Showing 99001 words to 102000 words out of 228147 words

Chapter 34 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10419

a hannunta wai ita ta tafi sport? Wani sakarai ne baya son tab'a jikinta? Wani irin zaman aure ne zai yi da ita bayan yana da dar da irin kasancewarta mace marar kamun kai? Aure fa aka ce,
Idannuwansa ya kuma rintsewa yana jin wani irin haushinta a kasan zuciyarsa
Me ya sa kika gama iskancinki zaki kare a gidana?
Har kansa ya ringa sarawa a irin wannan tunani da ya yi.

Kwonciyarsa ya gyara yana mai lumshe idannuwansa da suka yi ja sannan sukai nauyi yana tunanin rayuwa
A yau bama zai je wajen gudu ba dan baya tunanin idan ya fita zai iya aiwatar da wani abu

Tabas Anmy na cikin farin ciki madaukakin farin ciki, hakama yayanta da kuma DAYABU
Sai dai basu cika nunawa ba domin zaune suke sunna kara tsara ta inda zasu hayo mata

Anmy kan ji har gabanta ya fadi idan ta tuna yanda za'a sha fama da ita

Farko, harkar saloon,
Biyu harkar fita
Uku auren kansa da wanda za'a d'aura mata bayan tana tsalen fad'in ai ita ga wanda take so *HUZAIFA*

Abih ya dubi agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa na hagu ya kalli Anmy ya ce" Bilkissu, wai karfe nawa take dawowa ne, na ga lokacin ace ta dawo ya yi gamu dare dare a zaune shiru

Anmy ta kalli agogo itama, mikewa ta yi tana fadin" k'warai, zuwa yanzu ya ci ace sun dawo duba da tun da na dora mata dokar lokaci bata taba kaiwa lokacin bama take dawowa dan wataran har sai ta rigayi Ummukulsum wace ke zuwa wajen lesson da Professor

Wayarta ta gwada kira shiru, hakan yasa ta nemi layin SHAHEED.

Ta jima tana ringin kafin ya d'aga.

Anmy a tausashe ta ce" ALLAH ya taimake ka baci ka yi?"

SULTAN dake zaune saman sallaya ya d'an girgiza kansa yana fitar da hucin zafin dake cikin zuciyarsa ya dan girgiza kai tamkar tana ganninsa sannan ya d'an furta" Ummu."

Anmy ta k'ara tausasa muryarta ta ce "Dama, so nake ka bani number amintacenka, zan yi kiransa ya yi kiran dogarin dake tare da Najeeba, shiru basu dawo ba."

Idannuwansa ya k'ara rintsewa a k'asan zuciyarsa yana fadin" yaya zata yi ta dawo yanzu? Sai ta gama bi kwararo kwararo tana siyen naman bakin titi ta je wajen da ta nasa k'wai ta zauna daga cen kuma idan ta raya mata ai sai ta nufi wani wajen? Yanzu Anmy wannan ce kika zaba min matar aurena?.

Du a k'asan zuciyarsa yake bayaninsa kafin ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya furta "Ina zuwa."

Kashewa ya yi ya mik'a hannu ya d'auko wayarsa mai d'auke da numbobin du wasu dogaran gidan.

Abin layo layo ne,
DOG NAJ ya kamo kafin ya danna kira.

Daga b'angaren da suke cikin tashin hankali kira ya shigo masa sam bai duba ba ya d'aga ya kai kunnnensa a lokacin kuwa d'an uwan nasa na fadin" Bayan nan ina zamu nufa nemanta? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une."

"Hello? Hello?" Ya ringa maimaitawa.

Shaheed kuwa na sauraron irin yanda dayan ke ta ambatar" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une." Hankali tashe yana fadin "Kuma wajen mai nama bata nan, mun je wajen mai ice cream bata cen, mun je stade bata cen, to wai ko dai tana cikin saloon d'in nata bamu duba da kyau bane."

Shima hankalin nasa a tashe ya ce" ba ka ga suturar da ta fita da ita bace a jikin yar aikin nata? Yaya aka yi ta fita bamu ganeta ba?"

