamansu kan uba yarinyar fa sa'arsu ce, kuma wai abincin me zata hana masu yau kuma?

Murmushi Abih ya yi a hankali ya ce" tashi ki je ki saka a dafa ma y'ayanki abinci Mardiya

Dubansa take, sai dai sam bata gano abinda yake dannewa ba, hakan ua sakata fadin" ai suma sun girma su je waje su ci

Da sauri ya ce" to dauke wannan din, nima yau tunda amaryana zata min rowar abincin ai sai mu hakura mu duka

Wani malulun bakin ciki da mamakin mahaifin nasu ne ya tsaya masu a zuciya

Zahra ce ta sada kanta tana jinjina lale sun bata ran mahaifin nasu da har yau ya nuna halin rashin damuwa a kansu , bayan sun san irin tarin kaunar da yake nuna masu wada dalilin hakan yawancin rabuwarsa da wasu matan nasa su ne sila

Yayansu kuwa kure Aban nasu ya yi da ido yana hango irin yanda yake danne bacin ransa

Bilkisu kamar ta ciji matar mahaifin nasu,

Najeeba a hankali ta kalli mahaifin nasu ta ce" ABIHNA

Wani hararan ya zabga mata kafin ya ce" NAJEEBA MUTALAB, meye?

Idannuwanta lumshe nan da nan suka cika da kwallah a hankali ta ce" kar ka hore mu da fushinka Abih, ba abinda muka yi

Da karfi ya ce" makaryaciya, marar kunyar banza kawai! Ke ba har marin matana kika yi ba??

Da gadara gadara Mardiya ta ce" marina ta yi sannan ta shaki wuyan aunty

Ummulkhair ta ce" ita ba zagin mahaifiyarta kika yi ba?

Ummu kulsum ta ce" zaginta kennan kulun sai tana zagin mana iyaye bayan mun san ciwonsu muna son abinmu

Da haushi Abih ya ce" ai dama na san su ke zuga ku shine zaku mi rashin da'a a nan?

Kai DAYABU ya girgiza ya kalli kannensa ya ce" ku tashi mu je waje mu siya

Du mikewa suka yi , wanda hakan ya saka zuciyarsa tsinkewa sai dai ya ki sakar masu yar karamar da DAYABU ya miko hannu ya bashi

A hankali DAYABU ya ce" saketa mu je na shiryata kar mu yi lati ka ga sai mun sayi abinci kafin mu tafi

Hannunsa ya bige ya ce" da kaniyarka y'arka ce? Na ki na sakin

Hannunsa ya janye yana dan yatsine fuskarsa ya ce" kanwata ce, kuma dole a bani abina domin ni tana gaba da dukan wata katuwa, kuma walahi idan y'a ta kuma cewa ita uwata ce wannan karon ba marin kanwata zata sha ba, zata dauki mari ne daga hannuna!

Yana gama fada ya juya ya shiga tura su du suka fito kowane ransa bace

A hankali ta kamo hannun DAYABU ta sanyaya muryarya ta ce" domin Allah meye laifina a cikin nan yaya?

Ido ya tsura mata da mamakinta, yanzu tambaya take meye laifinta bayan ta wankawa mace biyu mari a jiya matan dake da fada a ji a cikin garin baki daya?
A gaban sarki ta mari matarsa sannan ta tsinkawa matar mahaifinsu mari

Kansa kawai ya girgiza ya ja hannayensu
Sai da ya kaisu bangarensu ya ce" maza ku shirya bara na sa a kawo mana abin kari daga restaurant abusa maza ku shirya kowa ya karya a hanya


Sunna fita Abih ya mike ya ajiye yar saman kujera

Juyowa ya yi rai bace ya nunata da yatsarsa ya ce" ke, aman baki da hankali ko? Yaran a cikin gidan ubansu ki ce ba zaki basu abincin da ba ke ke na ba ba kuma ke ke girkawa ba? Look Mardiya, bana hada y'ayana da kowa , bana iya jure rashin mutunci a kan yarana bayan su kadai malaka duniya
Na rabu da ke ba wani abu bane , lale y'ayana basu kyauta ba aman ki sani ke suka baiwa laya ba ni ba, kuma ke kika tabo har haka ya faru da ke, da baki ringa wulakanci kina jifansu da kalamai kina zagar masu iyaye ba, da ba'a nuna sune masu iya asiri ke aa ba, da du haka bata faru ba


Da kakausar murya, ya jirgice mata tamkar ba shi ba ya ce"
Daga yanzu, daga rana mai kamar ta yau, ki kiyaye hannawa y'ayana abinci, ki kiyaye shiga hurumin da ba naki ba idan ba haka ba Mardiya gorin da kike masu cewa kin fi baki daya iyayensu jimawa da ni zai zo karshe
Walahi bana hada y'ayana da kowa!

.............................................

Kai kawon da yake ya fi a kirga, hankalinsa a matukar tashe, ransa sai suya yake yana kara gwada number da ta dora masa

Wayar ya wurga jikin bango yana dafe kansa

Yaronsa dake nemo masa mata ne ya yi gagawar zuwa ya dauko wayar yana kallon ogan nasa da tarin tambaya da kuma mamakin irin budurwar nan da ta dauki hankalin ogansa har haka

Da sauri ya ce" oga, ka yi hakuri ka kwatanta min kamaninta, ni kuwa zan bazama na samo maka ita koma yar waye na kawo maka ita ko na kawo maka numberta na gaskiya dan da dukan alamu ba numberta bane ta baka dan ana fadin number nan babuma ita wato ba'a dorata daidai ba

Sai da ya sauke huci ya dago kafcecen bakin hannunsa ya ce" isa, yarinyar idan ka ganta tama dauke da idannuwan mage
Ka san yaya idannuwan mage suke? Sunna da girma da wani irin lu.u lu.u a cikinsu wanda idan har ka shagala zaka iya zubar da salabe tsabar kyansu da dukan zuciyarsu
Bakinta madaidaici ne, lebenta na kasa ya dan fi na sama girma sannan lebenta yanda ka ga ruwan kasa haka yake yana sheki kamar wani diamonds
Fuskarta yar doguwa ce, mai dauke da gashin gira wadatace wanda yake gyare kamar na yar tsana
Hancinta dogo ne sosai sannan da dan fadinsa kadan
Gashinn idannuwanta dogaye ne sannan bakake ne sidik ga cika wa'inda suka karawa fuskar nata wani irin kyau da haske
Gashin kanta wanda ya leko sosai ta kasan dan kwalinta baki ne sidik yana wani irin kyalkyali
Wani kanshi da take shi ya kara fuzgata zuwa gareta
A zaune take a cikin mota ba zan iya fadin yannayin jikinta ba aman abinda na sani ta tara hips domin irin yanda cinyoyinta suka baje a cikin bakar doguwar rigar dake jikinta
Fatarta kalar bak'a ce, bakin nan mai hasken gaske, ta shafa mai mai dan maski wanda ya saka fatar nata yin wani mus mus tana kara fitar da sirrin kyanta

Da mamaki ya ce" oga bak'ar mace fa kace? Aman oga ina ce ka tsani bak'ar fata domin ka sha fadin kai ko haukacewa ka yi ba abinda zaka ci da bakar mace dan ba zaka iya kayan haushi ba

Murmushi yana girgiza kansa ya ce" to ka dauka na sheka maka karya a wancen karon, ka dauka du da nake fadin hakan ban hadu da ainahin mace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login