D'ayan ya furta" baka gannin yau abin ya kasance da wani irin cinkoso gashi dare ya yi mutane wasu sai fitowa suke wasu na shiga ta yaya kake so mu ganeta bayan yau ko fitilar kofar saloon din ba'a kunna ba."

" *INA TA SHIGA?*" Ya fad'a a dake wanda sai a lokacin dogarin nan ya ciro wayar daga kunnensa da wani irin fad'uwar gaba ya lek'a sunnan da ya kira shi
" *GURNANIN ZAKI*."

Wayar ce ta sub'uce daga hannunsa yayi wani irin sama da hannayensa kafin ya furta "Mun mutu."

Wayar ya bi ya wawura dan kuma kaiwa kunnansa yana mai zubewa k'asa tamkar yana gaban Shaheed d'in hakama d'an uwansa na ganin wannan lamari yayi tunanin lalle wani babba ne a fadar yayi kira idan ba amintacen sarki ba to fa wani babba ne shi baima kawo cewar sarkin ne ba.

"A kashe , ya kashe, Attahir shikenan, dawama a cikin gidan kurkukun k'urya ya tabbata a garemu, GURNANIN ZAKI ne ya kira wayana da kansa kuma hankulanmu tashe ban duba ba na daga du ya ji abubuwan da muke fad'a."

Zuciyarsa ya dafe cikin tashin hankali yana jin cikinsa na murd'awa dan mad'aukakiyar tashin hankalin da ya hangowa kansu harma bakinsa ya kasa furta komai.

Mik'ewa yayi ya damk'i hannunsa yace " Tashi mu kuma bin waje wajen da ta saba zuwa, dan ina mai rantse maka ba zamu taba komawa fada ba tare da ita ba!"


Murmushi tayi da jus d'in dake ajiye saman lafiyayen table din da aka jera masu kayan k'walam da mak'ulashe.

Cikin wani irin shauk'inta yake , cikin dabara yake d'an k'ara kusanta kansa da ita yana mai kasheta da kallon soyaya.

Cike da farin cikin ganinta yace "Ban san a kan wani dalili yayanmu ya hana mu ganin junna ba, yace min zai waiwayeni har yanzu shiru, Najeeba ina jin tsoron kar a je ya hana min ke?"

Najeeba ta dan yi murmushi bata ce masa komai ba, hankalinta du yana kan agogonta so take ta mike aman kuma kar ya ga tana wulakantashi da yawa bayan uban nacin da ya ringa mata su hadu koda wani wajen ne bukatarsa ya ganta ya yi missing din kyakyawar fuskarta fiye da tunaninta hakan ya sa ta tsara fitarta yau du ta ringa yarda da yan kwaliya da masu gyaran jiki tun safe take cin wahalalen aiki wajen ya rikice sai shiga ake ana fita sannan ta ki kunna fitilar waje, sai da wajen ya zama sun daina duba wanda zai fita ko wada zata shiga tana hankalce da su kafin suka cenza sutura da AIDA ta fice fittt tamkar Aidar ce ta fita dan takan aiki Aidar siyo wani abin

"Lokacin komawarki ya yi ko?" Ya tambayeta cike da kulawa.

Najeeba ta sakar masa murmushi tace " Ka san doka ce, kayi hak'uri ina ji a jikina zai waiwayeka soon."

Murmushi yayi yana mai jin dad'i har abokansa ya gayyata su ganewa idanuwansa dan su yarda cewar shi d'in fa ba k'aramin k'waro bane, yau shine ya kawo NAJEEBA restaurant.

Mik'ewar da tayi da doguwar rigar AIDA jikinta du bata jin dad'in kasancewarta a cikin rigar mutane ya saka shi mik'ewa shima yana kallon table d'in yace "Baby baki ci komai ba fa?"

Najeeba ta d'an girgiza kanta da jus d'in hannunta tace "Ba ga Jus na sha ba? Ka san bana iya cin abu a gaban mutane haka bana jin dad'in ci."

Murmushi yayi ya d'auki wani croissant ya nufi bakinta da shi.

Sai kawai ta kula kamar an yawaita kallonsu ba mazan ba matan wanda bata san dalilin hakan ba ko dan bata saba zuwa irin wajen takanas ta zauna ta ci abinci bane? Takan zo Abusa restaurant aman ba dan ta zauna ba, daga cikin motarta ake mik'o mata dukan abinda ta buk'ata , aman yau ita Najeeba dan ta farantawa saurayi ta shigo d'are d'are ta zauna saman kujera, hakan ya hanna mata nutsuwa jinta take tamkar a saman k'aya du bata fahimtar abubuwan da yake fad'a.

Murmushi yayi, shi baban soyayya ya kai bakinsa ya gutsura ya tauna ya had'iye yace " Ko tsoro kike a je na saka wani abu a ciki?"

Najeeba tayi yak'e tana d'an zama gefe tana d'an waige waige a sanyaye tace "Huzaifa tafia zan yi dare fa ya yi."

Murmushi yayi yace "Dan Allah manta da wani dare yayi, babbar yarinya da ke za'a wani d'ora maki dokar dawowa gida da wuri sai kace wata yar daji?"

D'an tsai tayi tana kallonsa, a k'asan zuciyarta kuwa fad'i take lallai baka da wayo, ai wayewar tawa bata kai wajen da zan iya bijirewa Gimbiya ba, sai ta daki hak'oran banza a zauna k'alau.

Ambatar Gimbiya da tayi ya sakata jin gabanta ya fad'i, firgigita tayi ta shiga wawurar jakarta mai d'auke da wayarta.

Dubawa tayi dan ganin ina wayar? Sai dai cikin ikon Allah bata ciki, hankalinta ne ya tashi ta mik'e da sauri ta kama hanyar fita.

Shima mik'ewar yayi yana mik'awa abokinsa wayarta da ya zare, ya yiwa kansa alk'awarin zai je ya binciki wayarta du wani d'an iskan saurayinta dake mata magana ya d'ud'ura masa ashar da zumar itace sanan ya masa kashedin sake shiga hanyarta, zai shiga wajen hotunanta da vidos dinta ya tura wa'inda sukai masa kafin ya yarda wayar ya siya mata sabuwa _(HATARA dai yan matanmu, waya ta zama balaki, tashin hankali, fitinar dake hanna kwonciyar hankali a wannan zamani, wasu yan matan kan yarda su ringa d'aukan hotunan wasu sasa na jikinsu haka kawai suna bari a cikin wayarsu wasun kuwa samarinsu suke turawa, zaka ga budurwa ta yi hoto rabin nonowanta a fili harshe a waje tamkar wata karya da k'walelen kai a fili tana wani langwab'ewa ita ga kyakyawa ta ajiye a allon wayarta, shin k'anwata, yayata, y'ata idan wayarki ta fad'i a titi ya kasance wani mugu ya tsinceta ya je ya yi anfani da abubuwan dake ciki, ciki kuwa harda munanan hotunan nan naki ina zaki shiga da ranki? Wani saurayin ya zo gidanku ne dan ya lalata tarbiyar iyayenki ya yi tafiarsa, wani ya zo ne dan ya wulakanta ki ya kara gaba, ciki d'aid'aiku ne suka zo dan soyaya idan wayarki ta fad'a hannun wanda kike wulak'antawar nan ya je ya fitar da vidio d'inki kina wasu irin abubuwa ke ba yar bariki ba ke ba mahaukaciya ba yaya kike tunanin zai yi da su? Dan Allah mu rufawa kanmu asiri da lamarin nan, wallahi, wallahi idan wani abu bai tona mana asiri ba wayoyinmu zasu tona mana Allah ya kare mu baki d'aya)._ Bayanta ya biyo da sauri.

Kusan motarsa take tsaye tana son bud'ewa.

Ta bayanta ya zagayo ya rungumeta a jikinsa hakan ya saka gabanta ya yanke ya fad'i harma jikinta ya fara b'ari b'ari.

Da sauri ta ringa kiciniyar k'wacewa hakan yasa ya k'ara ruk'unk'umeta a jikinsa a sanyaye yana furta " Baby meye haka? Ki tsaya na ji d'umin jikinki a jikina, ba wani abu zamu yi da ke ba sai an mana aure aman irin yar rungumar nan ba zan samu ba? Ki duba fa ki ga irin yanda wasu ke tsotsar bakin junna wa'inda basuma kaimu wayewa ba aman ke sai ki ringa guduna?"

"Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une ..." Najeeba ta fad'a da k'arfin gaske kafin ta tura shi tayi baya baya ya gamu da jikin motar.

Da sauri ya saketa gannin zata tara masa mutane yana kallonta da mamaki.

Rasa me ma zata yi ta yi, yanzu Huzaifa ne ya ruk'unk'ume mata jiki haka ya d'ora mata kai a wuyanta Idannuwanta ta lumshe tana jin wata tsanarsa na mamaye gurbin birgetan da ya fara.

A sanyaye tace "Wai ko wani namijin ma d'an iska ne, ko dai nice mai sifar yan iskan da bana iya tarayya sai da d'an iska? Wai kowa haka yake soyaya ko matar da zaka aura sai ka nuna mata akuyanci?"

"HUZAIFA." Ta fad'a a sanyaye hawaye tuni ya fara wanke mata fuskarta tace "Dama dan ka d'ana jikina ka shigo jikina har ka saka na kamu da soyayarka?"

Huzaifa yayi gagawar girgiza kansa ya mik'o hannunsa dan tab'a nata aman sai ta kauce da sauri tana kallonsa, shi yama rikice sam bai d'auki haka a matsayin wata damuwa ba, a kan me zata wani damu daga yar runguma, yo yan matan yanzu meye ba'a yi da su? Aman ita daga yar runguma ta kama kuka haka me take nufi da shi?
A sanyaye yace "Najeeba, ba fa wani abu na maki ba, rungumeki na yi a jikina wanda yanzu hakan ba wani abu bane , Najeeba aurenki fa zan yi ko kin manta?"

Najeeba ta d'an lumshe idanuwanta tana d'an girgiza kanta a hankali tace "Da ace ina yarda da rungume rungumen nan da baka tardo ni a haka ba, Huzaifa da ace ban d'auki irin haka a bakin komai ba da ina ga cikin biyu an yi d'aya, ko duniya ta d'ad'a ni da k'asa ko kuwa ina wani wajen da kai baka isa ka hango ni ba, dan na rantse maka tun ina da shekara goma sha hud'u nake tara samari, Huzaifa da ace na biyewa samari mun ringa soyayar zamanin da kake fad'a da na tara y'aya da yawa a duniya, duniyar ta gama yayina ko na zama rik'ak'iyar yar barikin da ba dai k'ananun yara ba sai manya." Tana gama fad'a ta juya a hankali ta shiga tafia a k'afarta.

Huzaifa ya waiga ya ga abokansa biyu na lek'e hakan ya saka ya ji kamar ya k'urma ihu a wajen ( kai, ta zo maka da sauki baka sha mari ba?)
Me ya sa ta masa haka? Shi sam bai ga wani abinda yayi na laifi ba, koda yake zai je ya gama aiyukan da zai yi a wayarta sannan ya je saloon dinta gobe ya shiga koda da gudu ne ya bata hak'uri, zata sauko ne abinda ta fad'a da bakinta cewar ta kamu da son sa?.

Sam bai bi bayanta ba, itama hakan ya fi mata alkhairi tana tafe tana share hawaye ta bi ta gaban comisaria ta kama tudun poste a k'afarta tana tafe tana had'a hanya tamkar zata fad'i k'asa.

Ficewarsu biyu ta hanyar da take bi aman sun kasa ganeta, sai da suka dawo da wani irin gudu suka lura da budurwar dake tafe tana had'a layi kasancewar hanyar itane hanyarta ta bi kullum idan zata koma fada.

Wani irin birki suka ci a gabanta, da sauri d'ayan ya fito hankalinsa tashe ganninta tana ta hawaye gashi ba kayanta ne a jikinta ba.

Bata kula irin rikicewarsu ba ta bud'a baya ba gardama ta shiga ta kwontar da kanta jikin kujerar
*da ban je ba, da ban ga wulak'anci ba, da ban ba da hanya ba, da bai rungumi jikina ba, ni Najeeba, ni ba yar iska bace* wannan abubuwan take fad'awa kanta a cikin zuciyarta har suka k'araso fada.

Su sun fita shiga damuwa domin sun san cewa an san basa tare da ita gashi sun d'ora lokaci sosai a kan lokacin dawowarta.

Tun daga yannayin Amintace suka k'ara sarewa har suka gama parking da motar ta bale ta fita ta nufi b'angaren Anmy su kuwa sun kasa fitowa daga cikin motar domin tsaye yake hakimce hannayensa rungume a k'irjinsa da yanayi irin na zaku ci ubankun nan yana jiran su gama k'umbiya k'umbiya su fito su tarkata su yo b'angaren SULTAN.



*Masha Allah*
[31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



33


Tana shiga ta tarar da Anmy zaune tana rike da wayarta

DAYABU na tsaye da wayarsa shima yana dokawa haka Abih na zaune aman kansa a kasa

Tana shigowa Anmy ta fara ganninta hakan ya saka ta mike da sauri tana fadin" NAJEEBA, daga ina kike? Waye ya daga wayana yake ce min na shafa maki lafia na bar kiran ki? Ina wayarki take? Me ya same ki?

Dayabu ya juyi da sauri yana kallon yanda ta yi wani irin turus sannan kukan da take ga kuma irin yanda jikinta ke bari gabansa ne ya fadi hakan ya saka da wani irin sauri ya karaso ya kamo hannayenta ya yi ciki da ita

Sai da suka shige daki ya zaunar da ita har jikinsa na rawa ya ce" daga ina kike? Kukan me kike?

Anmy da ta biyo bayansu ji take kafafuwanta sai bati suke kamar zasu rabu da gangar jikinta dan tsoro da fargaba

A kidime ta karasa shigowa tana fadin" wani ya maki wani abu? Wani abu ya same ki?

Fashewa ta yi da kuka tana zumburo bakinta ta ce" Anmy, wayata ce ta bata

Ba anmy ba, shi kansa sai da ya ji ya sauke ajiyar zuciya duda ba wani yarda ya yi da maganarta ba

Abih ne ya shigo ya zauna bakin gadon yana kallonta

A sanyaye ya dubi Anmy ya ce" Bilkissu, mu je

Anmy sai da ta kamo hannun Najeeba ta rike tana kallonta a sanyaye ta ce" wannan shine alfarma ta fari da zan nema a wajenki nurul khalb

Najeeba ta kurawa fuskar Anmy ido aman ta kasa tambayar menene har suka fita

Sunna fita Anmy ta ringa sintiri ta kasa zama, dama sun yanke sai dai Dayabu ya tarbeta da maganar dan shi kawai zai iya fatatakarta kuma ta saurareshi


Cikin daki

Na san karya kike da maganar dan an sace wayarki kike kuka, ki fada min abinda ya saka ki kuka tun raina bai baci ba

DAYABU ya fada yana kuma mai jin tsoron abinda zata ce ya sakata yin kukan

Sai da ta rintse idannuwanta wasu hawayen suka kara zubowa daga gurbin idannuwanta, cike da jin kunyar abinda zata fada ta shiga kwatanta masa abinda ta aikata wanda ta tabata sai ya babala mata mari aman kuma da ta rike ita daya ta yi ta jin haushi gwara ta fada masa ya wanwanka mata mari ko zai huce

Da mamaki yake kallonta kafin ya girgiza kansa a sanyaye ya ce " Najeeba, kin san irin darajar da Allah ya yi maki har kike aikata halaya irin na wasu sakakun mata? Najeeba kin kuwa san irin daukakar da Allah ya maki har zaki je ki zubda kanki haka? Najeeba kin kuwa san irin matsayin da Allah ya maki har zaki yarda wani sakarai ya rungumi jikin ki? Yaya aka yi kika kasance mai saurin sakarwa maza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login